Tattalin Arziƙin Juriya
Tattalin Arziƙin Juriya wata kalma ce a fannin tattalin arziƙi wadda ke da alaƙa kai tsaye da tattalin arziƙin Musulunci. Bisa wannan ra'ayi, ana iya sarrafa matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta a lokacin rikice-rikice, sannan a wani ɓangaren kuma zai haifar da sakamako mai kyau ga tattalin arzikin ƙasa; kamar ƙarfafa ƙirƙirar ayyukan yi, kawo sauyi da ci gaban tattalin arziki, da kuma haɓɓaka jarin zamantakewa wanda da turanci ake kiransa (Social capital)
An fara gabatar da wannan tunani ne karo na farko ta hannun Abbas Ma'arif, masanin falsafa kuma mai tsara ra'ayoyi ɗan Iran (Rasuwa:2002M), a shekarar 1997M. Amma daga baya, saboda jaddadawar Sayyid Ali Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tun daga shekarar 2010M, an fara ɗaukar wannan tunani a matsayin wata hanya ta ƙarfafa tattalin arziƙi domin kawar da tasirin takunkumin tattalin arziƙi da ƙasashen waje suka daƙarawa Iran. Game da wannan ra'ayi na tattalin arziki, an rubuta littattafai da bincike da dama.
Muhimmanci Da Matsayi
Daya daga cikin ayyukan tattalin arzikin juriya shi ne magance matsalolin gaggawa (economic shocks) da ka iya afkawa tattalin arziki. Sassaucin tsarin wannan ra'ayi yana sa tattalin arziƙi ya iya jurewa manyan matsalolin tattalin arziƙi, kuma a matsayin wani tsari na dogon lokaci zai iya sauya ginshiƙan tattalin arzikin ƙasa.[1] Saboda wasu ƙa'idojin tattalin arziƙi a Musulunci suna da daidaito da ra'ayin tattalin arzikin juriya, wasu masana suna ganin cewa tushen tattalin arziƙin Musulunci yana da alaƙa da wannan tsari. Daga cikin irin waɗannan ƙa'idoji akwai: ƙa'idar nafyus sabil (Hana kafirai rinjaye kan Musulmi), hana lalata tsarin zamantakewa, hana Israfi da Itraf da almubazzaranci da ɓarna wajen kashe kuɗi.[2]
Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran fara amfani da kalmar tattalin arzikin juriya a ranar 7 Satumba 2010M.[3] Gabanin haka, Abbas Ma'arif ya riga ya gabatar da wani shiri mai wannan suna ga gwamnatin Iran a 1997M.[4] Bayan jagoran Iran ya yi amfani da wannan kalma, ta ja hankalin jama'a da cibiyoyi da dama, wanda ya sa aka kafa cibiyoyi da shirye-shirye masu yawa a wannan fanni; kamar kafa makarantar koyar da tattalin arzikin juriya ta yanar gizo,[5] da kuma ƙungiyoyi masu bin diddigi da sa idanu kan aiwatar da manufofinta a hukumar shari'a.[6] Rubutu kan siyasoshi da adadin ayyuka a wannan fage suna cikin matakai da aka ɗauka.[7]
Daga cikin sakamakon da ake dangantawa da tattalin arzikin juriya akwai: rage rashin aikin yi, ƙaruwa da ingancin aikin ma'aikata, ƙaruwa da jarin zamantakewa (Social capital) daidaituwar ci gaban tattalin arziki, da kuma bambancin hanyoyin samun kuɗin shiga daga fitar da kaya.[8] Kan asasin bincike d aka yi kan yadda aka sanar da manufofin tattalin arzikin juriya a Iran da kuma yadda aka aiwatar da su Daga shekarar 2010M da bayanta a cikin Iran, bisa la'akari da ya nuna cewa wasu alamomin tattalin arziƙi an ɗan samu ci gaba.kamar misalin bunƙasa tsarin kuɗi da bankuna, shigar jama'a cikin harkokintattalin arziki, bunƙasa kamfanonin ilimi-tushen da ƙarfafa tattalin arziƙi na cikin gida,[9] daga cikin babban dalilin dalilin samar da wannan tsari shi ne fuskantar takunkumin tattalin arziƙi da aka ƙaƙaba wa Iran, inda aka samu nasarori kamar dogaro da ƙarfin cikin gida da rage buƙatar waje.[10]
Ma'ana Da Misalai
An bayyana ma'anar tattalin arzikin juriya ta hanyoyi daban-daban. A mahangar da fahimtar Sayyid Ali Khamna'i, tattali arziƙi na gwagwarmaya shi ne tattalin arziƙin da, tare da tsayawa ƙyam kan yaƙar matsin lambar maƙiya, zai iya kawo ci gaba da bunƙasar ƙasa. Wato tattalin arziƙi da yake da ƙarfin juriya ta ciki, ta yadda sauye-sauyen duniya ba za su cutar da shi ba.[11] Cibiyar nazarin tattalin arƙikin Musulunci ta hauzar ilimi ta Ƙum ta bayyana tattalin arzikin juriya a matsayin: "tattalin arziƙi da ya samo asali daga al'adun juyin juya hali da na Musulunci, wanda ke ƙarfafa tattalin arziƙi a gaban barazanar tsarin mulkin duniya tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki."[12] Haka kuma, ana kiran jerin manufofida siyasoshin tattalin arziƙi da aka gina bisa tsarin gida, al'adu da ilimi a jamhuriyar Musulunci ta Iran da suna tattalin arzikin juriya.[13]
An gabatar tattalin arzikin juriya da fassara shi cikin adadin sasanni a cikin bayanan Sayyid Ali Khamna'i, daga cikin misalan tattalin arzikin juriya akwai: rage tsawon lokacin aiwatar da shirye-shirye na tattalin arziƙi, gujewa yanke shawara na gaggawa ba tare da tsari ba, samar da dokoki don rage dogaro da ƙasashen waje, mayar da hankali kan shirye-shirye na dogon lokaci, tallafa wa kamfanonin ilimi-tushen, da ƙara amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.[14]
Sayyid Ali Khamna'i, wanda ya kasance daga mutane da suka samar tunanin tattali arziƙi na gwagwarmaya, yana cewa: wannan tsarin tattalin arziki wani tsari ne na kimiyya da ya dace da Iran, wanda yake daga cikin tattalin arzikin da ke fitowa daga ƙarfin cikin gida, amma fa bai kasance tattalin arzikin da ya rufe kansa ga duniya ba; a a yana neman ci gaba da faɗaɗa.[15] Adil Paiƙami daga Jami'ar Imam Sadiƙ ya na da ra'ayin cewa tattali arziƙi na gwagwarmaya ba lallai ya zama tattalin arziƙi daga matsayi na rauni ko kariya kawai ba. Saboda haɗa tattalin arzikin ilimi-tushen a cikinsa, yana iya zama ma tattalin arziƙi mai tsarin kai farmaki wajen ci gaba.[16]
Bayanin kula
- ↑ Kawiyani wa Sayyid Shukri, Eqtesad-e Moqawamati, sh. 1.
- ↑ Kawiyani wa Sayyid Shukri, Eqtesad-e Moqawamati, sh. 8–9
- ↑ Yusufi, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, sh. 32.
- ↑ Ṭarḥ-e Marḥūm Abbas Maʿarif be Dowlat-e Khatami darbare-ye Eqteṣad-e Moqavemati, shafin labarai na Alif.
- ↑ Nokhostin Daneshgah-e Mardomi-ye Eqteṣad-e Moqavemati Rah-andazi Shod, kamfanin dillancin labarai na Daneshju.
- ↑ Bargozari-ye Nohomin Neshast-e Setad-e Markazi-ye Peygiri-ye Ejra-ye Siyasat-ha-ye Eqteṣad-e Moqavemati dar Quwwa-ye Qaḍa’iyya, kamfanin dillancin labarai na daliban jami'a.
- ↑ Barrasi-ye Gozaresh-e Ejra-ye Band-e Dovvom-e Siyasat-ha-ye Kolli-ye Eqteṣad-e Moqavemati dar Hey’at-e ʿali-ye Neẓarat-e Majma, kamfanin dillancin labarai na daliban jami'a.
- ↑ Kawiyani da Sayyid Shukri, "Iqtisade Muqawamati", shafi na 12–14.
- ↑ Shaqaqi Shahri, Arzyabi-ye Vaz'iyat-e Ejra-ye Eqtesad-e Mokawamati, sh. 79–82.
- ↑ Makiyan wa Zangi Abadi, Tahrim-ha wa Elzamat-e Eqtesad-e Moqawamati, sh. 41 da 55.
- ↑ Yusufi, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, sh. 32.
- ↑ Yusufi, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, sh. 33.
- ↑ Yusufi, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, sh. 33.
- ↑ Kawiyani wa Sayyid Shukri, Eqtesad-e Moqawamati, sh. 3–8
- ↑ Yusufi, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, sh. 33.
- ↑ Rahbord-e Kelan be Nam-e Eqteṣad-e Moqavemati; Bankin Musulunci
Nassoshi
- Kawiyani Zahra wa Khashayar Sayyid Shukri, Eqtesad-e Moqawamati, (Tattalin arziki juriya) a cibiyar bincike na Majalisar-e Shura ta Musulunci, lamaba 12546, 2012–2013 Miladiyya..
- Makiyan, Sayyid Nezamuddin wa Parvaneh Zangi Abadi, Tahrim-ha wa Elzamat-e Eqtesad-e Moqawamati, (Haramtawa da Wajibai na Tattalin Arzikin Juriya.), A cikin Mujallar-Taron Bita na Tattalin Arzikin Juriya, lamba ta 1, 2016–2017 Miladiyya.
- Yusufi, Ahmad Ali, Nezam-e Eqtesadi-ye Moqawamati, Qum, Mawallafar Negah-e Farsi, 1395 sh.
- طرح مرحوم عباس معارف به دولت خاتمی درباره اقتصاد مقاومتی, (Shirin marigayi Abbas Maaref da ya gabatar wa gwamnatin Mohammad Khatami game da tattalin arzikin juriya), Kamfanin Dillancin Labarai na Seda wa Sima – ranar wallafa: 20 Afirilu 2017, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya
- کتاب اقتصاد مقاوم و پایدار منتشر شد, (Tattalin Arziki Mai Juriya da Dorewa), Diyar Mirza – ranar wallafa: 2 Afirilu 2023, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023.
- درآمدی بر راهبردهای اقتصاد مقاومتی در بازار., (An fitar da littafin Gabatarwa kan Dabarun Tattalin Arzikin Juriya zuwa kasuwa), Kamfanin Dillancin Labarai na Dunya-ye Eqtesad – ranar wallafa: 15 Agusta 2016, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- راهبردی کلان به نام اقتصاد مقاومتی، ( Wata babbar dabara mai suna tattalin arzikin juriya), Bankin Musulunci– ranar wallafa: 9 Afirilu 2014, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023.
- برگزاری نهمین نشست ستاد مرکزی پیگیری اجرای سیاستهای اقتصاد مقاومتی در قوه قضاییه, (An gudanar da zama na tara na Kwamitin Tsakiya na bibiyar aiwatar da manufofin tattalin arzikin juriya a bangaren shari’a), Kamfanin Dillancin Labarai na Daneshju – ranar wallafa: 8 Fabrairu 2023, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- بررسی گزارش اجرای بند دوم سیاستهای کلی اقتصاد مقاومتی در هیئت عالی نظارت مجمع, (An duba rahoton aiwatar da sashe na biyu na manyan manufofin tattalin arzikin juriya a Majalisar Kula ta Babba ta Majma), Kamfanin Dillancin Labarai na Daneshju – ranar wallafa: 16 Nuwamba 2022, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- نخستین دانشگاه مردمی اقتصاد مقاومتی راهاندازی شد, (An kafa jami’ar jama’a ta farko ta tattalin arziki na gwagwarmaya), Kamfanin Dillancin Labarai na Daneshju – ranar wallafa: 24 Afirilu 2021, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- "خاکریز-اقدام-و-عمل-منتشر-شد "خاکریز اقدام و عمل" منتشر شد، (An wallafa littafin Katanga ta Aiki da Aiwatarwa), Kamfanin Dillancin Labarai na Seda wa Sima – ranar wallafa: 20 Afirilu 2017, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- راز پیشرفت و افول اقتصاد آمریکا در کتاب "اقتصاد مقاومتی در آمریکا, (Sirrin ci gaba da koma bayan tattalin arzikin Amurka a cikin littafin Tattalin Arzikin Juriya a Amurka), Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA – ranar wallafa: 21 Yuni 2020, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- کتاب درسنامه اقتصاد مقاومتی رونمایی میشود., (Za a ƙaddamar da littafin darasi mai taken Darussan Tattalin Arzikin Juriya), Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr – ranar wallafa: 2 Maris 2020, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya."
- کتاب سیاستهای اقتصاد مقاومتی در بیان رهبر انقلاب چاپ شد، (An buga littafin "Manufofin Tattalin Arzikin Juriya a bayanan Jagoran Juyin Juya Hali", wato Ali Khamenei), Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr – ranar wallafa: 2 Maris 2020, ranar dubawa: 14 Oktoba 2023 Miladiyya.
- Shaqaqi Shahri, Vahid, Arzyabi-ye Vaz'iyat-e Ejra-ye Eqtesad-e Moqawamati, (Kimanta Matsayin Aiwatar da Tattalin Arzikin Juriya.), A cikin mujallar kwata-kwata Eqtesad Pazhuhi, lamba 79, 2019–2020 Miladiyya