Jump to content

Daƙiƙa:Ayar Khairul Bariyya

Daga wikishia
Ayar Khairul Bariyya
bayanan aya
sunan ayaAyar Khairul Bariyya
akwai shi cikin suraBayyina
lambar aya7
bayanan abin da yake ciki
wurin saukaMadina
game daGirmamar matsayin Imam Ali (A.S) da Shi'a


Ayar khairul bariyya, (Larabci: سورة البينة) bayyina aya ta 7, tana daga cikin ayoyi da suka sauka game da sha'anin Imam Ali (A.S). kan asasin wata riwaya da ta zo a madogaran Shi'a da Ahlus-Sunna da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) ma'anar jumlar "Khairul bariyya" shi ne mafi alherin halittu, sune Imam Ali (A.S) da mabiyansa.

Ba'arin malaman tafsiri sun fitar da natija daga wannan aya da cewa mutanen da suka kasance daga muminai da salihai suna da fifiko hatta kan mala'iku, saboda kalmar "Albariyya" tana tattaro dukkanin halittu.

Aya Da Tarjama

Aya ta bakwai suratul Bayyina aya ce da ta shahara da ayar Khairul bariyya.[1]

إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ
Lalle ne waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan nagari, su ne mafi alherin halittu.



(Quran: Bayyina: Aya ta 7)


Matsayi Da Muhimmanci

Jabir Bin Abdullahi Ansari:
Mun kasance tare da Annabi (SAW), sai Aliyu (AS) ya iso. Annabi (SAW) ya ce:"Na rantse da wanda rayuwata take a hannunsa, wannan da mabiyansa su ne rabautattu waɗanda za su yi nasara a ranar kiyama." Sai wannan ayar ta sauka: "Lalle waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan nagari, su ne mafi alherin halittu." Kuma duk lokacin da Ali (A.S) ya iso, sahabban Annabi (SAW) su kan ce "Khairul Bariyya (Mafi alherin halittu) ya iso".

Ibn Asakir, Tarikh Dimashƙi, 1415H.Q, juzu'i 42 shafi na 371.

Ayar khiarul bariyya ana lissafa ta cikin falalar Imam Ali (A.S).[2] An naƙalto daga Ibn Abbas cewa wannan aya ta sauka ne game da Imam Ali (A.S).[3] A faɗin malaman Shi'a, Imam Ali (A.S) a lokacin zaman kwamitin shura mai mutum shida domin ayyana magajin Umar ya kafa hujja da wannan aya kan gaskiya da cancantuwa da halifanci da kuma cewa sha'anin saukar ayar ta ya kasance game da Imam Ali (A.S).[4]

Ayatullahi Makarim Shirazi (Haihuwa:1926m), daga cikin shahararrun malaman tafsiri na Shi'a, tare da jingina da wata riwaya daga Annabi da take magana kan sha'anin saukar wannan aya cikinta an yi magana game da Alah da mabiyansa,[5] Malamin ya ce kalmar Shi'a tun lokacin Annabi (S.A.W) aka fara bijiro da ita, kuma abin nufi daga Shi'a a cikin wannan riwaya, sune wasu keɓantattun mabiyan Imam Ali (A.S).[6]

Ma'anar Khairul Bariyya

Cikin litattafan riwaya na Shi'a da Ahlus-Sunna, akwai hadisai da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) wanda cikinsu aka fassara khairul bariyya (Mafi alherin halittu) a matsayin Imam Ali (A.S) da ƴanshi'arsa[7] Hakim Haskani (Rasuwa: 490H) daga malaman Ahlus-Sunna, a cikin littafin Shawahidut Tanzil ya kawo fiye da riwayoyi 20 tare da mabambantan sanadi.[8] Daga cikin ya naƙalto daga Ibn Abbas cewa a lokacin da wannan aya ta sauka Annabi (S.A.W) ya cewa Imam Ali (A.S) kai da ƴanshi'arka ku ne mafi alherin halittu. A ranar alƙiyama kai da ƴanshi'arka zaku zo cikin halin farin ciki da yarda Allah kuma yardaddu.[9]

Gaɓoɓin Tafsiri

Daga cikin gaɓoɓin tafsiri masu jan hankali da malaman tafsiri suka fitar da natijoji daga gare su, shi ne cewa mutane masu imani kuma salihai suna da fifiko hatta kan mala'iku, saboda kalmar “Albariyya” cikin jumlar khairul bariyya (Mafi alherin halittu) ta haɗa da dukkanin halittu.[10]

Saukar Wannan Aya A Makka

Kan Asasin ba'arin riwayoyi, ayar khairul bariyya ta sauka ne a lokacin da Annabi yake a Makka a cikin masallacin harami.[11] Bisa abin da ya zo a littafin tafsirin Al-Amsal, wannan mas'ala ba ta cin karo tare da kasancer saukar ayar a Madina, saboda zai iya yiwuwa surar ta sauka ne a Madina ita kuma wannan aya ta sauka ne cikin tafiye-tafiyen da Annabi (S.A.W) ya yi daga Madina zuwa Makka.[12]

Bayanin kula

  1. Allama Hilli, Nahj al-Haqq, 1402Q, S189.
  2. Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S213.
  3. Nagah kunid be Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411Q, J2, S473; Shushtari, Ihqaq al-Haqq, 1409Q, J20, S27.
  4. Tabari, al-Mustarshid, 1415Q, S354; Istarabadi, Ta’wil al-Ayat al-Zahira, 1409Q, S803.
  5. Suyuti, al-Durr al-Manthur, 1404Q, J8, S589; Amini, al-Ghadir, 1416Q, J2, S57 wa 58.
  6. Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S213-214.
  7. Suyuti, al-Durr al-Manthur, 1404Q, J6, S379; Istarabadi, Ta’wil al-Ayat al-Zahira, 1409Q, S80-803; Alusi, Ruh al-Ma’ani, 1415Q, J15, S432
  8. Nagah kunid be Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411Q, J2, S459-473.
  9. Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411Q, J2, S461.
  10. Tabataba’i, al-Mizan, 1417Q, J20, S340; Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S209.
  11. Haskani, Shawahid al-Tanzil, 1410-1411Q, J2, S467.
  12. Nagah kunid be Makarim Shirazi, Tafsir Numune, 1374Sh, J27, S212.

Nassoshi

Alusi, Mahmoud bn Abdullahi, Ruhul Ma’ani fi Tafsirin Alkur’ani Al’azim da Sab’ul Mathani, Tahqiq Ali Abdulbari Atiyya, Beirut, Darul Kutubul Ilmiyya, Manshurat Muhammad Ali Baydun, 1415H.

  • Ibn Asakir, Tarikh Dimashq, Tahqiq Amru bn Ghurama Al-Umrawi, Beirut, Darul Fikr, 1415H.
  • Istarabadi, Sayyid Ali, Ta’wilul Ayatis Zahira fi Fadailil ‘Itratit Tahira, Tahqiq Husain Ustaduli, Qum, Nashrul Islami, 1409H.
  • Amini, Abdulhusain, Al-Ghadir fi Al-Kitab was Sunnah wal Adab, Qum, Markazul Ghadir lid-Dirasat al-Islamiyya, 1416H.
  • Haskani, Ubaidullah bn Abdullahi, Shawahidut Tanzil li Qawa’idut Tafsil fi Al-Ayatin Nazila fi Ahlul Bayt, Tahqiq Muhammad Baqir Mahmudi, Beirut, Tehran, Wizaratul Thaqafa wal Irshad al-Islami, 1410–1411H.
  • Suyuti, Abdurrahman bn Abi Bakr, Ad-Durrul Manthur fi Tafsiril Ma’thur, Qum, Maktabat Mar’ashi Najafi, 1404H.
  • Shushtari, Qadi Nurullah, Ihqaq al-Haqq wa Izhaq al-Batil, Qum, Maktabat Ayatullah al-Mar’ashi Najafi, 1409H.
  • Tabataba’i, Sayyid Muhammad Husain, Al-Mizan fi Tafsiril Qur’an, Qum, Intisharat Islami, 1417H.
  • Tabari, Muhammad bn Jarir, Al-Mustarshid fi Imamat Ali bn Abi Talib (AS), Tas’hih Ahmad Mahmudi, Qum, Kushanpur, 1415H.
  • Allama Hilli, Hasan bn Yusuf, Nahjul Haqq wa Kashful Sidq, Beirut, Darul Kitab al-Lubnani, 1402H.
  • Makarem Shirazi, Naser, Tafsir Namune, Tehran, Darul Kutubul Islamiyya, 1374Sh.

Sadarwa Ta Waje