Ali yana tare da gaskiya

Daga wikishia
zanen rubutun hadisin Ali yana tare da gaskiya

Ali yana tare da gaskiya (arabic: حديث علي مع الحق) kuma gaskiya tana tare da Ali; ishara ce zuwa ga wata riwaya daga Annabi (S.A.W) da take nuni da cewa Imam Ali (A.S) a koda yaushe shi da gaskiya suna tare da juna, wannan hadisi ya zo da lafuzza mabanbanta wasu daga Malamai sun bayyana cewa wannan hadisi an nakalto shi daga bangaren `Yan Shi’a da Ahlus-sunna kuma ya kai matsayin haddin tawatiri, amma kuma tare da haka Ibn Taimiyya Harrani yayi inkarin wadannan riwayoyi da bayanna cewa babu wata hanya da suka zo da raunana ne. A cikin kwamitin Shura mai dauke da mutane shida wanda Umar Bn KHaddab ya samar domin ayyana wanda zai gaje shi, Hazrat Ali (A.S) ya kafa hujja da wannan hadisi kan cancantar da matsayin Halifanci, haka kuma wasu ba’ari daga cikin Sahabbai da Malaman Ahlus-sunna sun kafa hujja da wannan hadisi kan ingantar ayyukan Hazrat Ali (A.S). Daga wannan hadisi za a iya ciro fifikon Imam Ali (A.S) kan sauran Sahabbai, isma, wajabcin da'a, Imamanci da gadon kujerar Halifancin Annabi (S.A.W) da kuma haramncin Zaginsa.

Matani da kuma Abin da Makalar ta kunsa

Kasancewa tare da gaskiya daya ne daga Falalolin Sarkin Muminai Ali (A.S) da ya zo cikin wata riwaya daga Annabin Muslunci (S.A.W) wacce cikinta aka yi ishara zuwa ga hakan, ya zo cikin wannan riwaya kamara haka:

*علی مع الحق و الحق معه*

Ali yana tare da gaskiya kuma gaskiya tana tare da shi. [1] An rawaito wannan hadisi daga Annabi (S.A.W) da mabanbanta lafuzza a munasabobi mabanbanta. [2] Allama Hilli ya tafi kan cewa ba za a iya kidaya adadin riwayoyin da suka zo kan wannan batu ba. [3] wannan hadisi ya zo ta hanyoyi daban-daban cikin litattafai misalin Kashaful Yakini, [4] Kashaful Gumma, [5] Biharul Anwar, [6] Alghadir, [7] Mizanul Hikma, [8] sannan Sayyid Hashim Bahrani cikin littafin Gayatul Maram cikin babi biyu ya kawo kusan wannan hadisi da makamancinsa a wurare har ashirin da shida. [9]

Inganci

Wasu sun tafi kan cewa wadannan hadisai tabbatattu ne kuma ingantattu [10] anyi ittifaki kansu [11] daga bangarori biyu shi’a da Ahlus-sunna, [12] kuma sun kai matsayin haddin tawatiri [13] haka kuma wasu sun ce wani yanki daga matanin wannan hadisai suna kurewar darajar inganci ta tabbata kuma sun sami karbuwa daga bangaren `Yan Shi’a da Ahlus-sunna [14] kuma babu wata matsala da aka samu kan marawaitansu da Isnadi [15] Ibn Abil Hadid ya tafi kan tabbatuwa da ingancin isnadin wadannan hadisai [16] haka a ba’arin litattafan Sihahu Sitta da sauran littafan Ahlus-sunna [17] an samu kusan wurare 130 da suka kunshi ma’anar wannan hadisi na Ali yana tare da gaskiya. [18]

Da’awar Ibn Taimiyya

Ibn Taimiyya Harrani cikin littafin Minhajus AS-Sunna ya tafi kan cewa babu wani mutum da ya nakalto wannan hadisi daga Annabi (S.A.W) ko da kuwa da rarraunan isnadi ne, ya kuma tuhumi Allama Hilli kan nakalto wannan hadisi ya bayyana shi a matsayin makaryaci [19] Dandakakkun Malaman Shi’a cikin amsar da suka bawa Ibn Taimiyya sun yi ishara da hadisan Sahabbai [20] haka Allama Amini cikin littafin Alghadir bayan nakalto maganar Ibn Taimiyya sai ya kawo tarin riwayoyi daga Manyan Malaman Ahlus-sunna da kuma ingantattun litattafai. [21]

Marawaita

Sahabbai dai-dai har guda ashirin da uku ne suka nakalto wannan hadisi daga Annabi (S.A.W) [22] daga jumlar su akwai Halifa na farko [23] Sa'ad Bn Ubbada [24] Abu Zar Gifari [25] Mikdadu [26] Salmanul Farisi [27] Ammar Yasir [28] Abu Musa Ash’ari [29] Abu Ayyub Ansari [30] Sa’ad Bn Abi Wakas [31] Abdullahi Bn Abbas [32] Jabir Bn Abdullahi Ansari [33] Huzaifatu Bn Yaman [34] A’isha [35] Ummu Salma. [36] anyi isharar wannan hadisi a cikin riwayoyin Ahlil-baiti wani nakali daga Imam Sadik (A.S) da kakanninsa. [37]

Kafa Hujja

Hazrat Ali (A.S) da wasu Sahabbai a wuraren daban daban sun kafa hujja da wannan hadisi:

Ahamd Bn Hanbal [44] Ibn Abil Hadid [45] Ibn Jauzi [46] Sibdu Ibn Jauzi [47] daga cikin Malaman Ahlus-sunna sun yabi Imam Ali (A.S) bisa dogara da wannan hadisida kuma bada shaida kan ingancin aikin sa.

Abubuwan da Aka Amfana Daga Wannan Hadisi

A rubuta wannan hadisi a cikin Haramin Imam Ali (A.S) [48] Malaman Ahlus-sunna cun ciro wasu abubuwa daga wannan hadisi:

Zanen rubutun hadisin Ali yana tare da gaskiya a jikin Haramin Imam Ali (A.S)

Ali (A.S) shi ma’auni ne na banbance karya daga gaskiya Imam Ali (A.S) koda yaushe yana tare da gaskiya, shi mai ganin gaskiya mai fadar gaskiya madubin banbance gaskiya da karya. [49] bisa dogara da wannan hadisi wasu suna hukunta masu rigima da shi a matsayin batattu da suka fita daga gaskiya. [50] kuma suna ganin mabiyansa sune Firka da take kan tsira da rabauta [51] Malam Fakhrur Razi Babban Malamin Tafsiri a wurin Ahlus-sunna bisa kafa dalili da wannan hadisi ya tafi kan cewa duk wanda yake kwaikwayar Imam Ali (A.S) a cikin tafiyar addini to lallai ya samu shiriya. [52] haka cikin cigaba kan wannan hadisi ya zo cewa Annabi (S.A.W) ya cewa Ammar Yasir: idan dukkanin mutane suka bi wata hanya shi kuma Imam Ali (A.S) ya bi wata hanya daban to ka bi hanya da ya bi shi Ali (A.S) hanyar zai kasance. [53]

Imamanci da Halifancinsa Kai Tsaye Babu Shamaki da Yankewa

Malaman Shi’a sun tafi kan cewa daga cikin natijojin kasancewar Imam Ali (A.S) tare da gaskiya, akwai fifiko da ya samu kan sauran Sahabbai ta kowanne bangare. Daga ciki akwai cancantar sa Saki babu kaidai kan imamanci, jagoranci da halifanci ba tare da shamaki ba [54] da ace bai kasance ya cimma kololuwar darajar ilimi da kyawawan dabi’u da kwarewa a fannin siyasa ba, da ba zai taba kasancewa wanda ake Magana da kansa ba a wannan hadisi. [55] Allama Majlisi yace: Mu’utazilawa bisa dogara da wannan riwaya sun tafi kan fifitar Imam Ali (A.S) kan sauran Sahabbai. [56]

Ismar Imam Ali (A.S)

Shaik Mufid ya tafi kan cewa Imam Ali (A.S) tare da wadannan siffofi da ya samu daga bakin Annabi (S.A.W) ba zai taba zama ya afkwa aikata kuskure ko shakku cikin hukunce-hukuncen Allah ba. [57] ba zai taba bin hanyar bat aba. [58] wasu suna ganin cewa bisa la’akara da kasantuwar rashin samun sharadi ko kaidi cikin kasancewa Imam Ali (A.S) tare da gaskiya wannan wani dalili kan isma da yake da ita.[59] Baki dayan rayuwarsa ta kasance tare da gaskiya cikin kowanne fage daga fagagen [60] ilimi shari’a da zamantakewa [61] da mutane da dabi’a. [62] kowanne bangare baka samunsa da aikata kuksure a kowanne irin hali [63] saboda aikata Zunubi ko da sau daya ne yana cin karo da dawwamarsa tare da gaskiya, saki babu kaidin da ya zo cikin fadin Annabi (S.A.W) zai zamana ya samu warwara. [64]

Wajabcin yi masa biyayya da hani kan kiyayya da shi

Tare da dogara da wannan hadisi ya zama wajibi a yi wa Imam Ali (A.S) saki babu kaidi [65] wasu suna ganin wannan hadisi shine kurewar dalili kan falala da karama da girmama Imam Ali (A.S) Kuma suna ganin mafi karancin abin da za a iya fahimta daga wannan hadisi shine haramcin yakarsa da La'anta kansa da bayyana gaba da kiyayya da shi. [66]

Kirkirar wata riwaya mai kama da wacce ta gabata don Halifa na biyu

Wasu daga Ahlus-sunna sun nakalto wata riwaya mai kama da wacce ta gabata da suka danganta ta zuwa ga Annabi (S.A.W) dangane da Umar Bn Kaddab wai cewa Hazrat Muhammad (S.A.W) yace Allah ya yiwa umar rahama hakika ya kasance mai fadin gaskiya amma sai gaskiya din ta barshi, shi bashi da aboki. [67] A wannan fage wasu Dandakakkun Malamai sun tafi kan cewa matani da isnadin hadisin Ali yana tare da gasiya shi kansa yana hana inkarin asalinsada kuma raunana shi, da wannan dalili ne Makiyansa suka baki kokarinsu kan samarwa abokan gasarsa hadisan falaloli da suke kama da nasa, ko kuma kara wani abu cikin hadisan falalolinsa da zai fifita su a kansa ta yanda wannan falala ba za ta iyakantu kansa kadai ba. [68]

Bayanin kula

  1. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Juzu'i na 1, shafi na 294; Khazaz Qomi, Kefayat Athar, 1401 AH, shafi na 20; Ibn Hayyun, Sharh al-Akhbar, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 60; Sheikh Mufid, Al-Fusul Al-Mukhtarah, 1413H, shafi na 97.
  2. Tankabani, Zia al-Qulob, 2003, juzu'i na 2, shafi na 203.
  3. Allameh Hili, Kashf Al-Yekin, 1411 AH, shafi na 237.
  4. Allameh Hali, Kashf al-Iqin, 1411 AH, shafi na 233-236.
  5. Erbali, Kashf al-Ghamma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 146-148.
  6. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1404H, juzu'i na 38, shafi na 29-40.
  7. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 3, shafi na 251-256.
  8. محمدی ری‌شهری، میزان الحکمة، ۱۴۲۲ق، ج۱، ص۱۸۴.
  9. Amadi, Ghaya Al-Maram, 1413 AH, juzu'i na 5, shafi na 282-291.
  10. Milani, Sharh Minhaj al-Karamah, 2006, juzu'i na 2, shafi na 95.
  11. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 12, shafi na 110.
  12. Talghani, Manhaj al-Rashad, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 30 da 31.
  13. Hurrul Amili, Isbatul al-Hudat, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 318.
  14. Fakihu Imani, Hakku Ba Ali Ast, 1377H, shafi na 47.
  15. Sheikh Mofid, Al-Jamal, 1413H, shafi na 81.
  16. Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 297; Juzu'i na 18, shafi na 72-73.
  17. Tirmidhi, Sunan al-Tirmidhi, Beirut, juzu'i na 5, shafi na 633.
  18. Don Karin bayani duba: Faqih Imani, Haq ba Ali ist, 1377, shafi na 58-49.
  19. Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah, 1406 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 238.
  20. Amini, Nazrah fi Kitab Minhaj Sunnah al-Nabawiyah, shafi na 104; Faqih Imani, Haq ba Ali ist, 1377, shafi
  21. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 3, shafi na 251-256.
  22. Rizvani, Shi'eh shinasi Fasuk be Shubuhat, 2004, juzu'i 1, shafi 55; Fakihu Imani, Hakku Ba Ali Ast
  23. Tabarsi, al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 88.
  24. Hara’mili, Isbatul Al-Huda, 1422 H., juzu’i na 3, shafi na 298; Tabari, Kamil al-Baha'i, 1426 AH, juzu'i na 1, shafi na 325; Shushtri, Ihqaq al-Haq, 1409H, juzu’i na 2, shafi na 348..
  25. Eskafi, "Nakadu Uthmaniyah", 1378, shafi na 228; Shajari Jarjani, Al-Khamisiyyah al-Amali, 1422 AH, Mujalladi na 1, shafi na 189.
  26. Shushtri, Ihqaq al-Haq, 1409 AH, juzu’i na 4, shafi na 27.
  27. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashku, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 41; Hilali, littafin Sulaim bin Qays, 1405 AH, shafi na 881; Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 1, shafi na 32
  28. Eskafi, Al-Mayar da Al-Mawazna, 1402 AH, shafi na 35-36; Motaghi Handi, Kanz al-Amal, 1401 AH, juzu'i na 11, shafi na 613.
  29. Ibn Mardawayeh, Manaqib Ali (AS), 1424H, shafi na 115.
  30. Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 13, shafi na 188; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 472; Ibn al-Adim, Baghiyyah al-Talab, Beirut, juzu'i na 1, shafi na 292.
  31. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 20, shafi na 361; Haytami, Majma al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 7, shafi na 235.
  32. Hamawi Al-Shafi'i, Faraid al-Samatin, 1400 AH, juzu'i na 1, shafi na 177; Kundozi, Yanabi Al-Mouda, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 311; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 42; Ganji al-Shafi'i, Kefayyah al-Talib, 1404 AH, shafi na 187; Dhahabi, Mizan al-Etdal, 1382 AH, juzu'i na 2, shafi na 3; Ibn Hajar Asqlani, Lasan al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 2, shafi na 414; Haskani, Shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 246.
  33. Kundozi, Yanabi Al Mouda, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 173.
  34. Khwarazmi, al-Manaqib, 1411 AH, shafi na 177; Ibn Taus, al-Taraif, 1400 AH, juzu'i na 1, shafi na 103.
  35. Ibn Marduwyeh, Manaqib Ali (AS), 1424H, shafi na 115; Allameh Hilli, Nahj al-Haq, 1982, shafi na 225; Erbali, Kashf al-Ghamma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 154.
  36. Hakim Neishaburi, Mostadrak al-Sahihin, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 129; Ibn Marduyeh, Manaqib Ali (AS), 1424H, shafi na 115; Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 14, shafi na 322; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 449; Ibn Kathir, al-Bedaya wa al-Nehaya, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 360.
  37. Hamed Hossein, Ebakat al-Anwar, 1366, juzu'i na 1, shafi na 222.
  38. Allameh Hilli, Kashf Al-Yekin, 1411 AH, shafi na 425; Allameh Hilli, Nahj al-Haq, 1982, shafi na 394; Ibn Maghazali, Manaqib Ahlul Baiti (AS), 1427 AH, shafi na 189; Allameh Hilli, Minhaj al-Karamah, 1379, shafi na 94.
  39. Ibn Qutaiba, Al-Imamah wa Al-Siyaseh, 1410 AH, Mujalladi na 1, shafi na 98; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 AH, Mujalladi na 3, shafi na 62; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1404H, juzu'i na 38, shafi na 28.
  40. Sheikh Mufid, Al-Jamal, 1413H, shafi na 433.
  41. Erbili, Kashf al-Ghamma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi 147; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1404 AH, juzu'i na 33, shafi na 332; Juzu'i na 38, shafi na 35.
  42. Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 13, shafi na 188; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 472; Ibn Al-Adim, Baghiyyah al-Talab, Beirut, juzu'i na 1, shafi na 292.
  43. Ibn Asaker, TariKH MadinaTI Dimashk, 1415 AH, juzu'i na 20, shafi na 361; Haytami, Majma al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 7, shafi na 235.
  44. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 Hijira, juzu'i na 42, shafi na 419.
  45. Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 9, shafi na 88.
  46. Ibn Juzi, Said al-Khater, 1425 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 397.
  47. Sabt bin Jozi, Tazkire Al-Khawas, 1418H, shafi na 35.
  48. https://media.imamali.net/?id=349
  49. Faqih Imani, Haq ba Ali ist, 1377, shafi na 47.
  50. Hurrul Amili, Isbatul al-Hudah, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 318; Muhaddith Ermoi, Talikat al-NaKadu, 1358, juzu'i na 2, shafi na 712; Sanad Sahaba bainal Eadala wal-Isma, 1426 AH, shafi na 203
  51. Tijjani Samavi, Al-Shi’a Hum Ahlus-Sunnah, 1428H, shafi na 114.
  52. Fakhr Razi, Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 180.
  53. Ibn Taus, al-Taraif, 1400 AH, juzu'i na 1, shafi na 104; Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 1, 143; Allameh Hilli, Nahj al-Haq, 1982, shafi na 224.
  54. Misali, duba: Tabarsi, Elamul Alwara, 1390 AH, shafi na 159; Mughniyeh, Al-Jawami wa Al-Fawariq, 1414 AH, shafi na 92-93.
  55. Fakihu Imani Hakku Ba Ali Ast, 1377, shafi na 137.
  56. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1404H, juzu'i na 38, shafi na 29.
  57. Sheikh Mofid, Al-Fusul Al-Mukhtarah, 1413 AH, shafi na 339.
  58. Sheikh Mofid, Al-Fusul Al-Mukhtarah, 1413 AH, shafi na 211.
  59. Hakim da Imamatu wa Ahlul-Baiti (AS), 1424H, shafi na 225.
  60. Tusi, Talkhis al-Shafi, 2002, juzu'i na 2, shafi.257; Mughniyeh, Al-Jawama wa Al-Fawariq, 1414 AH, shafi na 92; Majlisi, Haq al-Iqin, Tehran, shafi na 136; Sobhani, haruffa da kasidu, 1425 AH, juzu’i na 5, shafi na 382.
  61. Sanad Sahaba baina Adala wal-Isama, 1426H, shafi na 203.
  62. Ibn Attiyah, Abhi al-Morad, 1423 AH, juzu'i na 1, shafi na 807; Moghaddis Ardabili, Hadiqa al-Shi’a, 2003, juzu’i na 1, shafi na 327.
  63. Sobhani, Al-Adwa'u, Qum, shafi na 389; Buhus fi Melali wa-Al-Nehal, Qum, juzu'i na 6, shafi na 274.
  64. Fakihu Imani, Hakku Ba Ali Ast, 1377, shafi na 145-146.
  65. Ibn Attiyah, Abhi al-Morad, 1423 AH, juzu'i na 1, shafi na 569; Tunkabani, Zia al-Qulob, 2003, juzu'i na 2, shafi na 203; Kashif Al-Ghita, Al-Aqid al-Jaafariyyah, 1425 AH, shafi na 53.
  66. Tusi, Talkhis Al-Shafi, 1382, juzu'i na 2, shafi na 136.
  67. Bazar, Musnad al-Bazar, 1409 AH, juzu'i na 6, shafi na 98; Tirmidhi, Sunan al-Tirmidhi, Beirut, juzu'i na 5, shafi na 633; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Dimashk, 1415 Hijira, juzu'i na 44, shafi na 126.
  68. Fakihu Imani, Haq ba Ali ist, 1377, shafi na 101.

Nassoshi

  • Amadi, Saif al-Din, Ghaya al-Maram a cikin ilimin al-kalam, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1413 AH.
  • Ibn Abi al-Hadid, Abd al-Hamid bin Hibatullah, Sharh Nahj al-Balaghah, Qum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, 1404H.
  • Ibn Taimiyyah Harrani, Ahmed bin Abdul Halim, Minhaj Sunnah al-Nabwiyyah fi Nakdi Kalam Rafida al-Qadriyah, bincike na Muhammad Rashad Salem, Imam Muhammad bin Saud Islamic University, 1406 AH.
  • Ibn Juzi, Abu al-Fraj Abdul Rahman bin Ali, Said al-Khater, Damascus, Darul Qalam, 1425H.
  • Ibn Juzi, Sabbat, Tazkira Al-Khwas, Qum, Al-Sharif al-Radhi's Manshurat, 1418H.
  • Ibn Hajar Asqlani, Ahmad bin Ali, Lasan Al-Mizan, Research of Al-Marief al-Naziami Department, Beirut, Al-Alami Foundation for Press, bugu na biyu, 1390 AH.
  • Ibn Hayyoun, Nu'man Ibn Muhammad, Sharh Al-Akhbar fi Fada'il al-Imam al-Atahar (AS), Qom, Jamia Madrasin, 1409 AH.
  • Ibn Shahrashob Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Menaqib Al Abi Talib, Qum, Allameh, 1379H.
  • Ibn Taaws, Seyyed Razi al-Din, Al-Taraif Fi Marafah Madhab al-Tawaif, Kum, Khayyam Publishing House, 1400 AH.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madinati Damascus da ambaton kyawawan halaye da sunan mafita na, binciken Ali Shiri, Beirut, Darul Fikr, 1415H.
  • Ibn Atiyah, Jamil Hamoud, Abhi al-Morad Abha fi Sharh Muatamar Ulama Bagdad, Beirut, Mu’assasa Al-alami, 1423H.
  • Ibn Qutaiba Dinuri, Abdullahi bin Muslim, Imamatu wa siyasa wanda aka fi sani da tarihin halifofi, Ali Shiri, Beirut, Darul-Awat, 1410H ya yi bincike.
  • Ibn Kathir Damaschi, Ismail Ibn Omar, al-Badaiya wa al-Nahiya, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
  • Ibn Marduyeh Isfahani, Ahmad Ibn Musa, Manaqib Ali Ibn Abi Talib (AS), Kum, Darul Hadith, bugu na biyu, 1424H.
  • Ibn Maghazali, Ali Ibn Muhammad, Menaqib Ahl al-Bait (A.S.), Tehran, Al-Majjam al-Alami don kusanci tsakanin mazhabobin Musulunci, 1427H.
  • Ibn al-Adeem, Omar Ibn Ahmad, Baghiya al-Talab a cikin tarikh Halab, binciken Sohail Zakar, Beirut, Darul Fikr, Bita.
  • Abu Yali Mosuli, Ahmad Bin Ali, Musnad Abi Yali, Damascus, Dar al-Ma'mun for Heritage, Binciken Hossein Salim Asad, 1404H.
  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, Tabriz, Bani Hashemi, 1381H.
  • Skaffi, Muhammad bin Abdullah, Al-Ma'yar da Al-Muwazna fi Fadhail al-Imam Amir al-Mu'minin Ali bin Abi Talib, Allah ya kara masa yarda, Beirut, 1402H.
  • Scafi, Muhammad bin Abdullah, nakade Otmaniyya, Qum, Makarantar Ayatullah al-Marashi, 1383-1378.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir fi Al-Kitab wa Sunnah da Al-Adab, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, 1416H.
  • Amini, Nazrah fi Kitab Minhaj Sunnah al-Nabawiyyah, edited by Ahmad Kanani, Tehran, Mashaar Publishing House, Beta.
  • Bazzar, Ahmed bin Amr, Bahr al-Zakhar (Musnad al-Bazar), Mahfuz al-Rahman Zainullah's research, Beirut, Al-Qur'an Science Foundation, 1409 AH.
  • Tirmidhi, Muhammad bin Isa, Sunan al-Tirmidhi, Beirut, Dar Ihya al-Tarath al-Arabi, bincike na Ahmed Mohammad Shakir, 1998.
  • Tankabani, Muhammad bin Abdul Fattah, Zia al-Qulob, Qum, Islamic Reserve Assembly, 1382.
  • Tijjani Samavi, Muhammad, Al-Shi’a Hum Ahal-Sunnah, Qum, Mu’assasat Ansari, bugu na 10, 1428H.
  • Hakeem Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, Mustadrak al-Sahihin, bincike na Mustafa Abdulqadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1411H.
  • Har Amili, Muhammad bin Hasan, Isbatul al-Huda, Beirut, Al-Alami Foundation, 1422 AH.
  • Haskani, Obaidullah bin Abdallah, Shawaheed Al-Tanzil na Qabam al-Tfadil, Tehran, Dandalin Rayar da Al'adun Musulunci, 1411H.
  • Hakim, Sayyid Muhammad Baqir, Al-Imamah wa Ahlul-Baiti (A.S.) Al-Nazariyyah da Al-Istidlal, Kum, al-Maqqar al-Islami al-Mawdin, 1424H.
  • Joyni, Ibrahim bin Muhammad, Faraed al-Sumatiin fi Fadail al-Mortaza wa al-Batul wa al-Sabatin wa al-Imaam min Zaritham (a.s.), Qom, Al-Mahmoud Foundation, 1400 AH.
  • Khazaz Qomi, Ali bin Muhammad, Kefayat al-Athar fi Nass Ali al-Imam al-Thini Eshar, Qom, Bidar Publications, 1401 AH.
  • Khatib al-Baghdadi, Ahmed bin Ali, Tarihin Bagadaza, Mustafa Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, ya yi bincike, 1417H.
  • Khwarazmi, Muwaffak bin Ahmad, al-Manaqib, Kum, Jamia Madrasin, bugu na biyu, 1411H.
  • Dhahabi, Shams al-Din Muhammad bin Ahmed, Mizan al-Etdal fi Naqd al-Rijal, bincike na Ali Muhammad al-Bajawi, Beirut, Daral al-Merfeat don bugawa da bugawa, 1382.
  • Rizvani, Ali Asghar, fasuk shubhat u, Tehran, Mawallafin Mashaar, bugu na 2, 2004.
  • Zamakhshari, Jarallah, Rabi al-Abrar da Nusus al-Akhyar, Beirut, Al-alami Foundation, 1412 AH.
  • Sobhani, Ja’afar, al-Aqid al-Aqied al-Shi’a al-Imamiyah, Kum, Imam Sadiq (a.s.) Institute, Bita.
  • Sobhani, Jafar, Buhusu fi Melali wa-Al-Nehal, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation, daban-daban.
  • Sobhani, Resa'el wa Makalat, Kum, Imam Sadik (a.s.), bugu na biyu, 1425H.
  • Sanad, Sheikh Muhammad, Sahaba bainal Adalati wal-Isma, Qum, Lasan al-Saddeq, bugun farko, 1426H.
  • Shajari Jarjani, Yahya bin Hossein, Tartibi Amali Al-Khamisiyyah, wanda Muhammad Hasan Muhammad Hasan Ismail ya yi bincike, a Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1422H.
  • Shushtri, Qazi Nurullah, Ihqaq al-Haq da Iqhaq al-Batil, Kum, Mazhabar Ayatullahi al-Marashi al-Najafi, 1409H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Jamal wa al-Nusra na Sayyid al-Utrah a yakin Basra, Qum, Al-Khangir al-Alami na Sheikh Al-Mufid, 1413H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Fusul Al-Mukhtarah, Qum, Al-Khangir al-Alami na Sheikh Al-Mofid, 1413H.
  • «الصور الأكثر مشاهدة لعام 2012م» Imam Ali (a.s.) kafar yada labarai, ziyarar ranar: 18 ga Maris, 1400.
  • Taleghani, Mohammad Naeem, Manhaj al-Rashad fi Marafah al-Ma'ad, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1411H.
  • Tabatabaei, Sayyid Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar malamai ta Qum Seminary Society of Teachers, bugu na biyar, 1417H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Elamul Al-Wara Media na Alam Al-Hadi, Tehran, Islamia, bugu na uku, 1390H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Ihtjaj, Mashhad, bugun Al-Mortaza, 1403H.
  • Tabari, Hasan bin Ali, Kamil al-Baha'i, Muhammad Shua Fakhir, Qum, al-Maktab al-Haydariyya, ya fassara, 1426.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Talkhis Al-Shafi, Kum, Al-Mohbein Publications, 2002.
  • Alameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Kashf al-yaqeen fi Fadael Amir al-Momenin (AS), Tehran, Ministry of Culture and Islamic Guidance, 1411 AH.
  • Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Minhaj al-Karamah fi Marafah al-Imamah, Mashhad, Ashura Foundation, 1379.
  • Allameh Hilli, Hassan bin Yusuf, Nahj al-Haq da Kashf al-Saddeq, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, 1982.
  • «علی مع الحق و الحق مع علی» The official page of Seyyed Abulfazl Sarwar on Instagram, visit date: 18
  • Fakhrazi, Muhammad bin Omar, Mufatih al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Faqih Imani, Mahdi, Haq ba Ali ist, Qom, ofishin yada farfagandar Musulunci, 1377.
  • Kundozi, Suleiman bin Ibrahim, Yanabi' Al-Mouda Lzavi al-Qorbi, Qum, Osweh Publishing House, bugu na biyu, 1422H.
  • Kashif al-Ghata, Sheikh Jafar, Al-Aqeed al-Jaafariyyah, Qum, Mu'assasar Ansari, bugu na uku, 1425H. Ƙarin amfani
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Littattafan Musulunci, bugu na 4, 1407H.
  • Sashen Ilimi da Bincike na Musulunci, Ghadeer Hadith, Guayai Wilayat Document, Qum, Makarantar Imam Ali Bin Abi Talib (AS), bugu na 8, Beta.
  • Ganji Shafi'i, Muhammad bin Yusuf, Kefaiya Talib fi Manaqib Ali bin Abi Talib, Tehran, Dar Ehiya Tarath Ahl al-Bait (AS), bugu na biyu, 1404H.
  • Motaghi al-Hindi, Ali bin Hossam, Kanzal-Amal fi Sunan al-Aqwal al-Afeal, Research: Bakri Hayani, Safwa al-Saqqa, Beirut, Al-Risalah Foundation, bugu na 7, 1401 AH.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1404H.
  • Majlisi, Mohammad Baqer, Haq Aliqin, Tehran, Islamia Publications, Beta.
  • Muhaddith Ermoi, Mirjalaluddin, "Talikatu Nakdi", Tehran, Wallafe-wallafen Ƙungiyar Ƙwararru ta Ƙasa, 1358.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad, Mizan al-Hikmah, Qum, Darul Hadith, 1422H.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, Al-Jawami'u da Al-Fawariq tsakanin Sunnah da Shi'a, Beirut, Ezzeddin Foundation, 1414 AH.
  • Moghaddis Ardabili, Ahmed bin Muhammad, Hadiqa al-Shi'a, Qom, Ansarian Publications, bugu na uku, 2003.
  • Mirhamed Hussain, Abqat al-Anwar a cikin Hujjar Imamancin Imaman Athar, Isfahan, Laburare Amir al-Momenin, bugu na biyu, 1366.
  • Milani, Sayyid Ali, Sharh Minhaj al-Karama fi Marafah al-Imamah, Qom, Cibiyar Nazarin Musulunci, 1386.
  • Hilali, Sulaimu bin Qays, littafin Sulaimu bin Qays al-Hilali, Kum, Al-Hadi, 1405H.
  • Haythami, Ali bin Abi Bakr, Majma al-Zawa'ed kuma Tushen Fa'idodi, Bincike na Hossam al-Din al-Qudsi, Alkahira, Mazhabar Qudsi, 1414H.