Alullah

Daga wikishia

Ahlullah, (Larabci: آل الله) kalma ce da ake nufi Ahlul-Baiti, kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi, kuma masu wa'azi da mawaƙa na Ahlul-Baiti (A.S) an yi amfani da ita don nuni ga ƴan mutane gidan Manzo Allah (S.A.W). wannann kuwa saboda girman matsayin da suke da shi a wurin Allah ta'ala, ba kamar yadda ake zaton su mutanen Allah ne a zahirin ma'anar kalmar ba. Kuma ana kiran ƙuraishawa da Ahlullah, dangin Allah. Saboda alaƙarsu da ɗakin Allah mai alfarma.

Abin da Ake Nufi Da Alullah

Abin da ake nufi da ahlullah sune iyalan gidan manzo (s.a.w)[1] kalmar Alu a yaran larabci an ciro ta daga kalmar al-ahlu kuma tana nufin mutanan gida, amma a asali tana nufin kusanci, kuma ana kiran mabiya da wannan,[2] kuma ita wannan kalma ta zo a cikin alƙur'ani mai girma, misali Alu Imran,[3] iyalan Imrana ya ƙunshi Maryam (A.S) da kuma Isa (A.S)[4] abin nufi daga Alu Luɗ[5] sune iyalan Annabi Luɗ[6] da Alu Fira'auna[7] sune mabiyan shi da sujojinsa,[8] amma a Luga idan aka raba Ali ga Allah,to nuni ne na girma da ɗaukaka da matsayi babba. ba ana nufin cewa su `ƴa`yan Allah ne da mata shi ba.Allah bai haifa ba kuma ba'ahaife shi ba.

Su Wanene Alullah

Bisa abin da yazo a ruwayoyi, imamai suna da ilimi na masamma saboda sune sirrin Allah kuma Alullah wato makusantan Allah kuma sune magada annabawa,[9] sabo da hakane masu wa'azi da mawaƙa sukayi amfani da kalmar Ahlulallah akan Ahlulbait wato iyalan gidan manzo domin nuni akan matsayinsu ya zo a cikin waƙa;

وبنيه بين يزيدها وزيادها من عصبة ضاعت دماء محمد وأكف آل الله في أصفادها صفدات مال الله ملء أكفها[10]

Wasu dangi sun zubar da jini muhammad da `ya`yansa daga wannan dangi ne yazidu da ziyad suka fito Sun cika hannayansu da dukiyar Allah. Amma nauyin jini Ahlullah wato iyalan gidan Manzo akan wiyansu.

Dalilin da yasa ake cewa Imamai Alullah saboda tsananin kusancinsu da Allah ne da ɗaukakarsu da falalar su da ɗaukakar matsayinsu a gun Allah maɗaukaki. kuma saboda hakane ake ce musu waliyan Allah da hujjar a doran ƙasa.[11] Kamar yadda akayi anfani da kalmar alullah akan ƙuraishawa saboda sune masu kula da Ka'aba (ɗakin Allah) kamar yadda aka kira su da makwabtan Allah da mazauna ɗakin Allah.[12] kamar yadda wani malamin Shi'a Mansur ɗan Husain Al'abi a ƙarni na biyar yace;Abin da ya faru na Ashabil-Fi yasa ƙabilar ƙuraish ta zama babba a idan larabawa kai har abin yake da anakiransu da Ahlullah.[13]

Bayanin kula

  1. ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟
  2. Al-Misbah Al-Munir: 28
  3. Suratul Al-Imran, aya ta 33.
  4. Makarem Al-Shirazi, Tafsir al-amsal, juzu'i na 2, shafi na 472.
  5. Suratul Naml, aya ta 56; Suratul Hajr, aya ta 61.
  6. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 15, shafi na 376.
  7. Suratul Baqarah, aya ta 50; Suratul Anfal, aya ta:54.
  8. Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-amsal, juzu'i na 1, shafi na 224; Qurashi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1391, juzu'i na 1, shafi na 120.
  9. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 592, shafi na 184
  10. الأميني، الغدير، ج 4، ص 216.
  11. ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟
  12. Ibn Abd Rabbah, al-Iqdul al-Farid, Dar al-Kutub Al-Elamiya, juzu'i na 3, shafi na 226; Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 15, shafi 258; Sheikh al-Sadooq, Amali, 1417 AH, shafi na 317.
  13. Al-Abi, Nasr Al-Durri, 1424H, shafi na 273.

Nassoshi

  • Al-Abi, Mansour bin Hossein, Nasr al-Adr fi al-Mahaderat, bincike: Mahfouz Khaled Abdul Ghani, Beirut, Dar al-Kitab Al-Alamiya, 1424 AH/2004 AD.
  • Al-Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir fi Al-kitab, wa Sunnah wa Adab, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Arabiyya, 1397 - 1977 Miladiyya.
  • Makarim Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsir Al-Qur’an Al-Manzil, Kum, Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib (a
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, bugun Mu'assasar Al-Wafa, 1403H.
  • Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, Islamic Publications Notebook, 1417 AH.
  • Ibn Abd Rabbihi, Ahmed bin Muhammad, Al-Iqdul Al-farid, edited by: Abdel Majeed Tarhini, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah.
  • Qurashi, Ali Akbar, Tafsir Ahsan al-Hadith, Navid Islam Publication Notebook, 1391 AH..s), 1379H.
  • ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟ مركز الأبحاث العقائدية، آخر مراجعة 16 ديسمبر/كانون الأول 2020 م.