Muwaddatu Ahlil-Baiti (A.S)

Daga wikishia
Wannan wata kasida ce da take magana game da kauna da son Ahlul-Baiti (A.S) Domin sanin Ayar Muwadda, duba Ayar Muwadda
Ayar muwadda a kan haramin Imam Husaini (a.s)

Kaunar Ahlil-Baiti (A.S) (Larabci: مودة أهل البيت (ع)) na nufin bayyana soyayya ga Ahlin Gidan Annabi (S.A.W) kan asasin aya ta 23 cikin suratul Shura an ajiye bayyana musu soyayya matsayin ladan Sakon Annabi (S.A.W), kan asasin wata riwaya da `yan Shi’a da Ahlus-sunna suka nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa: Hakika son Iyalan Annabi (S.A.W) asasin Muslunci ne, a cewar Sayyid Muhammad Tijjani, Hakika ra'ayin Musulmi ya yi ittifaki kan wajabcin soyayya Iyalan Annabi (S.A.W) da wannan dalili ake ganin son su zai zama wani sababi da ya dace kan hadin kan Musulmi, wasu ba’arin Masu bincike sun bayyana cewa hikimar wajabcin son su shi ne yi musu biyayya. A cikin wasu riwayoyi an kawo wasu tasiri da amfani a gidan duniya da lahira dangane da soyayyar Iyalan Annabi (S.A.W) daga ciki akwai samun Ceton Ahlil-Baiti, karbar ayyuka, tabbatuwar kafafuwa kan Siradi duka suna cikin tasiri da alfanu na Lahira, sannan kuma Tuba kafin mutuwa, kauracewa abin hannun mutane da kuma gudanar Hikima kan harshen mutum suna cikin tasiran duniya ga wadanda suke son Iyalan Annabi (S.A.W), kan asasin wasu Hadisai an bayyana son Iyalan Annabi (S.A.W) Matsayin Alamar Tsarkin haihuwa, sannan nuna soyayya ga Makiyan su alamace dake bayyana a hakika mutum ba Masoyin Iyalan Annabi (S.A.W) bane. Muhammad Raishahri: zaman Makoki domin Iyalan Annabi (S.A.W) daya daga cikin hanyoyin nuna soyayyar su ce, haka Ziyartar Kaburburan su (A.S) da farin ciki a ranakun Farin cikin su da kuma sanya sunayen su a `ya`yan da aka Haifa mana duka suna cikin hanyoyin nuna soyayya gare su, wasu ba’arin Masu bincike sun ambaci hanyoyin nuna soyayya ga Ahlil-baiti (A.S) ambaton Falaloli da al’adun su da samar da Maukibobin addini suna daga cikin nuna musu soyayya. Wasu ba’arin Mutane tare da jingina da Riwayoyin son Ahlil-Baiti (A.S) suna ganin son Ahlil-Baiti (A.S) yana wadatarwa kan samun farin cikin lahira kuma sun yi Imani kan cewa matukar kana tareda soyayyar su to aikata zunubi ba zai cutar da kai ba a ranar lahira, sai dai cewa Malaman Shi’a basu yarda da wannan Halasta haramun din ba, sun dora wadannan Hadisai kan wata ma’ana daban, sun ce wadannan Hadisai suna Magana kan Zunuban da aka aikata a halin gafala, sam sam wadannan Hadisai basu da kowacce irin danganaka da zunuban da aka aikata su da gangan. An rubuta littatafai daban-daban kan maudu’in soyayyar Ahlil-Baiti daga jumlar su zamu iya ishara da littafin (Hubbu Ahlil-Baiti fil-Kitab was-Sunna) talifin Muhammad Takiyu Assayid Yusuf Alhakim da kuma littafin (Kur’an wa-Muhabbat Ahlil-Baiti) talifin Aliyu Rida Azimi Fur

Muhimmanci da Matsayi

Kaunar Ahlil-Baiti wani Isdilahi ne da aka ciro daga aya ta 23 suratu Shura ayar da aka fi sani da ayar Muwaddat, ma’ana ayar soyayyar Ahllin Gidan Annabi wacce kan asasinta aka bayyana nuna soyayya gare su matsayin ladan sakon da Annabi (S.A.W) ya zo da shi [1] wasu ba’arin Malaman Shi’a misalign Muhammad Rida Muzaffar yana ganin wajabcin son Ahlil-Baiti cikin laruran addinin Muslunci [2] cikin ziyarar Jami’atul Alkabira ya zo cewa soyayyar Ahlil-Baiti ita ce dai soyayyar Allah [3] kuma cikin hadisan shi’a da Ahlus-sunna an nakalto daga Annabi (S.A.W) cewa soyayyar Ahlil-Baiti itace asasi da tushen Muslunci [4] a cikin wata riwaya daga Imam Bakir (A.S): soyayyar Ahlil-Baiti itace ainahin Imani kuma kiyayyar su shine Kafirci [5] Allama Hilli Masanin Fikhu da Kalam a Shi’a a Karni na takwas: sabawa Imam Ali (A.S) ba ya dacewa da soyayyar sa. Daidai lokacin da soyayyarsa take wajibi soyayyar sauran Halifofi ba wajibi bace, da wannan ne ya kafa dalili kan Imamancin Imam Ali (A.S) da kuma gaskiyar Mazhabar Shi’a [6] An nakalto daga Shafi’i daya daga cikin Fakihan Mazhabobi hudu:

نْ كانَ رَفْضاً حُبُّ آلِ مُحَمَّد فَلْيَشْهَد الثََقلان أنّى رافِضی

Idan son Ahlin Muhammad shine Rafidanci* Mutane da Aljanu su shaida ni Barafide ne [7] Mawaddatu na nufin soyayya [8] da Tawalli [9] ko kuma madaukakin martaba da sama da soyayya [10] kuma reshe ce daga soyayyar Allah [11]

Girmama Sha'a'ir

Muhammad RaiShahri Mai bincike kan Hadisan Shi'a, ya tafi kan cewa Zaman Makoki domin Ahlil-Baiti daya ne daga cikin hanyoyin nuna soyayya gare su kuma Misdaki ne na girmama Sha'a'ir [12] hakama Ziyartar Kaburburan A'imma (A.S) [13] da farin ciki lokutan farin cikin su [14] da Ambaton Falalolin su [15] da sanya sunayen su a yaran da aka haifa mana [16]

Wajabcin Son Ahlil-Baiti

Wasu ba'arin Masu bincike sun bayyana cewa Son Ahlil-Baiti hakki ne [17] kan dukkanin Musulmi kuna sun yi tarayya cikin su [18] kuma ya kasance wani sababi da mafi dacewa kan hadin kan Al'ummar Musulmai [19]wasu ba'arin Malaman Shi'a sun tafi kan cewa wajabcin Son Ahlil-Baiti wani abu da dukkanin al'ummar Musulmi suka yi ittifaki a kansa in banda Nasiba (Makiya Ahlil-Baiti) [20] Shamsuddini Zahabi daya daga cikin Malaman Ahlus-Sunna ya bayyana cewa kowacce irin shakka da kokwanto kan wajabcin Son su ababen watsi ne [21] Fakrur-Razi Babban Malamin Tafsiri na Ahlus-Sunna tare da wannan kafa dalili cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana son Ali da Fatima da Hassan da Husaini kuma `da ga Annabi wajibi kan dukkanin Musulmi, saboda haka Son Ahlil-Baiti wajibi ne kan dukkanin Musulmi [22] An nakalto daga Shafi'i [23] Ya Ahlin gidan Manzon Allah hakika Sonku*wata farilla ce da Allah ya saukar da ita cikin Kur'ani. [24]

Falsafar Wajabci

Allama Tabataba’i Marubucin Tafsir Almizan ya tafi kan cewa Falsafar wajabcin soyayyar Ahlil-Baiti ba komai illa Marja’iyyar su ta ilimi domin Musulmi ta fuskanin soyayya garesu su koma zuwa gare su cikin mas’aloli, da wannan dalili ne Malamin ya tafi kan cewa soyayyarsu ita ce ke lamince wanzuwar addini [25] a ra’ayin Muhammad Rida Muzaffar Malami Marubuci a Shi’a a karni na goma sha hudu, babu kokwanto wajabcin soyayyar Ahlil-Baiti da kaunar su (A.S) sakamakon kusancin su ga Allah da mastayin su da mukamin da suke da shi a wurinsa sakamakon tsarkakar su daga dukkanin nau’in Shirka da Zunubai daga kuma dukkanin abinda yake nesanta Bawa da Ubangijinsa [26] Ayatullahi Khamna'i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran,yana ganin wannan soyayya ga Imamai ma'anar ta shine biyayya ga Ahil-Baiti, ya tafi kan cewa mutane za su samu kariya ne ta hanyar wilayar su ga Ahlil-Baiti, [27] a cewar Muhammad Takiyu Misbahu Yazdi daya daga cikin Malaman karni goma sha hudu hijira Shamsi, soyayyar Ahlil-Baiti wajibi ce sakamakon dangantakar su da Annabi (S.A.W) bari dai wajibi ce sakamakon sun kai kololuwa cikin bauta ga Ubangiji [28] haka Ali Rabbani Golfaigani daya daga cikin Malamai a fagen ilimin Kalam a Hauza Ilmiyya, ya tafi kan cewa Falsafar wajabcin son ahlil-Baiti ba wnai abu bane sai `da’a gare su, domin Kauna ta hakika tana tabbata ne cikin biyayya da `da’a [29] a cewar Jawad Muhaddisi Marubuci a Hauza Ilmiyya da ke birnin Qum, gwargwadon soyayya da kauna suka karu gwargwadon yanda biyayya da za ta karu [30]

Kufaifayi

Aya ta 23 Suratul Shura. Ayar Mawadda

قُل لَّا أَسْأَلُکُمْ عَلَیهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِی الْقُرْبَی وَمَن یقْتَرِفْ حَسَنَةً نَّزِدْ لَهُ فِیهَا حُسْنًا إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ شَکُورٌ؛

Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijãra (lada) a kan wancan (saƙon) fãce soyayya ga ma'abota kusanci. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai

Shura aya ta 23

Masu bincike, hakika soyayyar Ahlil-baiti wani sababi ne na motsi zuwa ga Kamalul Mudlak [31] sababi ga danfaruwar zukatan Masoya Ahlil-Baiti (A.S) ga junan su [32] da kuma tsaftatar addini [33] kan asasin wani hadisi daga Imam Ali (A.S) wanda Abu Na’im Isfahani da Ubaidullahi Hasakani Malaman Ahlus-sunna a Karni na biyar suka nakalto shi (Muminai kadai suke kiyaye soyayyar Ahlil-Baiti) [34]

Wasu Kufaifayi

Kan asasin wata riwaya daga Annabi (S.A.W) amfani son sa da iyalan gidansa bayyananne a wurare guda biyar: 1 lokacin Mutuwa 2 cikin Kabari 3 Ranar Lahira 4 Lokacin karbar Takardar Ayyuka 5 Lokacin Hisabi 6 Kusa da Mizani 7 Yayin Ketare Gadar Siradi [35] kan asasin wata riwayar daban da Ahlus-sunna suka nakalto, duk wanda ya mutu tareda soyayyar Ahlil-Baiti misalinsa misalin Shahidi, an gafarta masa kuma yana mutuwa da kammalallen Imani, lokacin mutuwarsa za a yi masa bushara da Aljanna, za bude kofofi biyu na zuwa Aljanna a cikin Kabarinsa, kuma Allah zai sanya Mala’iku su dinga kai masa ziyara a cikin Kabari [36] sauran Kufaifayi da aka ambata dangane da soyayyar Ahlil-Baiti sune kamar haka:

  • Samun ceto; cikin wani hadisin Annabi ya zo cewa duk mutumin da yake tareda soyayyar Ahlil-Baiti zai shiga Aljanna da ceto na Ahlil-Baiti [37]
  • Za a tashe shi tareda Ahlil-Baiti; kan asasin wata riwaya daga Annabi (S.A.W) hakika Masoya Ahlil-Baiti za a tashe su tareda su ranar lahira [38] 1
  • Karbar Ayyuka; a wata riwaya da Abu Hamza Simali ya nakalto daga Imam Ali (A.S): sauran ayyuka Masoya Ahlil-Baiti za su samu karbuwa, amma idan babu soyayyar su sauran ayyukan ba zasu karbu ba [39]
  • Bakiyatus Salihat,; ya zo cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyana cewa soyayyar Ahlil-Baiti tana daga cikin Bakiyatus Salihat [40]
  • Tabbatuwar Digadigai kan Siradi; ya zo a wata riwaya daga littafin Jafariyat duk mutumin da yake da soyayyar Ahlil-Baiti mai yawa Digadigansa zasu tsayu kyam kan Siradi [41]
  • Gafarta zunubai; ya zo a wata riwaya daga Annabi (S.A.W) ana gafarta zunubai albarkacin soyayyar Ahlil-Baiti [42] Ibn Hajar Haitami daya daga cikin Malaman Ahlus-sunna a karni na goma tareda nakalin hadisin Babul Hidda(Kofar Kankare Zunubai) ya tafi kan cewa kamar yanda Allah ya sanyawa Banu Isra’ila shiga ta Kofar Hidda sababin gafara gare su, haka ya sanya soyayyar Ahlil-Baiti sababin gafara cikin wannan al’umma ta Annabi (S.A.W) [43]

Kufaifayi na nan Duniya

Cikin wata riwaya daga Annabi (S.A.W) an bayyana wasu wurare da ake ganin Kufaifayin soyayyar Ahlil-Baiti (A.S) akwai misalin: Zuhudu, Shaukin yin aiki. Tsentseni cikin addini, Shaukin yin Ibada, Tuba kafin mutuwa, Samun Nishadi cikin raya Dare da Ibada, Rashin kwadayin Abun Hannun mutane, Yafiya, Dawwama kan umarni da hanin Ubangiji da kuma rashin son duniya [44] a wata riwaya daga Imam Bakir (A.S) Allah yana tsarkake zukatan Masoya Ahlil-Baiti [45] a wani hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zo cewa duk wanda ya iya tabbatar da soyayyar Ahli-Baiti a zuciyar sa Hikima zata gudana akan Harshensa [46]

Alamomi

Daidai da wata riwaya daga Imam Bakir (A.S): soyayyar Ahlil-Baiti da bata haduwa waje guda da son Makiyansu, soyayyar Makiyansu alama ce ta cewa ba a son su a hakika, [47] haka kan asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) idan ya zamana mutum baya son Masoyan Ahlil-Baiti lallai baya cikin Masoya Ahlil-Bati [48] kan asasin wani hadisin daban ya zo cewa: Marasa kishi, `Ya`yan zina, Mazajen da suke kamanta kansu da Mata, da kuma wadanda Mahaifiyarsu ta dauki cikinsu a lokacin Jinin Haila sune wadanda basa son Ahlil-Baiti [49] a wata riwayar ya zo cewa son Ahlil-Baiti alama ce ta tsarkin Haihuwa, biyayya ta aiki [50] suna daga cikin misdakin muhimmi da kuma alama ta gaskiyar soyayyar mutum ga Ahlil-Baiti

Halasta Haram Bisa Raya Dogaro Da Soyayyar Ahlil-Baiti

Wasu Ma’abota addini sun yi Imani kan cewa dukanin zunubi na gogewa tareda Albarkacin soyayyar Ahlil-Baiti, wai kuma zunuban Masoya Ahlil-Baiti baya cutar da su a ranar lahira [51] a cewar Ali Nusairi daya daga cikin Masu bincike a Hauza Ilmiyya, yawancin Masu halasta haramun basu da zurfin Ilmi jingina da Hadisai misalin [52] (Soyayyar Ali wani kyakkyawan aiki da babu wani zunubi da zai cutar da ita, Kiyayyar Ali zunubi ne da matukar yana na to babu wani kyakkyawan aiki da zai amfanar) [53] Muhakkik Bahrani wanda ya rayu tsakanin shekara 1070-1125 ya tafi kan cewa wannan Hadisi ne da ya kai matsayin Istifaza [54] Nasiri, “Ebahegeri, Afatu Dindari”, shafi na 12 anmma wasu Malaman Shi’a sun bawa wannan hadisi wata ma’ana ta daban wacce bata dacewa da ra’ayi da tunanin masu halasta haramun alal misali Shaik Mufid daya daga cikin Masana Kalam na Shi’a ya kawo fuska ma’ana cewa mutane masu aikata zunubi da suke da soyayyar Ahlil-Baiti za a musu azaba a iya Barzahu domin a tsarkake su daga zunubansu ranar lahira su samu kbuta daga wutar Jahannama [55] a ra’ayi wasu ba’ari Masu bincike iya zunuban da suka aikata a halin gafala ne za a yafe musu albarkacin soyayyar da sukewa Ahlil-Baiti, bawai zunuban da suka aikata da ganganci ba [56] a cewar Nusairi irin wannan tunani an same shi a sauran addinai kuma yana da tarihi a addinin Muslunci, wasu ba’ari Firkoki misalin Murji’a da Karamiyya daga bangaren Ahlus-sunna da kuma Gullatu daga Shi’a suna Akidu kwatankwacin na Masu Halasta haram saboda soyayyar Ahlil-Baiti [57] wannan Malami ya tafi kan cewa Akidar halasta haramun ta samu ne cikin wurin wasu sakamakon rashin waiwayen fatawowin Malaman addini [58], Jawadi Muhaddisi, ya tafi kan cewa da’awar son Ahli-Baiti tareda aikata ayyukan sabo ba a zama wuri guda, hakika soyayya ta gaskiya ana ganinta cikin biyayya [59] cikin Fikhu Arrida (A.S) littafin da ake danganta shi ga Imam Rida (A.S) dangantaka tsakanin aiki nagari da kuma son Ahlil-Baiti dangantaka ce mai bangare biy, saboda haka ba zaka zabi day aka ajiye daya ba [60] kan asasin wata riwaya daga Imam Bakir (A.S) duk wanda yake bin umarnin Allah hakika shi Masoyin Ahlil-Baiti ne kuma duk wanda yake sabawa umarnin Allah hakika shi Makiyin Ahlil-Baiti ne [61] Littafin (Muwaddatu Ahlil-Baiti wa-Fada’ilihim fi-Kitab was-Sunna) talifin Muhammad Takiyu Assayid Yusuf Hakim kan Maudu’in soyayyar Ahlil-Baiti.

Bayanin kula

  1. Bashoy, Hukuk Ahlul Baiti (A) dar tafasir Ahlul-Sunnat, 1434H, shafi na 103.
  2. Muzaffar, Akayed Al-Imamiyyah, 2007, shafi na 72; Mousavi Zanjani, Akayed Al-Imamiyah Al-Ithna Al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181.
  3. Sheikh Saduk, Man La Yahzara Al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 2, shafi na 613.
  4. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 46; Sheikh Saduk, Man La Yahdrah Al-Faqih, 1413 AH, Mujalladi na 4, shafi na 364; Ibn Asaker, Tarikh Damashk, 1415 Hijira, juzu'i na 43, shafi na 241.
  5. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 188.
  6. Allameh Hilli, Minhaj Al-Karamah, 1379, shafi na 122.
  7. Shafi'i, Diwan Al-Imam Al-Shafi'i, Alkahira, shafi na 89.
  8. Fakhlai, Ashinayi Ba-Pishe Mabani wa-Didgahe Mazhab Shi'eh, 2007, shafi na 118.
  9. Fakhlai, Ashinayi Ba-Pishe Mabani wa-Didgahe Mazhab Shi'eh, 2007, shafi na 123
  10. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 16, shafi na 166; Javadi Amoli, Tasnim, 1389 AH, juzu'i na 6, shafi na 51-50.
  11. معنویAmini wa-Digaran, Hamsanji Arzeshe Aklaki Ettihad wa-Ulfat Ba-Muwaddat Zil-Kurba wa'tasire An dar Rushd Ma'anawi, Insan Az Didgahe Kur'an wa-Hadis, shafi na 11
  12. Mohammadi Rayshahri, Farhang Nameh Marsiye Sarayi Sayyid Al-Shohada, 1387, shafi na 11-12.
  13. Akbarian, “Mahabbat Ahlul Baiti (AS) dar Kur’an”, shafi na 42.
  14. Akbarian, “Mahabbat Ahlul Baiti (AS) dar Kur’an”, shafi na 42.
  15. Khademi, “Mahabbat Payambar wa-Ahlul-Baiti Az Didgahe Kur’ani da hadisai”, shafi na 25.
  16. Khademi, “Mahabbat Payambar wa-Ahlul-Baiti Az Didgahe Kur’ani da hadisai”, shafi na 26
  17. Bashoy, Hukuk Ahlul Baiti (a.s.) dar Tafasir Ahlul-Sunnat, 1434H, shafi na 103.
  18. Fakhlai,Ashinayi Ba-Pishine Mabani wa-Didgahe Mazhab Shi'eh, 2007, shafi na 119
  19. Taskhiri, Wahdat Islami Bar Paye Marja'iyyat Ilmi Ahlul Baiti (A), 2008, shafi na 92.
  20. Muzaffar, Akayed Al-Imamiyyah, 2007, shafi na 72; Mousavi Zanjani, Akayed Al-Imamiya Al-Ithna Al-Ashriya, 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 181; Tijjani, Fas'alu Ahlul-Dhikr, 1427 Hijira, shafi na 237
  21. Dhahabi, Al-Muntaka Min Minhaj Al-Etidal, 1413 AH, shafi 451-452
  22. Fakhr Razi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 27, shafi na 595
  23. یا أهلَ بیتِ رسولِ الله حُبُّکُم فَرضٌ مِنَ الله فِی القرآنِ أنزَلَه
  24. Shafi'i, Diwan Al-Imam Al-Shafi'i, Alkahira, shafi na 121
  25. Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 18, shafi na 46-47.
  26. Muzaffar, Akayed Al-Imamiyyah, 2007, shafi na 73.
  27. <a class="external text" href="https://farsi.khamenei.ir/speech-content?id=8513">«بیانات در دیدار با جمعی از طلاب و روحانیون»</a>
  28. Muzaffar, Akayed Al-Imamiyyah, 2007, shafi na 73.
  29. Rabbani Gulfaigani <a class="external text" href="https://www.eshia.ir/feqh/archive/text/rabani/morajeat/94/950201/">«درس امامت»</a>
  30. Mohaddisi, “Rahaye Ijad Mahabbat Ahlil-BAiti dar Nojawanan wa-Jawanan” shafi na 11.
  31. Hashemi da sauransu, “Karkardahaye Tarbiyati Muwaddat Ahlul Baiti (AS)”, shafi na 22.
  32. Hashemi da sauransu, “Karkardahaye Tarbiyati Muwaddat Ahlul Baiti (AS)”, shafi na 23
  33. Amini wa-Digaran, Hamsanji Arzeshe Aklaki wa-Ulfat Ba-Muwaddat Zil-Kurba wa-Tasiri An dar Rushd Ma'anawi Insan Az Didgahe Kur'an wa-Hadis.
  34. Isbahani, Tarikh Isbahan, 1410 AH, juzu'i na 2, shafi 134; Hasakani, Shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 205.
  35. Sheikh Saduk, Khesal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 360.
  36. Thaalbi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422 AH, Juzu'i na 8, shafi na 314.
  37. Barki, Al-Mahasen, 1371, juzu'i na 1, shafi na 61.
  38. Khazaz Razi, Kefaiya Al-Athar, 1401 AH, shafi na 300.
  39. Safar, Basair Al-Derajat, 1404H, shafi na 364.
  40. Sheikh Mofid, Al-Ehtasas, 1413H, shafi na 86.
  41. Ibn Ash'ath, Ash'athyat, Maktaba Al-Ninawi, shafi na 182.
  42. Sheikh Tusi, Amali, 1414H, shafi na 164.
  43. Hitmi, Al-Sawa’iq al-Muhraka, 1417 Hijira, juzu’i na 2, shafi na 447.
  44. Sheikh Sadouq, Khesal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 515.
  45. Qummi, Tafsirin Qummi, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi.372
  46. Barkhi, Mahasen, 1371, juzu'i na 1, shafi na 61.
  47. Qummi, Tafsirin Qummi, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 172.
  48. Sheikh Mufid, Amali, 1413 AH, shafi na 334
  49. Qutbuddin Ravandi, Al-Khara'ij wa-Al-Jara'ih, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 178.
  50. Barki, Mahasen, 1371, juzu'i na 1, shafi na 138.
  51. Nasiri, “Ebahegeri, Afatu Dindari”, shafi na 12.
  52. Sheikh Mufid, Awa'il al-Makalat, 1413 AH, shafi na 335; Ibnshahr Ashub, al-Manakib, 1379H, juzu'i na 3, shafi na 197.
  53. Nasiri, “Ebahegeri, Afatu Dindari”, shafi na 12
  54. Mohagheq Bahrani, Al-Arboun, 1417 AH, shafi na 105.
  55. Sheikh Mufid, Awa'il Al-Makalat, 1413 AH, shafi na 75-76.
  56. Tarkashund, "Mahabbat Ahlul Baiti" wa-Rastegari, shafi na 24.
  57. Nasiri, “Ebahegeri, Afatu Dindari”, shafi na
  58. Nasiri, “Ebahegeri, Afatu Dindari”, shafi na 14
  59. Mohaddisi, “Rahaye Ijadi Mahabbat Ahlul Baiti dar Nojawanan wa-Jawanan” shafi na 15.
  60. An jingina ga Imam Rida (AS), Fikhul Riza, 1406H, shafi na 339.
  61. Kulaini, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 75.

Nassoshi

  • Ibn Ash'ath, Mohammad bin Mohammad, Ash'athyat, Tehran, Al-Ninavi School, Beta.
  • Ibnshahr Ashub, Muhammad bin Ali, al-Manakib, Kum, Alameh, 1379H.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn al-Hassan, Tarikh Damashk, Bija, Darul Fikr, 1415H.
  • Asbhani, Abu Naim, Tarikh Asbahan, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1410H.
  • Akbarian, Sayyid Muhammad «محبت اهل‌بیت(ع) در قرآن»، A cikin mujallar Reh Toshe, lamba 115, bazara da bazara na 2018.
  • Al-Hakim, Muhammad Taqi Al-Sayyid Yusuf, Hubbu Ahlul Baiti Fi Al-Kitab was-Sunnah, Holland, Al-Fikr al-Islami Foundation, 1424H.
  • Al-Hakim, Muhammad Taqi Al-Sayyid Youssef, Muwaddah Ahlul-Baiti wa-Fada'elihim fi-Al-Kitab wa-sSunnah, Qum, Risala, 1419H.
  • Amini, Siddiqa, da sauransu.«هم‌سنجی ارزش اخلاقی اتحاد و الفت با مودت ذی‌القربی و تأثیر آن در رشد معنوی انسان از دیدگاه قرآن و حدیث»،A cikin mujallar nazarin al'adu da zamantakewa na filin, lamba 11, bazara da bazara na 1401.
  • Barghi, Ahmad bin Muhammad, Al-Mahasen, Kum, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1371.
  • Bashvi, Mohammad Yaqoub, Hukuk Ahlul-Baiti (a.s.) dar Tafasir Ahlul-Sunnat, Qum, Al-Mustafa International Translation and Publishing Center, 1434H.
  • Tkashund, Hassan,"Soyayyar Ahlul Baiti da Ceto" A cikin mujallar al'ada ta Ziarat, lamba 26, Afrilu 1395.
  • Taskhiri, Muhammad Ali, wahdat Islami bar Paye Marja'iyat Ilmi Ahlul-Bait (a.s.), wanda Jalal Mir Aghaei, Tehran, Majalisar Kididdigar Addinin Musulunci ta Duniya, 2008 ya fassara.
  • Tijjani, Muhammad, Fas'alu Ahl-Dhikr, Qum, Cibiyar Al-Baiti (A.S.), 1427H.
  • Thaalbi, Ahmed Ibn Ibrahim, Al-Kashf wa-Al-Bayan Tafsir Kur'ani, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1422H.
  • Jamali, Abdul Reza, Mohabbate Najatbakhsh, Qom, Zamzam Hedayat, 2013.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tasnim, Kum, Israa, 1389 AH.
  • Haskani, Obaidullah bin Ahmad, Shawaheed Al-Tanzil, Tehran, Buga da Buga na Ma'aikatar Shiryar da Musulunci, 1411 Hijira.
  • Khadmi,Ainullah,"Soyayya ga Annabi da Ahlul Baiti ta mahangar Alqur'ani da hadisai",
  • Khamenei, Sayyid Ali,«بیانات در دیدار با جمعی از طلاب و روحانیون»،A shafin yanar gizon ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar shiga: 22 ga Disamba 1388, ranar ziyarta: 6 Maris 1401.
  • Khazaz Razi, Ali bin Muhammad, Kefaiya Al-Athar fi Nass Ali al-Imam al-Athni Eshar, Qom, Bidar, 1401 AH.
  • Zahabi, Shams al-Din, Al-Muntaka Min Minhaj Al-Etidal, Riyadh, Babban Shugaban Hukumar Binciken Kimiyya da Al-Ifta, Da’awah da Al-Arshad, 1413 Hijira.
  • Rabbani Golpayegani, Ali, «درس امامت»، A gidan yanar gizon Makarantar Faqahat, kwanan watan shigarwa: 2 Mayu 1395, ranar ziyarta: 6 Maris 1401.
  • Shafi'i, Muhammad bin Idris, Diwan al-Imam al-Shafi'i, Alkahira, Ibn Sina School.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Al-Khesal, Qum, ofishin yada labaran musulunci, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Man la Yahzara al-Faqih, Qum, Islamic Publications Office, 1413 AH.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Amali, Kum, Darul Taqfa, 1414H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Numan, Al-Amali, Qum, World Hazara Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Nu'man, Al-Ekhtasas, Qum, World Hazara Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Nu'man, Awa'il Makalat fi Mazahib wa-Al-Mukhtarat, Beirut, Dar Al-Mofid, 1413H.
  • Safar, Muhammad bin Hasan, Basa'er al-Darajat fi Fadael Ale-Muhammad (a.s), Kum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, 1404H.
  • Taherzadeh, Ali Asghar, Mabani Nazari wa-Ilmi Hubbi Ahlul Baiti (AS), Isfahan, Lab Al Mizan, 2013.

Tabatabai, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Islamic Publications Office, 1417 AH.

  • Azimifar, Alireza, Alqur'ani wa Mahabbat Ahlul Baiti (a.s), Kum, Faculty of Principle of Religion, 1394.
  • Allameh Hilli, Hassan bin Yusuf, Minhaj al-Karamah, Mashhad, Tasu'a, 1379.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir Al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Fakhlaei, Mohammad Taqi, Ashinayi Ba-PIhineh Mabani Az Didgahe Mazhab Shi'eh, Tehran, gidan buga littattafai na Mashaar, 2007.
  • Qutb al-Din Rawandi, Saeed bin Hebatullah, Al-Kharaij wa Al-Jaraih, Qum, Imam Mahdi Institute (A.J.), 1409H.
  • Qummi, Ali bn Ibrahim, Tafsir Qummi, Kum, Darul Katab, 1404H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Darul-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Muhaddisi, Jawad, «راه‌های ایجاد محبت اهل‌بیت در نوجوانان و جوانان»، A cikin mujallar Farhang Kausar, lamba 29, Agusta 1378
  • Mohagheq Bahrani, Sulaiman Al-Mahhouzi, Al-Arbaun hadis fi-Isbati Imamati Amiril Muminina, Kum, Al-Hughiq, 1417H.
  • Mohammadi Rayshahri, Mohammad, Farhang Nameh Marsiye Sarayi Azadari Sayyid Al-Shohda, Tehran, Mash'ar, 2007.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taki,Pendahaye Imam Sadiƙ Be-Rahjuyane Sadiƙ Nasihar, Qum, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, 1391.
  • An jingina ga Imam Rida, Ali Ibn Musa (AS), Fikhu Al-Reza (AS), Mashhad, Cibiyar Al-Bait (AS), 1406 Hijira.
  • Nusairi.,«اباحه‌گری، آفت دین‌داری» A cikin mujallar nazarin littafi, lamba 40, 2015
  • Hashimi Fatimeh wa-Digaran, «کارکردهای تربیتی مودت اهل‌بیت(ع)»،A cikin mujallar Musulunci ta Tarbiat, lamba ta 37, faduwar 1400.
  • Haitami, Ibn Hajar, Al-Sawa'ik al-Muhrika Ala Ahli Al-Rafaz wa Al-Dalal wa Al-Zindaqah, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1417 AH.