Jump to content

Suratul Insan

Daga wikishia
Suratul Insan
Lambar Sura76
Juzu'i29
Jerantuwa Ta Sauka98
Adadin Ayoyi31
Adadin Kalmomi243
Adadin Haruffa1089
Makkiya/MadaniyyaMadaniyya


Suratu Insan (Larabci: سورة الإنسان) ko kuma Hal-Ata ko Dahri sura ce ta 76 a cikin jerin surori, sannan tana daga cikin surori da suka sauka a Madina da take juzu'i na 29, suratu Insan tana kunshe da sakon halitta da shiriyar mutum, siffofin Rabautattu da ni'imomin da Allah ya yi musu da kuma muhimmancin Kur'ani da mashi'ar ubangiji. A mahangar Malaman Tafsiri na Shi'a da wasu ba'arin Ahlus-sunna sun bayyana cewa aya ta takwas cikin wannan sura wacce aka fi sani da Ayar Iɗ'am ta sauka ne kan sha'anin Hazrat Ali (A.S) da Fatima (S) da Hassan da Husaini (A.S) da hadimarsu Fidda, sun yi bakance da daukar Azumi tsawon kwanaki uku tare da cewa suna cikin yunwa sai suka sadakar da abincin buda bakinsu ga Mabukaci da Maraya da kuma Fursunan yaki. Daga ladan karatun wannan sura akwai kasancewa tare da Annabi (S.A.W) a ranar lahira.

Gabtarwa

  • Dalilin Sanya Mata Wannan Suna

Wannan sura ta shahara da sunaye kamar haka Insan, Hal-Ata da kuma Dahri,[1] wadannan sunaye sun samu ne sakamakon wadannan kalmomi guda uku duka sun zo cikin aya ta farko[2] haka zalika ana kiranta da sunan suratu Abrar (Rabautattu) saboda wannan Kalmar ta zo cikin aya ta biyar gabanin rabin surar an kawo bayanin halin wadannan mutane (Rabautattu).[3]

  • Mahalli Da Jerantar Sauka

Suratu Insan a tsarin jerantuwar sauka sura ce ta 98 da ta sauka ga Annabi (S.A.W) a tsarin Kur'ani a yanzu tana sura ta saba'in da shida[4] a juzu'i na Ashirin da tara,[5] akwai sabani cikin garin da ta sauka Makka ne ko Madina, amma a fadin Shaik Nasir Makarim Shirazi daya daga cikin Malaman Tafsirin Shi'a ya tafi kan cewa Malaman Tafsiri na shia'a sun yi ittifakin ra'ayi kan cewa baki dayan wannan sura ko kuma ace wani bangare daga ayoyinta suna magana ne kan mukaman Rabautattu da kyawawan ayyukansu a Madina ta sauka,[6] Kurdabi daya daga Malaman Tafsirin Ahlus-sunna malamin karni na takwas shima ya tafi kan cewa Mashhurin Malaman Ahlus-sunna sun tafi kan cewa ta sauka ne a Madina[7] amma tare da haka wasu bangare daga Malaman tafsirin Ahlus-sunna sun tafi kan cewa a Makka ta sauka wasu kuma sunce aya ta farko a Makka[8] ta sauka sauran ayoyin kuma a Madina.[9]

  • Adadin Ayoyi Da Wasu Siffofi

Suratul Insan tana da aya 31 kalmomi 234 haruffa 1089, bisa la'akari da girma ana kirga cikin surori Mufassilat (matsakaitan surori da aka faifaice bayaninsu da gajeren ayoyi) kuma ana iya snaya cikin kananun surori,[10] ayoyin wannan sura suna cikin ayoyin kur'ani da aka cancada ado da su kan sabon Kabarin Hazrat Abbas (A.S).[11]

Abin da Ta Tattara Akai

Tafsir Namuneh ya kasa abin da ta kunsa zuwa abubuwa biyar da mihwari:

  • Halittar mutum, fara halittarsa daga maniyi, shiriya yanci da irada,
  • Ladan mutanen kirki da Rabautattu wanda yake Magana kan Ahlil-baiti (A.S).
  • Siffofin mutanen kirki da take zama sababin samun lada daga Allah.
  • Muhimmancin Kur'ani, hanyar zartar da hukuncinsa da kuma hanyar daukaka da gina kai.
  • Hakimancin mashi'a da abin da Allah yake so.
  • Ni'imomin Aljanna, Malam Alusi Mufassiri daga Ahlus-sunna ya nakalto cewa kasancewar wannan surar ta sauka ne kan sha'ani da kuma falalar mutane biyar daga iyalan Annabi (S.A.W) Fatima Zahra (S.A) day ace daga cikinsu wacce saboda da girmama ta ne ba a amabci sunan Matan Aljanna ba
    "Domin kiyaye alfarma Batul sanyin idaniyar Manzon Allah (S.A.W)
  • Domin kiyaye alfarma Batul sanyin idaniyar Manzon Allah (S.A.W)[12]

Nukɗoɗin Tafsiri

Siffofin Masu Kyawawan Ayyuka

Asalin Kasida: Abrar

A cikin Suratul Insan (a cikin ayoyi 7-11), an bayyana siffofi biyar na masu kyautatawa (Abrar): 1 Suna cika alkawarin da suka yi. 2 Suna tsoron ranar da azaba da wahala za su mamaye. 3 Duk da cewa suna bukatar abincinsu, suna ba da shi ga matalauta, marayu, da fursunoni. 4 Suna yin wannan aiki ne don yardar Allah kawai, ba sa tsammanin lada ko godiya daga kowa. 5 A ranar da take cike da bakin ciki da tsanani (wato ranar kiyama), suna tsoron Ubangijinsu.[14]

Rashin Ishara Zuwa Ga Hurul Ini A Cikin Wannan Sura

Allama Taba'taba'i shima cikin tafsiri Almizan ya yi Magana kan wannan nukta cewa ba a kawo sunan Hurul Ini[15](mata masu dara-daran idanu) ba wanda suke daya daga muhimman ni'imomin Aljanna, da wannan zamu iya fahimtar cewa suma mata suna daga Rabautattu da ayar ta sauka kan sha'aninsu.[16]

Shahararriyar Aya

Ayar Iɗ'am

Tushen Kasida: Ayar Iɗ'am
Allon kyakkyawan zanen rubutun hannu na Ayar It'am
وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَى حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا»

suna ciyar da abinci tare da bukatarsa mabukaci maraya da fursunan yaki, aya 8 aya ta takwas cikin suratul Insan tare da ayoyin da suke gabaninta da bayanta ana kiransu da ayar ciyarwa[17] a fadin Ayatullahi Nasir Makarim Shirazi Malamai sun yi ittifaki kan wannan aya tare da aya ta sha takwas daga wannan sura ko kuma ace baki dayan ayoyin sun sauka ne kan daukar azumi kwanaki uku da Ali (A.S) da Fatima (S) da Hassan da Husaini (A.S) da Fidda mai musu hidima.[18] An nakalto cewa tare da kasancewa suna cikin yunwa amma suka yi sadakar abincin buda bakinsu ga Mabukaci da Maraya da Fursunan yaki,[19] akwai tarin riwayoyi da suke nuni kan sha'anin saukar wannan aya[20] Ayatullahi Nasir Mukarim Shirazi tare da ishara da riwayar Ibn Abbas dangane da sha'ani da falalar Ahlil-baiti (A.S) an nakalto daga marawaita daidai har guda talatin da hudu daga marawaitan Ahlus-sunna wanda Allama Amini ya tattaro su cikin littafin Alghadir[21] wadannan riwayoyi sun kai darajar Mashur kai sun kai ma darajar tawatiri a wurin Ahlsu-sunna.[22]

Ayar Tsarkakakken Abin sha

«وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا» (آیه ۲۱)

(Aya Ta 21)

Tarjama: Kuma ubangijinsu ya shayar da su tsarkakakken abin sha!

Mawallafin tafsirin Almizan ya bayyana sharaban dahura a matsayin tsarkaka daga dukkanin nau'in kazanta da rashin tsafta, daga cikin kazantar gafala da haramci da nisantuwa daga lurar ubangiji matsarkaki tare da shan wannan tsarkakakken abin sha da zai zamana babu wani hijabi da ya rage tsakanin Rabautattu da ubangijinsu, kamar yanda ya zo cikin aya ta goma a cikin suratu Yunus da yake cewa gameda su:

وَآخِرُ دَعْوَاهُمْ أَنِ الْحَمْدُ لِله رَبِّ الْعَالَمِينَ

Karshen kiran rabautattu a cikin Aljanna shi ne dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin Talikai. Allama Taba'taba'i cikin littafinsa Almizan ya tafi kan cewa jumlar

وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا

Allah ya cire tsani da wasida shi ne da kansa kai tsaye ya shayar da su, wannan wata falala ce da daraja da ni'ima da yan aljana ke samunta, hakika ya saka tsammani cewa wannan baiwa ta yan aljanna ita ke gasgata Karin ni'imomin da ke wurin Allah da ya zo cikin aya 35 cikin suratu Kafu da Allah yake cewa:

لَهُمْ مَا يَشَاءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ

`Yan Aljanna suna da dukkanin abin da suke so a cikinta mu kuma muna da kari kan haka,[23]

Hakim Sabzawari ya bayyana kofi (giya) na masu tafiya zuwa ga Allah a cikin rubutunsa na Saki-nama kamar haka:

چو ساغر منزه ز چون و زچند
چو خورشید تابان بر اوج بلند
نباشد صداعش نیارد خمار
کند یاربینش هم از چشم یار

Tarjama: Kamar kofi mai tsabta daga duk wani abu Kamar rana mai haske a saman kololuwa Ba zai kawo ciwon kai ba, ba zai kawo maye ba Yana ganin Ubangiji daga idon masoyi[24]


Ayoyin Hukunce-hukunce

Aya ta bakwai cikin suratu Insan ana kirga cikin ayoyin hukunce-hukunce,[25] wannan aya da take Magana kan cika bakance daya daga cikin siffofin masu kyautata ayyuka da akayi bayaninsu[26] hakika an fa'idanu da wannan aya ta bakwai kan halasci koma ince wajibi cika bakance idan aka kulla shi,[27]

Falala Da Hususiya

Ku duba: Falalolin Surori

Ya zo cikin riwaya ladan karanta suratul Insan Aljanna da Matan Aljanna[28] da kuma zama tare da Annabi (S.A.W) ranar lahira[29] haka ya zo daga Imam Rida (A.S) ya kasance a cikin sallar Asubahi ta ranar litinin da Alhamis yana karanta Fatiha da suratul Insan a raka'a ta farko sannan ya karanta Fatiha da suratul Gashiya a raka'a ta biyu, yana cewa duk wanda yayi haka to ubangiji zai kare shi daga sharri cikin wadannan ranaku.[30] An nakalto wasu hususiya dangane da karanta wannan sura daga akwia cewa idan wani ya lazimci karanta ta idan yana fama da raunin ruhi zai samu karfafar ruhi,[31] sannan karanta ta domin karfafa jijiyoyi da nesantar da rudewa yana da amfani.[32]

Nazari

Kari kan tafsirin cikin littafan tafsirin Kur'ani to an wallafa tafsiri mai cin gashin kansa iya nata kadai misali: Sayyid Jafar Murtada Amili, Tafsiru suratu Hal ata, Bairut, Markaz Islami, 1424 h. Assayid Abbas Karimi Husaini, Auju Insaniyat, Tafsiru Suratu Insan, Qom, Darul Huda, 1383.

Bayanin kula

  1. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, juzu'i na 25, shafi na 327.
  2. Tafsir Namuneh, juzu'i na 25, shafi na 327
  3. Khorramshahi, Daneshnameh Qur'an, Qur'an Pajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi 1260
  4. Marafet, Amuzeshi ulumin kur’an, 1371, juzu’i na 1, shafi na 168.
  5. Khorramshahi, Daneshnameh Qur'an, Qur'an Pajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi 1260
  6. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 25, shafi na 328
  7. Qurtubi, Al-Jamael Ahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 19, shafi na 117.
  8. Thaalbi, Al-Kashf da Al-Bayan, 1422 AH, Mujalladi na 10, shafi na 92; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 30, shafi na 739.
  9. Tabarani, Al-Tafsir al-Kabir; Tafsirin al-Qur'an al-Azeem, 2008, juzu'i na 6, shafi.398.
  10. Khorramshahi, Daneshnameh Qur'an, Qur'an Pajuhi, 1377, juzu'i na 2, shafi 1260
  11. «امشب قرص قمر در کربلا طعنه به خورشید می‌زند»، سایت خبری فردا، تاریخ بازدید ۲۱ شهریور ۱۳۹۵ش.
  12. Khamegar, Mohammad, Saktare Surahaye Kur'an Kareem, wanda Cibiyar Al'adu ta Kur'ani da Atrat Noor al-Saqlain, Qum, Nashra Publishing House, Ch1, 1392 suka shirya.
  13. Khamagar, Muhammad, Sakhtar-i suraha-yi Qur'an-i karim, Mu'assisa-yi Farhangi-yi Qur'an wa 'Itrat-i Nur al-Thaqalayn, Qom: Nashra, ed.1, 1392 Sh.
  14. Makarim Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371 kalandar Farisa, Juz 25 shafi na 351-355
  15. Alousi, Tafsirin Rooh al-Ma'ani, juzu'i na 15, shafi na 170-174.
  16. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 25, shafi na 351-355.
  17. Duba: Rouhani Nia, Forough Ghadir, 2006, shafi na 146; Ansari, Ahlul Baiti, amincin Allah ya tabbata a gare shi, Majmaal al-Fikr, shafi na 173. Mazaheri, Zindagi caharda Ma'asum, Alaihimu Salam, 1378, shafi na 56; Deilmi, Ershad al-Qulob, Tehran, juzu'i na 2, shafi na 136; Bashoy, “Matsayin Ahlul Baiti (AS) a cikin suratu Dahr az Digahe Fariqaini” shafi na 68; "Imam Ali (A.S) a cikin tambayoyin Alqur'ani", shafi na 108.
  18. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 25, shafi na 345.
  19. Zamakhshari, al-Kashaf, 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 670; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 30, shafi na 746; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi.612; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 25, shafi na 343.
  20. Duba: Tabarsi, Majmam al-Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 611 da 612.
  21. Duba: Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 3, shafi na 155-161.
  22. Makarem Shirazi, Tafsir al-Namuneh, 1371, juzu'i na 25, shafi na 345.
  23. Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 20, shafi na 130 da 131.
  24. Sabzawari Diwan Ash'ar, Saki Nameh
  25. Sabzevari, Divan Ash'ar, Saqi Namah
  26. Irvani, Darus Tahmidiyeh, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 451.
  27. Makarem Shirazi, Tafsir Namoneh, 1371, juzu'i na 25, shafi.351.
  28. Irvani, Darus Tahmidiyeh, 1423 AH, Juzu'i na 1, shafi na 451.
  29. Tabarsi, Majma Al Bayan, 1372, juzu'i na 10, shafi na 206.
  30. Sheikh Sadouq, Sawabul A-mal wa-Ikabul A-mal, 1406 Hijira, shafi na 121.
  31. Sheikh Sadouq, Man La Yahdara al-Faqih, Jamia Modaresin Publications, Mujalladi na 1, shafi na 307-308.
  32. Bahrani, al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 543.

Nassoshi

  • Tauzihatul Alkur'ani mai girma, Muhammad Mehdi Foladvand, Tehran: Darul Kur'an al-Karim, 1418H/1376H.
  • Alqur'ani mai girma, Tarjama, Tauzihatu Wajeh Nameh: Bahauddin Khorramshahi, Tehran: Jami, Nilofar, 1376.

"Imam Ali (a.s.) Dar Fursashehaye Qur'ani", Mujallar Farhang Kausar, lamba ta 48, Maris 1379.

  • Irvani, Baqir, Darus Tahamidiyyah fi Tafsiri Ayat al-Ahkam, Kum, Darul Fiqh, 1423H.
  • Ansari, Muhammad Ali (Khalifa Shushtri), Ahl al-Bait (amincin Allah ya tabbata a gare su): Imamatham Hayatham, Kum, Majmael al-Fikr al-Islami, Bita.
  • Bahrani Sayyid Hashim Alburhan Fi Tafsiril Al-kur'an, Bincike: Sashen Nazarin Addinin Musulunci, Cibiyar Al-Ba'ath, Qom, Tehran, Asalin Buga, 1416H.
  • Bashoi, Mohammad Yaqub, "Matsayin Ahlul Baiti (A.S) a cikin suratu Al-Dahr az Didgahe Farikaini", Journal of Hikmat and Islamic Falsafa, No. 19, Fall 2006.
  • Thaalbi, Ahmad bin Muhammad, Al-Kashf da Al-Bayan (Tafseer al-Thalabi), Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, bugu na farko, 1422H.
  • Khamegar, Muhammad, Saktare surahaye Kur'ani mai girma, wanda Cibiyar Al'adu ta Kur'ani da Atrat Noor al-Saqlain, Qum, Nashra Publishing House, Ch1, 1392 suka shirya.
  • Khorramshahi, Bahauddin, Encyclopedia of Quran and Quran Studies, Tehran: Dostane-Nahid, 1377.
  • Deilmi, Hossein bin Mohammad, [[Arshad al-Qulub], gabatarwar Shahabuddin Marashi, wanda Hedayatullah Mostarhami ya fassara, Tehran, Bouzar Jamehari Mostafavi kantin sayar da littattafai, Beta.
  • Rouhani Nia, Abdur Rahim, Forough Ghadir, Qom Mashoor, 2006.
  • Zamakhshari, Jarallah, Al-Kashaf Ghuwamaz al-Tanzil da Ayun al-Aghawil, Qum: Al-Balagheh Publishing House, 1415H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Thawab al-Amal da Aaqab al-Amal, Qom, Dar al-Sharif al-Razi, bugu na biyu, 1406H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Laihzara al-Faqih, Kum, Jamia Modaresin Publications, bugu na biyu, beta.
  • Tabarani, Sulaiman bin Ahmad, Al-Tafsir al-Kabir; Tafsir al-Qur'an al-Azeem, Jordan-Irbad, Dar al-Kitab Al-Thaqafi, bugun farko, 2008.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, bincike da gabatarwa na Mohammad Javad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow Publications, bugu na uku, 1372.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir (Mufatih al-Ghaib), Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
  • Qurtubi, Muhammad bin Muhammad, Al-Jame Lahkam Al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow, bugun farko, 1364.
  • Mazaheri, Hossein, Zindagi ceaharda Masum, Alaihimu Salam, tare da sharhin Vali Fatemi, Tehran, Payam Azadi, 1378.
  • Marafet, Mohammad Hadi, Koyarwar Ilmin Alqur'ani, Qum, Cibiyar Buga Cibiyar Yaɗa Addinin Musulunci, bugun farko, 1371.
  • Makaram Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugun na 10, 1371.