Jump to content

Saudatu Ƴar Imaratu Alhamdaniyatu

Daga wikishia
Saudatu Hamdaniya
Cikakken SunaSaudatu Ƴar Amaratu Bin Ashtar
LaƙabiHamdaniya, Yamaniya
Mahallin RayuwaKufa. Madina
Daga SahabbaiNa Imam Ali (A.S)
AyyukaHalartar yakin siffin, rera wa ƙo ƙin goyan bayan Imam (A.S).


Saudatu yar Amara Alhamdaniyatu (Larabci: سودة بنت عمارة الهمدانية) Wata mata ce wadda take cikin magoya bayan Imam Ali (A.S), kuma ta kasance ɗaya daga cikin mawaƙa na Shi'a kuma ta kasance tare da Imam Ali (A.S) a filin yaƙin Siffin,ta rubuta ƙasida kan taimakawa da ƙarfafar sojojin Imam Ali (A.S) kazalika bayan shahadar Imam Ali (A.S) ta haɗu da Mu'awiya domin shigar da ƙorafinta kan Busru ɗan Arɗa daya daga cikin ƴan kanzagin Umayyawa, kuma a wannan haɗuwarma sai da ta rera waƙa kan yabon Imam Ali (A.S), wasu suna ganin cewa lokacin da Suwaida ta bayyana soyayyarta ga Imam Ali (A.S) a yayin da ta haɗu da Mu'awiya dalili ne kan kyakkyawan tarihinta da kasantuwarta mutuniyar kirki da ta tabbata kan Wilayar Imam Ali (A.S).

Wani Ɓangare Daga Tarihinta

Sawaida Al-hamdaniya (Ta rasu a ƙarni na farko bayan hijira),[1] ta kasance ƴarshi'a kuma mai goyan bayan Imam Ali (A.S)[2] kuma an ce tana ɗaya daga cikin shahararrun mata ƴan ƙabilar Hamadan.[3] Kuma an anbaci suna dayawa ga mahaifinta kamar Imara ɗan Ashtar[4] ko Amar ɗan Al'asak[5] ko Imara ɗan Asad.[6] kuma bayan laƙabi na Hamadaniya.[7] Anayi mata laƙabi da Al-Hamadaniyya.[8] Sai dai litattafai na tarihi ba su kawo shekara da aka haifeta ba da kuma shekarar da ta yi wafati.[9]

An san Suwaida Al-Hamdaniya a matsayin mawaƙiya,[10] kuma mai rawaito hadisi sannan marubuciya[11] Wasu suna ganin cewa ta kasance ɗaya daga cikin mawaƙan Larabawa mawaƙa, kuma kalamanta sun kasance masu hazaka da balaga.[12] Kamar yadda Nahla Al-Garwi Alna'ini ya zo da shi a cikin littafin Muhadasat shi'a, Suwaida ta nakalto hadisi daga Imam Ali (A.S), kuma maruwaita irin su Muhammad ɗan Ubaida Allah da Amir Al-Shabi su ma sun ruwaito daga gare ta.[13]

Rera Waƙarta Domin Taimakon Imam Ali (A.S) A Yaƙin Siffin

Suwaida, tare da Jarwa ƴar Murra Attamimiyya, da Ummu Sinan, da Zarƙa'u ƴar Adiyyu Al-Hamdanyya, da Ummul Kair ƴar Harish Al-Barƙiyya, na daga cikin matan Kufan da suka halarci da kuma goyan bayan Imam Ali (A.S) a yakin Siffin[14] kuma ta shirya waƙa da baitika domin taimakon Imam Ali (A.S) a yaƙin siffin.[15] Wasu suna ganin wannan ƙasida ta shahara,[16] kuma ita Suwaida a wannan ƙasida ta ta bayan kare Imam Ali (A.S)[17] da ta yi kuma ta yi nuni da falalolinshi ta ƙarfafi sojojin shi kan sojojin ƙasar Sham.[18] sabo da haka ake ganinta a matsayin mace jarima,[19] mai yin gwagwarmaya da harshanta wato maganarta[20]

Daga cikin abin da waƙarta ta ƙunsa akwai nemawa Imam Ali (A.S) taimako a matsayin shi na ɗan uwan Annabi kuma mai ɗauke da tutar shiriya.

شمّر كفعل أبيك يا ابن عمارة
يوم الطّعان و ملتقى الأقران
و انصر عليا و الحسين و رهطه
و اقصد لهند و ابنها بهوان
إنّ الإمام أخو النّبي محمّد
علم الهدي و منارة الإيمان
فقَدِّ الجيوشَ و سِرْ أمام لوائه
قدما بأبيض صارم و سنان

Tarjama: Ka ja ɗamara ya ɗan Amara kamar dai yadda mahaifika A ranar yaki da gamuwar abokan gaba Ka taimaka wa Ali da Husaini da mutanensa Ka fuskanci Hind da ɗanta da ƙyama Lallai Imam yana ɗan uwan Annabi Muhammad Shi ne jagoran shiriya kuma hasken imani Ka jagoranci mayaƙa, ka tafi gaba da tutarsa ka yi gaba da takobi mai kaifi gayawa jini na wuce da mashi mai tsini.[21]


Nuna Soyayyarta Ga Imam Ali (A.S) Domin Asan Ba Ta Tare da Mu'awiya

Bisa abin da ya zo a litattafai na tarihi Suwaida ta haɗu da Ma'awiya domin ta gabatar da kokenta a kan ɗaya daga cikin yaran Mu'awiya wanda ake kira da Busru ɗan Arɗa'a,[22] a yayin wannan haɗuwa ne Mu'awiya ya tina mata wata ƙasidar ta wace ta rubuta kan yiwa Mu'ayiwa zanbo da sojojin Sham a wajan yaƙin siffin [Tsokaci 1] Mu'awiya ya zargi Suwaida da taimakon Imam Ali (A.S) da kuma harziƙa sojojin Imm Ali (A.S) kan sojojinsa, sai Suwaida sai ta kada baki ta ce son Imam Ali da bin shi gaskiya ce kuma hakan shi ne sanadiyar yin ƙasidar ta.[23]

Sannan Suwaida ta zayyanu wasu daga cikin cin mutunci da Busru ya yiwa mutane kuma ta nemi Mu'awiya ya sauƙe shi daga kan muƙaminshi, ya mayar da haƙƙi ga masu shi, sai dai cewa daga farko Mu'awiya bai yarda da hakan ba, kai sai dama ya yi mata barazana, nanfa Saudatu ta rera waƙa kan Imam Ali (A. S), kuma ta anbaci abin da Imam Ali (A.S) ya yi na sauke ɗaya daga cikin gwamnoninshi sakamakon ƙorafi da ya samu daga gare ta, bayan ya yi mata barazana kamar yadda ya gabata, Mu'awiya ya jinjina irin wannan jarimta ta Saudatu da abin da Imam Ali (A.S) ya gina a cikin zukatan mabiyanshi, to nan ne Mu'awiya ya umarci da a mayar da dukiya ga masu ita.[24]

Ana ɗaukar waƙar da Sauda ta yi a gaban Mu'awiya kan Imam Ali (A.S) a matsayin ɗaya daga cikin sananniyar waƙa a gurin ƴanshi'ar Kufa a ƙarni na biyu bayan hijirar Annabi (S.A.W).[25]

صلّى الإله على جسم تضمّنه
قبر فأصبح فيه العدل مدفونا
قد حالف الحقّ لا يبغي به بدلا
فصار بالحقّ و الإيمان مقرونا

Tarjama: Saboda haka, adalci ya zama a cikin kabarin an binne shi Ya kasance tare da gaskiya, ba ya neman wani sauyi Saboda haka, an haɗa shi da gaskiya da imani.[26]

Ana la'akari da wannan ƙasidar da Sauda ta yi a lokacin da ta haɗu da Mu'awiya a matsayin kyakyawan tarihinta.[27] Da kuma tabbatar ta kan wilayar Imam Ali (A.S).[28]

Bayanin kula

  1. markaz mudiriyat hauzat ilimiyya nisa'iyya, Nisa Alimat wa asarahunna, 1379, shafi na 25.
  2. Hassoun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520; Al-Tastri, At-tabyin fi Ashab Imam Amirul Muminin (a.s.) wa ruwat anhu, 1430, Mujalladi na 1, shafi na 541.
  3. Malik Lo, "Souda Hamadani", 2017, shafi na 108.
  4. Al-Amini, Ashab Amirul Muminin (a.s.)wa al-Rawat anhu, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 670; Hassun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520.
  5. Shushtri, Qamoos al-Rajal, 1410 AH, juzu'i na 12, Al-Qab al-Mansobah, shafi na 284; Al-Amin, Ayan Shi'a, 1403H, juzu'i na 7, shafi na 324.
  6. Mahalati, Riyahin al-Sharia, Tehran, juzu'i na 4, shafi na 354.
  7. Al-Amini, Ashab Amirul Muminin (A.S) wa ruwat Anhu. 1412 Hijira, Mujalladi na 2, shafi na 670; Hassun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520.
  8. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415, juzu'i na 42, shafi na 587.
  9. Duba: Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 587; Ibn Atham, al-Futuh, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 59-61.
  10. Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415, juzu'i na 42, shafi na 587.
  11. Markaz mudiriyat hauzat ilimiyya nisa'iyya, Ma'awanatu buhus nisa'i alimat wa asarahunna , , shafi na .
  12. Hassoun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520; Al-Amini, Ashab Amirul Muminina (a.s.) wa al-Rawat anhu, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 670.
  13. Al-Gharavi Al-Naini, Muhadasat Shi'a, 1375, shafi na 222.
  14. Al-Aqd al-Farid, Dar al-Kutub Al-Elamiya, juzu'i na 1, shafi na 347.
  15. Ayine Vand, Adabiyat siyasi Tashayyu, 2017, shafi 50.
  16. Al-Qami, Tarikh Qum, 1385, shafi na 474
  17. Ayine Vand, Adabiyat siyasi Tashayyu, 2017, shafi 50.
  18. Al-Amini, Ashab Amirul Muminin (a.s.) al-Rawat anhu, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 670; Shabestri, At-tabyin Ashab Imam Amirul Muminin (a.s.) wa Al-Rawat Anhu, 1430H, Mujalladi na 1, shafi na 541; Ayine Vand, Adabiyat siyasi tashayyu, 2017, shafi 50.
  19. Gharvi Naini, Muhadasat Shia, 1375, shafi na 220; Arfa, "Hamiyan Velayat, RasaBanuwan Shi'a dar hemayat Velayat", shafi na 12.
  20. Hassun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520.
  21. Al-Dhabi, Akhbar al-Wafdat, 1403 AH, shafi na 67; Ibn Tafur, Balagat al-Nisa, shafi na 47.
  22. Ibn Atham, al-Futuh, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 59-61; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415, juzu'i na 42, shafi na 587.
  23. Ibn Atham, al-Futuh, juzu'i na 3, shafi na 60; Al-Dhabi, Akhbar al-Wafdat, 1403 AH, shafi na 67-70; Ibn Tifur, Balaghat al-Nisa, Kum, shafi na 47-49; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 587; Hassun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520.
  24. Ibn Atham, al-Futuh, juzu'i na 3, shafi na 60; Zabi, Akhbar al-Wafdat, 1403 AH, shafi na 67-70; Ibn Tifur, Balaghat al-Nisa, Kum, shafi na 47-49; Ibn Asaker, Tarikh Madinati Damashk, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 587; Hassun, Aalam al-Nisa al-Mominat, 1421 AH, shafi 520.
  25. Malek Lo, "Souda Hamedani", 2017, shafi na 108.
  26. Akhbar al-Wafdat, 1403 AH, shafi na 69; Ibn Tifur, Balagat al-Nisa, Kum, shafi na 48.
  27. Namazi Al-Shahrudi, Mustardakat Alam Rijal al-Hadith, 1414H, juzu'i na 8, shafi na 582.
  28. Mahalati, Riyahin al-Sharia, Tehran, juzu'i na 4, shafi na 354; Al-Gharavi Al-Naini, Muhaddsat Shi'a, 1375, shafi na 220.

Tsokaci

  1. ba'arin masu nazari suna ganin dalilin da ya sanya mu'awiya rike wannan kasida a zuciyar shi ne kasancewa banu hamdan suna rera wannan wak,a a lokacin yakin siffin

Nassoshi

  • Ayinvand, Sadiq, Mujam Ash-shu'ara'il Al-arab, Tehran, Nashar Alam, 1387H.
  • Ibn A’tham al-Kufi, Ahmad, Kitab al-Futuh, bugun Ali Shiri, Beirut, Darul-Adwaa, 1411H.
  • Ibn Tayfour, Muhammad bin Abi Tahir, Balagat nisa, Kum, Al-Sharif Al-Radi, D.T.
  • Ibn Abd Rabbo, Ahmed bin Muhammad, Al-akdul Al-farid, Edited by Abdul Majid Tarhini, Mufid Muhammad Qamiha, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, 1407 AH.
  • Ibn Asakir, Ali bin Al-Hassan, Tarikh Madinati Damashk, Beirut, Darul Fikr. 1415 AH.
  • Arfaa, Fatima Sadat, “Hamian welayet;” Rasa banuwan shi'a, der Hamayat Az Velayat," Mujallar Shi'a Banwan, No. 3.
  • Al-Amin, Sayyed Mohsen, A'ayanul Shi'a, Beirut, Dar Al-Ta'arif Publications, 1403 AH.
  • Al-Amini, Muhammad Hadi,Ashab Amirul Muminin, (A.S) wa Al-rawan anhu, Beirut, Dar Al-Ghadir, 1412H.
  • Al-Hassoun, Muhammad, Annisa'ul Muminat, Tehran, Aswa, bugu na hudu, 1421H.
  • Shabestari, Abdul Hussein, Al-Tabyin fi Ashab Imam Amirul Muminin, (A.S), wa Al-rawat anhu, Qum, na musamman dakin karatu na tarihi, 1430H.
  • Al-Tasturi, Muhammad Taqi, Kamus Rijal, Qum, rukunin malamai a makarantar hauza ta Musulunci da ke birnin Qum, Mu’assasar buga littattafan Musulunci, bugu na biyu, 1410H.
  • Al-Dhabi, Abbas bn Bakkar,Akhbarul wafidat minal nisa'i ala mu'awiya bin abi sufyan, Beirut, Mu'assasa Al-Resala, 1403H.
  • Gharwi Naini, Nahla, Muhaddasat Shi'a, Tehran, Daneshgah, Tarbet Mudarres, 1375H.
  • Al-Qumi, Hassan bin Muhammad, TarikhQum, Muhammad Redha Al-Ansari Al-Qumi, Qum, Laburaren Ayatullahi Al-Marashi, 1385H.
  • Mahalati, Zabihullah, Riyahin al-Shari’ah a fassarar Daneshmandan Banwan Shi’a, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, D.T.
  • Markaz mudiriya hauzat nisa'iyya, mu'awanatu buhus nisa alaimat wa asarahunna, Qum, Seminary na Qom, Cibiyar Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Mata, 1379 St.
  • Malak Law, Siddiqa, “Sawda Hamadani”, Mausu'atu Al-alam islami, juzu’i na 25, Tehran, 1397H.
  • Namazi Al-Shahrudi, Ali, Mustadrakat Ilm Rijal Al-Hadith, Tehran, Ibn Al-Marubuci, 1414H.