Ramadan
| Wata na tara cikin kalandar hijira ƙamari | |
|---|---|
| Bayanai na gaba ɗaya | |
| Wasu sunaye daban | Ramadan Al-Mubarak, Ramadan Al-Mu'azzam |
| Watan da ya gabata | Sha'aban |
| Watan da ya biyo baya | Shawwal |
| Ayyuka da al'adu | Nafilolin watan Ramadan, Itikafi, Raya dararen lailatul ƙadri |
| Cikin al'adu na addini | |
| Addu'o'i | Addu'ar shiga wata Ramadan, gajerun addu'o'i na yau da kullun, Du'a'u Iftitahi, Du'a'u Sahar, Du'a'u Abu Hamza Sumali, Du'a'u Mujir, Du'a'u Al-jaushanul Kabir |
| Hukunce-hukuncen shari'a | Azumin wajibi, duba jinjirin wata, Kaffaratul jam'i, Kaffarar azumi |
| Watanni masu alfarma | Baya ciki |
| Abubuwa da suka faru da munasabobi | Saukar Kur'ani, Yaƙin Badar, Fatahu Makka, Wilaya ta Ahad Imam Rida (A.S), Daren da aka sari Imam Ali (A.S), Mi'irajin Annabi, Ranar Ƙudus |
| Al'adun gargajiya | Raba abincin buɗa baki, Sahur, Girki da kuma kayan zaki na musamman na wannan watan, Sanar da lokacin Sahur |
Ramadan, ko Ramadan Mubarak ma'ana wata na tara cikin jerin watannin hijira ƙamari, wata ne wanda cikinsa aka wajabta yin azumi kan Musulmi, cikin riwayoyin Musulunci an yi bayanin falaloli masu yawan game da wannan wata, kuma wata ne na liyafar Allah, wata ne na rahama da gafara da albarka, haka kuma ana kiransa da bazaran Kur'ani. Bisa abin da ya zo a cikin wasu hadisai, a cikin wannan wata ana buɗe ƙofofin aljanna kuma ana rufe ƙofofin Jahannama. Cikin wannan wata lailatul Ƙadri da saukar Kur'ani suka kasance. Haka kuma wasu daga litattafan sama kamar Attaura da Injila suma an saukar da su a cikin wannan wata. Ramadan shi kaɗai ne watan da sunansa ya zo cikin Kur'ani. Watan Ramadan wata ne da yake da matsayi na musamman da girma da daraja a wurin Musulmi, A wannan wata al'ummar Musulmi suna himmatuwa sosai da ibada. A cikin litattafan addu'a an naƙalto ayyuka da ibada daban-daban. Daga cikin mafi muhimmancin ayyukan wannan wata akwai karatun Kur'ani, raya lailatul ƙadri, addu'a, sallah, istigfari, raba buɗa baki da kuma taimakon mabuƙata.
Daga muhimman abubuwan da suka faru a wannan wata akwai misalin saukar da Kur'ani a lailatul ƙadri da yaƙin Badar, wanda shi ne yaƙi na farko da ya fara faruwa tsakanin Musulmi da mushrikan ƙuraishawa ƙarƙashin kwamandancin Annabi (S.A.W), bugu da ƙari a dai cikin wannan wata ne Imam Ali (A.S) ya yi shahada, wanda ya kasance Imami na farko a wurin ƴanshi'a an shahadantar shi a rana ta 21 Ramadan. Imam Hassan Mujtaba (A.S) shima an haife shi 15 ga wannan wata.
Ibada da ɗaukar azumi wani ɓangare ne daga siffofi da alamomi na Musulmi, a cikin alumomin Musulmi, akwai wasu ladubba da ala'du daban-daban da ake yi a cikin wannan wata kamar shirya walima da taron jama'a, tsaftace masallatai da wuraren addini, da tarukan sulhu, da shirya nau'uka daban-daban na abincin buɗa baki.
Matsayi
Watan Ramadan, shi ne wata na tara cikin jerin watannin hijira ƙamariyya.[1] An wajabta azumi kan Musulmi a wannan wata.[2]
Kur'ani mai girma[3] da wasu litattafan sama kamar suhufu Ibrahim, Injila, Attaura da Zabura an saukar da su ga Annabawa a cikin wannan wata.[4]
Sau ɗaya aka ambaci kalmar Ramadan a cikin Kur'ani[5] Kuma shi kaɗai ne watan da sunansa ya zo a cikin Kur'ani:[6]
"Watan Ramadan shi ne watan da aka saukar da Kur'ani a cikinsa, a matsayin shiriya ga mutane, tare da bayyanannun hujjojin shiriya da kuma ma'aunin rarrabe gaskiya da ƙarya. Don haka duk wanda ya halarci wannan wata daga cikinku, to ya wajaba ya yi azumi a cikinsa. Amma wanda yake da rashin lafiya ko yana tafiya, to ya rama da adadin wasu kwanaki daban."
Haka kuma lailatul ƙadri da saukar da Kur'ani[7] Bisa abin da ya zo a riwayoyi[8] da tafsirai[9] sun faru ne a cikin watan Ramadan[10] Bisa mafi shaharar naƙali, Badar, yaƙi na farko a Muslunci da ya faru tsakanin Musulmai da maƙiyansu ƙarƙashin jagorancin Manzon Allah (S.A.W) da asubar ranar Juma'a 17 ga Ramadan[11] a wani naƙalin kuma an ce ya faru a ranar Litinin 17 ko 19 ga watan Ramadan[12] shekara ta biyu bayan hijira.
Kalmar "Ramadan" a harshen Larabci tana nufin zafin rana.[13] an naƙalto cewa da wannan dalili ne ake kiran wannan wata da suna Ramadan saboda yana ƙone zunubai.[14] Haka kuma cikin madogaran riwayoyi, an bayyana cewa Ramadan ɗaya ne daga cikin sunayen Allah.[15]
Siffofi
Manzon Allah (S.A.W) cikin huɗubar watan Sha'aban ya yi bayanin wasu falaloli da watan Ramadan yake da su, daga cikinsu akwai:
- Cikin wannan wata an gayyaci mutane liyafar Allah.
- A wannan wata ne aka sanya lailatul ƙadri daren da ya fi watanni dubu alheri.
- Raya ko wane dare daga dararen wannan wata da sallah daidai yake da sallah guda sabain a cikin sauran watanni
- Wata ne na haƙuri, kuma aljanna ce ladan haƙuri.
- Wata ne na taimako da tausayawa mabuƙata.
- Wata ne da arziƙin muminai yake ƙaruwa.
Annabi (S.A.W) ya ce: watan Ramadan wata ne da ace za a san darajar da yake tare da ita, da mutum ya yi buri da fatan ace baki ɗayan shekara ta kasance Ramadan.[16] Bisa wata riwaya daga Annabi (S.A.W) yana cewa watan Ramadan, wata ne da ake ƙulle ƙofofin Jahannama kuma ana buɗe ƙofofin Aljanna, kuma wata ne da ake ɗaure shaiɗanu da sasari da sarƙa.[17]
- A zamanin Annabi (S.A.W) an kasance ana kiran da watan Ramadan da sunan Marzuƙ (Azurtacce)[18][Tsokaci 1]
Haka kuma ya zo cikin riwayoyin maasumai cewa watan Ramadan wata ne da aka siffanta shi da watan Allah,[19] watan rahama da afuwar Allah,[20] watan albarka da ninka ladan ayyuka da goge zunubai[21] wata ne da idan har ba a yi wa mutum gafara a cikinsa ba to babu fatan samun gafara gare shi cikinsa sauran watanni.[22]
Ayyuka
Ramadan 1448 Watan Ramadan yana da hukunce-hukunce da ayyuka na musamman; wasu daga cikinsu na gama-gari ne ga dukkan kwanakin watan, wasu kuma an keɓe su ne ga wasu kwanaki na musamman.
Wajabcin Azumi
A cikin watan Ramadan an wajabta yin azumi kan Musulmi[23] Azumi na nufin kaucewa yin wasu ayyuka daga jumla ci da sha tun daga farkon kiran sallar asubahi har zuwa kiran sallar magariba.[24] Umarni kan ɗaukar azumi da kuma bayanin hukunce-hukuncensa ya zo a cikin Kur'ani[25] da litatttafan fiƙihu. Bisa fatawar malaman fiƙihu idan mutum ya zamanto an masa afuwa daga ɗaukar azumi to bai kamata ya fito cikin mutane yana cin abinci ba.[26]
Karanta Addu'a
Karatun addu'o'in Sahar, daga jumla Du'a'ul Baha da Du'a'u Abi Hamza Sumali.[27] Kazalika Du'a'ul Iftitahi cikin dararen wannan wata[28] da Du'a'u Ya Ali Ya Azim, Allahumma Adkhil Ala Ahlil ƙuburis surura da "Allahumma arzuƙni Hajja baitikal harami" bayan sallolin farilla[29] sun kasance daga cikin gama-garin ayyuka a wannan wata.
Karatun Kur'ani
Cikin baarin riwayoyi, an bayyana watan Ramadan da bazaran Kur'ani[30] Hakazalika ladan karanta aya ɗaya a cikin watan Ramadan daidai yake da ladan kammala karatun Kur'ani a cikin sauran watanni.[31] A Wasu ƙasashen Musulunci, Musulmi tun daga farkon wannnan wata har zuwa ƙarshensa a ko wace rana suna karanta juzu'i guda na Kur'ani wanda zuwa ƙarshen watan suna kammala karanta baki ɗayan Kur'ani, wannan khatama da kammala karatun Kur'ani mafi yawan lokutan tana kasancewa ne a masallatai da sauran wuraren addini cikin tsarin adadin wasu jamaa. Haka kuma a ƙasar Iran ana watsa shirin karatun juzu'i tashoshin talajijin da radiyo.[32]
Raya Lailatul Ƙadri

Bisa abin da ya zo a riwayoyi, lailatul ƙadri ya kasance ɗaya daga cikin dararen 19, 21, ko kuma 23 a watan Ramadan.[33] Cikin wasu riwayoyi, an ayyana daren 23 Ramadan matsayin lailatul ƙadri.[34] Shaik Saduƙ ya ce malamanmu sun yi ittifaƙi da cewa daren 23 Ramadan shi ne lailatul ƙadri.[35] A cewar Allama Ɗabaɗaba'i, maganar da ta shahara tsakankanin Ahlus-Sunna daren 27 Ramadan shi ne lailatul ƙadri.[36] Shi'a a ko wace dararen 19, 21 da 23 a wuraren addini ko gidajensu, suna raya waɗannan darare da ibada har zuwa lokacin sahur.[37] Daga cikin mafi alherin ayyuka da ake buƙatar yi cikin lailatul akwai misalin karanta Du'a'ul Jaushanil Kabir da ɗora Kur'ani aka.[38]
Sallolin Mustahabbi
Sallolin Mustahabbi suna daga cikin ayyukan watan Ramadan; Wasu daga cikin waɗannan nafiloli gama-gari ne da ake yin su cikin baki ɗayan dararen Ramadan, wasu kuma ana yinsu a wasu keɓantattun darare da ko wasu keɓantattun ranaku.[39]
Daga cikin ayyuka da suka shahara akwai umarni da yin sallah rakaa dubu da ake yi a cikin dararen Ramadan[40] An bayyana tsarinta kamar haka: daga dare na farkon Ramadan zuwa dare na 20, a ko wane dare za a yi rakaa 20. Daga dare na 20 har zuwa ƙarshen Ramadan, cikin ko wane za a yi rakaa 30, sannan cikin dararen da ake sa ran dacewa da lailatul ƙadri banda waɗannan rakaoi da aka ambata ana ƙara rakaa 100[41] Ahlus-Sunna a cikin ko wane dare suna yin sallar mustahabbi raka'a 20 wace suke kira da suna salatul tarawihi.[42] Ahlus-Sunna bisa biyayya da bin sawun halifa na biyu suna yin wannan sallah cikin tsarin jami, wanda yin haka bidia ne a wurin Shi'a.[43]
Itikafi A Goman Ƙarshe
Itikafi a goman ƙarshen yana daga ayyuka na mustahabbi da suke tattare da tarin falaloli.[44] Goman ƙarshe, shi ne mafi kyawun lokaci na yin iitikafi wanda ladan yin iitikafi a cikinsa ana ɗauƙarsa daidai da ladan hajji guda biyu da umara guda biyu.[45] Annabi Akram (S.A.W) a farko ya fara zaɓar goman farkon watan Ramadan, sai kuma goma ta biyu, sai kuma goma ta uku domin yin iitikafi, bayan nan sa ya ci gaba da yin iitikafi a goman ƙarshe har zuwa ƙarshen rayuwarsa.[46]
Ladubba Da Al'adu
Cikin alummun Musulunci akwai ladubba da alada da suka yaɗu a watan Ramadan.
Teburin Ifɗar (Abincin Buɗa Baki)
A ƙasashe daban-daban Musulmi kan shirya taron buɗa baki a wurare addini.[47] Haka kuma a ƙasar Iran mutane suna gayyatar juna zuwa gidajensu domin buɗa baki, haka nan a wuaren addini a lokacin buɗa baki ana raba abincin bakance..[48] Bisa wata riwaya daga Annabi (S.A.W) ladan duk wanda ya yi sadakar abincin buɗa baki ga mumini ko da gwargwadon ɗigon ruwa ko ɗanyen dabino yana daidai da ƴanta bawa.[49] A wasu yankuna, kai tsaye bayan kiran sallah ana tsayawa a yi buɗa baki, a wasu yankuna kuma sai bayan idar da sallar magariba da Isha.

Tashin Mutane Domin Sahur
A wasu birane ana sanar da lokacin sahur da tashin mutane daga bacci ta hanyoyi daban-daban kamar zagayawar mai sanarwa da masu shela loko-loko da saƙo-saƙo unguwanni da tituna domin sanar da lokacin sahur. Haka kuma ana Kunna fitilu a hasumiyoyin masallatai, kaɗa ganga da busa ƙahom buga ƙofofin gidaje da harba bindiga duka domin sanar da mutane lokacin sahur.[50] Haka kuma a gidajen radiyo da talabijin da bututun lasifiƙar masallatai a ƙasar Iran kafin kiran sallar asubahi ana karanta addu'o'in sahur, haka kuma gabanin magariba ana karanta munajati rabbana.

Aika Muballigai
Malaman Shi'a, a watan Ramadan suna zuwa birane da ƙauyuka domin wayar da kanmu mutane da koyar da su hukunce-hukuncen sharia da shirya laccoci da kuma limanci sallar jami.[51] Haka kuma cibiyoyin tabligi suna aika muballigai yankuna daban-daban na cikin ƙasar Iran da wasu ƙasashe domin tabligi.[52]
Karatun Addu'o'i Na Yau Da Kullum Cikin Taron Jama'a
ƳanShi'abayan idar da sallolin jami na yau da kullun, suna karanta adduar "Ya Aliyu Ya Azim" cikin taron jamaa, haka kuma mafi yawan lokuta ɗaya daga cikin masallata yana ɗaga sauti ya karanta adduar"Allahumma Adkhil ala ahlil ƙuburis surara" da adduar da ake karantawa a ko wace rana a watan Ramadan, sauran masu saurarensa kuma a ko wace gaɓa suna faɗin amin-amin.
Muzaharar Ranar Ƙudus
Imam Khomaini domin nuna goyan baya ga mutanen Falasɗinu a shekarar 1978M, ya sanya wa ranar Juma'a ta ƙarshen Ramadan cikin ko wace shekara da suna rana ranar ƙudus.[53] Musulmi a ƙasashe daban-daban na duniya a wannan rana cikin ko wace shekara suna shirya zanga-zanga nuna goyan baya ga mutane Falasɗinu da kuma ƴanto masallacin Al-Aƙsa.[54]
Ayyana Farko Da Ƙarshen Ramadan
Ana tabbatar da farko da ƙarshen Ramadan ƙarƙashin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi kamar haka:

- Ganin jaririn wata: tabbatar da ganin jaririn wata a farko da ƙarshe
- Samun yaƙini daga maganar wasu adadin mutane.
- Shaidar maza adalai guda biyu da maganarsu ba ta ci karo da juna ba.
- Cika kwanaki talatin da shigar wata.
- Hukuncin shugaban shari'a.[55]
Wasu hadisai, sun bayyana cewa watan Ramadan kwanaki talatin ne.[56] Wasu jamaa daga malaman Shi'asun yi imani da wannan magana;[57] Akasin haka, bisa abin da ya zo cikin wasu riwayoyi, haƙiƙa watan Ramadan kamar dai sauran watanni yana yawo ne tsakanin kwanaki 29 ko 30.[58] Kuma mafi yawan malaman fiƙihu sun tafi kan wannan ra'ayi.[59]
Watan Ramadan yana zuwa ƙarshe bayan shigar watan Shawwal da kuma sanar da ranar idin ƙaramar sallah, daga cikin ayyuka idul fiɗri akwai ba da zakkar fidda kai da sallar idi.[60]
Abubuwan Da Suka Faru Da Kuma Muhimman Ranaku
- Shelar Wilaya tau Ahadi Imam Rida (A.S) (7 Ramadan shekara 201H)[61]
- Wafatin Sayyida Khadija (10 Ramadan da shekara 10 ga Bi'isa)[62]
- Taron ƙulla ƴan uwantaka tsakanin sahabban Annabi (S.A.W) da kuma tsakanin Manzon Allah (S.A.W) da Imam Ali (A.S) (12 Ramadan shekara 1H)[63]
- Haihuwar Imam Hassan Mujtaba (A.S)(15 Ramadan 3H)[64]
- Yaƙin Badar (17 Ramadan shekara 2H)[65]
- Lailatul ƙadri da saukar da Kur'ani (Daren 19 Ramadan ko 21 ko 23 shekara 1H)
- Fatahu Makka (20 Ramadan shekara 8H)[66]
- Shahadar Imam Ali (A.S) (21 Ramadan shekara 40H)[67]
Bayanin kula
- ↑ Ƙurashi, Ƙamus Qur'an, juzu'i 3, shafi 123.
- ↑ Bostani, Farhange Abjadi, shafi 443.
- ↑ Suratul Baƙara, aya ta 185.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i 2, shafi 629.
- ↑ Baƙara, aya ta 185.
- ↑ Ƙara'ati, Tafsire Nur, juzu'i 1, shafi 285.
- ↑ Suratul Ƙadri, aya ta 1.
- ↑ Misali, ku dub: Kulaini, Al-Kafi, juzu'i 4, shafi 66, 157 da 158.
- ↑ ku duba: Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i 10, shafi 786.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i 20, shafi 334.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i 2, shafi 14-15; Yaƙubi, Tarikh Yaƙubi, juzu'i 2, shafi 45.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attabaƙatul Kubra, juzu'i 2, shafi 14-15.
- ↑ Ragib, Mufradatul Alfazil Kur'an, shafi 366.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 55, shafi 341.
- ↑ Mazandarani, Sharhu Al-Kafi, juzu'i 6, shafi 110.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 93, shafi 346.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 93, shafi 348.
- ↑ Shaik Saduƙ , Man La Yahduruhu al-Faqih, juzu'i 2, shafi 160.
- ↑ Saduƙ , Al-Amali, shafi 19, hadis 1.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 93, shafi 342.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 93, shafi 340.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i 4, shafi 66.
- ↑ Ɗabaɗaba'i Yazdi, Al-Urwatul Wusƙa (Muhashi), juzu'i 3, shafi 521.
- ↑ Allama Hilli, Tazkiratul Fuƙaha, juzu'i 6, shafi 5.
- ↑ Suratul Baƙara, aya ta 183-185 da 187.
- ↑ Ku duba: Musawi Golfaigani, Majma'ul Masa'il juzu'i 3, shafi 215.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Al-Iƙbal, juzu'i 1, shafi 156–185.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Al-Iƙbal, juzu'i 1, shafi 138.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Al-Iƙbal, juzu'i 1, shafi 79 da 80.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i 2, shafi 630.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i 93, shafi 341.
- ↑ «زمان پخش ترتیل جزءخوانی قرآن کریم در تلویزیون + جدول»، Kamfanin dillancin labarai na ISNA.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 4, shafi 156–160
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 4, shafi 158, hadisi na 8; Saduƙ , Al-Khisal, juzu'i na 2, shafi 508, hadisi na 1.
- ↑ Saduƙ, Al-Khisal, juzu'i na 2, shafi 519.
- ↑ Ɗabaɗaba'i, Almizan, juzu'i na 20, shafi 334.
- ↑ Majidi Khamna'i, «Shabhaye Ƙadri Dar Iran,» shafi 21.
- ↑ Majidi Khamna'i, «Shabhaye Ƙadri Dar Iran,» shafi 22.
- ↑ Duba: Ƙummi, Mafatihul Jinan, shafi 183 da 238 da 239.
- ↑ Ƙummi, Mafatihul Jinan, shafi 183 da 184.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 12, shafi 187–190.
- ↑ «چرا شیعیان نماز تراویح نمیخوانند؟»، Shafin yanar gizo na Namayandegi Wali Faƙih Dar Umuri Hajji Wa Ziyrat.
- ↑ Sadiƙi Fadaki، تراویح»، Daneshname Hajji Wa Haramaini Sharifaini
- ↑ Ƙummi,Mafatihul Jinan, shafi 234.
- ↑ Ƙummi, Mafatihul Jinan, shafi 234.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i4, shafi 175r, hadisi na 3.
- ↑ «رمضـان در کشورهای مختلف جهان»، Shafin Keyhan
- ↑ «افطاری»، Cibiyar Da'iratul Ma'arif Buzurg Islami.
- ↑ Saduƙ, Uyunu Akhbarir Rida (A.S), juzu'i na 1, shafi 295-297, hadisi na 53.
- ↑ Duba: Rahimi, «Ramadan».
- ↑ «تبلیغ، قلب دین»، Kamfanin Labarai na Fars.
- ↑ «آغاز ثبتنام مبلغان در خارج از كشور».، Hukumar Khabarguzari Rasmi Hauze.
- ↑ Imam Khomaini, Sahife Imam, juzu'i na 9, shafi 267.
- ↑ «جهان و روز جهانی قدس»، Kamfanin Labarai na Tasnim.
- ↑ Imam Khomaini, Taudihul Masai'l (mahashi), juzu'i na 1, shafi 959.
- ↑ Hurru Amili, Wasa'ilush Shia, juzu'i na 10, shafi 268–274.
- ↑ Sayyid Ibn Ɗawus, Al-Iƙbal, juzu'i na 1, shafi 33–35.
- ↑ Hurru Amili, Wasa'ilush Shia, juzu'i na 10, shafi 261–268.
- ↑ Duba: Bahrani, Al-Hada'iƙ An-Nadira, juzu'i na 13, shafi 270–271; Amoli, Misbahul Huda, juzu'i na 8, shafi 384.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu'i na 11, shafi 332-333.
- ↑ Ya'qubi, Tarikh Ya'qubi, juzu'i na 2, shafi 465.
- ↑ Ibn Sa'ad, Attaƙabatul Kubra, juzu'i na 8, shafi 14.
- ↑ Ƙummi, Waƙa'iul Ayyam, shafi 58.
- ↑ Shaik Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 2, shafi 5; Ɗabari, Tarikhuɗ Ɗabari, juzu'i na 2, shafi 537.
- ↑ Ya'qubi, Tarikh Yaƙubi, juzu'i na 2, shafi 45.
- ↑ Ɗabari, Tarikhuɗ Ɗabari, juzu'i na 2, shafi 343.
- ↑ Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 1, shafi 9.
Tsokaci
- ↑ Bisa ga rahotanni, abin da aka ƙaddara wa mutane kamar abubuwan da suka faru, masĩfu, da arziki, ana ƙayyade su a cikin wannan dare. A haƙiƙa, duk arziki da rabon su na zahiri da na ruhani ana rubuta su.
Nassoshi
- «ماه مبارک رمضان نمادی از هویت دینی جامعه اسلامی است»،, (Wata Mai Alabraka Ramadan alama ce ta ainihin addinin al'ummar Musulunci) Kamfanin Labarai Khabarguzari Bainal Milali Qur'an. Ranar saka labarin: 28 Mayu 2016. Ranar ziyartar labarin: 7 Afrilu 2022M.
- Amoli, Mirza Muhammad Taƙi, Misbahul Huda fi Sharhi Al-Urwatul Wusƙa, Tehran, Mawallafar al-Mu'allif, 1380H.
- Fatima Rahimi «رمضان», (Ramadan), Daneshname Jahane Islam (Juzu'i na 20), ranar dubawa:7 Afrilu 2022M.
- Hurru Amili, Muhammad Bin Hassan, Wasa'ilush Shi'a, Qom, Cibiyar Alul Bait (A.S), 1409H.
- Kulaini, Muhammad ibn Yaƙub, Al-Kafi, Bincike da gyara wa Ali Akbar Gaffari da Muhammad Akhundi, Tehran, Mawallafar Darul Kutubil Islamiyya, bugu na hudu, 1407H.
- Majlisi, Muhammad Baƙir, Bihar al-Anwar al-Jami'atu li Durar Akhbar al-A'immah al-Aɗhar (A.S), Beirut, Mawallafar Darul Ihya' Turasil Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Mazandarani, Sharhu Al-Kafi (Al-Usul wa al-Raudah), Bincike da gyara Abul Hassan Sha'arani, Tehran, Mawallafar Al-Maktabatul Islamiyya, bugu na farko, 1382H.
- Musawi Golfaigani, Sayyid Muhammad Rida, Majma'ul Masa'il, Bincike da Gyarawa: Ali Karimi Jahromi, Ali Sabiti Hamadani, wa Ali Niyyiri Hamadani, Mawallafar Darul Kur'anil Kareem, Qom, bugu na biyu, 1409H.
- Mufid, Muhammad Bin Muhammad, Al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-'Ibad, gyara Cibiyar Alul Bait, Qom, Kongire Shaik Mufid, bugu na farko, 1413H.
- Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalam fi Sharh Shara'i'il al-Islam, Beirut, Mawallafar Darul Ihya' Turasil Arabi, bugu na bakwai, babu tarihin shekara
- Ƙara'ati, Muhsin, Tafsire Nur, Tehran, Cibiyar Farhangi Az Darsehaye Az Kur'an, bugu na farko, 1388 Sh.
- Ƙummi, Shaik Abbas, Faizul al-'Alam fi 'A'amal al-Shuhur wa Waƙayi' al-Ayyam, Mawallafar Subhe Pirouzi, babu kwanan wata.
- Ƙummi, Shaikh Abbas,Mafatihul Jinan, Qom, Mawallafar Uswe, babu kwanan wata.
- Saduƙ , Muhammad Bin Ali, Al-Khisal, Bincike da gyara Ali Akbar Gaffari, Qom, Jami'e Mudarrisin, bugu na farko, 1362Sh.
- Sayyid Ibn Ɗawus, Ali Bin Musa, Al-Iƙbal bil A'amalil Hasana Fima Yu'mal Marratan fis Sana, Bincike da Gyarawa Jawad Ƙayyumi Isfahani, Qom, Ofishin Tabligate Islami, bugu na farko, 1376 Sh.
- Ɗabari, Tarikh al-Umam wal Muluk, Bincike Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Beirut, Darul Turas, bugu na biyu, 1387H.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an, Tehran, Nasir Khusraw, bugu na uku, 1372Sh.
- Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwatul Wusƙa, (Muhashi), Qom, Ofishin Mawallafar Islami, bugu na farko, 1419H.
- Ɗabaɗaba'i, Sayyid Muhammad Husaini, Almizan fi Tafsiril Kur'an, Beirut, Mawallafar al-Alami Lil Ma, bugu na biyu, 1390 H.
- «چرا شیعیان نماز تراویح نمیخوانند؟»،, (Me yasa 'Yan Shi'a ba sa sallar Tarawihi?), Namayandegi Wali Faƙih Dar Umuri Hajji Wa Ziyrat, ranar wallafa bayani: 13 Janairu 2013. Ranar duba: 7 Afrilu 2022M.
- در کشورهای مختلف جهان»، (Ramadan a Ƙasashen Duniya Dabam-dabam) Shafin Keyhan. Ranar wallafawa: 14 Afrilu 2023. Ranar duba: 30 Afrilu 2023M.
- «افطاری»، (Abincin ɓuda baki) Shafin CCibiyar Da'iratul Ma'arif Buzurg Islami. Ranar wallafawa: 12 Mayu 2021.Ranar duba: 30 Afrilu 2023M.
- «تبلیغ، قلب دین، (Tabligi, isar da sakon Musulunci shi ne Zuciyar Addini»), Kamfanin Labarai na Fars. Ranar wallafawa: 29 Yuni 2019. Ranar duba: 30 Afrilu 2023M.
- «آغاز ثبتنام مبلغان در خارج از كشور»، (Fara Rijistar Muballigai na Ƙasashen Waje) Hukumar Khabarguzari Rasmi Hauze. Ranar saka labarin: 30 Mayu 2011. Ranar dubawa: 18 Afrilu 2023M.
- Saduƙ , Muhammad ibn Ali, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na shida, 1376 Sh.
- Saduƙ , Muhammad ibn Ali, Uyun Akhbarir Rida (A.S.), Bincike da Gyarawa Mahadi Lajwardi, Tehran, Maallafar Jahan, bugu na farko, 1378 H.
- Majidi Khamna'i, Faride، «شبهای قدر در ایران», ( Yadda ake gudanar da Lailatul ƙadr a Iran), A cikin mujallar wata uku-uku ta Golestane Kur'an, lamba ta 37, 22 Nuwamba - 21 Disamba 2000M.
- Ragib, Husaini Bin Muhammad, Mufradatul Alfazil Kur'an, Beirut - Dimashƙa, Mawallafar Darul Ƙalam - da al-Shamiya, bugu na farko, 1412H."