Rukunan Sallah

Daga wikishia
wannan wata kasida ce da aka rubuta domin bayani kan ra'ayin fikihu da ba zai iya zama madogarar a ayyukan addini duba wata madogarar don ayyukan addini
Risala Ilmiyya

Rukunan Sallah (Larabci: أركان الصلاة) yana cikin jerin Farillan sallah wadanda yin kari cikin su ko ragi ko da cikin halin rafkana ne yana bata sallah, Mashhur din Malaman Fikhun Shi’a suna kirga, Niyya, tsayuwa, Takbiratul Ihrami, Ruku’u, da Sujjada guda biyu a hade da juna matsayin rukunan sallah.

Bayanin Rukuni

Rukuni yana daukar ma’anar asasi da jigo kowanne abu, sannan a cikin ibada yana kasancewa wani juzu’i da rage shi ko kara shi hatta cikin halin rafkana yana haifar da lalacewar ibada [1] wasu ba’ari juzu’an Sallah, Hajji da Umara suna kasancewa rukunai [2]

Rukunan Sallah

Rukunan sallah kan asasin shahararriyar Magana sune: Niyya, Tsayuwa, Tkbiratul Ihrami, Ruku’u, Sujjada biyu a hade [3] abin da ake nufi da niyya shine dai yin da niyyar sauke umarnin Allah da neman kusanci da shi wanda yake faruwa sakamakon fadakuwa da mai kira (Niyya). hallaro da wani abu a kwakwalwa ko kuma furta lafuzza a kan harshe duka ba dole bane [4] abin da ake nufi da tsayuwa shine tsayuwa a tsaye a lokacin yin kabbarar harama da kuma tsayuwa da take hade da ruku’u, ma’ana bayan ka tsaya a tsaye sai ka rankwafa ruku’u kai tsaye [5] Wasu ba’ari suna kirga fuskantar Alkibla a halin zabi cikin rukunai [6] kamar yanda bayani ya gabata daga wasu Malaman Fikhu, an nakalto kasancewa karatun sallah cikin rukunai [7]

Ragewa da Kara Rukuni

Mashshur Fakihai, sun tafi kan cewa ragi ko kari cikin rukuni da gangan ko cikin halin rafkana ya lalata sallah [8] amma wasu ba’ari kuma sun tafi kan cewa kara rukuni cikin mantuwa da rafkana baya lalata sallah [9] Mawallafin littafin (Urwatul Wuska) ya tafi kan cewa kara niyya da ma’anar kari cikin niyyar sauke sallah wani abu da ma ba zai yiwu ayi tunanin yiwuwarsa ba, da ma’anar hallaro da kera surar sallah a kwakwalwa, yana ganin hakan zai cutar da sallah ko lalata ta. [10]

Barin Rukuni Bisa Rafkana

Duk lokacin da Masallata suka bar rukini sakamakon rafkana, har zuwa lokacin da basu shiga wani rukunin ba zasu iya maimaita shi.[11]

Bayanin kula

  1. Mohaghegh Hilli, Shara'i al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 62; Najafi, Mohammad Hassan, Jawaharlal Kalam, juzu'i na 9, shafi na 239.
  2. Khomeini, Tahrir al-Wasila, Mawallafi: Cibiyar Tattalin Arzikin Ayyukan Imam Khumaini (RA), Mujalladi na 1, shafi na 153.
  3. Alameh Hilli, Moktalafu al-Shi’a, 1412 AH, juzu’i na 2, shafi na 140-139.
  4. Tabatabaei Yazdi, al-Urwa al-Wughta, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 434.
  5. Yazdi, al-Urwa al-Waghti, 1419 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 473.
  6. Ibn Hamzah Tusi, al-Wasila, 1408H, shafi na 93.
  7. Sheikh Tusi, Al-Mabsut, Makarantar Al-Mortazawi, juzu'i na 1, shafi na 105.
  8. Shahid Sani, Al-Rawda Al-Bahiya, Islamic Scientific Publications, juzu'i na 1, shafi na 644.
  9. Najafi, Jawaherul Kalam, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 9, shafi na 241-239.
  10. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 433.
  11. Najafi, Javaher al-Kalam, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 12, shafi na 238-239.

Nassoshi

  • Ibn Hamzah Tusi, Muhammad bin Ali, al-Wasila al-Nil al-Fadilah, bincike na Muhammad al-Hasoun, Qum, mazhabar Ayatullah al-Marashi al-Najafi, 1408H.
  • Hili, Hasan bin Yusuf, 'Moktalaf Shi'a fi Ahkam Shari'a, bisa kokarin Cibiyar Bincike da Nazarin Musulunci ta Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci, 1412H.
  • Shahid Thani, Zain al-Din, al-Ruda al-Bahiya fi Sharh al-Lum'a Al-Damshaqiyya, Tehran, Islamic Islamic Publications, [beta].
  • Tousi, Mohammad bin Hassan, al-Mabusut fi fiqhu al-Umamiyyah, na Mohammad Baqer Behboodi, Tehran, al-Mortazawiyya school, [beta].
  • Najafi, Mohammad Hasan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shariah al-Islam, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1362 AH.
  • Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghti, Qom, Dar al-Tafsir, Ismailian, 1419 AH.