Jump to content

Ghadiriyya

Daga wikishia

Ghadiriyya, (Larabci: الغديرية) suna waƙoƙi ne da aka rera su game da ghadir khum. Farkon ghadiriyya da aka fara rerawa ta kasance ghadiriyya da Hassanu Ɗan Sabit ya rera a ranar ghadir. Ta fuskacin lura da ma'anar da suke ƙunshe da su, ƙari kan tattare batun abin da ya faru a ranar ghadir waɗannan waƙoƙi sun haɗo da bayanin falalolin Imam Ali (A.S) game da halifancin Annabi (S.A.W) da sauran abubuwa misalin hadis ukuwat, hadis manzilat da labarin abin da ya faru a lailatul al-mabit.

Allama Amini (Wafati: 1390. h. ƙ), ya tattaro tarihin rayuwar fiye mutum ɗari daga waɗanda suka rera waƙoƙin ghadir daga larabawa a cikin littafin Al-ghadir. Mawaƙan ghadiriyya cikin harshen farisanci sun kasance daga ƙarni na huɗu zuwa na sha huɗu bayan hijira kamar yadda aka gabatar da su a cikin litattafan ghadiriyya na farisanci.

Gabatarwa

Ghadiriyya suna ne da ake amfani da shi kan waƙoƙin da aka rera game da waƙi'ar ghadir khum da falalolin Imam Ali (A.S) da imamancinsa, musammam ma tare da ambaton ghadir da ghadir khum cikin rera waƙoƙin.[1] waɗannan waƙoƙi yawanci ana rera su cikin zirin ƙasidu.[2] wasu sun tafi nkan cewa ghadiriyya dole ya zama sun fi mayar da hankali da tattarara kan waƙi'ar ghadir da halifancin Imam Ali (A.S), ba a kiran waƙoƙin da ake rera su cikin zallan falalolin Imam Ali (A.S) da darajojinsa da cikinsu aka yi ishara da waƙi'ar ghadir da sunan ghadiriyya..[3]

A ra'ayin Jawad Muhaddisi, malamin addini kuma mawaƙi marubuci ɗanshi'a, tsarin littafin Al-ghadir na Allama Amini ya ƙarfafa kan ghadiriyya da ya tattaro tarihin mawaƙan da suka rera waƙoƙin ghadir tun daga zamanin Annabi (S.A.W) har zuwa zamanin marubucin.[4]

A ra'ayin wasu ba'ari, ghadiriyya ba ta tsaya cikin surata wata waƙi'a gida ɗaya kaɗai ba, bari dai suranta wata haƙiƙa da ilimi da suka kasance maɓuɓɓugar dukkanin sauran ilimi da kuma zanen al'adu na asali.[5]

Larabawa Da Suka Rera Ghadiriyya

Hassanu Ɗan Sabit, farkon wanda ya fara rera ghadiriyya a tarihi tare da izinin Annabi (S.A.W) ya rera ta ne a ranar ghadir.[6] Bayansa sauran mawaƙa sun rera cikin falalar ghadir tare da bayyana ƙauna da soyayyar da suke yi wa Imam Ali (A.S), daga jumlarsu akwai Kumaitu Ɗan Zaidu Asadi (Wafati: 126. h. ƙ), Sayyid Isma'il Himyari (Wafati: 173. h. ƙ), Al'abdi, Abu Tamam Habib Ɗan Ausi Al-ɗa'i (Wafati: 231. h. ƙ) da kuma Di'ibal Ɗan Ali Khuza'i (Wafati: 246. h. ƙ). Allama Amini ya lissafo sunayen kusan mutum ɗari tun daga ƙarni na farko zuwa ƙarni na goma sha ɗaya ya kawo wannan bayani tsakanin mujalladi na biyu zuwa na bakwai a littafinsa Al-ghadir.[7]

Budu da ƙari ya kawo sunayen ba'arin maƙiya Imam Ali (A.S) cikin taken waɗanda suka rera ghadiriyya; kamar misalin Amru Ɗan Asi (Wafati: 43. h. ƙ) wanda ƙasidarsa mai suna ƙasidatu Juljuliyya ta shahara a wannan fage.[Tsokaci 1]

Zahara Fatahullahi, ƴar shi'a mai binciken ilimi. Ta yi bincike game da fitattun mutane guda takwas da suka rera ghadiriyya a cikin ƙarni na sha huɗu da sha biyar hijira ƙamari, misalin Bulis Salam, Sa'id Aƙal, Georg Shakur da Biktor Ilikik, ta ce abin da ya fi jan hankula cikin ghadiriyya ta larabci, shi ne ghadiriyyar Josep Auni da Georg Zakiyyu Al-haj daga mawaƙan wannan zamani cikin larabawa kiristocin ƴan ƙasar labanun da suka rera da gama-garin larabci.[8]

Ma'anonin Ghadiriyya

Kubra Salibi Cikin risalar kammala daurar karatu mai taken "Nigahi SabakShinasane Be Ghadiriyehaye Asre Awwal Abbasi”, tana ganin ghadirriya sun kasance kan waɗannan ma'anoni da batutuwa kamar haka:[9]

Mawaƙan Ghadiriyya Cikin Harshen Farisanci

Tushen ƙasida: Fihirisar Mawaƙan Ghadiriyya A Harshen Farisanci

Muhammad Sihhati Sardarudi, malamin shi'a a cikin littafin "Ghadirihaye Farsi Az ƙarne Ceharom Ta ƙarne Cehardahom"tare da ɗaukowa daga littafin Al-Ghadir kan tsarin littafin ya tattaro jerin mutum 179 daga mawaƙan ghadiriyya cikin harshen farisanci.[10]

Ba'arin ghadiriyyar harshen farisanci da suke danganewa da ƙarni na bakwai hijira ƙamari sune kamar haka: Baba Afzal Kashani[11] Mutum mafi fifiko cikin ilimi da falala shi ne Ali Cikin madogarar Sanin Allah Ali ne Sarki Bayan Annabi Jagora Imamin duniyoyi biyu wallahi Ali ne summa billahi Ali ne

Maulawi[12] Don haka Annabi ya sanya masa suna Ali Maula wanda ya kasance misalin kankin kansa Ya ce duk wanda ya yarda da nake mijaɓancin lamarinsa masoyinsa To ɗan baffana Ali majiɓancinsa ne kuma masoyinsa

Littafin Ghaidriyya Farsi (daga karni na 4-14. talifin Muhammad Sihhati Sardarudi

Khawajawi Kermani[13] Tushe da lambun, lu'ulun shiriya Fitilar wilaya hasken idanun masoya Shinge da ganuwar ƙasar addini, Zakin Mai kashe maƙiya Wasiyyin Mustafa Duk wanda ya bi hanyar Haidar lallai ya samu rayuwa

Bisa bayanin ba'arin malamai, tsanantawar sarakunan ahlus-sunna kan aƙidun shi'a ya kasance sababin bambantuwar ma'anonin waƙoƙin ghadiriyya gabanin zamanin safawiyya da bayansa, alal misali Firdausi an kore shi zuwa fadar Gaznawi, waziri Mu'izzi tare da dukkanin matsayin da yake da shi cikin masarautarsa da sarkin Sanjar duk lokacin da ya yi amfani da kalmar "wasiyyu"cikin baitukan waƙarsa sai ya nemi ayi masa afuwa bisa zamiyar baka domin gudun fushin sarki da ba'arin malaman ahlus-sunna, saboda kalmar "wasiyyu"kalma ce da ƴanshi'a suke amfani da ita kan Imam Ali (A.S).[14]

Sanin Littafi

  • Al-ghadir, na Allama Amini da tarjamar Muhammad Baƙir Behbudi, bugun nashar kitabekhune buzurgi islami.
  • Ghadir Dar Shi'iri Farsi, na Mustafa Musawi Germarudi, bugun Dalilu Nashar.
  • Ghadirihaye Farsi (Daga ƙarni 4-14) na Muhammad Sihhati Sardarudi, bugun Ma'aikatar kula da al'adun muslunci ta Iran.
  • Golbange Ghadir, na Muhammad Mahadi Behdrawandi, tehran, bugun Nashar Payame Azadi.
  • Dar Sahil Ghadir, na Ahmad Ahmadi Birjandi, Mashhad, Bunyade Pajuheshhaye Islami Astane ƙudus Rezawi.
  • Khalwati Ba Ghadir, na Muhammad Mahadi Behdrawandi, tehran, bugun Nashar Hurra.

Bayanin Kula

  1. Mohaddisi, Farhang Ghadir, 2004, shafi na 444.
  2. نقش شیعیان در گسترش غدیریه‌ها
  3. نقش شیعیان در گسترش غدیریه‌ها
  4. Muhaddi, Farhang Ghadir, 2004, shafi na 336
  5. نمکی آرانی، «مدحت کن و بستای کسی را...»، ص۱۰۹.
  6. Mohaddisi, Farhang Ghadir, 2004, shafi na 336; Helali, Kitabe Sulaim bin Qays al-Hilali, 2004, juzu'i na 2, shafi na 828-829.
  7. Duba Amini, al-Ghadir, 1416 AH, juzu'i na 2-7; C11.
  8. Fathallah Nouri, Ghadiriya Sarayan,Arab wa Muarrifi Ghadiriya Anha, 1391 AH, shafi na 28.
  9. Negahi be Sabakeshinas Ghadiriyahaye Asre Awwal Abbasi, 1394H.
  10. Sahhati Sardarudi, Ghadiriyahaye farsi (Az Qarn Chaharam Ta Chahardham), 1379 AH.
  11. Marqi Kashani, Rubayat, 1363 AH, shafi na 51.
  12. Mawlawi, Kulliayt Diwan Shams Tabrizi, 1377 AH, shafi 980.
  13. Khajovi Kermani, Divan Ash'ar, 1369, shafi na 134.
  14. نگاه کنید به نقش شیعیان در گسترش غدیریه‌ها، سایت آیین رحمت.

Tsokaci

  1. Ghadiriya Amro bin As ya shahara da wakar “Joljuliyyah” [ma’ana kararrawa] kuma labarinta ya kasance kamar haka Muawiya ya yi wa Amr al-Aas, wanda ya zama shugaban Masar barazana, da ya ki aika haraji. Amr al-As a martaninsa ga Muawiyah ya rubuta Baitukan waka 66, wadda aka fi sani da wakar Jaljuliyyah, Wannan waka ta kunshi wasu bayanai na tarihi a wancan lokacin, Wakar ta fara da wannan baiti: معـاويـة الفضل لا تنس لي * وعـن نهـج الحـق لا تعـدل...ـإن كـنت فيـها بلغت المنى * فـفي عـنقي عـلق الجُلجُل. Amini, Al-ghadir, juz 3 shafi na 213.

Nassoshi

  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir Fi Al-Kitab wa Sunnah wa Al-Adab, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, bugun farko, 1416 AH/1995 miladiyya.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir , Mohammad Baqer Behboodi ya fassara, Tehran, Big Islamic Library, 1368 ya fassara.
  • Khajawi Kermani, Mahmoud bin Ali, Divan Ash'ar, Ahmad Sohaili Khansari ya shirya. Tehran, Pajang, 1369.
  • Jovini Khorasani, Ibrahim bin Muhammad, Faraed al-Samatin fi Fadael al-Mortaza da al-Batool da al-Sabatin, binciken da Mohammad Baqir al-Mahmoudi, Beirut, Al-Mahmoudi Institute, 1978 ya yi.

Sayyid Razi, Muhammad bin Hussain, Khasa'isu A'imma, Mashhad, Haramin Razawi, Majma al-Pakhuh al-Islami, 1406H.

  • Salehi, Kobri, Negahi beh Sabakeshainasi Ghadiriya Asre Awwal Abbasi, karatun Masters, Faculty of Theology and Islamic Studies, Ahvaz, Jami'ar Shahid Chamran, 2014.
  • Saheti Sardarodi, Mohammad, Ghadiriyeh Farsi (daga karni na 4 zuwa na 14), Tehran, wanda Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci ta buga, 1379.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtjaj Ali Ahl al-Jajj, Mashhad, Mawallafin Morteza, 1403H.
  • Fethullah Nouri, Zohra, Ghadiriya sarane Muasir Arab wa muarrifi Ghadiriya, karatun digiri na biyu, adabi da zamantakewa, Tehran, Jami'ar Azad Islamiyya, Reshen Tehran ta Tsakiya, 2013.
  • Mohaddisi, Javad, Farhang Ghadir, Qom, Marouf, 2004. * Murqi Kashani, Baba Afzal, Rubayat, Tehran, Farabi Publishing House, 1363. * Maulvi, Jalaluddin Mohammad Balkhi, Babban Kotun Shams Tabrizi, Tehran, Negah, 1377.
  • نقش شیعیان در گسترش غدیریه‌ها، سایت آیین رحمت، تاریخ بازدید: ۳ اسفند۱۴۰۳ش.
  • نمکی آرانی، میثم، «مدحت کن و بستای کسی را...»، ماهنامه کیهان فرهنگی، شماره ۱۷۰، ۱۳۷۹ش.
  • Helali, Sulim bin Qais, Kitabe Sulaimi bin Qais al-Hilali, Qom, wanda Mohammad Baqer Ansari Zanjani ya buga, 2004.