Amina Bint Shuraidi

Daga wikishia

Amina bint Shuraidi (Larabci:آمنة بنت شُرَيد) ita ce matar Amru hamaƙ khuza'i ya rasu 508 h ƙamari, wanda aka kulleta a gidan yari da umarnin Mu'awiya, hakanne ya janyo shaharar ita wannan mata.

Tsinuwar Wannan Mata Kan Mu'awiya.

"Ya kai Mu'awiya, Allah ya maida ƴaƴanka marayu, Allah ya rabaka da iyalanka, kada Allah ya gafarta maka"[1]

Tsinuwa da Amina ɗiyar Shuraidi da ta yi kan Mu'awiya
Ya Mu'awiya, Allah ka sanya `ya`yanka su zama marayu, ka karkatar da iyalanka daga barinka, kada Allah ya yafe maka.

Tarikh Bayigani

Amina bint Shuraidi ta kasance ɗaya daga cikin haziƙan matan garin Kufa kuma ita ce matar Amru bin Hamaƙ Khuza'i,[2] kuma tana daga ƴan Shi’ar Imam Ali (A.S).[3] Ibn ɗaifur masanin tarihi daga malaman Ahlus-Sunna (204-280H) a cikin littafinsa na Balagatun-nisa ya kawo maganganun da ta yi ga Mu'awiya Bn Abi Sufyan.[4] Hakama ya zo a Aayanush-shi'a.[5] da Aalamun-nisa'i' M'uminat.[6] inda ibn ɗaifur ya rawaito. Zarkali, masanin tarihi a ƙarni na 14, ya kawo cewa : dalilin da yasa Amina ta yi suna da shahara shi ne ɗaure ta da kuma maganganun da ta yi kan Mu'awiya [7] Bayan shahadar Imam Ali (A.S) Mu'awiya bin Abi Sufyan ya tsananta wa wasu 'yan Shi'a ciki har da Amru bin Hamaƙ Khuza'i. ya gudu ya ɓuya, don haka bisa umarnin Mu'awiya aka kama matarsa Amina aka ɗaure a Dimashƙu har na tsawon shekaru biyu.[8]

Bayan shahadar Amru bin Hamƙ Khaza'i a shekara ta 50 bayan hijira, bisa umarnin Mu'awiya, an kai shi Dimashƙu aka ajiye shi a gaban Amina a kurkuku. Anan ne Amina ta yi kakkausan kalamai a matsayin mijinta, ta zagi Mu’awiya sosai. [9] Bayan faruwar haka, suka sake ta suka aika ta Kufa. Amina ta rasu kan hanyar ta zuwa garin hams sakamakon ciwan annoba da ya faru shekara ta 50 bayan hijira.[10]

Bayanin kula

  1. Ibn Tefur, Balaghat Al-Nisa, 1972, shafi na 87.
  2. Zarkali, Al-Alam, 1989, juz.1, shafi na26.
  3. Hassoun, , I'lamul Nisa'il Al-Muminat, 1421H, juzu’i na 1, shafi na 107.
  4. Ibn Tefur, Balaghat al-Nisa, 1972, shafi na 87-89.
  5. Amin, Ayan al-Shia, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 95.
  6. Hassoun, Alam al-Nisa’ al-Mu’mininat, 1421 BC, shafi. 107-111.
  7. Zarkali, Al-Alam, 1989, juz.1, shafi na 26.
  8. Ibn Tayfur, Balagat al-Nisa, 1972, shafi na 87-89.
  9. Ibn Tayfur, Balagat al-Nisa, 1972, shafi na 87-89.
  10. Zarkali, Al-Alam, 1989, juz. 1, shafi na 26.

Nassoshi

  • Ibn Tayfour, Ahmed, Balagat Al-Nisa'i, Beirut, 1972 AD.
  • امین، سید محسن، اعیان الشیعه، تحقیق حسن امین، بیروت، دارالتعارف للمطبوعات، ۱۴۰۳ق.
  • حسون، محمد و مشکور، ام‌علی، اعلام النساء المؤمنات، تهران، اسوه، ۱۴۲۱ق.
  • زرکلی، خیرالدین، الاعلام، بیروت، دار العلم للملایین، ۱۹۸۹م.