Jump to content

Zunubi

Daga wikishia

Zunubi (Larabci: الذنب) shi ne sabawa dokokin Allah, wato aikata wani abu da Allah ya haramta ko barin wani abu da Allah ya yi umarni da shi. Zunubai sun kasu kashi biyu: manya da kanana. Babban zunubi zunubi ne da aka bayyana a matsayin babba a cikin Alkur'ani ko hadisi, ko kuma aka yi alkawarin hukunta wanda ya aikata; Kamar misalin Shirka, kisan kai, zina, cin dukiyar marayu da Cin Riba. Bisa koyarwar addini, wasu zunubai suna da tasiri na musamman kamar rasa albarka, da kuma gaggauta mutuwa. Kamar yadda ayoyin Alkur'ani suka ce, wasu ayyukan alheri suna kai ga tsarkake zunubai. Wannan shi ake kira takfir. a bisa wasu Riwayoyi, Allah yana kankare zunuban bayinsa ta hanyar abubuwa kamar rashin lafiya da talauci. Haka nan ya zo a cikin Alkur'ani cewa idan mai zunubi ya tuba, Allah zai gafarta masa zunubansa. yan Shi'a, sun tafi kan cewa Allah ya kubutar da Annabawa da Ma'asumai Goma sha hudu daga aikata zunubi.

Sanin Kalmomi

Zunubi yana nufin sabawa dokokin Allah[1] Ma'ana aikata wani abu da Allah ya haramta[2] ko barin wani abu da Allah ya yi umarni da shi, sun sani a larabci.[3]

Mafi Girman Zunubi

Kamar yanda ya zo a Kur'ani Shirka ita ce Mafi Girman zunubi kuma ta kasance `bata mafi nisa.[4] a cikin suratul lukman an anbaci Shirka matsayin zalunci mai girma[5] daga cikin zunubon da Kur'ani ya bayyana shi mafi girman zalunci shi ne kirkirar Karya da jinginawa Allah[6] jinginama Allah karya ya tattaro duk wata bidi'a daga Asalai na addini ko Rassa[7] daga cikin manyan lefuka da zunubai akwai zalunci ana ma kirga shi daga mafi munin lefuka.[8]cikin da yawa-yawan ayoyin Alkur'ani Allah ya tsoratar da masu aikata zalunci da wutar Jahannama, gargadi mai tsanani ya zo kansu wanda ba kasafai ake samun sa ba kan sauran masu aikata lefuka.[9] daga cikin Manyan lefuka akwai Kisan Kai,[10] ya zo cikin Kur'ani cewa Kashe rai daya daidai yake da kashe baki dayan mutane.[11]

Rabe-rabe

La'akari da Lefuka ta Fuskanin Girma da Kankanta

Dangane da zunubi babba da karami A cikin wasu littafan Aklak, an raba zunubai zuwa Kanana da Manya [12] Tushen wannan rabon shi ne Alkur'ani da Riwayoyi[13] Misali a cikin aya ta 31 a cikin suratul Nisa'i, an ce: "Idan kuka nisanci manya abubuwa da aka hane ku, za mu kankare muku munanan ayyukanku kuma zamu shigar da ku guri mai girma."[14] A cewar Sayyid Muhammad Husaini Tabataba'i, ma'anar "shari'a" a cikin ayar kananan zunubai ne; Domin ya zo da manyan zunubai. Wannan ayar tana bayyana cewa zunubai sun kasu kashi biyu, kanana da manya.[15] A cikin littafin Urwatul Al-Wuska, an ce babban zunubi ne da aka ayyana shi a matsayin babba a cikin Alkur'ani ko hadisi, ko kuma aka yi alkawarin hukunta wanda ya aikata shi, .[16] Kashe rai, da Zina, tuhumar Kamammiyar Mace, da cin dukiyar Marayu, da cin Riba, da barin sallah, da sata, da yanke kauna daga rahamar Ubangiji, suna daga cikin manya-manyan zunubai da aka ambata a cikin hadisai.[17]

Rabe-raben Zunubai Bisa la'akari Da Tasirin Cutarwa Da Suke

A wasu Riwayoyi, zunubai suna rarraba bisa ga sakamakonsu. Misali a cikin Ma'ani Akhbar, a cikin wani hadisi daga Imam Sajjad (A.S), zunubai sun kasu kashi da dama, daga cikinsu akwai kamar haka;

  • Zunuban da ke cire ni'ima daga mutane: Zalunci, barin umarni da kyakkyawan aiki da hani da mumnmuna. da butulcewa ni'ima
  • Zunuban da ke jawo nadama: kisan kai, yanke zumunci, barin sallah da rashin ba da zakka.
  • Zunuban da ke jawo azabar Allah: Izgilanci ga mutane.
  • Zunuban da ke lalata sunan mutum: shan Barasa, Caca, wargi, tono laifukan Mutane.
  • Zunuban da ke kawo bala'i: rashin taimakon wanda aka zalunta, watsi da Umarni da Kyakkyawa da hani da mummuna.
  • Zunuban da ke gaggauta mutuwa: yanke zumunta da dangi, da Zina da Rantsuwar karya.[18]

Miyagun Kufaifayi Da Zunubi yake Haifarwa

Kamar yadda ya zo a cikin wani hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) idan mutum ya aikata zunubi sai a sanya baKin tabo a cikin zuciyar sa. Idan ya Tuba, zai tsarkaka; Amma idan ya kara Aikata zunubai sai a kara masa baki har sai ya rufe zuciyar sa baki daya. a wannan yanayin, ba zai taba samun ceto ba.[19][Tsokaci 1] Imam Ali (A.S) a cikin wani hadisi da ya kawo wannan ayar ta kur'ani da ke cewa "idan musiba ta same ku, to saboda abin da ku ke aikatawa" [20] ya dauki zunubai a matsayin sababin duk wata musiba da ta sami mutum a rayuwa; Ko da tabo da fadowa a kasa.[21]

Murtada MUtahhari
Zunubi gabaɗaya misalin [fashewa ne] domin ya kauce wa tsarin matafiyar halitta. Idan mutum ya yi aiki bisa ga tsarin dabi'a, idan ya kiyaye hakki da iyakokin jikinsa da ruhinsa a tsakani, ba zai fada cikin zunubi ba. Amma idan ya fita daga matsakaici, waɗannan zunubai suna faruwa kamar yanayin misalin fashewa, yana kama da zunubi. Yana magana da zunubi, kamar haka. Misali, saboda wasu dalilai, mutum yana cike da rudani, keta, hassada, da makamantansu. Sannan kuma a wani wuri yakan fadi wata kalma wadda ko hankalin yaro ya gane cewa bai kamata ya fada ba, idan kuma ya fadi hakan to zai yi wa kansa illa - kamar wani dutse mai aman wuta da ke tashi daga ciki.

https://lms.motahari.ir/book-page/27/آشنایی%20با%20قرآن،%20ج10?page=193

Abubuwan Da Suke Tsarkake Zunubi

Mataki na farko na kankare zunubi shi ne tuba. tuba na gaskiya shi ne tuba da nadama ga zunubi, wanda ke buƙatar yanke shawara na barin aikata zunubi nan gaba.[22] Wani abu kuma bayan tuba shi ne gafaraf zunubi, wanda ya zo a cikin Alkur’ani a matsayin abin da ake bukata na gafarar Allah[23] Istighfari shi ne neman gafara daga Allah, tuba kuma yana nufin nadama akan aikata sabo. A cikin ayoyin Alkur'ani da dama, tuba da gafara suna haduwa.[24] daga cikin abin da ke kankare zunubai shi ne aikata ayyukan alheri.[25] takawa[26] da yin sadaka.[27] A cikin littafin Mizanul al-Hikma, a wani sashe mai suna “Mukaffirat Zunub” (masu kankare zunubai) an kawo wasu abubuwan da suke kankare zunubai bisa dogara da riwayoyi [28] A cewar wannan littafi, talauci, rashin lafiya, alheri, kuka. ga wanda aka zalunta, sujjada da suna daga cikin wadannan abubuwa.[29]

Tuba Daga Zunubi

A cikin madogaran fikihun Shi'a, a ko da yaushe ana jaddada wajabcin tuba ga zunubi, kuma ana ganin wajibcinsa na gaggawa, Sheikh Muhammad Hassan Najafi, [30] Sayyid Yazdi yana ganin tuba daga zunubai a matsayin lamari mafi muhimmanci kuma mafi wajabtar Wajibai [31] Kamar yadda ayoyin Alkur’ani da suka hada da aya ta 82 a cikin suratul Taha ta nuna cewa Allah yana karbar tuban mai zunubi kuma yana gafarta masa zunuban shi ko da wana iri ne.[32]

Isma wani Mukami na Nisantar Zunubi

A addini, Katanguwa daga aikata laifi wani hali ne da mutum ba ya yin zunubi [33] Irin wannan ana kiran shi da mutuman da baya laifi [34] A cewar Shi'a, wanda ba shi da laifi ba ya aikata zunubi da son rai,sabo da yasan munin zunubi da son zuciya mai karfi [35] Shi'a Imamiyya sun yi imani da cewa Annabawa da Imamai goma sha biyu da Hazrat Zahra (S) tsarkakakku ne daga aikata zunubi, suna da mukamin Isma. A cikin littafin Mizan al-Hikma, a wani sashe mai suna "Mukaffirat Zunub" (masu kankare zunubai) an kawo wasu abubuwan da suke kankare zunubai bisa ruwayoyi [36] A cewar wannan littafi, talauci, rashin lafiya, alheri, kuka. ga wanda aka zalunta, sujjada suna daga cikin wadannan abubuwa.[37]

Bayanin kula

  1. Qaraeti, Guna shinashi, 1377, shafi na 7.
  2. Sajjadi, Farhang Maarif Islamic, 1362, juzu'i na 2, shafi.429.
  3. Duba Qaraeti, Guna Shinasi, 1377, shafi na 7.
  4. Suratu Nisa aya ta 48 da 116
  5. suratu Lukman aya ta 13
  6. Suratul An'am, aya ta 21, 93 da ta 157; Suratul A'araf, aya ta 37; Suratul Yunus, aya ta 17; Suratul Kahf, aya ta 15; Suratul Ankabut, aya ta 68; Suratul Zammar, aya ta 32; Suratul Saf, aya ta 7; Suratul Nisa’i, aya ta 50. Suratul Hud, aya ta 18.
  7. Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsir Alqur’an, Part 8, shafi na 112.
  8. Tabatabaei, Al-Mizan fi Tafsir Alqur’an, juzu’i na 7, shafi na 44.
  9. Suratul Ma'idah, aya ta 72; Suratul Fatir, aya ta 37; Suratul Shuri, aya ta 8; Suratul Ghafar, aya ta 18; Suratul Furqan, aya ta 37; Suratul Ibrahim, aya ta 22; Suratul Al-Imran, aya ta 151; Suratul Ghafar, aya ta 52; Suratul A'araf, aya ta 44; Suratul Kahf, aya ta 29; Suratul Furqan, aya ta 27; Suratul Rum, aya ta 57; Suratul Mu’min, aya ta:52.
  10. Suratul Furqan, aya ta 68; Suratul Ma'idah, aya ta 29; Suratul Isra, aya ta 33
  11. suratu Ma'idah aya ta 32
  12. Duba Dasghib, Ghunahe Kabira, 1375, juzu'i na 1, shafi na 31; Qaraeti, Ghuna Shinasi, 1377, shafi na 13-15.
  13. Qaraeti, Ghuna Shinasi, 1377, shafi na 13
  14. suratu Nisa aya ta 31
  15. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1417H, juzu'i na 4, shafi na 323.
  16. Zadi, Al-Arwat al-Wuthqi, 1428 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 681.
  17. Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 276-278.
  18. Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 270 da 271.
  19. Kulainy, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 271; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 70, shafi na 327.
  20. suratu Shura aya ta 30
  21. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 70, shafi na 362.
  22. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, juzu'i na 24, shafi na 289.
  23. Suratul Al-Imrana, aya ta:135.
  24. Kayani Farid, "Toba", juz 8. zailu madkal
  25. Suratul Hud aya ta 114, Suratul Qasas aya ta 54.
  26. Suratul Anfal aya ta 29, suratun Nuhu aya ta 3 da ta 4, suratu Hadid aya ta 28.
  27. Suratul Baqarah aya ta 271.
  28. Duba Mohammadi Rishahri, Mizan al-Hikma, 1379, juzu'i na 4, shafi na 1906-1913..
  29. Duba Mohammadi Rishahri, Mizan al-Hikma, 1379, juzu'i na 4, shafi na 1906-1913.
  30. Kayani Farid, "Toba", juzu'i na 8.
  31. Suratul Hud aya ta 114, Suratul Qass aya ta 54.
  32. Suratul Anfal aya ta 29, suratun Nuhu aya ta 3 da ta 4, suratu Hadid aya ta 28.
  33. Mesbah Yazdi, Amuzeshe Akayid, 1378, juzu'i na 2, shafi na 31.
  34. Mesbah Yazdi, Amuzeshe Akayid, 1378, juzu'i na 2, shafi na 31
  35. Mesbah Yazdi, Amuzeshe Akayid, 1378, juzu'i na 2, shafi na 31
  36. Mesbah Yazdi, Amuzeshe Akayid, 1378, juzu'i na 2, shafi na 31
  37. Mesbah Yazdi, IAmuzeshe Akayid, 1378, juzu'i na 2, shafi na 30 da 31.

Tsokaci

  1. Allama Majlisi yana cewa: Allah ya halicci zuciyar mumini da haske kuma mai karbar siffofin haske, kuma da kowanne zunubi wani bangare na wannan haske yana canzawa zuwa baki (duhu) kuma da kowanne tuba yana komawa zuwa yanayin da ya kasance a baya, kuma idan zunubi ya ci gaba, duhun yana yaduwa har sai ya mamaye dukkan zuciya kuma zuciyar tana rasa damar karbar siffofin haske kuma sakamakon shine rashin samun ceto na har abada.

Nassoshi

  • Alqur'ani mai girma
  • Javadi Amoli, Abdullah, Tasnim, Ali Islami Research, Qum, Israa Publishing Center, bugu na biyu, 2007.
  • Khoei Saidabul al-Qasim, Sarat al-Najat, Musa Mofiduddin Asi Ameli, Qom, Makaranta Nasr al-Muntakhb, bugun farko, 1416H.
  • Dastghaib, Seyyed Abdul Hossein, Qom, Ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na 9, 1375.
  • Sobhani, Ja'far, Paqhufi Fi Millam da Al-Nahl; Dirasatu Maudu'iyya Lilmazahib Islamiyya, Qum, Cibiyar Gudanar da Seminary ta Kum, bugun farko, 1370.
  • Sadouq, Mohammad Bin Ali, Ma'ani-al-Akhbar, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1403H.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qum, Islamic Publications, bugu na biyar, 1417H.
  • Qaraati, Mohsen, Ghuna Shinasi, wanda Mohammad Mohammad Eshtherdi ya shirya, Tehran, Cibiyar Farahgani, Darussan Kur'ani, bugu na farko, 1377.
  • Kashif al-Ghata, Hassan bin Jafar, Anwar al-Faqaha, Najaf, Kashif al-Ghata Institute, bugun farko, 1422H.
  • Kulaini, Mohammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike na Ali Akbar Ghafari da Mohammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Kayani Farid, Maryam, "Tauba", Daneshanameh Jahani islami, Tehran, Islamic Encyclopedia Foundation, 2013.
  • Majlesi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaa Leder Akhbar al-Imaa al-Athar, Beirut, Darulfa, 1403 AH.
  • Mohammadi Rishahri, Mohammad, Mizan al-Hikma tare da fassarar Farisanci, wanda Hamidreza Sheikhi ya fassara, Qum, Dar al-Hadith, bugu na biyu, 1379.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, Amuzeshi Akayid, Tehran, Kamfanin Dillancin Labaran Musulunci na Duniya, bugu na biyu, 1378.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir al-Namuneh, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyya, 1371.
  • Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghqi, Qum, Imam Ali Bin Abi Talib Publications School, bugun farko, 1428H.