Jump to content

Ciyarwa A Ranar Ghadir

Daga wikishia
Ciyarwa A Ranar Ghadir
Shirye-shiryen dafa abinci da za a rabawa mutane dubu ashirin a ranar Idul Ghadir a haramin Abdul-Azim Hasani[1]
Shirye-shiryen dafa abinci da za a rabawa mutane dubu ashirin a ranar Idul Ghadir a haramin Abdul-Azim Hasani[1]
Lokacin da aka shirya18 ga watan Zil-Hijja na ko wace shekara
Wurin da aka shiryaMasallaci, gidaje, takaya da husainiyoyi
Tushe na tarihiSirar Ma'asumai (A.S)
Matsayin AlamiSabunta bai'a ga Imam Ali (A.S)


Ciyarwa a Ranar Ghadir (Larabciالإطعام في عيد الغدير) yana daga cikin ladubba da al'adun ƴanshi'a cikin girmama ranar ghadir wanda aka yi wasicci da yin hakan a ciki riwayoyi, kan asasin wata riwaya da aka naƙaltota daga Imam Rida (A.S), ladan ciyarwa a ranar ghadir dai-dai yake da ladan bakiɗayan Annabawa da Siddiƙai, an buƙaci ƴanshi'a gwargwadon ikon da mutum yake da shi da ya ciyar a wannan rana. Ciyarwa ranar Ghadir ana yi a ƙasashen Musulmi daban-daban kamar misalin ƙasar Iran, Afganistan, Fakistan da Turkiyya ta hanyoyi daban-daban, a ƙasar Iran mutane su na raba abinci a gidaje, masallatai da husainiyoyi, cikin biki mai nisan kilo mita goma wanda aka shirya shi a shekara ta 2023 m, haka an rarraba abinci cikin adadin Maukibai guda 1300.

Al'adar Ƴanshi'a

Shirya mutane dubu ashirin abinci a ranar Idul Ghadir wanda ya kasance a Haramin Shah Abdul-Azim Hasani a watan Yuli 2023.[2] Ciyarwa a ranar Ghadir ko kuma rabawa mutane abinci a ranar Idin Ghadir yana daga cikin al'adar da ladubban ƴanshi'a a ranar Ghadir,[3] ciyarwar ranar Ghadir ɗaya daga al'adun ƴanshi'a cikin godiya ga Allah a ranar Ghadir da kuma ƙara sabunta bai'a ga Imam Ali (A.S)[4] cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) an raɗawa ranar Ghadir suna ranar ciyarwa.[5]

Ciyawarwar Ghadir, wata al'ada ce da ta ja hankulan ƴanshi'a a ƙasashe daban-daban, a ƙasar Afganistan Sharifai suna raba abin ci da kuma bakance zuwa ga danginsu, 5 a wurare daban-daban a ƙasar Fakistan misalin garin Lahore, Karaci, Kuwaita da Peshawar nan ma ana shirya bikin Idin Ghadir tare da shimfiɗa shimfiɗar ciyarwa,[6] a ranar Ghadir Alawiyyawa cikin ba'arin yankunan ƙasar Turkiyya suna raba wani nau'in abin ci da ake kira da suna Huwaisa.[7]

A ƙasar Iran ana raya wannan al'ada cikin rabawa mutane abinci a gidaje da Husainiyoyi,.[8] cikin bikin Idul Ghadir mai nisan kilo mita goma wanda aka shirya shi a shekarar 2023 m, a babban birnin Tehran wannan bikin ya kasance tare da halartar baƙi mutum milyan ɗaya, sannan fiye da Maukibi 1300 suka yi tarayya cikin wannan biki[9] tare da hidima ga mutane da basu abinci, kuma an raba akushin abinci guda milyan ɗaya.[10]

Riƙo Da Wasicccin Imamai Da Sirarsu Cikin Ciyarwar Ranar Ghadir

Kan asasin wani gutsire daga rahotannin Imamai, sun kwaɗaitar da ƴanshi'a kan ciyarwa a ranar Ghadir; kamar yanda cikin hadisi aka yi umarni da ciyarwa a ranar ghadir kusa da umarnin ciyar da masu azumi, da kuma bada kyauta da sadar da zumunci,[11] cikin wata riwaya daga Imam Rida (A.S) ya buƙaci ƴanshi'a su ciyar ranar Ghadir gwargwadon ikon da mutum yake da shi.[12] Kan asasin wata riwaya daga littafai daban-daban misalin Misbahul Al-Mutahajjid na Shaik ɗusi wanda ya rasu 413 h ƙamari, an naƙalto cewa Imam Rida (A.S) a magaribar ranar ghadir ya dagatar da Sahabbansa a wurinsa domin su yi buɗa baki sannan kuma ya aikawa iyalansu da abinci tare da kyaututtuka.[13]

Ladan Ciyarwa A Ranar Ghadir

Cikin wata riwaya daga Imam Rida (A.S) an naƙalto cewa ladan ciyar da mumini a ranar ghadir daidai yake da ladan bakiɗayan Annabawa da Siddiƙai,[14] haka kuma cikin wata huɗubar Imam Ali (A.S) a ranar ghadir wace Imam Rida (A.S) ya naƙalto ta: "Duk wanda ya ciyar da mumini abincin buɗa baki a ranar Ghadir, an ce kamar ya ciyar da gungun Jama'a goma". Imam Ali (A.S) ya fassara duk gungun jama'a guda ɗaya yana daidai da Annabawa dubu ɗari da Siddiƙai da shahida, da kuma lamincin Allah daga kafirci da talauci ga waɗanda suke ciyarwa ranar Ghadir.[15]

Cikin wata riwaya an yi umarni da ciyar da Mabuƙata,[16] Muminai,[17] ƴan'uwa na addini[18] da bada buɗa baki ga masu azumi[19] a ranar Ghadir, mustahabbancin yin azumi ranar Ghadir[20] wani abu ne ya shahara a wurin ƴanshi'a[21]

Bayanin kula

  1. «اطعام غدیر / پخت و توزیع بیش از ۲۰ هزار غذا در روز عیدسعید غدیرخم / عکس: اسدی»،Tsarkakakken haramin Sayyid Abdul-Azim Hasani.
  2. «طعام روز غدیر؛ سنتی فراموش شده»، gidan labarai na Mehr.
  3. «آداب و رسوم کشورهای مختلف برای برگزاری عید ولایت»،Hukumar labarai Mehr
  4. «عید غدیر خم چه آداب و رسومی دارد؟»، Kamfanin labarai Mizan.
  5. Hali, Al-Adadul Al-Qawiya, 1408H, shafi na 169.
  6. «آداب و رسوم کشورهای مختلف برای برگزاری عید ولایت»،Kamfanin labarai Mehr.
  7. «Gadir Hum Nedir, Ğadir Hum Bayramı Nasıl Kutlanılır»، Bölge Gündem Haber.
  8. «جشن غدیر از آذربایجان تا خوزستان/سفره علوی در سراسر ایران پهن شد»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  9. «جزئیات جشن ۱۰ کیلومتری غدیر در تهران اعلام شد»، بCibiyar Labarai ta Jawanan.
  10. «برپایی پویش “اطعام غدیر” و جلب مشارکت مردمی، یک میلیون وعده غذا را در سراسر کشور طبخ و توزیع شد»، بنیاد کرامت رضوی.
  11. Hali, Al-Adadul Al-Qawiya, 1408H, shafi na 169.
  12. Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411H, juzu'i na 2, shafi na 757.
  13. Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 758; Ibn Tawoos, Iqbal al-Aqmaal, 1409 AH, Juzu'i na 1, shafi na 461.
  14. Ibn Tawoos, Iqbal Al-Amal, 1409H, juzu'i na 1, shafi na 465.
  15. Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 758; Ibn Tawoos, Iqbal Al-Amal, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 463-464; Kafami, Al-Masbah, 1405 AH, shafi na 700; Sheikh Hurrul Amili, Wasa'il Al-Shia, 1409 AH, juzu'i na 10, shafi na 445.
  16. Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 757; Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 94, shafi na 117.
  17. Ibn Tawoos, Iqbal al-Amal, 1409 AH, Juzu'i na 1, shafi na 463.
  18. Ibn Tawoos, Iqbal al-Amal, 1409 AH, Juzu'i na 1, shafi na 475.
  19. Sheikh Tusi, Misbah Al-Mutahajjid, 1411H, juzu'i na 2, shafi na 758
  20. Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, Beirut, juzu'i na 8, shafi na 284.
  21. «آیا حدیث اطعام روز غدیر امام صادق(ع) صحت دارد؟»، *Dey News

Nassoshi

«برپایی پویش “اطعام غدیر” و جلب مشارکت مردمی، یک میلیون وعده غذا را در سراسر کشور طبخ و توزیع شد»،"Bunyade Karamat Razavi, Ranar wallafa: 8 Murad 1400 (Kalanda na Iran), Ranar ziyara: 28 Aban 1402 (Kalanda na Iran)."