Jump to content

Daƙiƙa:Jihadin Bayyanawa

Daga wikishia

Jihadin bayyanawa, ana fahimtarsa a matsayin aikin wayar da kai da bayyana gaskiya bisa bincike da aikin ilimi, domin tunkarar abokan gaba da kuma yaudarar da suke yaɗawa. An fara amfani da wannan kalma ne daga bakin Ayatullah Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a watan Ordibehesht shekarar 1395sh (Mayu 2016). Daga baya, a Azar 1400sh (Disamba 2021), ya yi bayani dalla‑dalla tare da nazari kan ma'anarta. A cewarsa, tushen wannan ra'ayi yana fitowa ne daga wasiyyar Imam Ali (A.S) Hasanaini (Hassan da Husaini). Ya bayyana cewa idan aka aiwatar da wannan aiki yadda ya kamata, zai haifar da sakamako kamar: hana karkatar da gaskiya, kare goyon bayan jama'a ga al'umma, da kuma taimakawa wajen magance matsaloli.

AyatullahKhamna'i ya kuma nuna cewa akwai batutuwa da dama da suke buƙatar a bayyana su da gaskiya. A ganinsa, irin wannan bayyanawa ya kamata a yi shi bisa salon Annabawan Allah da Imaman Shi'a, waɗanda ake kallonsu a matsayin jagorori na farko a irin wannan jihadi, domin a kiyaye kyawawan ɗabi'u da ladabin Musulunci yayin gudanar da shi.

Gabatar da wannan ra'ayi daga gare shi ya jawo tattaunawa da martani a tsakanin malamai na hauza (Makarantar addini), jami'o'i, da kuma hukumomin gwamnati a ƙasar Iran. Daga cikin abubuwan da suka biyo baya akwai wallafa wani littafi mai taken Jihad Tabyin da harshen Farsi da Larabci, da kuma kafuwar wasu ƙungiyoyi a wasu biranen Iran da ake kira Cibiyoyin ko rundunonin Jihadin Bayyanawa

Nazarin Ma'ana

Asalin marubuci: Ayatullah Khamna'i Ayatullahi Khamna'i, jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya bayyana "Jihadin Bayyanawa" da cewa shi ne gudanar da aikin ilimi da bincike, yin magana da bayyana gaskiya domin tinkarar abokan gaba da kuma kawar da yaudarar da suke yaɗawa.[1]

Ya fara ambaton wannan kalma a watan Ordibeheshti shekarar 1395sh (Mayu 2016),[2] sannan a Azar shekarar 1400sh (Disamba 2021) ya yi cikakken bayani a kanta.[3] Duk da haka, tun kafin wannan lokaci ma ya kan yi nuni da irin wannan ra'ayi, yana mai cewa idan aka bayyana tunanin Musulunci yadda ya kamata, mutane za su gamsu a fannin tunani, kuma hakan zai motsa su su bi tafarkin manufofin Musulunci.[4]

Har ila yau, yana ganin wasu kalmomi kamar "Jihadin riwaya"[5] "motsin bayyanawa",[6] "yaɗawa",[7] da "wayar da kai"[8] suna da ma'ana iri ɗaya ko kuma suna tafiya daidai da ma'anar Jihadin Bayyanawa.[9]

Matsayi Da Muhimmancin Jihadin Bayyanawa

' Jihadin Bayyanawa na Fāṭima Zahra (A.S):'
Sayyid Ali Khamna'i:

Daga cikin siffofi masu girma fitattu na Faɗima Zahra (A.S), ɗaya daga cikin mafi shahara shi ne jihadin bayyanawa da ta yi.

Ta gabatar da jawabai biyu masu matuƙar muhimmanci da shahara. Na farko shi ne jawabin da aka sani da wanda ta fara da kalmomin: "Alḥamdu lillāhi ala ma an'ama wa lahu al‑shukru alā ma alhama", wanda ta yi a gaban sahabbai. Game da wannan jawabi, wasu malamai sun ce yana cikin manyan huɗubobin da suka yi kama da mafi kyawun hudubobin Nahjul Balaga. Masu ilimin balaga da fahimta sun bayyana cewa wannan huɗuba ta cika da ma'arifa, hikima, da manyan gaskiyoyi.

Jawabi na biyu kuwa shi ne wanda Sayyida Faɗima (A.S) ta yi ga matan Muhajirun da Ansar, inda ta fara da kalmomin:

"اَصبَحتُ وَ اللَهِ عائِفَةً لِدُنیاکُم قالِیَةً لِرِجالِکُم» یا «عائِفَةً لِدُنیاکُنَّ قَالِیَةً لِرِجالِکُنَّ").

Waɗannan jawabai biyu ana kallonsu a matsayin misalan jihadin bayyanawa na Faɗima Zahra (A.S), waɗanda ta gabatar a cikin ɗan gajeren lokaci bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W), domin bayyana gaskiya da kare saƙon Musulunci.

.Jawaban Ayatullah Khamna'i a taron ganawa da mawaƙa masu yabon Ahlul-Baiti (A.S)[10]

A cewar Sayyid Ali Khamna'i, kalmar "Jihad Tabyin" (Jihadin Bayyanawa) ta samo asali ne daga wannan sashe na wasiyyar Imam Ali (A.S.) "Ina haɗaku da Allah! ina haɗaku da Allah! ku yi jihadi da dukiyarku, da rayukanku, da harsunanku a cikin tafarkin Allah."[Tsokaci 1][11] ga Hasanaini[12] Ya bayyana cewa wannan kalma an samo ta ne daga wannan magana. Haka kuma ya ce hanyar jihadin da yawancin Ahlul-Baiti (A.S) suka bi ita ce jihadin bayyanawa, wato jihadin bayyana gaskiya da ilimantar da mutane.[13]

Ya kuma nuna muhimmancin bayyana da fassara addini da fahimtar Ahlul Baiti (A.S.),[14] yana mai cewa "jihadin bayyanawa" wajibi ne na shari'a ga kowa, kuma wajibi ne na gaggawa (wato wajibi ne da ya kamata a aiwatar da shi a farkon lokacin da ya yiwu).[15]

A cewarsa, ɗaya daga cikin sakamakon Jihadin Bayyanawa shi ne hana karkatar da gaskiya; wato hana sauya ko ɓatar da gaskiyar tarihi, misali irin yunƙurin tsarkake ko kyawuntar fuskar mulkin Pahlawi.[16] Haka kuma ya bayyana cewa daga cikin tasirin Jihadin Bayyanawa akwai: Ƙirƙirar gaɓa ko ra'ayin jama'a wato samuwar wata fahimta ko tunani da ya zama ruwan dare a tsakanin mutane kuma ya zama abin da jama'a ke nema.[17] Kare goyon bayan jama'a a cikin al'umma, wato tabbatar da cewa mutane suna ci gaba da kasancewa a cikin harkokin zamantakewa da al'amuran jama'a.[18] Har ila yau, ya yi imani cewa magance matsaloli da wahalhalu ma na iya yiwuwa ta hanyar Jihadin Bayyanawa. Wato idan masu tunani, malamai, da masu al'adu da adabi suka yi bayani mai kyau, mai ma'ana, kuma a kan lokaci, to mutane za su iya taimakawa wajen warware matsalolin da ake fuskanta.[19][20]

A gefe guda kuma, Aminul Islam Ɗabrisi, marubucin tafsirin Majma'ul Bayan, a cikin bayaninsa kan aya ta 52 Suratul Furƙan: "Kada ka bi kafirai, kuma ka yi jihadi da su da shi (Al‑ƙur'ani) jihadi mai girma."

Ya ce wannan aya tana nuna cewa jihadin malamai masu muhawara (Mutakallimun) wajen kawar da shubuhohi da masu ƙin addini ko maƙiyan addini ke jefa wa mutane yana daga cikin mafi girman jihadi kuma yana da matsayi na musamman a wajen Allah.

Har ila yau, wataƙila abin da ake nufi da "jihadul Akbar" (babban jihadi) a cikin hadisin Annabi: "Mun dawo daga ƙaramar jihadi zuwa babbar jihadi"[Tsokaci 2] yana nufin jihadi da Al‑ƙur'ani da kuma tunkarar shubuhohi da ƙaryar maƙiyan addini.[22]

Batutuwan Da Suke Buƙatar Bayyanawa

A ra'ayin AyatullahKhamna'i, wasu daga cikin batutuwan da ke buƙatar bayani : sun haɗa da: Batutuwan Da Suke Buƙatar Bayyanawa

Batutuwan da suke buƙatar bayani
'Sahu' 'Misalin da ke bayyana abu' 'Dalili'
1 Bayyana Nasororin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana taka rawa wajen ƙarfafa cimma tushen goyon bayan jama'a ga tsarin da kuma kiyaye ɗorewarsa.[23] Domin abokan gaba na ƙoƙarin zuga jama'a cewa tsarin ba ya aiki yadda ya kamata[24] Kuma yana nuna wa mutane nasarorin da Iran ta samu bayan juyin juya halin Musulunci a matsayin ƙanana ko marasa muhimmanci.[25]
2 Hanyar fita daga matsalolin tattalin arziƙi ita ce dogaro da damar cikin gida kamar “tattalin arziƙin juriya da kuma amfani da ƙwarin matasa.[26] و An ɗauki ba da fifiko ga samarwa na cikin gida a matsayin muhimmin abu, wanda yake buƙatar bayani da wayar da kai.[27][28]
3 Rubuta tarihin zamanin Mashrūɗiyya bisa hujjoji da takardu na daga cikin batutuwan da ya kamata a yi masa bayani sannan a wallafa shi a matakai daban‑daban (na ɗaliban makaranta da na jami'a, da kuma na ilimi da bincike).[29]Domin gaskiyar wannan lokaci na tarihi da kuma danniyar da aka yi wa mutane a wannan lokacin ta hannun wasu gwamnatoci masu alaƙa da ƙasashen Yamma, suna buƙatar a bayyana su a sarari.[30]
4 Haɗarin kutsen tasiri Batun kutsen tasiri a cikin ƙasar Iran an bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye‑shiryen abokan hamayya, kuma ana ganin yana gudana ne da nufin canza yadda shugabanni ke yin lissafi da yanke shawara wajen tafiyar da ƙasa, da kuma canza ra'ayoyin jama'a game da siyasar Musulunci da juyin juya halin Musulunci na Iran.[31] Wannan ma batu ne da ya kamata a bayyana wa dukkan mutane na al'umma, kamar yadda ake bayyana batun yaƙi da takunkumi..[32]
۵ Ra'ayin gwagwarmaya Domin kada a ɗauka cewa… Saboda abversari (maƙiyi) yana da bama-bamai, makamai masu linzami, ko kuma na'urorin yaɗa labarai da kafafen watsa shirye‑shiryen ƙarfafa, ba yana nufin ya kamata mu ja da baya ba; dole ne a fayyace kuma a yaɗa ka'idar asali ta “Juriyar tsayuwa” (resistance) ta fuskar ilimi da ta aiki.[33]
6 Salon rayuwar Musulunci Salon rayuwa ya kamata ya kasance bisa fayyace bayanin tushen ilimomin Musulunci..[34][35] Domin salon rayuwa mara kyau—wanda yake fitowa daga matsalolin al'adu da kuma al'adar da ta mamaye tunanin mutane—yana samuwa ne sakamakon kwaikwayon salon rayuwar Yammacin duniya.<[36]
7 Kiyaye haɗin kai Manufar haddasa rarrabuwa tsakanin musulmi -daga ɓangarorin da ke adawa da Musulunci - ta fi kowace yaƙi na soja ko motsi na siyasa ko ƙalubalen tattalin arziƙi araha (watau tana fi su sauƙin aiwatarwa kuma tana fi su amfani gare su).[37] Ana aiwatar da hakan ne da niyyar galabaitar bangaren gaskiya da tilasta masa yin ja da baya; don haka ya zama wajibi a yi aiki akasin hakan — wato, a ƙarfafa batutuwan da ke haɗa kan mutane da yaɗa saƙonnin haɗin kai..[38]
8 Haƙƙoƙin Mace Bayyana haƙƙoƙin mata da bambance-bambancen su da haƙƙin maza, yana da muhimmanci, kuma dole ne a yi hakan bisa ga koyarwar Musulunci da kuma yanayi da halittar ɗabi'a ta kowannensu.[39] Domin a ƙasashen Yamma, da sunan 'yanci, mace ta fuskanci zalunci kuma an wulaƙanta ta (wato an lalata haƙƙoƙinta da ƙimarta); saboda haka bayyana wannan lamari yana da muhimmanci..[40]
9 Iyali da haihuwar ƴaƴa Mace da uwa su ne ginshikin iyali, wanda kuma a kan lokaci haihuwar 'ya'ya ya rataya a wuyansu, kuma bayyanar da wannan al'amari na daga cikin muhimman ayyuka na asali[41] Domin a ƙasashen Yamma, ta hanyar kafafen yaɗa farfaganda, an yi ƙoƙari a rage muhimmancin matsayin mace da na uwa, tare da rage darajar ayyuka da hidimomin da mace ke bayarwa[42]
10 Hijabi Hijabi yana daga cikin ƙimomin da suka dace da halittar ɗan adam, kuma ya kamata a bayyana shi kuma a inganta shi.[43]Domin tsiraici, wanda ya saba da halittar ɗan adam, ya samo asali ne daga yaɗa fina‑finan da ke nuna rayuwar mutanen Yamma, kuma yana da tasiri mara kyau ga rayuwar mutum ɗaya da ta zamantakewa gaba ɗaya[44]
11 Hankalin aiki da bin doka a zamantakewa: ayyukan tattalin arziƙi, na al'adu, na siyasa da na zamantakewa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna buƙatar a bayyana su da kuma a yaɗa su yadda ya kamata cikin tsari da ƙarfi..[45] Domin samar da ruhin kishin aiki da kuma ladabi/tsari na zamantakewa yana samuwa ne sakamakon kyakkyawan tsari da shirye‑shirye da kuma yaɗa su; domin ayyuka su samu daidaito da ƙarfi[46]
12 Darajar malami Yaɗa da bayyana matsayi Malami A cikin jama'a, saboda rawar da yake takawa wajen tarbiyyar “Ƙarfin ɗan adam na daidaito na Jamhuriyar Musulunci ta Iran,” yana daga cikin ayyuka masu muhimmanci da dole..[47]
13 Sadaukarwa a cikin Tsaron Ƙasa Mai Tsarki An buƙaci masu shirya fina‑finai da sauran masu sana'ar fasaha su bayyana.[48] Domin ƙungiyoyin da suka ɗauki nauyin tallafa wa yaƙin suna amfani da damar ruhaniya da na kayan aikinsu wajen kare juyin juya halin Musulunci na Iran.[49]
14 Tarihin rayuwa da ɗabi'un shahidai Halaye na rayuwar mutum ɗaya da ta zamantakewa na shahidan zamanin Tsaron Mai Tsarki, kamar yadda suke a hakikanin gaskiya, suna buƙatar bayani da gabatarwa ta fuskar ilimi da fasaha.[50] Halaye na rayuwar mutum ɗaya da ta zamantakewa na shahidan zamanin Tsaron ƙasa Mai Tsarki, kamar yadda suke a hakikanin gaskiya, suna buƙatar bayani da gabatarwa ta fuskar ilimi da fasaha.[51]
15 Ranakun Allah Allah A wani ɓangare na aya ta 5 ta Suratul Ibrahim, an umarci Manzon Allah (S.A.W) da ya tunatar da mutane ranakun Allah (ayyāmu‑llāh), domin kada su zamo abin mantuwa..[52] Domin kuwa waɗannan ranaku sun kasance masu gina tarihi, wato sun yi tasiri a cikin harkokin siyasa, zamantakewa da al'adu.؛[53] da kuma ranaku kamar 19 De 1356 shamsi،[54] 29 Bahman shekarar[[1356 Shamsi|1977 Miladiyya]،[55] 22 Bahman 1977 Miladiyya[56] Da kuma janazar Shahid Ƙasim Sulaimani) An kuma kira su ranakun Allah (Ayyāmullāh) a cikin watan De na shekarar 1398 Hijirar Shamsiyya (Disamba 2019 – Janairu 2020m)..[57]
16 Jamhuriyar Musulunci «Jamhuriyar Musulunci wadda take neman samar da«Dimokuraɗiyyar Addini» ('Yancin mutane a cikin … amma cikin tsarin ƙa'idojin Musulunci.[58] dole ne a fayyace ta (a bayyana ma'anarta), domin wannan kalma baya ga ƙimomin ruhi da na tauhidi tana ɗauke da nufin jama'a (shawarar mutane) tare da ita, ba kuma ta tilasta wa mutane komai ba..[59]
17 Darajojin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran batutuwa kamar Rayuwa Mai Kyau (Rayuwa mai daɗi a duniya da lahira.)،[60] «Adalcin zamantakewa shi ne raba damarmaki da albakatun ƙasar Iran cikin adalci da hikima[61] «Ƴanci da ƴanci kai da suke dogara da abokan gaba da baƙi[62] Suna daga cikin manufofi da burikan juyim juya halin Musulunci na Iran waɗanda suka buƙatar ƙarin bayani da fayyacewa.[63] Saboda manufar bayyana su ita ce kubuta daga mamayar girman kai na duniya (Gwamnatin Amurka).[64] An sani cewa idan ba a bayyana su ba, to hakan yana haifar da rikicewa da rudani.[65]
18 Bayyana ƙimar aiki da ma'aikaci ga dukkan mutane cikin al'umma ta Musulunci na daga cikin aikace‑aikacen shugabanni..[66] Domin ban da cewa a Musulunci yana da ƙima,،[67] yana biyan bukatun halittar ɗan Adam (kamar samar da abinci, tufafi da sauransu).[68]
19 Bayyanawa da haskaka ƙa'idar mulkin addinin Musulunci a kan dukkan al'amuran rayuwar mutum an ɗauka a matsayin aikin dukkan masu tunani da masana a fannoni daban‑daban da kuma a hujjar ilimi (hawza ilmiyya)..[69] Domin ƙoƙarin maƙiya bayan kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kasance a kan cewa a takaita "Musulunci ga aikace‑aikacen mutum ɗaya da kuma imanin zuciya", sannan a tabbatar da cewa ba shi da alaƙa da al'amuran zamantakewa da rayuwar jama'a..[70]

Misalai Abin Koyi

Don ƙarin bayani, a duba kuma: Mutum Mai Shekara 250 Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana danganta da wani ɓangare na huɗuba ta farko a Nahju al‑Balāgha, ya bayyana annabawan Allah a matsayin tushen masu aikin bayyanawa,[71] kuma ya yi imanin cewa bayyanawa shi ne mafi muhimmancin aikinsu.[72] A cewarsa, Annabi na ƙarshe (S.A.W) ma, duk da wahalhalu da yawa a farkon kiran mutane zuwa Musulunci, ya kasance yana bayyana gaskiyar saƙonsa.[73]

Har ila yau, ya ɗauki bayyanawa da wayar da kai a matsayin ɗaya daga cikin siffofin gwamnatin Imam Ali (A.S), kamar yadda yake bayyana a cikin huɗubobi da wasiƙu na Nahjul Balaga.[74]

Haka kuma yana ganin cewa layin jihadi da gwagwarmaya na Imaman Shi'a (A.S.) ya ci gaba a cikin tsawon shekaru 250 a siffofi daban‑daban, kuma manufarsa ita ce bayyana Musulunci tsantsa, fassarar da ta dace ta Alƙur'ani, da kuma batun Imama.[75]

Ya kuma kawo wasu misalan ababen koyi, kamar ƙoƙarin Sayyida Zainab (A.S) wajen bayyana gaskiyar Ashura a Kufa da Sham.[76]

Haka nan yana ganin cewa wasu sahabban Annabi (S.A.W) kamar Ammar bin Yasir ma sun yi wayar da kai da bayyana gaskiya a lokacin yaƙin Siffin.[77]

Ayatullahi Khamna'i ya kuma ambaci mutane kamar Imam Khomaini,[78] Sayyid Asadullah Madani,[79] Murtada Muɗahhari, da Sayyid Muhammad Beheshti a matsayin misalan masu bayyanawa, yana mai cewa su ma sun kasance suna bayyana gaskiyar addini ga mutane.[80]

Ƙa'idojin Ɗabi'a

Ayatullahi Khamna'i ya bayyana cewa bayyanawa da wayar da kai dole ne su kasance tare da kula da ɗabi'a da ladabin Musulunci, kuma ya jaddada muhimmancin nisantar munanan kalamai da cin mutunci.[81]

Ya kuma yi ishara da wani ɓangare na huɗuba ta 206 a Nahjul Balaga, inda ya ba masu yin bayyanawa shawara da su nisanci gulma (Gība) da zargi mara hujja (Tuhuma), kuma ya yi imanin cewa ya kamata a guji magana ba tare da ilimi ba, kamar ƙarya.[82]

A ganinsa, kula da ɗabi'a da ladabin Musulunci a rubuce‑rubuce ma wajibi ne. Saboda haka ya ce jaridu da kafafen watsa labarai su guji rigingimu ƙanana marasa muhimmanci, kuma kada su shiga yaɗa jita‑jita.[83]

Martanoni Da Ra'ayoyi

Kalaman Ayatullah Khamna'i game da "Jihadin Bayyanawa" sun haifar da martani iri‑iri daga malamai na hauza, malamai na jami'a, da hukumomin gudanarwa a Iran.

  • Ali Zu Alam, wanda yake daga cikin malamai a Cibiyar Juyin Juya Hali, yana ganin cewa Jihadin Bayyanawa dole ne ya kasance a cikin yanayin hankali, dimokuradiyya, ƙa'ida, da ci gaban al'umma domin ya yi tasiri yadda ya kamata.[84]
  • Hadi Sadiƙi, malami a jami'a da hauzar Qum, ya bayyana cewa littafin Haske a Basirar Imam – wasiƙar 26 Maris 1989 miladiyya." na marigayi Muhammad Muhammadi Rai Shahri yana daga cikin misalan Jihadin Bayyanawa, domin marubucin ya yi ƙoƙarin bayyana tunanin Imam Khomaini tare da kawar da kuskuren fassara da ake yi a kansa..[85]
  • Muhammad Hassan Zamani ya bayyana cewa Ayatullah Khamna'i yana jaddada yaɗa wannan nau'in jihadi a tsakanin al'umma saboda, a fahimtarsa, yaƙin kafofin yaɗa labarai na ƙasashen waje yana ƙoƙarin rage girman nasarorin Iran da faɗaɗa matsalolinta, kuma Jihadin Bayyanawa yana taimakawa wajen tinkarar wannan tasiri.[86]
  • Majalisar Dokokin Iran ta amince da wani kasafin kuɗi domin tallafa wa Jihadin Bayyanawa, amma Ayatullah Khamna'i bai goyi bayan wannan mataki ba, yana ganin cewa irin waɗannan kuɗaɗe galibi ana yin ɓarna da su ba tare da samun ingantaccen sakamako ba.[87]
  • Bayan jawabin sa, an kafa "Hedikwatar Jihadin Bayyanawa" a wasu garuruwa kamar Qum,[88] Shahrekorde,[89] Nahawandi[90], da Khuzestan, domin su bayyana wa jama'a ayyukan da hukumomin gwamnati ke aiwatarwa da kuma ɗaukar nauyin wayar da kan al'umma.[91]

Bayanin kula

  1. بیانات در دیدار مداحان اهل‌بیت(ع)، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  2. Khamna'i, Jihade Tabyin, sh 23
  3. بیانات در دیدار پرستاران و خانواده شهدای سلامت،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  4. Khamna'i, Jihade Tabyin, sh 43
  5. بیانات در دیدار پرستاران و خانواده شهدای سلامت،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  6. Khamna'i, Jihade Tabyin, sh 23
  7. Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i..
  8. بیانات در دیدار ائمه جمعه سراسر کشور،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  9. Khamna'i, Jihade Tabyin, sh 23
  10. https://farsi.khamenei.ir/newspart-index?tid=4082
  11. Nahjul Balaga, Tas'hihu Subhi Salih, name 47, sh 422"
  12. بیانات در دیدار اعضای مجلس خبرگان رهبری، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i."
  13. بیانات در دیدار مداحان اهل‌بیت(ع)،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  14. پیام به کنگره‌ی علمی بین‌المللی امام علی‌بن‌موسی‌الرضا(ع)، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  15. بیانات در دیدار فرماندهان و کارکنان نیروی هوایی و پدافند هوایی ارتش، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  16. بیانات در دیدار جمعی از دانشجویان،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  17. بیانات در دیدار رئیس و اعضای مجلس خبرگان رهبری، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  18. بیانات در اجلاس جهانی علما و بیداری اسلامی،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i."
  19. ديدار چند تن از شخصيت‌هاى فرهنگى، مذهبى و علمى جهان اسلام، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  20. بیانات در پایان مراسم عزاداری اربعین حسینی، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i."
  21. Majlisi, Raudatul Muttaƙin, Sh 599
  22. Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, Sh 303
  23. Khamna'i، Armaƙan، Sh 4.
  24. بیانات در دیدار کارگزاران نظام‌, Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  25. بیانات در مراسم پانزدهمین سالگرد رحلت امام خمینی (رحمه‌الله)، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  26. بیانات در جلسه تبیین سیاست‌های اقتصاد مقاومتی،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  27. بیانات در دیدار مسئولان نظام،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  28. بیانات در جلسه تبیین سیاست‌های اقتصاد مقاومتی،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  29. ‌‌‌بیانات در دیدار شورای مرکزی و کمیته‌‌های علمی همایش صدمین سالگرد مشروطیت، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  30. بیانات در خطبه‌های نمازجمعه، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  31. بیانات در دیدار رئیس و اعضاى مجلس خبرگان رهبرى، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  32. بیانات در دیدار اعضای شورای هماهنگی تبلیغات اسلامی، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  33. بیانات در دیدار دانش‌آموزان و دانشجویان، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  34. بیانات در دیدار جمعى از دانشجویانShafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  35. بیانات در دیدار اعضای مجلس خبرگان رهبری،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  36. بیانات در نخستین دیدار رئیس‌جمهور و اعضای هیئت دولت سیزدهم، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  37. ‌بیانات‌ در دیدار کارگزاران حج، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  38. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 247–248.
  39. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 243.
  40. بیانات در دیدار بانوان نخبه‌ در آستانه سالروز میلاد حضرت زهرا(س)، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  41. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 244–245.
  42. بیانات در ارتباط تصویری با مداحان، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i..
  43. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 246
  44. بیانات در جلسه پرسش و پاسخ مدیران مسئول و سردبیران نشریات دانشجویی، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  45. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 284.
  46. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 285..
  47. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 286-287
  48. بیانات در دیدار عوامل تولید فیلم سینمایى «شیار ۱۴۳»، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  49. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 274-275.
  50. بیانات در دیدار اعضای برگزاری کنگره شهدای استان‌های کهگیلویه و بویراحمد و خراسان شمالی، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i..
  51. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 278-280
  52. بیانات در دیدار دست‌اندرکاران راهیان نور، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  53. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 271-272
  54. مبدأ تاریخِ تحولات جدید دنیا، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i..
  55. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 271-272
  56. بیانات در دیدار فرماندهان و کارکنان نیروی هوایی ارتش، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  57. خطبه‌های نماز جمعه تهران، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  58. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. -96
  59. Khamna'i , Jihad Tabyin, sh. 202-203
  60. Khamna'i, Roshnayi Ayandeh, sh 3
  61. Khamna'i, Roshnayi Ayandeh, sh 67 da 73.
  62. Khamna'i, Roshnayi Ayandeh, sh 50.
  63. Khamna'i، Jihade Tabyin, Sha 216.
  64. Khamna'i , Falasɗinu, ṣ. 142..
  65. بیانات در دیدار شرکت‌کنندگان در اجلاس جهانی اساتید دانشگاه‌های جهان اسلام و بیداری اسلامی، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  66. بیانات در دیدار کارگران، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  67. Ibn Athīr, Usdul al‑Ghābah, j. 2, ṣ. 269..
  68. Khamna'i , Jihad Tabyin, ṣ. 282-284..
  69. Khamna'i , Jihad Tabyin, ṣ 194
  70. Khamna'i , Jihad Tabyin, ṣ 188
  71. Khamna'i, Jihade Tabiin, sh 75-76.
  72. بیانات در دیدار مسئولان نظام و سفرای کشورهای اسلامی،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  73. Khamna'i, Siyasat, sh 324
  74. Khamna'i, Jihade Tabyin, sh 78
  75. Khamna'i, Amine Zamane Wa Adab Farsi,1397Sh, Sh 234.
  76. Khamna'i, Aftabe Dar Mosaf, Sh 272.
  77. Khamna'i, Jihade Tabyin, 1400sh, sh 82-83.
  78. Khamna'i, Ma'arif Inƙilab, Sh 445.
  79. بیانات در دیدار با اعضای کنگره بزرگداشت شهید آیت‌الله مدنی‌،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  80. Khamna'i, Hauze Wa Ruhaniyat, Sh 1086
  81. Khamna'i, Jihade Tabyin, 1400sh, sh 99.
  82. بیانات در دیدار کارگزاران نظام‌، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  83. Ghaffari, Fitna‑ye Taghallub, shafi na 412.
  84. «جهاد تبیین»؛ مقدمه‌ای برای اصلاح، تحول و مطالبه،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan AyatullahKhamna'i.
  85. آخرین اثر آیت‌الله ری‌شهری مصداق «جهاد تبیین» است، Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullah Khamna'i.
  86. راز تاکید رهبر معظم انقلاب بر جهاد تبیین چیست؟، Shafin yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Daliban Iran (ISNA).
  87. رهبر انقلاب: تخصیص بودجه سنگین برای جهاد تبیین، غلط است، Shafin yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Daliban Iran (ISNA).
  88. تشکیل قرارگاه عملیاتی‌ "جهاد تبیین"‌ و پیگیری تبیین ارزش‌ها، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Imna.
  89. قرارگاه جهاد تبیین در چهارمحال و بختیاری فعال شد،Shafin yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
  90. تشکیل قرارگاه جهاد تبیین در شهرستان نهاوند، Shafin yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Mehr.
  91. نشست قرارگاه جهاد تبیین استان خوزستان برگزار شد، Shafin yanar gizo na Gwamnatin Lardin Khuzestan.

Tsokaci

  1. Ku ji tsoron Allah! Ku ji tsoron Allah! Kada ku yi sakaci wajen yin jihadi da dukiyarku, da rayukanku, da harshenku a tafarkin Allah
  2. Wasu daga cikin rahotanni, Annabi Muhammad (S.A.W) bayan ya dawo daga Yaƙin Tabuk, ya faɗi wannan magana: "Mun dawo daga ƙaramin jihadi zuwa ga babban jihadi.[21]

Nassoshi

Ranar wallafa: 30 Afrilu 2022. Ranar dubawa: 5 Disamba 2022M.