Haihuwar ƳaƳa

Daga wikishia

Haihuwar ƴaƴa (Larabci: إنجاب الأطفال) ana lissafa shi matsayin abu mai kyau a mahangar kur'ani da hadisan ma'asumai. addu'ar da Annabi Ibrahim (A.S) da Annabi Zakariyya (A.S) su ka yi na roƙon Allah ya azurta su da zuriya alhalin lokacin sun rigaya sun tsufa, da busharar Allah da amsa addu'arsu, duka alamu ne da suke nuni kan irin muhimmancin da wannan batu yake da shi. haka nan ya zo a hadisi da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) cewa ranar ƙiyama zai yi alfahari da yawan al'ummarsa.

Rage yawan haihuwa yana haifar da mummunan sakamako, daga jumlarsu akwai rage bunƙasar tattalin arziƙi da haifar da matsalar samun wadatattun matasa da za su cike guraben ayyuka da ake buƙatarsu su cike su, da kuma samun matsala a ɓangarorin siyasa da al'adu. Wasu na ganin yawan haihuwa ƴaƴa na yin tasiri mara kyawu cikin tarbiyta da tattalin arziƙi, tare da tasirin mai girma cikin canja salon rayuwar mutane, masu adawa da ragen yawan haihuwa suna cewa shi arzikin duk wani yaro da aka haifa yana hannun Allah , shi ne mai lamintar da arziƙin kowa da kowa. Haka nan sun yi imani da cewa idan har haihuwa za ta zama matsala a batutuwan da aka ambata to ya kamata mu samu masu haihuwar yaro guda ɗaya su masa tarbiyyar ta musammam ta buga misali.

Sakamakon ƙaruwar al'umma a ƙasar Iran a shekaru 40 da suka gabata gwamnati ta ƙarfafi siyasar konturon din yawan haihuwa; sai dai kuma a shekarar 2012 miladi Ayatullahi Khamna'i ya bayyana cewa ci gaba da tafiya kan siyasar ragen yawan haihuwa kuskure babba, ya ƙarfafa larurar siyasar yawaita haihuwa. Majalisar shura islami Iran, a ranar 24 ga watan shekara 2021 miladi sun rattaba hannu kan dokar ƙarfafar samar da iyalai matasa.

Matsayi

Cikin kur'ani an ambaci ɗa da siffofi da kalmomi misalin ni'ima[1] adon rayuwa,[2] hasken idanu,[3] sababin taimakon Allah.[4] waɗannan siffofi da aka faɗa kan ɗa suna bayyana kasancewar haihuwar ƴaƴa matsayin abu mai kyawu a mahangar kur'ani.[5] haka nan addu'ar da Annabi Ibrahim (A.S) [6] da Annabi Zakariyya (A.S) [7] suka domin neman zuriya lokacin da sun rigaya sun tsufa da kuma busharar Allah da amsa addu'arsu[8] suma duka alamu ne da suke nuni da irin muhimmancin da batun haihuwar ƴaƴa yake da shi a mahangar kur'ani.[9]

Cikin riwayoyi ma akwai adadin hadisai da aka rawaito daga ma'asumai da suke bayani kan buƙatar haihuwar ƴaƴa da ƙara yawan adadin iyali. [10] cikin littafin Al-kafi daga ingantattun madogaran hadisi na shi'a, akwai riwayoyi da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W) da suke ƙarfafa auren mace mai haihuwa, kuma an yi bayani cewa Annabi zai yi alfahali da yawan al'ummarsa ranar ƙiyama.[11] cikin wani hadisin daban da sanadinsa ya samu karɓuwa,[12] ƙarara a fili Annabi ya yi umarni da yawaita haihuwar ƴaƴa. [13]

Irin Sakamakon Da Yake Biyo Bayan Ragen Yawan Haihuwa

Cikin ba'arin bincike da aka yi “tsofan ƴan ƙasa” shi ne asalin mummunan sakamakon da ya biyo bayan rage yawan haihuwa, ana cewa wannan batun na ragen haihuwa yana haifar da illatuwa da ba zata taɓa gyaruwa ba: daga jumlar illolinsa:

  • Matsalar tattalin arziƙi: raguwar haɓɓaƙuwa da bunƙasar tattalin arziƙi, nauyayar kuɗaɗen inshora, yawaitar samar da tsare-tsaren taimakawa waɗanda suka yi ritaya daga aiki wanda ahaka yana illata tattalin arziƙin ƙasa.
  • ƙarancin matasa ma'aikata: domin kaucewa matsalar ƙarancin ma'aikata da ka iya haifar da rufe kamfanoni da wasu muhimman ma'aikata dole a yi amfani da ƴan ƙasar waje domin cike wannan gurbi wanda haka ka iya zama matsala ga ƙasa.
  • Barazana da hatsarin a siyasance da kuma ɓangaren tsaro: canji cikin tsarin tafiyar al'umma da kuma raguwar matasa yana illata ɓangarorin tsaro na ƙasa.[14]

Dalilai Da Fargabar Da Take Hana Wasu Haihuwar Ƴaƴa

An lissafa Adadin Matsaloli da fargaba da take hana wasu haihuwar ƴaƴa.[15] ba'ari daga waɗannan matsaloli su ne kamar haka:

Matsalar Tattalin Arziƙi

Fargaba rashin iya ɗaukar nauyin yaran da za a haifa ɗaya ce daga manya-manyan matsalolin da iyaye suka kasance suna fuskanta game da haihuwar ƴaƴa;[16] daidai lokacin koyarwar muslunci ta nuna cewa shi arziƙinka da ana abin da ka haifa Allah ne yake lamintar da shi.[17] cikin kur'ani magana zuw aga mutanen da a lokacin jahiliyya suke kashe ƴaƴansu sakamakon tsoron talauci, an bayyana wannan aiki na su matsayin babban zunubi: "Mu ne muke azurta su"[18] haka nan cikin littafin Al-kafi ya zo cewa ɗaya daga sahabban Imam Kazim (A.S) cikin wata wasiƙa yana nemi jin ta bakin Imam game da haihuwar ƴaƴa sakamakon irin wahalar da take cikin tarbiyyarsu da ƙarancin kuɗi da yake fuskanta. Imam ya bashi amsa ka kasance cikin neman haihuwa, Allah ne yake saukar da arziƙin abin da aka haifa.[19]

Damuwa Game da Tarbiyya

Wasu na ganin cewa yawan yara yana da tasirin cikin rashin samun ingantacciyar tarbiyya, da wannan dalili ne basu da sha'awar haihuwar yara da yawa.[20] cikin amsar da aka bayar kansu an ce da farko dai, bisa lura da ba'arin ayoyin kur'ani,[21] ita tarbiyyar yara da shiriyar da su tana hannun Allah ne, na biyu kuma idan har mas'alar tarbiyya a haƙiƙa ta kasance ɗaya daga cikin matsaloli na asali cikin wannan batu to ya kamata mu ga waɗanda suke wadatuwar da haihuwar yaro guda ɗaya rak ya kasance mafi kyawun tarbiyya abun buga misali. Na uku da ace mihiwarin da tushen tarbiyyar yara zai kasance kan soyayya da wilayar Ahlul-baiti (A.S) da tabbas da yawa-yawan damuwa da matsaloli cikin tarbiyyya sun zama tarihi.[22]

Sauya Salon Rayuwa

Daga cikin abubuwan da suke hana haihuwar ƴaƴa akwai sauya salon rayuwa da tsarin da wasu iyalai suka runguma domin kyawuntar yanayin rayuwa da samun wadatuwa;[23] ma'ana son kai da wasu iyalai ke da shi da rashin ƙarfin gwiwar sadaukarwa, hakan ya haifar da rashin ko in kula da kasancewar ɗansu bashi da ƙani ko ƙanwa, babu abin da suke tunani sai kansu da rayuwarsu su kaɗai, saboda suna tunani cewa haihuwar ƴaƴa ba komai bane sai illata tsarin jin daɗin rayuwarsu;[24] daidai lokacin da a tsarin salon rayuwar muslunci, wadata da jin daɗi ba su ne asalin hadafin rayuwa ba, jin daɗi ko wahala matuƙar dai sun kasance domin bauta ga Allah to ababen yabawa ne. [25]

Siyasar Haihuwar ƴaƴa A Ƙasar Iran

Daga shekarar 1355-1375 hijira shamsi al'ummar ƙasar Iran sun ninka ninki biyu.[26] bayan ɓullar matsala cikin fannin ilimi da koyarwa, lafiya da matsuguni tare kuma da hasashe kan cewa shekaru masu gabatowa za a samu yawaitar aure-aure tsakanin matasa ga kuma matsalar ƙarancin gidaje da sauransu, sai gwamnatin ƙasar Iran ta yanke shawarar zartar da siyasar rage yawan haihuwa.[27] na'am a shekarar 2012 miladi Ayatullahi Khamna'i jogaran ƙasar Iran tare da bayyana cewa ita wannan siyasa ta rage haihuwa a farkon ta kasance siyasa mai kyau amma ci gaba da tafiya a kanta bayan shekaru ashirin daga fara aiki da ita kuskure ne, ya kuma ƙarfafa siyasar yawaita haihuwa..[28]

Majalisar shura ta muslunci a Iran a ƙoƙarinsu na ƙarfafa iyalai kan yawaita haihuwa sun rattaba hannu kan ƙudirin dokar samar da iyalai matasa.[29] cikin wannan ƙudirin doka an sauƙaƙa bada lamuni da bashi kai hatta bada kyautar filin gina gida ga waɗanda suka haifa ƴaƴa guda uku zuwa sama da haka.[30]

Nazari

Risala Nikahiye; Kaheshe Jam'iyyat, Zarbe Sahamigin Bar Faikare Muslimin, talifin Sayyid Muhammad Husaini Tehrani, wannan littafi wasu adadin laccoci ne da marubucin littafin ya yi su a watan Ramadan a shekarar 2011 miladi a masallacin ƙa'im da yake birnin tehran, bayan tattara su an kaiwa marubucin ya yi gyara sannan aka buga aka fitar da shi kasuwa, wannan littafi martani ne kan siyasar Konturol ɗin haihuwa.[31]

Bayanin Kula

  1. Suratul Nahal, aya ta 72.
  2. Suratul Kahf, aya ta 46.
  3. Suratul Furqaan, aya ta:74. ↑
  4. Suratul Isra, aya ta 6 da suratun Shu'ara, aya ta 133.
  5. حیدری و غبیشاوی، «فرزندآوری در آئینه آیات قرآن»، آیین رحمت.
  6. Suratu Safat, aya ta 100.
  7. Suratul Al-Imran, aya ta 38; Suratul Maryam, aya ta 5 da ta 6.
  8. Suratul Hud, aya ta 71-73; Suratul Maryam, aya ta 7 da ta 8.
  9. حیدری و غبیشاوی، «فرزندآوری در آئینه آیات قرآن»، آیین رحمت.
  10. Mousavi, Musbat Seh, 1400, shafi na 44.
  11. Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 5, shafi na 333 da 334, hadisi na 1, 2, 3 da na 4.
  12. حیدری و غبیشاوی، «فرزندآوری در آئینه روایات اسلامی»، آیین رحمت.
  13. Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 2, hadisi na 3.
  14. موسوی، مثبت سه، ۱۴۰۰ش، ص۳۵-۳۹؛ غبیشاوی، «فرزندآوری در میزان عقلانیت اجتماعی و اخلاق»، آیین رحمت.
  15. Heydari wa digaran, "Farzande awari: Awamil Suq dahande", shafi na 243.
  16. Mousavi, Musbat seh, 1400, shafi na 96
  17. حیدری و غبیشاوی، «فرزندآوری در آئینه روایات اسلامی»، آیین رحمت.
  18. Suratul Isra, aya ta 31.
  19. Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 3, hadisi na 7.
  20. Musawi, Musbet Seh, 1400 AH, shafi 109.
  21. Suratul Qasas, aya ta 56.
  22. Musawi, Musbet Seh, 1400 AH, shafi na 109-111.
  23. Musawi, Musbet Seh, 1400 AH, shafi na 117-119.
  24. «خودخواهی و عدم ایثار والدین عامل اصلی کاهش فرزند»، وبگاه بلاغ.
  25. Musavi, Musbet Seh, 1400 AH, shafi na 118.
  26. «سیاست‌های کنترل جمعیت؛ اهداف و نتایج»، پرتال جامع علوم انسانی.
  27. «سیاست‌های کنترل جمعیت؛ اهداف و نتایج»، پرتال جامع علوم انسانی.
  28. «بیانات در اجتماع مردم بجنورد»، وبگاه دفتر حفظ و نشر آثار آیت الله خامنه‌ای.
  29. «قانون حمایت از خانواده و جوانی جمعیت»، مرکز پژوهشهای مجلس شورای اسلامی.
  30. «قانون حمایت از خانواده و جوانی جمعیت»، مرکز پژوهشهای مجلس شورای اسلامی.
  31. پایگاه اینترنتی مکتب وحی

Nassoshi