Jump to content

Allah

Daga wikishia
Wannan maƙala ce game da keɓantaccen sunan Allah. Domin sanin Allah da bahasosin sanin Allah ku duba shafin Khoda da Sanin Allah.

Allah (Larabci: الله) suna ne na musamman kuma shi ne sunan Allah mafi shahara a addinin Muslunci. A imanin malaman Muslunci, Allah suna ne da ya tattaro dukkanin siffofin kamala na Allah kuma ismul a'azam. Haka kuma suna cewa wannan suna yana da mafi ɗaukakar matsayi cikin Kurani da addu'a kuma ya kasance ginshiƙi na tauhidi, shahadataini da ayoyin Kur'ani. Kalmar Allahu ta keɓantu da Allah kuma ba a amfani da ita a kan waninsa. Wannan kalma an ambace ta a Kur'ani fiye da karo dubu biyu.

A cewar Jafar Subhani, mafi yawan malamin tafsirin Kur'ani, mafi yawan malaman hadisi da tafsiri sun tafi kan cewa an ciro kalmar Allahu daga "Alaha""da take da ma'anar wanda ya cancanci a bauta masa. Tare da haka akwai wasu ra'ayoyin daban da ake tsammani da aka yi bayaninsu daga jumla akwai cewa tana da ma'anar ruɗewa, firgici da dogaro da kuma kwanciyar hankali.

Daga cikin ayyukan zanen kwalliya na cikin Haramin Imam Husaini (A.S)

Cikin irfanin Muslunci, sunan Allah ya kasance a cikin salsalar ginshiƙan sunayen Allah kuma sauran sunayen sun samo asali ne daga wannan suna. Kalmar Allahu cikin al'adu da al'ummun Muslunci, an yi amfani da ita sosai. Alal misali an sanya wannan kalma jikin sulallan daurorin daulolin Muslunci da wurare masu tsarki kamar haramai da masallatai da tutoci da alamomi na ba'arin ƙasashen Muslunci kamar Iran, jamhuriyar Azerbaijan da Iraƙ.

Haka kuma jikin tambarin sojojin ƙasar Najeriya akwai rubutun "Nasara Daga Allah Take".

Matsayin Sunan Allah A Al'adun Muslunci

"Allah"suna ne na musamman[1] kuma mafi shaharar sunan Allah a Muslunci.[2] Malaman Muslunci suna la'akari da wannan suna matsayin jigo da ginshiƙi na tauhidi da Ikhlasi da yake tare da mafi ɗaukakar matsayi a Kur'ani da addu'a.[3] Haka kuma suna cewa kalmar Allahu kaɗai tana da misali guda ɗaya rak, kuma suna ne da ya tattaro dukkanin siffofi na kamala kuma ba a amfani da shi kan wanin Allah.[4] Saboda haka, Allahu ginshiƙi tattaunawa da bahasosi game da Allah a cikin littafin sama na Musulmi da kuma Nahajul Balaga, kuma an ce cikin Kur'ani ana tabbatar dukkanin siffofin kamala ga Allah.[5]

Kalmar Allahu ginshiƙi ne na take guda biyu na asali a Muslunci, ma'ana shahadataini, cikin shahada ta farko, an kore samuwar duk wani abin bautawa da gaskiya koma bayan Allah, cikin shahada ta biyu, an gabatar da Sayyidina Muhammad (S.A.W) a matsayin ɗan'aiken Allah.[6]

Kalmar Allahu, tare da sunaye kamar "Rabbu" da "Ilahu" sune mafi yawan sunayen Allah da aka fi amfani da su a cikin Kur'ani.[7] an ƙidaice adadin maimaicin kalmar Allahu a cikin Kur'an sau 2699[8]2707[9] da 2807.[10]

Da yawa-yawan malaman Muslunci suna ɗauƙar Allahu matsayin Ismul A'azam.[11] Daga jumlar dalilin kasancewar wannan kalma Ismul A'azam, ita ce tushe da asasin tauhidi, kuma tare da furta wannan kalma kafiri yana cirata zuwa ga imani, idan wani maimakon "La ilaha illallhu"sai ya furta "La ilaha Illar Rahman" hakan ba zai fitar da shi daga da'irar kafirci ba zuwa Muslunci.[12]

Cikin harshen Farsi kalmar Khoda ita take matsayin kalmar Allahu.[13] Cikin tarjamomi na baya-bayan nan na littafi mai tsarki na Yahudu da Nasara da Zartush, kalmomin "Yahuwa”, "Ta'us" da Ahuramazda da suke nuni zuwa ga Allah, an tarjama su zuwa kalmar Allah.[14] Tun kafin zuwan Muslunci an yi amfani da ita kuma a cikin aya ta 87 suratul Zukhruf da aya ta 25 suratul Luƙman an yi ishara da amfani da wannan kalma tun kafin saukar da Kur'ani.[15]

Asali Da Kuma Nazarin Ma'ana

Wasu suna ganin Allahu kalma ce ta Larabci[16] Wasu kuma suna cewa asalin wannan kalma daga harshen Ibraniya ko Suryaniyya take.[17] A imanin wasu malamai, kalmar "Allahu" a asali ta kasance "Al-Ilah" harafin alhamza na biyu sakamakon yawan amfani sai aka shafe shi kalma ta juya zuwa "Allahu".[18] A ra'ayin wasu kalmar Allahu ta samo asali daga "Lahu" sai alif da lamun suka gangara kanta ta zama Allahu.[19] Dangane da ciro kalmar Allah daga wata kalma daban ko kuma ba a ciro aka yi ba, malamai sun yi saɓani.[20] A cewar Fakhrur Razi, mafi yawan malaman fiƙihu da usul suna ganin wannan kalma ba a ciro ta daga wata kalma daban ba.[21] Waɗanda suka tafi kan cewa suna ne da aka ciro daga wata kalma daban, sun ambaci ra'ayoyi daban-daban game da asali da tushen ta[22] ba'ari daga wannan ra'ayoyi sun kasance kamar haka:

  • Allahu an ciro daga Alaha ma'ana wanda ya cancanci a bauta masa.[23] A cewar Jafar Subhani, malamin tafsirin Kur'ani, da yawa-wayan malaman hadisi da tafsiri sun yarda da wannan mahanga.[24] Haka zalika an naƙalto wannan ma'ana cikin riwayoyi.[25]
  • An ciro daga Aliha ko Waliha da ma'anar ruɗewa, saboda hankula suna ruɗewa cikin sanin zatin Allah.[26]
  • An ciro daga Ilahu da ma'ana firgici da dogara; saboda mutane a lokacin wahalhalu suna fakewa da Allah[27] kuma suna dogara da shi.[28]
  • An ciro daga Ilahu da ma'anar kwanciyar hankali da nutsuwa, saboda ambaton Allah yana samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.[29]
  • An ciro daga "Laha" da ma'anar kasancewa cikin ɓuya; saboda Allah ya ɓuya daga barin hankula da wahami da hiyali.[30]

Allahu A Cikin Irfanin Muslunci

A faɗin malaman irfani, a cikin irfanin Muslunci sunayen Allah suna da wani keɓantaccen tsari, sunan Allah da ya tattaro komai, shi ne ginshiƙin salsalar jerin sunayen Allah, bayansa ne sunaye huɗu (Ma'ana Farko, ƙarshe, bayyane, asirce) da sunaye bakwai duka suna ɓuɓɓugowa ne daga sunan Allahu, kuma haka har a kai ga sunaye ƙanana, saboda haka a cikin irafnin Muslunci baki ɗayan sunayen Allah suna komawa zuwa ga Allahu.[31]

Amfani Da Kalmar Allahu

An rubuta kalmar Allahu a jikin tuta da tambarin ƙasar Iran[32] da tambarin jamhuriyar Azerbaijan.[33] da tuta da tambarin ƙasar Iraƙ cikin shakali da tsari na Allahu Akbar.[34] Kalmar Allahu, ita kaɗai ko tare da wata kalmar ta kasance kan sulallan da ake bugawa a daulolin Muslunci da suka gabata.[35] Wannan kalma an rubutu ta a wurare masu tsarki daban-daban kamar haramai da masallatai. Haka kuma wannan kalma ta Allahu ta kasance take na sojojin ƙasar Najeriya da ke jikin tambarinsu.[36] Masu rubutun kwalliya da daman gaske sun yi aiki kan rubutu da kyakkyawan salo na wannan kalma cikin hanyoyi da salo daban-daban.

Rubutun Nasrun Min Allah a jikin bajon Sojan Najeriya

Bayanin kula

  1. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420ƙ, Jild 1, Shafi 143. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, 1390ƙ,, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 119.
  2. Kaf’ami, Al-Maƙam al-Asna, 1412ƙ,, Shafi 25.
  3. Kaf’ami, Al-Maƙam al-Asna, 1412ƙ,, Shafuka 25 da 26.
  4. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386SH, Shafi 36.
  5. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386SH, Shafuka 33–36.
  6. Pakatchi, «Allah», Shafi 73.
  7. Misbah Yazdi, Khudashnasi, 1396SH, Shafi 58.
  8. Ruhani, Al-Mu’jam al-Ihsai li-Alfaz al-ƙur’an al-Karim, 1372SH, Jild 2, Shafuka 244–262.
  9. Safi Golpaygani, Ilahiyyat dar Nahj al-Balagha, 1386SH, Shafi 34.
  10. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379SH, Shafi 357..Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377 SH, Shafi 63
  11. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379SH, Shafuka 357 da 361. Kaf’ami, Al-Maƙam al-Asna, 1412 AH, Shafi 26. Khomeini, Misbah al-Hidayah, 1392SH, Shafuka 12 da 13. Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377SH, Shafi 64.
  12. Kashfi, Jawahirin Tafsir, 1379SH, Shafi 361.Ashtiani, Tafsir Surah Fatiha al-Kitab, 1377 SH, Shafi 64.
  13. Jawadi Amoli, Tawhid dar ƙur’an, 1395SH, Shafi 228.
  14. Pakatchi, «Allah», Shafi 73
  15. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, 1390ƙ,, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafuka 116 da 117.
  16. Ku duba: Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420ƙ,, Jild 1, Shafi 148. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 116
  17. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420ƙ,, Jild 1, Shafi 148. Subhani, Manshur Jawid, 1390SH, Jild 2, Shafi 116
  18. Sheikh Saduƙ, Al-Tawhid, 1398ƙ,, Shafuka 195 da 196.. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-ƙur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, 1390ƙ,, Jild 1, Shafi 18. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118
  19. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-ƙur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91.
  20. Subhani, Manshur Jawid, 1390SH, Jild 2, Shafi 117.
  21. Fakhri Razi, Tafsir al-Kabir, 1420ƙ,, Jild 1, Shafi 143.
  22. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408ƙ,, Jild 1, Shafuka 55–57.
  23. Sheikh Saduƙ, Al-Tawhid, 1398ƙ,, Shafi 195.. Sheikh Tusi, Al-Tibyan fi Tafsir al-ƙur’an, Beirut, Jild 1, Shafi 27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafi 57. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, 1390ƙ,, Jild 1, Shafi 18
  24. Subhani, Manshur Jawid, 1390SH, Jild 2, Shafi 117.
  25. Kulayni, Al-Kafi, 1407ƙ,, Jild 1, Shafi 87. Sheikh Saduƙ, Al-Tawhid, 1398ƙ,, Shafi 221.
  26. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91. Tabatabai, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, 1390 AH, Jild 1, Shafi 18.
  27. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91. Subhani, Manshur Jawid, 1390 SH, Jild 2, Shafi 118.
  28. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafuka 55 da 56.
  29. Tabarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91. Subhani, Manshur Jawid, 1390SH, Jild 2, Shafi 118.
  30. abarsi, Majma’ al-Bayan, 1372SH, Jild 1, Shafi 91. Abu al-Futuh Razi, Rawz al-Jinan, 1408 AH, Jild 1, Shafuka 55 da 56. Subhani, Manshur Jawid, 1390SH, Jild 2, Shafi 118
  31. Yazdanpanah, Mabani wa Usool-e ‘Irfan-e Nazari, 1389SH, Shafuka 455–460. Amini-Nejad da wasu, Mabani wa Falsafe-ye ‘Irfan-e Nazari, 1390 SH, Shafuka 237–240.
  32. «[https://www.irna.ir/news/83855879۹۰ش، ص۲۳۷-۲۴۰. «طرح پرچم ایران؛ بازتاب گفتمان انقلابی و اسلامی]»،‌ Kafamin Labarai ta Jamhuriyar Muslunci.
  33. ««لفظ مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان»، Kafamin Labarai ta Aran
  34. ««پرچم عراق و سیر تحول آن»Shafin yanar gizo na Iraƙ Yar.
  35. Sarafrazi, «Sha’air Shia bar Sikkah-haye Islami ta Shakl-giri Hukumat Safawiyan», Shafuka 9–11, 19, 22 da 23
  36. Nigerian Army logo:https://nigerianfinder.com/nigerian-army-logo-description-and-meaning/?utm_source=chatgpt.com

Nassoshi

  • Ashtiyani, Jalaluddin, Tafsir Suratul Fatiha al-Kitab, Ƙum, Ofishin Kungiyar Mata Ɗalibai Musulmi, 1377SH.
  • Fakhr Raaziy, Muhammad bin Umar, At-Tafsirul Kabiir (Mafaatiihul Ghaib), Beirut, Mawallafar Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, bugun uku, 1420ƙ / 1999M.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Umar, al-Tafsir al-Kabir (Mafatih al-Ghayb), Beirut, Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, Chap Uku, 1420ƙ / 1999M.
  • Jawadi Amoli, Abdullah, Tasnim, Ƙum, Gidauniyar Wallafawa ta Isra, bugu na Uku, 1381SH.
  • Jawadi Amoli, Abdullah, Tawhid dar ƙur’an (az Silsilah Tafasir Mawzu’i Jild Doma), ba Koshish Haidar Ali Ayubi, Ƙum, Gidauniyar Bainal-‘Alami Nashr Isra, 1395SH.
  • Jawadiy Amuliy, Abdullahi, Tasniim, Ƙum, Gidauniyar Wallafawa ta Nashar Israa, bugun uku, 1381 sh.
  • Jawadi Amoli, Abdullahi, Tauhidi a cikin Al-Kur’ani (daga jerin tafsirin maudu’i, juzu’i na biyu), da kokarin Haidar Aliy Ayyubiy, Ƙum, Giduaniyar Duniya na Nashar Israa, 1395SH.
  • Kaashifiy, Mullah Husain, Jawahirut-Tafsiir, Tehran, Cibiyar Bincike na Miraas Maktoob, 1379SH.
  • Kafa‘ami, Ibraahiim bin Ali, Al-Maƙaamul Asnaa fii Tafsiiril Asmaa’il Husnaa, Bincike Faaris Al-Husun, Ƙum, Cibiyar Ƙaa’im Aal-Muhammad (A.F), 1412ƙ / 1370SH.
  • Kaf’ami, Ibrahim bin Ali, al-Maƙam al-Asna fi Tafsir al-Asma’ al-Hasna, Bincike Fars al-Huson, Ƙum, Cibiyar Ƙa’im Al-Muhammad (AJ), 1412ƙ/ 1370SH.
  • Kashfi, Mulla Husayn, Jawahir al-Tafsir, Tehran, Cibiyar Bincike ta Mirath Maktub, 1379SH.
  • Khomeini, Sayyid Ruhullah, Misbah al-Hidayah ila al-Khilafah wa al-Wilayah, Tehran, Cibiyar Tsarawa da wallafa Ayyuakn Imam Khomeini, 1392SH.
  • Khumaini, Sayyid Ruhullahi, Misbaahul Hidaayah ilal Khilaafah wal Wilaayah, Tehran, Cibiyar Tsarawa da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 1392SH.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, al-Kafi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1407ƙ.
  • Kashfi, Mulla Husain, Jawahirin Tafsiri, Tehran, Cibiyar Bincike na Gado na Rubuce-rubuce, 1379SH.
  • Kaf’ami, Ibrahim bin Ali, Matsayin Mafi Girma a Tafsirin Sunayen Kyawawa, Gyara: Faris al-Hassoun, Ƙum, Cibiyar ƙa’im Aal Muhammad (AJ), 1412ƙ / 1370SH.
  • Misbaahu Yazdi, Muhammad Taƙiyu, Khudaa-shinaasiy, Ƙum, Mawallafar Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumainiy, 1396SH.
  • Najafiy, Muhammad Hassan, Jawahirul Kalaam fii Sharhi Sharaa’i‘il Islaam, Beirut, Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, bugun bakwai, 1362 sh.
  • Pakatchi, Ahmad *«، «الله» (Allah )A cikin Dayrah al-Ma’arif al-Buzurg Islami, Jild 10, Tehran, Markaz Dayrah al-Ma’arif al-Buzurg Islami, bugu na farko, 2021M.
  • Nigerian Army logo:https://nigerianfinder.com/nigerian-army-logo-description-and-meaning/
  • Rouhani, Mahmoud, al-Mu’jam al-Ihsai li Alfaz al-ƙur’an al-Karim (Farhang Amari Kalimat al-ƙur’an al-Karim), Mashhad, Astān ƙuds Razawi, 1372 HS / 1414 ƙ.
  • Ruhaniy, Mahmud, Al-Mu’ujamul Ihsaa’iy li Alfaazil Kur’aanil Kariim (Farhang Aamariy Kalimomin Al-Kur’ani Mai Girma), Mashhad, Aastan ƙuds Razawiy, 1372SH/ 1414ƙ.
  • Saafiy Gulpaaygaaniy, Lutfullah, Ilaahiyaat dar Nahjul Balaaghah, Ƙum, Mawallafar Bustaan Kitaab, 1386SH.
  • Safi Golpayegani, Lutfullah, al-Ilahiyat dar Nahj al-Balagha, Ƙum, Mawallafar Bustan Kitab, 1386SSH.
  • Sarafaraaziy, Abbas,«شیعی بر سکه‌های اسلامی تا شکل‌گیری حکومت صفویان »، (Alamomin Shi'a a Kan Tsabar Kuɗi na Musulunci Har zuwa Kafuwar Daular Safawiyya) Mujallar Shi’a-Shinasi (Nazarin Shi’a), lamba ta 51, watan Aban shekara ta 2015M.
  • Shaikh Saduuƙ, Muhammad bin Ali bin Baabawaih, At-Tauhiid, Ƙum, Jaami‘atul Mudarrisiin Hauzar Ilmin Ƙum, bugun farko, 1398ƙ.
  • Shaikh Tuusi, Muhammad bin Hasan, At-Tibyaan fii Tafsiiril ƙur’aan, Beirut, Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, ba tare da shekara ba.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Ali bin Babawayh, al-Tawhid, Ƙum, Jami’at Madarisin Hawzah ‘Ilmiyyah Ƙum, bugu na farko, 1398ƙ.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, al-Tibyan fi Tafsir al-ƙur’an, Beirut, Gidan Raya Gadon Adabin Larabawa, babu kwanan wata.
  • Sobhani, Ja’far, Manshur Jawid, Ƙum, Cibiyar Imam Sadiƙ (A.S), 1390SH.
  • Subhaaniy, Ja’afar, Manshur Jaawid, Ƙum, Cibiyar Imam Sadiƙ (a), 1390SH.
  • Tabaatabaa’i, Sayyid Muhammad Husain, Al-Miizaan fii Tafsiiril ƙur’aan, Beirut, Cibiyar A‘lamiy domin Wallafe-wallafe, 1390ƙ.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma’ al-Bayan fi Tafsir al-ƙur’an, Tehran, Mawallafar Nasir Khosrow, bugu na Uku, 1372SH.
  • Tabarsi, Fadlu bin Hasan, Majma‘ul Bayaan fii Tafsiiril ƙur’aan, Tehran, Mawallafar Naasir Khusraw, bugun uku, 1372SH.
  • Tabataba'i, Sayyid Muhammad Husayn, al-Mizan fi Tafsir al-ƙur’an, Beirut, Cibiyar al-A’lami domin wallafe-wallafe, 1390ƙ.
  • Yazdaan-Panaah, Sayyid Yadullah, Mabaani wa Usul ‘Irfaan Nazariy, rubutu na Sayyid ‘Ataa Anzaliy, Ƙum, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini. bugun biyu, 1389SH
  • Yazdiy, Muhammad Kaazim, Al-‘Urwatul Wuthƙaa ma‘at-Ta‘liƙaat, Ƙum, Makarntar Ali bin Abi Talib (A.S), 1428ƙ/ 1326SH.
  • «مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان» (Kalmar Allah mai tsarki a tsakiyar tambarin gwamnatin Jamhuriyar Azerbaijan) Kamfanin Dillancin Labarai na Aran, ranar wallafa labarin:20 Agusta 2017, ranar duba/ziyara:18 Mayu 2025M.
  • «عراق و سیر تحول آن»، (Tutar Iraki da tarihin sauyowarta) Shafin yanar gizo na Iraƙ-Yar, Tarihin shigarwa:14 Nuwamba 2020 M, Tarihin ziyara: 18 Mayu 2025 M.
  • «لفظ مقدس الله در مرکز آرم حکومتی جمهوری آذربایجان» (Kalmar Mai Tsarki ‘Allah’ a tsakiyar tambarin gwamnatin Jamhuriyar Azerbaijan) Kamfanin Dillancin Labarai na Aran, ranar wallafa labarin: 20 Agusta 2017, ranar dubawa/ziyara: 18 Mayu 2025M.
  • ««طرح پرچم ایران؛ بازتاب گفتمان انقلابی و اسلامی»،‌ (Ɗaga Tutar Iran; Mayar da Martani ga Tunanin Juyin Juya Hali da na Musulunci) Hedikwatar Labarai ta Jamhuriyar Islama, Ranar Rubuta Labari:15 ga Yuli, 2020, Ranar Ziyara: 17 Mayu 2025M.
  • Abulfatuhu Razi, Husain bin Ali, Rawd al-Jinan wa Ruh al-Jinan fi Tafsir al-ƙur’an, Tashih Muhammad Mahdi Nasih wa Muhammad Ja’far Yahƙi, Mashhad, Astan Ƙuds Razawi,1408ƙ.
  • Amininejad, Ali wa Digiran, Mabani wa Falsafa Irfan Nazari, Ƙum, cibiyar Ilimi da nazari ta Imam Khomeini, Bugu na farko, 1390SH.