Ranakun Allah
Ranakun Allah (Larabci:أيّام اللّه) ana nufin ranakun da wasu muhimman abubuwa suka faru, kuma su abubuwan suna bayyana ƙudurar Allah fiye da lokacin da ya gabata, malaman tafsiri lokacin da suke fassar ayar da kalmar Ayyamullah ta zo a cikinta suna cewa, Ayyamullah tana nufin ranar da aka tseratar da al'umma da ranar da Allah ya saukaar da ni'ima akan muminai, kuma ranar da Allah ya saukar da azaba a kan kafurai, kuma malaman su na ganin abin da ya sa Allah ya yi umarni da a tina da su, shi ne mutane su farka da, kuma su ɗauki darasi daga waɗannan ranakun.
Bisa wata ruwaya daga Imam Baƙir (A.S) ya fassara Ayyamullah, da mikewar Imam Mahadi (A.S), da ranar Raja'a wato ranar da wasu daga cikin matattu za su dawo duniya domin girbar abin da suka shuka tin a duniya kafin ranar lahira, da kuma ranar Alƙiyama, kamar yadda ya zo a cikin wasu riwayoyi, cewa ranar Ashura tana daga cikin Ayyamullah.
Imam Khomaini wanda ya jagoranci juyin juya halin muslunci na Iran, yana ganin akwai wasu ranaku da suka faru a ƙasar muslinci ta Iran, waɗanda suna daga cikin ranakun Allah, wato Ayyamullah, kamar ranar ashirin 22 ga wata Bahaman 1357 hijira shamsiya, wanda ya yi daidai da 13 ga wata Rabi'u Awwal hijira 1399, ranar da juyin juya hali ya yi nasara a ƙasar Iran, kamar yadda ya tafi kan cewa, abin da ya faro a ranakun Allah, abu ne wanda yake ƙarfafar al'umma, kuma ya na sa al'umma ta ta shi tafarka, domin kwatar haƙƙinta, kuma wajibi ne raya irin waɗannan ranakun.
Abin Da Ake nufin Da Ayyamullah
Ranakun Allah, ana nufin ranakun da wasu muhimman abubuwa[1] suka faru, kuma su abubuwan suna bayyana ƙudurar Allah fiye da lokacin da ya gabata[2] ita wanna jumla (Ayyamullah), ta zo a cikin alƙur'ani mai girma sau biyu.[3] A cikin suratul Ibrahim, Allah ya umarci annabi Musa (A.S), cewa ya faɗakar da mutananshi kan ranakun Allah, saboda akwai darasi a cikinsu.[4] Kamar yadda aka umarci muminai a cikin suratul Jasiya, da su yi gafara ga waɗanda ba sa fatan ranakun Allah, domin Allah ya saka musu kan abin da suka aikata.[5] Ya zo cikin Tafsirul Amsal cewa tuna ranakun Allah, ya na da rawar da yake takawa kan motsa al'umma, da kuma ɗaukan darasi kan abubuwan da suka faru.[6] kamar yadda,[7] Imam Ali (A.S) ya nemi Ƙas'am ɗan Abbas, wanda yake ma'aikacin shi ne a Makka da ya tinatar da mutane ranakun Allah.[8]
Tafsirin Kalmar Ayyamullah
Ra'ayin masu tafsiri ya banbanta kan Ayyamullah:
- wasu daga cikinsu, sun tafi a kan cewa, ranakun ni'imar Allah ne, saboda Allah ya saukarwa Annabawa da mabiyansu ni'momi da yawa, kamar tseratar da annabi Musa (A.S) daga Fir'auna, kuma Allah ya tseratar da mutanan annabi Nuhu lokacinn da jirgin ruwa ya isa bakin teku lafiya, sannan Allah ya tseratar da annabi Ibrahim (A.S) daga Namarud.[9]
- Wasu malamai tafsirin sun tafi kan cewa,lalle ranakun Allah sun ƙunshi ranakun azaba, saboda Allah ya saukar da azaba akan mutane masu saɓo, Adawa da Samudawa.[10]
- Bisa wata ruwaya daga Annabi (S.A.W), ranakun Allah su ne ranakun da Allah ya saukar da ni'ima da ranakun da ya saukar da azabar shi akan mutane masu saɓo.[11]
- Amma Allama Ɗabaɗaba'i ya tafi kan cewa ranakun an jinginasu da Allah maɗaukakin sarki ne, saboda bayyanar al'amarin Allah a cikin su fiye da kowana lokaci, kuma ana nufi lokuta da yanayi da al'amarin Allah zai bayyana da ayoyi nasamuwar shi da ƙudirar shi.[12]
- Amma Makarim Shirazi yana ganin cewa, ranakun Allah su ne, duk wata rana da ɗan Adam ya fara wata rayuwa sabuwa, to wannan ranar tana daga cikin ranakun Allah, kamar ranar da aka turo wani annabi ko kuma ranar da wani azzalumin sarki ya mutu, duk suna cikin ranakun Allah.[13]
Amma malam Faizul Kashani ya ce, babu saɓani a tsakanin waɗanna ra'ayuyyukan, saboda ranar da ni'ima ta sauka kan muminai, to zai zamo kamar an saukar da azaba ne kan kafirai, zai zamo irin wanna ranakun ni'ima ce ga wasu mutane, kuma adaidai lokacin da azaba ce ga wasu.[14]
Wasu Daga Cikin Ranakun Allah
Ya zo a cikin ruwaya ma'anoni da yawa kan ma'anar Ayyamullah wato ranakon Allah, a cikin wani hadisi daga Imam Baƙir (A.S) yana cewa ranakun Allah guda uku ne, ta ɗaya ita ce ranar miƙewar Imam Mahadi, rana ta biyu ita ce ranar da wasu matattu za su dawo duniya, rana ta uku ita ce ranar alƙiyama.[15] Wanna ruwayar Aliyu ɗan Ibrahim Alƙummi ya kawo ta a cikin tafsirinshi, amma sai aka anbaci rana ta biyu ita ce ranar da mutum zai mutu madadin ranar da wasu matattu za su dawo.[16] Amma a cikin wasu ruwayuyin an anbaci ranar Ashura a cikin Ayyamullah.[17] Amma Imam Khomaini ya na ganin cewa, ranar da annabi ya yi hijira daga Makka zuwa Madina da ranar Fatahu Makka da ranar yaƙin Siffin da duk wata ranar da girgizar ƙasa ta faru ko kuma anbaliyar ruwa da ireiren su, to duk abubuwa ne da suke sa ɗan Adam ya faɗaka daga gafalar shi, to suna daga cikin abin da ake nufi da ranakun Allah.[18] Duk da yake Ayyamullah ba su taƙaita da iya wannan ranakun da na anbata ba akwai wasu ranakun, inji Imam Khomaini .[19]
Nasarar da juyin juya hali ya samu a Iran
Imam Khomaini wanda ya kafa juyin juya hali a ƙasar Iran, ya ce ranaku masu muhimmanci sun fara kan Jamhuriyyar musulinci ta Iran, waɗannan ranakun suna daga cikin ranakun Allah, kamar ranar 22 ga watan Bahaman a shekara ta 1357 hijirar Annabi (S.A.W), saboda a wanna ranar ne juyin juya hali ya yi nasara,[20] haka nan ranar 17 ga watan Shaharibar da 15 ga watan Kurdad ranaku ne da suke da tasiri kan ci gaban juyin juya hali.[21] Kazalika Imam Khomaini ya na ganin abubuwan da suka faru a cikin ranakun Allah, abubuwa ne da za mu koyi darasi a cikin su, kuma abubuwa ne da suke zama dalili na farkawar mutane gabaɗaya a tarihi, sabo da haka Imam Khomaini yana ganin dole ne a raya su kuma a dinga tinawa da su.[22]
Bayanin kula
- ↑ Shearani, Nasare Toubi's, 2013, juzu'i na 2, shafi na 604.
- ↑ ƙorshi Bana’i, ƙamus Kur’an, 1412 AH, juzu’i na 7, shafi na 281.
- ↑ Duba suratul Ibrahim, aya ta 5; Suratul Jathiya, aya ta 14.
- ↑ Suratul Ibrahim, aya ta 5.
- ↑ Suratul Jathiya, aya ta 14.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1393 Hijira, juzu'i na 18, shafi na 164.
- ↑ Makarem, Tafsir Namuneh, 1377, juzu'i na 10, shafi na 275.
- ↑ Nahj al-Balagha, Tahƙiƙ Sobhi Saleh, Nameh 67, juzu'i na 1, shafi na 457.
- ↑ Tabari, Jame al-Bayan, 1420 AH, juzu'i na 13, shafi na 239; Tusi, Tebyan, Beirut, juzu'i na 6, shafi na 274.
- ↑ Tabari, Jame al-Bayan, 1420 AH, juzu'i na 11, shafi na 227; Tabarsi, Majam Al Bayan, 1408 AH, juzu'i na 5, shafi na 209.
- ↑ Tabarsi, Majma al-Bayan, 1408 AH, juzu'i na 6, shafi na 467; Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1394 AH, juzu'i na 12, shafi na 18.
- ↑ Makarem, Tafsir Namuneh, 1377, juzu'i na 10, shafi na 272.
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Amali, 1414 AH, shafi na 491.
- ↑ Faiz Kashani, Tafsirin Safi, 1373, juzu'i na 3, shafi na 80.
- ↑ Sheikh Saduƙ, Al-Khisal, 1362, Juzu'i na 1, shafi na 108, h. 75.
- ↑ ƙomi, Tafsirul ƙommi, 1404 AH, juzu'i na 1, shafi na 397.
- ↑ Ibn Abi Jumhur, Awali al-Layali al-Azizia, 1405 H., Mujalladi na 1, shafi na 138.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifa Noor, 1369, juzu'i na 9, shafi na 63
- ↑ ƙorshi Bana’i, ƙamus Kur’an, 1412 AH, juzu’i na 7, shafi na 281.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifa Noor, 1369, juzu'i na 19, shafi na 101.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifa Noor, 1369, juzu'i na 9, shafi na 65.
- ↑ Imam Khumaini, Sahifa Noor, 1369, juzu'i na 17, shafi na 11.
Nassoshi
- Allameh Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Scientific Institute, Beirut, 3941 A.H.
- Faiz Kashani, Mohammad, Tafsir Al-Safi, Tehran, Sadr School, 1373.
- Ibn Abi Jumhur, Muhammad Bin Ali, Awali Al-Laali Al-Azizia fi Ahadith al-Diniya, Sahih Mojtaba Iraƙi, ƙom, Dar Seyyed al-Shohada, 1405H.
- Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Noor, Tehran, Soroush Publications, 1369.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1373.
- Nahj al-Balagha, tahƙiƙ Sobhi Saleh, Beirut, Dar al-Kitab al-Bani, B.T.A.
- ƙomi, Ali Ibn Ibrahim, Tafsirul ƙimmi, ƙum, Darul Kitab, 1404H.
- ƙorshi Banaei, Ali Akbar, ƙamus Kur'an, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1412H.
- Shearani, Abolhassan, Nasare Toubi, wanda Mohammad Gharib ya tattara, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 2013.
- Sheikh Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Al-Khisal, Kum, Jamia Modaresin, 1362.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Darahia al-Trath al-Arabi, Bita.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi ta'awil al-ƙur'an, Al-Risala Foundation, 1420H.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi al-Tafsir al-ƙur'an, Daral al-Marefa, Beirut, 1408 AH.