Jump to content

Ya'ajuju Da Ma'ajuju

Daga wikishia

Ya'ajuju Da Ma'ajuju (Larabci: يأجوج ومأجوج ) suna ne na wata ƙabila ko ƙabilu wanda aka ambace shi a Kur'ani da cikin nassoshi na addinin Kiristanci da Yahudanci, nassi na addini yana nuna cewa su Ya'ajuju da Ma'ajuju mutane ne masu cutar da mutum, saboda zalincinsu da wawashe kayan mutane, bisa abin da ya zo a ayoyi na kur'ani Zulƙarnaini ya gina katanga a tsakanin mutanan da Ya'ajuju da Ma'ajuju suke zalinta domin kada su shiga, kuma wannan katanga ita ce aka fi sani da katangar Zulƙarnaini kuma ta Ya'ajuju da Ma'ajuju. Rusa wannan katanga ana ɗaukarshi ɗaya daga cikin alamar ƙarshan duniya, wace aka ambata a cikin ƙur'ani. amma nassi a gun Mabiya addinin Kiristanci da Yahudanci suna nuna cewa wannan guri da aka gina katanga yana arewacin ƙasar Jojiya.

Shin Ya'ajuju Da Ma'ajuju Al'umma Ce Ko Dai Wani Mutumi Ne

An yi hasashe da yawa kan yadda Ya'ajuju da Ma'ajuj da suke:

  • Suna ne na mutum: Ya zo a wasu littafai cewa Ya'ajuju cda Ma'ajuj suna ne na mutum.[1] A cikin tsohon alƙawari Ma'ajuj suna ɗa ne na biyu ga Liyafasu shi Liyafasua ɗaya ne daga cikin ƴaƴan Annabi Nuhu (A.S).[2]
  • Sunan wani yanki ne: Bisa abin da ya zo a lttafai na addini yana nuna cewa Ya'ajuju da Ma'ajuj suna wani guri ne.[3]
  • Wata ƙabila ce da take rayuwa a arewacin Asiya: A littafai na Muslunci Ya'ajuju da Ma'ajuj wata ƙabila ce wacca take rayuwa a arewacin Asiya, kuma sun kasance suna kashe mutane da kwashe musu dukiya. Bisa abin da ya zo a wannan littafai sun kasance suna rayuwa a gabacin Asiya ne a yankin Tabat da Sin har zuwa daskararan tekun ƙanƙara na arewaci daga ɓangaran yamma kuma har Turkistan. Wannan ne yasa wasu daga cikin masu tafsiri suke ganin cewa asalin kalmar Ya'ajuju da Ma'ajuj ta samo asali ne daga wani harshe na Sin mai suna Mangug ko Manjug, da kalmar ta shiga cikin harshan Ibriyya da Larabci sai ta zama Ya'ajuju da Ma'ajuj, amma a Girik kuma suna ce mata Gag da Magaga.[4]
  • Suna ne na Magul: Wasu sunyi hasashem cewa wannan kalma ta Ya'ajuju da Ma'ajuj ƙabila ce ta Magul wadda ta kai hari daga matsuguninta a arewa masu gabas na kogin ƙazwin zuwa guraran da suke kusa da su, kamar bayan tafki da Armeniya da Azarbijan har zuwa Sin da yankin Indiya da Fakistan, sai suka gina katangar sin mai girma da Dam na Zulƙarnaini, domin tare su a ciki,[5] bisa haka bayyanarsu a ƙarshan zamani kamar yadda ya zo a alkur'ani ya dace da lokacin da Magul suka kai hari a ƙarni na 7 hijira.[6]

Madatsan Ruwa (Dam) Ya'ajuju Da Ma'ajuj

Zulƙarnaini ɗaya ne daga cikin shugabanin muminai, a ɗaya daga cikin tafi-tafiyanshi ya isa zuwa wani yanki tsakanin duwatsu guda biyu, sai mutanan wannan yanki suka bashi labarin cewa Ya'ajuju da Ma'ajuj za su shigo wannan yanki ta bayan dutse su kashe mutane, kuma su sace dukiyarsu, sai mutanan wannan yanki suka buƙaci cewa Zulƙarnaini ya gina musu Katanga su biyashi domin hana shigowar Ya'ajuju da Ma'ajuj da takura musu da suke yi, Zulƙarnaini ba tare ya nemi kuɗi ba da taimakon mutanan suka gina katangar ƙarfe domin hana zuwa da Ya'ajuju da Ma'ajuj yi dan su yaƙe su, kuma wannan Katanga ta shahara da katangar Zulƙarnaini ko katangar Ya'ajuju da Ma'ajuj.[7] Kur'ani ya kawo wannan ƙissa a aya ta 93 zuwa 98 a cikin suratul Kahaf.[8] Wasu suna ganin cewa wannan Katanga tana kan hanyar Dariyal a arewacin Taflis kan iyaka tsakanin Jojiya da Rasha.[9]

Bayyanar Ya'ajuju Da Ma'ajuj Tana Cikin Alamar Ƙarshan Zamani

ƙur'ani ya bada labarin dawowar Ya'ajuju da Ma'ajuj da kuma yin tawayansu a aya ta 93 a cikin suratul Anbiya a matsayin ɗaya daga cikin alamomin Ƙarshan zamani; ﴿ [10]

حَتَّى إِذا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَ مَأْجُوجُ وَ هُمْ مِنْ كُلِّ حَدَبٍ يَنْسِلُونَ

Ma'ana, har zuwa lokacin da za'a buɗe(wannan Katanga)) Ya'ajuju da Ma'ajuj za su ɓuɓɓugo daga loko da saƙo. Kazalika bayyanarsu a ƙarshan zamani ta zo a cikin tsohon alƙawari kan batun tafiyar Hazƙil da cikin mafarkin Yuhan a sabon Alƙawari.[11]

Bayanin kula

  1. Al-ahadul Qadim, Safru Hizqil Nabiyyi, Al-is'hahu 38 shafi na 2-3.
  2. Al-ahadul Qadim, Safru Takwin, Al-is'hahu10
  3. Al-ahadul Qadim, Safru Hizqil Nabiyyi, Al-is'hahu 38 shafi na 2-3.
  4. Al-Husayni Al-Tihrani, Ma'arifat Al-Ma'ad, Juzu'i na 4, shafuffuka 51 da 52
  5. Al-Husayni Al-Tihrani, Ma'arifat Al-Ma'ad, Juzu'i na 4, shafuffuka 51 da 52
  6. Jafari, Zu Al-Qarnayn da Qawm Yajuj wa Majuj, shafi na 99
  7. Makarem Al-Shirazi, Al-Amthal, Juzu'i na 9, shafuffuka 354-355
  8. Suratul Kahf, aya ta 93 zuwa 98
  9. Al-Husayni Al-Tihrani, Ma'arifat Al-Ma'ad, Juzu'i na 4, shafuffuka 51 da 52
  10. "Makarem Al-Shirazi, Al-Amthal, Juzu'i na 10, shafi na 245."
  11. Al-ahadul Qadim, Safru Hizqil Nabiyyi, Al-is'hahu 38 shafi na 2-3. da Al-ahadul jadid mafarkin Yuhana, Al-is'hahu 20 shafi na 7-zuwa 9

Nassoshi

  • Jafari, Ya'qub, Zu Al-Qarnayn da Qawm Yajuj wa Majuj, Waqf Mirath Jawidan, bazara da lokacin zafi na shekarar 1382 Shamsi, lamba 41 da 42, shafi na 99.
  • Husayni Tihrani, Sayyid Muhammad Husayn, Ma'adshinasi, Mashhad, wallafar Allama Tabataba'i, shekarar 1425 Hijira.
  • Khurrammu Shahri, Baha'uddin, Istilahat Qur'anidar Mahaware Farsi, Qom, mujallar Baynat, Ma'aikatar Adabi na Imam Reza (a.s), bazara ta shekarar 1373 Shamsi, lamba 1, shafi na 40.
  • Al-ahadul jadid, Nukahsafaa Yuhana, babi na 20, aya ta 7-9.
  • Al-ahadul Ataiq, littafin annabi Ezekiel, babi na 38, aya ta 2 da ta 3.