Assidiƙatush Shahida (Laƙabi)

Assidiƙatush Shahida (Larabci: الصديقة الشهيدة) laƙabi ne guda biyu na Sayyida Faɗima Zahra (S) Assidiƙa tana nufin mai gaskiya, Asshahida ma'ana wacce aka kashe cikin tafarkin Allah.
A cikin riwaya daga Imam Kazim (A.S) kuma riwayar ingantacciya ce.[1] a cikinta ne Imam Kazim ya yi amfani da wannan laƙabi guda biyu kan Faɗima Zahra (S) ya ce haƙiƙa Faɗima Azzahara Siddiƙa ce kuma mai gaskiya ce,[2] ya zo a cikin riwaya kamar haka: «السَّلَامُ عَلَيْكِ أَيَّتُهَا الصِّدِّيقَةُ الشَّهِيدَةُ» (Aminci ya tabbata a gareki yake mai gaskiya kuma shahida.[3] sai dai cewa bisa ra'ayin Muhammad Hadi Mazandarani yana ganin duk ziyarorin Faɗima Zahra (S) sun zo ne a cikin wannan littafin guda ɗaya. [4] kamar wannan maganar wadda ta ƙunshi kalmomi guda biyu Mai gaskiya da Shahida ba su zo cikin hadisi ba, kamar yadda Shaik Saduƙ ya ce, a cikin masallacin Annabi akwai wannan jamlar, (Aminci ya tabbata ga Faɗima), amma ba tare da ya jingina wannan magana ga wani Imami Ma'asumi ba.[5]
Assiddiƙa tana nufin mace mai gaskiya ko mai yawan gaskiya.[6] haƙiƙa wannan kalma ta Assiddiƙa ta zo cikin hadisai ita kaɗai a matsayin laƙabin na Faɗima, misali Imam Ali (A.S) ya kira sunanta da wannan yanayin (Assiddiƙa).[7] kamar yadda Imam Sadiƙ (A.S) ya ambaci sunaye guda tara na Sayyida agurin Allah (S) ɗaya daga cikinsu shi ne Assiddiƙa (mai gaskiya),[8] kamar yadda Imam Hassan Askari (A.S) ya yi bayanin yadda sallama ga Annabi da Wasiyyanshi, da kuma salla,ma ga Faɗima Zahra (A.S) ya ce: «اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى الصِّدّيقَةِ فَاطِمَة الزَّكِية...»Allah ka yi tsira ga Faɗima mai gaskiya kuma tsarkakakkiya.[9]
Shahida tana nufin wace aka kashe bisa tafarkin Allah.[10] Shi'a sun yi imanin cewa Faɗima Azzahara ta yi shahada ne.[11] kuma akwai abubuwan da suke tabbatar da shahadarta, ta hanyar harin da aka kai gidanta da yi mata barazana ta bankawa gidanta wuta, da kuma danna ta da aka yi tsakanin ƙofa da bango da zubar mata da ciki wanda ya yi watanni da haurinta da ƙafa da dukanta da gidan takobi da bulala da karya mata haƙarƙari sakamakon harin da aka kai a gidanta, duk wannan abubuwan sun zo a hadisai da tarihi.[12]
Bayanin kula
- ↑ Muhammadi Al-Ray Shahri, Hikmat Nameh Fatimi, Shafi na 688
- ↑ "Al-Kafi" na Al-Kulaini da "Masail Ali bin Ja'far" na Al-Uridhi, Masa'il Aliyu Bin Jafar shafi na 325 lambar hadisi 811
- ↑ Sheikh Al-Saduq, Man La Yahduruhu Al-Faqih. Juzu'i na 2, shafi na 573
- ↑ Sharh Furu' al-Kafi (Juzu'i na 5, shafi na 528)
- ↑ Sheikh Al-Saduq, Man La Yahduruhu Al-Faqih. Juzu'i na 2, shafi na 573
- ↑ Al-Kajuri, Al-Khasa'is Al-Fatimiyya ya rubuta, Juzu'i na 1, shafi na 218, Tafsir Imam al-Askari wanda aka jingina ga Imam al-Askari (Shafi na 340, Hadisi na 216)
- ↑ Minyat al-Murid Shahid al-Thani (Shafi na 115)
- ↑ Ilal al-Sharai' (Shafi na 178, Hadisi na 3), Al-Khisal (Shafi na 414, Hadisi na 3)
- ↑ Misbah al-Mutahajjid wanda Sheikh Al-Saduq ya rubuta (Shafi na 399), Jamal al-Usbu' wanda Ibn Tawus ya rubuta (Shafi na 296
- ↑ Sheikh Al-Turayhi, wanda ke cikin Juzu'i na 3, Shafi na 81.
- ↑ Muhammad Al-Ray Shahri, musamman shafuka 37 da 688
- ↑ Muhammad Al-Ray Shahri ya rubuta, kuma ya keɓanta da darussa da hikimomi daga rayuwar Sayyida Fatima Al-Zahra (A.S)
Nassoshi
- Jamal al-Usbu' na Ibn Tawus, da aka bincika ta Jawad Qayumi, bugu na shekarar 1371 (Shamsi).
- Minyat al-Murid fi Adab al-Mufid wa al-Mustafid na Shahid al-Thani, da aka bincika ta Rida Mukhtari, bugu a Qum, da Maktabat al-I'lam al-Islami, 1409 H.
- Al-Khisal na Sheikh Al-Saduq, da aka bincika ta Ali Akbar Ghafari, bugu a Qum, Mu'assasat al-Nashr al-Islami, 1362 (Shamsi).
- Man La Yahduruhu Al-Faqih na Sheikh Al-Saduq, bugu a Qum, Mu'assasat al-Nashr al-Islami, bugu na 2, 1413 H.
- Ilal al-Sharai' na Sheikh Al-Saduq, da aka bincika ta Muhammad Sadiq Bahr al-Ulum, bugu a Najaf, Maktabat al-Haydariya, 1385 H/1966 M.
- Majma' al-Bahrain na Fakhreddin al-Turayhi, da aka bincika ta Sayyid Ahmad al-Husayni, bugu a Tehran, Maktabat al-Murtadawi, bugu na 2, 1363 (Shamsi).
- Misbah al-Mutahajjid na Sheikh al-Tusi, bugu a Beirut, Mu'assasat Fiqh al-Shi'a, bugu na 1, 1411 H/1991 M.
- Masail Ali bin Ja'far wa Mustadrakatih na Ali bin Ja'far al-Uraydhi, bugu a Qum, bincike daga Mu'assasat Aal al-Bayt, bugu na 1, 1409 H.
- Al-Khasa'is al-Fatimiyya na Muhammad Baqir al-Kajuri, bugu a Qum, Sharif Radi, bugu na 1, 1380 (Shamsi).
- Al-Kafi na Muhammad bin Ya'qub al-Kulayni, gyara ta Ali Akbar Ghafari da Muhammad al-Akhundi, bugu a Tehran, Dar a-Kutub al-Islamiyya, bugu na 4, 1407 H.
- Sharh Furu' al-Kafi na Muhammad Hadi al-Mazandarani, bugu a Qum, Dar al-Hadith, 1388 (Shamsi).
- Tafsir Imam al-Askari wanda aka jingina ga Imam al-Askari, bugu a Qum, Makarantun Imam al-Mahdi, bugu na 1, 1409 H.
- Hikmat Nameh Fatimi na Muhammad al-Ray Shahri, bugu a Qum, Dar al-Hadith, 1395 (Shamsi).