At-Tahnik
At-Tahnik (Larabci: التحنيك) ɗaya ne daga cikin ladubban Muslunci, wanda yake nufin sa ruwa da abinci ɗan kaɗan a bakin jaririn da aka haifa, malaman fiƙihu na Shi'a suna ganin Tahnik na Jariri da ruwan Tafkin Furatu da ƙasar kabarin Imam Husaini (A.S) a matsayin mustahabbi, bisa abin da ya zo a wasu hadisai duk jaririn da aka yi wa Tahnik da ruwan ƙoramar Furat zai zama ɗan Shi'a kuma masoyin iyalan gidan Manzo Allah (S.A.W)
Ma'anar Tahnik
Yiwa yaro Tahnik, shi ne Sanya wani abinci ɗan kaɗan kuma marar nauyi a bakin jariri sabuwar haihuwa.[1] ungozoma ce za ta sa abincin a bakin jaririn ko wani mutumin daban.[2] Wannan ladabi na tahnik sunna ne a al'ada kuma an san shi da Tahnik na jariri.[3] Abin da ya sa mutane suke yin Tahnik a bisa aƙidar mutane gama-gari shi ne domin kariya da neman sauƙi yayin da mahaifiyarshi take shayar da shi, da kada ya tsinbure da sauƙaƙa tarbiyarshi kan addini idan ya girma.[4]
Muhimmanci Tahnik
Ya zo a cikin littafin Wasa'ilush Shi'a littafi ne na hadisi a gun `yan shi'a babi kan mustahabbancin yin Tahnik ga jariri da wasu hukunce-hukuncenshi.[5] Bisa abin da ya zo a wasu hadisai duk wanda aka yi wa Tahnik da ruwan Tafkin Furatu zai zama ɗan shi'a masoyin Ahlul-baiti (A.S).[6]
Ita wannan al'ada ta yin tahnik ta daɗe tin kafin zuwa Muslunci a alumu daban-daban,[7] wasu daga cikin littafan tafsiri na Ahlus-Sunna wajan fassara aya ta 25 cikin suratul Maryam sun faɗi cewa, ita wannan sunna ta yin Tahnik ga jariri, ta samo asali ne a lokacin da Sayyida Maryam (A.S) ta ci dabino a lokacin haihuwar [[Isa (Annabi)|Annabi Isa (A.S)],[8] daga cikin al'adar Sahabbai a farkon Musulinci a lokacin haihuwar jariri suna ɗaukashi zuwa ga Annabi (S.A.W) shi Annabi ya kasance yana yi mishi Tahnik da dabino kuma ya yi mishi addu'a,[9] A zamanin Imaman Shi'a kaɗan-kaɗan sai Tahnik da ruwan Furatu ya zama mustahabbi mai karfi daga Imamai bayan shahadar Imam Husaini (A.S) sai tahnik ya zama ana yin shi da ƙasar kabarin Imam Husain (A.S)[10]
Ladubbanshi A Fiƙihu
Ya zo a cikin hadisi yadda Annabi (S.A.W) da Imamai (A.S) suke yin tahnik, misali an karbo daga Imam Ali (A.S) cewa Annabi (S.A.W)a lokacin haihuwar Imam Hassan da Husaini (A.S) ya yi musu Tahnik da dabino.[11] a wata ruwayar kuma ya zo cewa Imam Kazim (A.S) ya yiwa ɗanshi Imam Rida (A.S) Tahnik da ruwan Furat.[12]
Kan abin da malaman fiƙihu suka kawo akwai la'akari da Tahnik a matsayin mustahabbi a lokacin haihuwa kafin ranar Suna.[13] Haka nan mustahabbi ne ayi tahnik da ruwan Furat da ƙasar kabarin Imamu Husaini (A.S),[14] idan babu ruwan furat sai ayi amfani da ruwa garai-garai zalla, idan babu sai ruwan gishiri sai a zuba dabino kaɗan a cikin ko zuma.[15] Ibnl Ƙayyum Aljauzi ɗaya daga cikin malaman Ahlus-Sunna yana ganin Tahnikin jariri a lokacin haihuwa mustahabbi ne.[16]
Bayanin Kula
- ↑ "Karimi, 'Tahnik Tifli, shafin Markazu Da'iratil Marif Islamiyya al-kubra,."
- ↑ "Karimi, 'Tahnik Tifli, shafin Markazu Da'iratil Marif Islamiyya al-kubra,."
- ↑ "Dehkhoda, 'Lugat nameh Dehkhoda,' karkashin kalmar 'Tahnikul Tifli'."
- ↑ "Karimi, 'Tahnik Tifli, shafin Markazu Da'iratil Marif Islamiyya al-kubra. "Al-Wahidi, 'Tahnik Tifli,' shafin Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan."
- ↑ "Al-Hurr Al-Amili, 'Wasail al-Shia,' 1409 AH, Juz'i 21, Shafi'i 407."
- ↑ "Ibn Qulawayh, 'Kamil al-Ziyarat,' 1356 SH, Shafi'i 49; Al-Majlisi, 'Rawdat al-Muttaqin,' 1406 AH, Juz'i 8, Shafi'i 622."
- ↑ "Al-Wahidi, 'Tahnikul Tifli,' shafin Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan."
- ↑ "Al-Zamakhshari, 'Al-Kashshaf,' 1407 AH, Juz'i 3, Shafi'i 13; Haqqi Bursi, 'Ruh al-Bayan,' Dar al-Fikr, Juz'i 5, Shafi'i 327."
- ↑ "Al-Subhani, 'Wahabiyya' 1388 SH, Juz'i 1, Shafi'i 337."
- ↑ "Al-Wahidi, 'Tahnikul Tifli,' shafin Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan."
- ↑ "Al-Hurrul Al-Amili, 'Wasail al-Shia,' 1409 AH, Juz'i 21, Shafi'i 407."
- ↑ "Al-Hurrul Al-Amili, 'Wasail al-Shia,' 1409 AH, Juz'i 21, Shafi'i 408."
- ↑ "Misali: Al-Muhaqqiq al-Hilli, 'Shara'i' al-Islam,' 1408 AH, Juz'i 2, Shafi'i 287; Al-Najafi, 'Jawahir al-Kalam,' 1404 AH, Juz'i 31, Shafi'i 252."
- ↑ "Al-Muhaqqiq al-Hilli, 'Shara'i' al-Islam,' 1408 AH, Juz'i 2, Shafi'i 287; Fakhr al-Muhaqqiqin, 'Idhahu al-Fawaid,' 1387 AH, Juz'i 3, Shafi'i 258; Allama al-Hilli, 'Qawa'id al-Ahkam,' 1413 AH, Juz'i 3, Shafi'i 97."
- ↑ "Al-Muhaqqiq al-Hilli, 'Shara'i' al-Islam,' 1408 AH, Juz'i 2, Shafi'i 287; Allama al-Hilli, 'Qawa'id al-Ahkam,' 1413 AH, Juz'i 3, Shafi'i 97; Fakhr al-Muhaqqiqin, 'Idhahu al-Fawaid,' 1387 AH, Juz'i 3, Shafi'i 258."
- ↑ "Ibn Qayyim al-Jawziyyah, 'Tuhfat al-Mawdud bi Ahkam al-Mawlud,' Maktabat al-Qur'an, Shafi'i 30."
Nassoshi
- Ibn Qulawayh, Ja'afar bin Muhammad, 'Kamil al-Ziyarat,' Najaf, Dar al-Murtadawiyya, 1st Edition, 1356 SH.
- Ibn Qayyim al-Jawziyyah, Muhammad bin Abi Bakr, 'Tuhfat al-Mawdud bi Ahkam al-Mawlud,' Misra, Maktabat al-Qur'an, no date.
- Al-Bahrani, Yusuf, 'Al-Hada'iq al-Nadira fi Ahkam al-'Itra al-Tahira,' Qom, Maktab Nashr al-Islam, 1405 AH.
- Al-Hurr al-'Amili, Muhammad bin al-Hasan, 'Wasail al-Shia,' Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (ع), 1st Edition, 1409 AH.
- Haqqi Bursi, Isma'il bin Mustafa, 'Tafsir Ruh al-Bayan,' Beirut, Dar al-Fikr, no date.
- Dehkhoda, Ali Akbar, 'Lugatnama Dehkhoda,' under the supervision of Muhammad Mu'in and Sayyid Ja'afar Shahidi, Tehran, Mu'assasat Intisharat wa Jami'at Tehran, 1377 SH.
- Al-Zamakhshari, Mahmoud, 'Al-Kashshaf 'an Haqaiq Ghawamid al-Tanzil,' Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 3rd Edition, 1407 AH.
- Allama al-Hilli, Hasan bin Yusuf, 'Qawa'id al-Ahkam fi Ma'rifat al-Halal wa al-Haram,' Qom, Maktab Nashr al-Islam, 1413 AH.
- Fakhr al-Muhaqqiqin, Muhammad bin Hasan, 'Idhahu al-Fawaid fi Sharh Mushkilat al-Qawa'id,' Qom, Mu'assasat Isma'iliyan, 1st Edition, 1387 AH.
- Karimi, Asghar, 'Tahnik al-Tifl,' website of the Center for the Islamic Encyclopedia, last update: 1 Azar 1400 SH, visit date: 20 Azar 1403 SH.
- Al-Majlisi, Muhammad Taqi, 'Rawdat al-Muttaqin fi Sharh Man La Yahduruhu al-Faqih,' Qom, Mu'assasat al-Thaqafa al-Islamiyya Kushanpur, 2nd Edition, 1406 AH.
- Al-Muhaqqiq al-Hilli, Ja'afar bin Hasan, 'Sharai' al-Islam fi Masa'il al-Halal wa al-Haram,' Qom, Mu'assasat Isma'iliyan, 2nd Edition, 1408 AH.
- Al-Najafi, Muhammad Hasan, 'Jawahir al-Kalam fi Sharh Sharai' al-Islam,' Beirut, Dar Ihyaa al-Turath al-Arabi, 7th Edition, 1404 AH.