Tufafin Mai Sallah

Daga wikishia
Wannan wani rubutgu ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Risala Ilmiyya

Tufafin Mai Sallah, (Larabci: لباس المصلي) kaya ne da wanda zai yi Sallah yake sawa, hakika Malaman Fikihu sun bayani kan Mikdarin Girman Kayan Mai Sallah tare da sharuddansu, Malaman Fikihu sun yi Ijma’i kan wajabcin Lullube Baki dayan Jikin Mace in banda Zagayen Fuska da tsintsiyar Hannu zuwa geffan yatsu a lokacin da ta tashi yin Sallah kuma babu bambanci gaban Muharraminta za ta Sallar ko gaban wanda ba Muharraminta ba, sannan babu wannan wajabcin kan Maza, kadai wajabcin Suturce Al’aura ne yake kan Maza a lokacin da za su yi Sallah. Daga cikin Sharuddan Tufafin Mai Sallah wajibi ne Tufafin ya kasance tsarkakakke kuma ya zama bai tabu da Najasa ba, kuma Tufafin nasa bai kasance daga sassan Dabbobin da aka Haramta cin Namansu ba, daga misalin Fata da gashinsu, dole ne ya kasance daga Dabbobin da aka halasta cin Namansu kuma aka yanka su yankan shari’a. Kan asasin Fatawar Malaman Fikihu sun ce baya halasta ga Maza Sanya Tufafin da aka dinka daga Zinare da wanda ya kasance daga Jinsin Alhariri, kuma Sallar da aka yi sanye da irin wannan nau’in Tufafin batacciya ce, haka kuma Malaman Fikihu sun yi bayanin Hukunce-hukunce na Mustahabbi da Makruhi da suke da alaka da Tufafin Mai Sallah.

Matsayi

Tufafin Mai Sallah a lokacin da ya tashi Sallah dole ne su kasance suna kan hukunce-hukunce da sharuddan Tufafin Mai Sallah, Malaman Fikihu cikin ba’arin Babukan Fikihu Kamar misalin Babun Dahara da Sallah sun yi bayani filla-filla Kan Tufafin Mai Sallah zai sanya a jiki lokacin da zai yi sallah [1] Hurrul Amili cikin Littafin Wasa’ilul Ash-Shi’a ya waro sashe guda da ya tsara shi cikin taken (Abwabu Libasul Al-Musalli) sannan ya zuba riwayoyin daban-daban da suke bayanin Hukunce-hukuncen Tufafin Mai Sallah ya tsara su cikin babi 64 mabambanta [2]

Mikdarin Tufafin Mai Sallah a Lokacin da zai yi Sallah

Mikdarin Suttura da Mata da Maza za su Sanya a Lokacin Sallah a Mahangar Fikihu:

  • Sutturtar Mace

A cewar ba’arin Malaman FIkihu, Malamai sun yi Ijma’I [3] kan cewa Mace idan ta tashi Sallah babu bambanci a gaban Muharraminta ne za ta yi Sallah ko Kuma a gaban wand aba Muharraminta ba [4] wajibi ta suturce baki dayan Jikinta in banda zagayen Fuska da tsintsinyar Hannu zuwa geffan Yatsa nan kadai ya halasta ta bari a bude, [5] na’am wasu Jama’a daga Malaman Fikihun Shi’a sun bayyana shakku kan wajabci Lulluba Gashinta [6] Ibn Junaidu daga Malaman Karni na 4 h Kamari yana ganin babu wata matsala idan mace bata lullube gashinta ba a lokacin da ta ke Sallah matukar dai babu wanda ba muharraminta ba a wurin. [7] Wasu ba’arin Malaman Fikihu sun tafi kan ra’ayin cewa Fuska da Hannu da saman Kafafu suma babu Matsala idan ba ta rufe su ba a lokacin da za ta yi Sallah [8] Tabataba’I Yazdi Mawalllafin Littafin Al-Urwatul Al-Wuska ya ce babu Matsala cikin barin Tafin Kafa a bude ba a lulluba a lokacin da ta ke Sallah. [9]

Sutturar Namiji

Malamai Sun yi Ijma’I, [10] kan cewa babu wajabcin kan Namiji cikin Sallah ya lullube wani abu daga jikinsa in banda Al’aurarsa [11] a cewar Tabataba’I Yazdi Mustahabbi ne Namiji ya lullube jikinsa daga cibiya zuwa Gwiwarsa, [12] a ra’ayin Mawallafin Littafin Al-Urwatul Al-Wuska yin Sallah ga Maza ba tare da lullube Jiki ba in banda Al’aura duk da cewa yin haka ya halasta amma fa makruhi ne. [13]

Ragowar Hukunce-hukunce

Malaman Fikihun Shi’ a sun yi Ijma’I kan cewa wajibi Tufafin Mai Sallah ya kasance Tsarkakakke [14] idan ya tabu da Najasa wajibi ne a kawar da wannan Najasa [15] na’am Malaman Fikihu suna ganin Tufafin da ya cudanyu da Jinin Miki da jinin Kurji ko kuma wani yanka da jinin yake diga daga gare shi, haka kuma jinin bai fi girman Dirhami ba da tare da sharadin kada jinin ya kasance daga Haila da Nifasi ko Istihada, babu matsala daga wadannan Jinane an togace su. [16] Haka kuma an ce Tufafin da baya yiwuwa a yi Sallah da su sakamakon kankatarsu na rashin lullube Al’aura, kamar misalin Safa, Hula, Safar Hannu, Hular Tashi Ka Fiye Naci, ko da sun tabu da Najasa babu matsala ayi Sallah sanye da su. [17] wasu ba’arin Malaman Fikihu sun ce kayayyaki da kayan amfani kanana-kanana kamar misalign Zobe, Makulli, Da Sulallan Zinare idan ko da kasance Najasa ba matsala cikin yin Sallah dauke da su. [18] Kan ra’ayin Mashhur daga Malaman Fikihun Shi’a [19] Matar da take Rainon Yaro Karami babu bambanci Namiji ko Mace ko kuma ita din ba Mahaifiyarsa bace sai ya zamanto Tufafi guda daya take da shi, idan wannan Tufafin ya Najastu da fitsarin Yaron, ya wadatar mata ta wanke sau daya tsawon yini ba dole bane idan ta tashi Sallah sai ta tsarkake shi ba [20]

Kasancewar Tufafin Daga Halas

Malamai sun yi Ijma’i kan wajabcin kasancewar Tufafin da za ayi Salklah da shi daga Tufafin Halas ma’ana bai kaasan ce daga Tufafin Kwace ba, [21] kan wannan bayani ne idan Mai Sallah ya yi Sallah da Tufaffin Haram alhalin ya san baya halasta a yi Sallah da wannan Tufafi to Sallarsa batacciya ce, [22] na’am idan ya kasance bai sani ba ko kuma ya manta cewa yana sanye da Tufafin Kwace to Sallarsa bata bacu ba, [23] amma idan ya tuna yana tsaka da yin Sallah sannan kuma akwai yiwuwar Kammala Sallarsa ba tare da wannan Tufafi da ya sanya ba, ma’ana akwai Mikdarin da zai lullube masa Al’aura daga Tufafin Halas, wajibi take kai tsaye ya cire wannan Tufafi na kwace ko da kuwa iya Raka’a daya rak zai iya yi a cikin lokacin Sallar, na’am idan ya zama me masa tilashi yin sallar da wannan Tufafi na kwace domin kare Ransa ko dukiyarsa babu matsala ya yi sallah da wannan Tufafi na kwace kuma Sallarsa ta inganta. [24] idan Mai Sallah ya yi sallah da Tufafin da aka saye su da Kudin da ba a cire Khumusi daga cikinsu ba, Sallarsa batacciya ce, [25] a fatawar Wasu Malaman duk da cewa amfani da kayan kwace misalin Zobe,wayar Salula, Belt ya Haramta, sai dai kuma kasancewa tare da su a lokacin yin Sallah baya bata Sallah. [26]

Jinsin Tufafi

Kan asasin Fatawar Malaman Fikihu Bai kamata Mai Sallah ya yi amfani da Tufafin da aka dinka shi daga wani Sassa daga Dabbobin da ba ya halasta a ci namansu kamar misalin Fatarsu, Gashinsum idan wani daga bangraen wadannan Dabbobi ya kasance tare da shi to Sallarsa batacciya ce, [27] haka kuma sun ce idan ya kasance abubuwa misalin Miyau da Kashin Dabbobin da ya haramta a ci Namansu suka damfaru da jikin Mai Sallah to Sallar da ya yi tare da su ta baci, [28] haka kuma Tufafin Mai Sallah ba ya halasta ya kasance daga Mushen Dabbobin da aka Haramta cin Namansu da ma wanda aka halasta cin namansu wanda ba a yanka su ba yanka ta hanyar Shari’a. [29] Sanya Tufafin da aka yi masa Ado da Zinare hakika ya haramta ga Maza, kuma Sallar da aka yi cikin wannan Tufafi batacciya ce, [30]haka kuma rataya Sarkar Zinare ko sa Zoben Zinare ko Agogon Zinare ya Haramta ga Maza, sannan a Fatawar wasu Malamai, Wajibi ne a cire su lokacin yin Sallah [31] Kan asasin Fatawowin Malaman Fikihu, ya haramta ga Maza Sanya Tufafi da ya kasance daga Alharir, kuma Sallar da suka yi sanye da wannan Tufafi Batacciya ce [32] sannan Abubuwa Misalin Safar Kafa, Hula,Hular Tashi Ka fi ye Naci, da misalansu idan an yi su daga tsantsar Alhariri hakika a ra’ayin wasu daga cikin Malaman Fikihu Sallar da aka yi sanye da su batacciya ce. [33]

Mustahabbai da Makruhai

Malaman Fikihu bisa la’akari da riwayoyin Imamai Ma’asumai (A.S) kari kan Fatawowinsu kan Tufafin Mai Sallah, hakika a wannan fage na Tufafin Mai Sallah sun yi bayani dangane da Mustahabbai da Makruhai. [34]

Mustahabbai

Wasu ba’arin wurare Na Mustahabbi ga Tufafin Mai Sallah:

  • Sanya Farin Kaya.
  • Sanya Abaya ga Namiji mace Kuma Hijabi.
  • Sanya tsaftaccen Tufafi.
  • Sanya Turare mai Kamshi.
  • Sanya Zoben Akik. [35]

Makaruhai

Hakika Mawallafn Littafin Al-Urwa Al-Wuska sai da ya kawo wurare 33 na Makaruhai cikin Tufafin Mai Sallah, ba’arin wasunsu ya kasance kamar haka:

  • Sanya Bakaken Kaya.
  • Sanya Kaya masu Datti.
  • sanya Tufafin da yake dauke da Hoton Mutum Ko Dabba.
  • Sanya Nikabi ga Mata.
  • Sanya Matsatsun Tufafi.
  • Sanya Siraran Kaya shara-shara su Kadai a jiki.
  • Sanya Tufafin Shuhra. [36]

Bayanin kula

  1. Misali, duba Bahrani, Hadaeq al-Nadrah, 1363, juzu'i na 5, shafi na 290; Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 327.
  2. Misali, duba Hurrul Ameli, Wasa'il al-Shia, 1416 AH, juzu'i na 4, shafi na 343-465.
  3. Mohaghegh Hilli, Al-Mutbar, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi 101; Hakim, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 250.
  4. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi.318; Marashi Najafi, Minhaj al-Mu’minin, 1406 AH, juzu’i na 1, shafi na 143.
  5. Mohaghegh Hilli, Al-Matbar, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi 101; Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi.318; Hakim, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 250.
  6. Misali, duba Mohaghegh Ardabili, Majma al-Fedat wa al-Barhan, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 105; Mousavi Ameli, Takardun Al-Ahkam, 1429 AH, Mujalladi 3, 189; Hakim, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, 1387 H., juzu'i na 5, shafi na 255.
  7. Ibnu Junayd, Majmu'eh fatawa Ibn Junayd, 1416 AH, shafi na 51
  8. Sheikh Tusi, Al-Mabusut, 1387 AH, juzu'i na 1, shafi na 87; Mohaghegh Hilli, Al-Mutbar, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi 101; Shahidi na daya, al-Alfiyah da al-Nafiliya, 1408H, shafi na 50.
  9. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 319
  10. Sabzevari, Mahezzab Al-Ahkam, Dar al-Tafseer, juzu'i na 5, shafi na 243.
  11. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 8, shafi na 175.
  12. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 319.
  13. Najafi, JawahirulKalam, 1362, juzu'i na 8, shafi na 175.
  14. Sabzevari, Mahezzab Al-Ahkam, Dar al-Tafseer, juzu'i na 5, shafi na 262.
  15. Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiya, 1410 AH, juzu'i na 1, shafi na 289; Bahrani, Al-Hdayek al-Nazara, 1362, juzu'i na 5, shafi na 290.
  16. Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiya, 1410 AH, juzu'i na 1, shafi na 289; Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, Mujalladi na 1, shafi na 210.
  17. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 219.
  18. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 219; Hakim, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, juzu'i na 1, shafi na 582.
  19. Bahrani, Hadaeq al-Nazara, 1363, juzu'i na 5, shafi na 345.
  20. Bahrani, Hadaeq al-Nazara, 1363, juzu'i na 5, shafi na 345; Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 221.
  21. Hakim, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, juzu'i na 5, shafi na 278.
  22. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 328.
  23. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, Juzu'i na 2, shafi na 328-329.
  24. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 232.
  25. Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 151.
  26. <a class="external text" href="https://makarem.ir/ahkam/fa/category/index/44581/شرایط-لباس-نمازگزار?page=6&sortby=0&sort=0&view=1">«شرایط لباس نمازگزار»</a>سایت جامع المسائل، مرکز پاسخگویی به احکام شرعی و مسائل فقهی، دفتر آیت‌الله مکارم شیرازی.
  27. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 337.
  28. Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 151.
  29. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 334.
  30. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 341; Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 152.
  31. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, Juzu'i na 2, shafi na 341-342.
  32. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, Juzu'i na 2, shafi na 343-344; Khumaini, Tahrir al-Wasila, 1434H, juzu'i na 1, shafi na 153.
  33. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Waghti, 1417 AH, Juzu'i na 2, shafi na 343-344.
  34. Misali, duba Sabzevari, Mahezzab Al-Ahkam, Dar al-Tafsir, juzu'i na 5, shafi.347
  35. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 361.
  36. Tabatabaei Yazdi, al-Arwa al-Waghti, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 360.

Nassoshi

  • Ibn Junayd, Muhammad Bin Ahmed, Majmu'eh Fatawa Ibn Junayd, wanda Alipanah Eshtredi, Qum, Mu’assasa Al-Nashar al-Islami ya yi bincike, 1416 Hijira.
  • Bahrani, Youssef, Hadaeq al-Nadrah, Qom, Al-Fakr al-Islami Foundation, 1363.
  • Hakim, Seyyed Mohsen, Mustamsk al-Arwa al-Waghti, Beirut, Dar Ehiya Tarath al-Arabi, 1391H. 1387 A.H.
  • Hurrul Amili, Muhammad bin Hassan, Wasa'il al-Shia, Qum, Al-Bait Institute, 1416H.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Tehran, Imam Khumaini Cibiyar Gyara da Ayyukan Bugawa, bugu na farko, 1434H.
  • Sabzevari, Seyyed Abdul Ali, Mahezzab Al-Ahkam, Qom, Dar al-Tafsir, Bita.
  • «شرایط لباس نمازگزار»، سایت جامع المسائل، مرکز پاسخگویی به احکام شرعی و مسائل فقهی، دفتر آیت‌الله مکارم شیرازی، تاریخ بازدید: ۲۶ مرداد ماه ۱۴۰۲ش.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Mabusut fi fiqhu al-Umamiyah, Tehran, Al-Mortazawiyya Library for Revival of Al-Jaafari, bugu na uku, 1387H.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghti, Qom, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1417H.
  • Tabatabaei Yazdi, Mohammad Kazem, Al-Arwa Al-Waghhi, bincike: Est. Al-Nashar al-Islami, Qum, bugun farko, 7 1419 AH.
  • Muhakkik Ardabili, Ahmed bin Muhammad, Majma al-Fedat wa Al-Barhan, Qum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1403H.
  • Muhakkik Sabzevari, Mohammad Baqer, Kefaiya Al-Ahkam, Qom, Al-Nashar al-Islami Est., 2001.
  • Mohagheq Hilli, Jafar bin Hasan, al-Muttabrah fi Sharh al-Mukhatsar, Qom, Cibiyar Seyyed al-Shahada (a.s), bugu na farko.
  • Marashi Najafi, Seyed Shahabuddin, Minhaj al-Momenin, Qom, Ayatullah Marashi Najafi Library, 1406 AH, juzu'i na 1, shafi na 143.
  • Mousavi Ameli, Seyyed Mohammad, Madarikul Al-Ahkam, Qom, Al-Nashar al-Islami Institute, 1429 AH.
  • Najafi, Mohammad Hassan, Javaher Al-Kalam, Beirut, Dar Ihya Tarath al-Arabi, 1362.
  • Naraghi, Mulla Ahmad, Mustanad Al-Shia, Qum, Al-Bait Institute (AS), 1415 AH.