Salatul Hadiyya
Appearance
Salatul hadiyya (Larabci: صلاة الهدية ) Sallar da ake sadaukar da ladanta, sallah ce da aka rawaito daga Imamai Ma'asumai,[1] mustahabbi ne a yi ta ranar Jumu'a, raka'a takwas ce, raka'a biyu sau huɗu, a sauran ranaku kuma ana yi raka'a huɗu ne, raka'a biyu sau biyu,[2] sai a sadaukar da ladanta ga ɗaya daga cikin Ma'asumai sha huɗu.[3] Bisa abin da ya zo a littafan Muslunci ga yadda ake yinta:
- Ranar Juma'a: A yi raka'a takwas, bayan duk raka'a biyu za a yi Tashahhud sai ayi sallama, wannan raka'a huɗu sai a sadaukar da ladan Annabi Muhammad (S.A.W) sauran raka'a huɗun za a sadaukar da su ga Faɗima Zahra (S)
- Ranar Asabar: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Ali (A.S)
- Ranar Lahadi: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Hassan (A.S)
- Ranar Litinin: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Husaini (A.S)
- Ranar Talata: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Sajjad (A.S)
- Ranar Laraba: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Baƙir (A.S)
- Ranar Alhamis Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Sadiƙ (A.S)
- Ranar Juma'a: Idan ta zagayo za a ƙara mai-maitawa kamar yadda ta gabata a ranar farko.
- Asabar: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Kazim (A.S)
- Ranar Lahadi: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Rida (A.S)
Ranar Litinin: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Jawad (A.S)
- Talata raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Hadi (A.S)
- Ranar Laraba: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Hassan Askari (A.S)
- Ranar Alhamis: Raka'a hudu, a sadaukar da ladanta ga Imam Mahadi (A.F).[4]
An ce bayan ko wace raka'a guda biyu, sai a karanta wannan Addu'ar ta musamman, sai a sa sunan Imami da za a sadaukar da Sallar gare shi madadin kalmar wane.[5]
Bayanin kula
- ↑ "Al-Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H, shafi na 322."
- ↑ "Sayyid bin Tawus, Jamal al-Usbu', 1408 AH, shafi na 23."
- ↑ "Majlisi, Tuhfat al-Zair, 1386 SH, shafi na 658."
- ↑ "Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H, shafi na 322."
- ↑ "Majlisi, Tuhfat al-Zair, 1386 SH, shafi na 658."
- ↑ "Sayyid bin Tawus, Jamal al-Usbu', 1408 AH, shafi na 24."
Nassoshi
- Tusi, Muhammad ibn Hasan, Misbah al-Mutahajjid, Qom, Mu'assasatu Fiqhi al-Shi'a, 1411 H.
- Sayyid bin Tawus, Ali ibn Musa, Jamal al-Usbu' bi Kamal al-Amal al-Mashru', Tehran, Dar al-Ridha, 1408 H.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Tuhfat al-Zair, Qom, Mu'assasatu Peyam al-Imam al-Hadi (AS), 1386 SH.