Ɗakin Annabi

Ɗakin Annabi (Larabci: الحجرة النبوية) ɗakin Annabi wuri ne wanda aka binne Annabi (S.A.W) ɗaki ne wanda ya kasance yana rayuwa tare da A'isha, a samar ɗakin akwai ƙubba koriya ta kabarin Annabi wannan ɗaki ɗaya ne daga cikin ɗakuna biyu da aka ginawa Annabi a gabacin masallacinsa, girmanshi ya kai kimanin mita uku da rabi zuwa hudu da rabi, wannan ɗaki yana da ƙofa guda biyu ɗaya zuwa masallaci ɗayar kuma ta fita waje, gidan Sayyida Faɗima (S) yana bayan wannan ɗaki, a cikin wannan ɗaki ya yi rashin lafiya kuma a ciki ya rasu kuma a ciki aka yi mishi sallah. Kuma bisa shawarar Imam Ali (A.S) an binne Annabi a cikin wannan ɗaki.
Bayan an binne Annabi kuma an binne Abubakar da Umar a ciki, kuma shima Imam Hassan (A.S) ya yi wasiyya da a binne shi a ciki kusa da Annabi, amma Ai'sha da Umayyawa sun hana a binne shi a ciki. Amma bayan gyara da aka yi daga baya ɗakin Annabi ya zama wani ɓangare na masallacin Annabi, kuma akwai ginin kabari da gidan Faɗima a ciki. Wannan ɗaki yana da girma babba a gun musulmi, kamar yadda an sadaukar da abubuwa masu tsada ga wannan ɗaki, har yanzu wasu suna nan a cikin ginin kabarin Annabi (S.A.W)
Bayanin Kan Wannan Ɗakin
Ɗakin Manzon Allah (S.A.W), wanda aka fi sani da Gidan Manzon Allah,[1] da kuma ɗakin Manzon Allah (S.A.W), wato ɗakin Annabi da matarsa A'isha,[2] Bayan gina masallacin Annabi da kuma kammala shi, an gina ɗakuna biyu kusa da masallacin Annabi na Annabi da matanshi, ɗakin Sauda, da ɗakin A'isha[3]
Wasu nassosin tarihi sun ambaci cewa ƙabilar Banu Najjar ce ta gina wa Annabi wannan ɗaki.[4] Wannan ɗaki yana gabas da masallacin Annabi,[5] kuma Manzon Allah (S.A.W) ya kasance a wurin har zuwa karshen rayuwarshi.[6]
Tsawon bangon wannan ɗaki na gabas da yamma ya kai kimanin mita hudu da rabi zuwa biyar, kuma tsayin katangar arewa da kudu an kiyasta kusan mita uku da rabi.[7] A saman ɗakin Annabi,[8] akwai koriyar ƙubba, kuma wannan ɗaki yana da ƙofa guda biyu, ɗaya tana billewa zuwa masallaci, ɗayar kuma tana fita waje.[9]
Gidan Fatima Zahra yana bayan ɗakin Manzon Allah (S.A.W) a bangaren arewa,[10] akwai wani fafajiya a tsakanin waɗannan gidaje guda biyu,[11] inda ake tambayar Annabi halin `yarshi. A wani dare sai aka samu sabani tsakanin Sayyida Fatima (S) da A'isha, sai Sayyida Fatima ta yi fushi da ita,[12] sai Annabi ya rufe ratar da ke tsakaninsu bisa buƙatar Fatima.[13]
Binne Annabi
Annabi ya rasu a Madina, a ɗakin da ya zauna tare da A'isha,[14] A bisa shawarar da Imam Ali (A.S) ya bayar,[15] sai mutane suka shiga ɗakin Manzon Allah jama'a rukuni-rukuni suna yi masa addu'a.[16] An samu saɓani dangane da wurin da za a binne Annabi, amma daga karshe bisa shawarar Imam Ali an binne Manzon Allah (S.A.W) a daidai wurin da ya rasu.[17]

Haka nan an binne Abubakar da Umar a cikin wannan ɗakin, sannan kan Abubakar ya kasance a saitin kafaɗar Annabi, kan Umar kuma yana a setin kafaɗar Abubakar,[19] Bayan an binne Umar sai A'isha ta sanya labule a tsakanin wurin zamanta da kaburburan.[20] Ance ta yi hakan ne sakamakon Umar ba muharraminta ba ne.[21]
Imam Hassan (A.S) ya ba da shawarar cewa a binne shi kusa da Annabi (S.A.W), kamar yadda yake ganin ya fi kowa cancanta da hakan,[22] Amma A'isha matar Annabi ta hana binne Imam Hassan a kusa da Annabi.[23]
Sabinta Wannan Ɗaki

Walid Bin Abdul-Malik, Halifan Banu Umayyah (Mulki: 86-96 H), ya sake gina ɗakin Manzon Allah da duwatsu, sannan ya gina katanga mai ɓangarori biyar a kewayen ɗakin, an ambaci cewa ya yi wannan ginin ne saboda kada wannan ɗaki ya yi kama da Ka'aba.[25] Ci gaban da aka samu a zamanin Walid ya sa ɗakin Manzon Allah ya kasance a cikin masallaci,[26] A shekara ta 557 bayan hijira, an zuba gubar harshashi a karkashin ƙasa kewaye da kabarin Annabi, hakan ya faru ne saboda yiwuwar kutsawar Yahudawa cikin yankin, yayin da suke shirin kai hari da kutsawa ta hanyar tekun Bahar Maliya, an yi hakan ne don hana su isa ga kabarin Annabi.[27]
A shekara ta 668 bayan hijira, Al-Zahir Baibars ya gina katanga mai kusurwa guda biyar a matsayin ɗakin kabari a kewayen waɗannan bangarori guda biyar, sannan ya haɗa da gidan Fatima,[28] A cikin wannan ginin, ɗakin Manzon Allah (S.A.W) da ɗakin sayyida Fatima, waɗanda ke kewaye da wata kewayen kabari ta ƙarfe suka shiga cikin masallacin da ke da nisa da katangar gabas ta masallacin.[29]
Cikin Ɗakin
A ƙarni na bakwai bayan hijira, wani basarake Isma'ili a ƙasar Masar da ake kira Ibn Abi al-Haija'a ya sanya labule da aka rubuta Suratul Yasin a kan kabarin Annabi.[30] Wannan al'ada tana nan har yau, ta yadda ake dora wani kyalle a kan kabari kodayaushe.[31]
Ana girmama ɗakin Manzon Allah (S.A.W) kuma musulmi da sarakuna sun bada gudummawar kayayyaki masu daraja.[32] Daga cikin tsoffin kyaututtukan da suka rage har da kayan masu tsada da aka lullube da zinare da azurfa, kamar waɗanda ake samu a cikin ɗakin Ka'aba.[33]
Kafin mulkin iyalan Alu-Sa'ud, akwai wata waƙa tin ƙarni na goma sha biyu bayan hijira da aka rubuta da zinare a kewayen ɗakin Manzon Allah da baitika na yabo Manzon Allah (S.A.W), Sai dai bayan da Alu-Sa'd sun karbi mulki, an goge wasu daga cikin baitukan, saboda kasancewar wasu kalmomi a cikin baitukan a cewarsu, suna nuni da shirka ga Allah, wasu kuma na ganin cewa wannan waƙar ta kasance misali ne na halalcin yin tawassuli.[34]
Bayanin kula
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausi'u Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 61.
- ↑ «الحجرة النبوية. الملائكة يحفون بالقبر الشريف»،Madina.
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausi'u Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 61.
- ↑ "Maqrizi, Imta al-Asma, J1, Sh67."
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausi'u Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 61.
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausi'u Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 61.
- ↑ «الحجرة النبوية، المسجد من الداخل»، Jagora zuwa Madina Munawwara
- ↑ «الحجرة النبوية، المسجد من الداخلJagora zuwa Madina Munawwara
- ↑ «الحجرة النبوية، المسجد من الداخل»، Jagora zuwa Madina Munawwar.
- ↑ «الحجرة النبوية، المسجد من الداخل»، Jagora zuwa Madina Munawwar.
- ↑ "Saghir, Imam Ali (A.S.), Siratuhu wa Kiyadatuhu Fi Dau'i Al-minhaj Attahlili, Sh31."
- ↑ "Samhudi, Wafa' al-Wafa', J2, Sh57."
- ↑ Sabri Pasha, Mawusat Mir'at al-Haramayn al-Sharifayn wa Jazirat al-Arab, J3, Sh262.
- ↑ Ibn al-Umrani, Al-Inba' fi Tarikh al-Khulafa', Sh45.
- ↑ Mufid, Al-Irshad, J1, Sh188.
- ↑ Ibn Sa'ad, Al-Tabaqat al-Kubra, J2, Sh220.
- ↑ al-Irbili, Kashf al-Ghumma, J1, Sh19.
- ↑ «الحجرة النبویة.. قبر الرسول المصطفی و صاحبیه أبوبکر و عمر»، Kamfanin labarai na Saudiyya.
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausiatu Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 62.
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausiatu Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 62.
- ↑ Ansari, Imara Wa Tausiatu Al-masjid Annabawi Sharif Abarar Tarikh, Sh 62.
- ↑ al-Tusi, Al-Amali, Sh 160.
- ↑ Ya'qubi, Tarikhu Ya'qubi, J 2, Sh 225.
- ↑ «العثمانیون. من قصف الکعبة إلی سرقة مقتنیات الحجرة الشریفة»،Madina.
- ↑ Ansari,Imara Wa Tausi'atu Al-masjid Sharif Abarar Tarikhi, Sh63.
- ↑ Ibn Kathir, Al-Bidaya wa'l-Nihaya, J9, Sh75.
- ↑ Jafarian, Aasar Islami Makkah wa Madina, Sh256.
- ↑ Jafarian, Aasar Islami Makkah wa Madina, Sh256.
- ↑ پیشوایی، «چرا پیامبر اسلام در خانه خود به خاک سپرده شد؟»، Portal Jam'iyyan Ilimi na Dan Adam.
- ↑ Jafarian, Aasar Islami Makkah da Madina, Sh256.
- ↑ Isma'il، «تفاصيل وأسرار "يرويها" قليلون دخلوا الحجرة النبوية الشريفة»، Al-arabiyya.
- ↑ Saban، «مقتنيات الحجرة النبوية الشريفة بموجب تقرير عثماني عام 1326 هـ.»
- ↑ Isma'il، «تفاصيل وأسرار "يرويها" قليلون دخلوا الحجرة النبوية الشريفة»، Al-arabiyya.
- ↑ «الحجرة النبوية، المسجد من الداخل»،Jagoranka zuwa Madina.
Nassoshi
- Ibn al-Umrani, Muhammad ibn Ali, Al-Inba' fi Tarikh al-Khulafa', gyarawa da Qasim al-Samarrai, Al-Qahira, Dar al-Afaq al-Arabi, 2001 M.
- Ibn Sa'ad, Muhammad ibn Sa'ad, Al-Tabaqat al-Kubra, gyarawa da Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, F1, 1410 H/1990 M.
- Ibn Kathir, Isma'il ibn Umar, Al-Bidaya wa'l-Nihaya, Beirut, Dar al-Fikr, 1407 H/1986 M.
- Isma'il Faraj، «تفاصيل وأسرار "يرويها" قليلون دخلوا الحجرة النبوية الشريفة»arabiya, Tarihin Idarji: 30/03/2006 M, Tarihin Kallo: 05/02/2025 M.
- Irbili, Ali bin Isa, Kashf al-Ghumma fi Ma'rifat al-A'imma, Qom, Nashir al-Radhi, F1, 1421 H.
- Ansari, Naji Muhammad, Imara Wa Tausi'atu Al-masjidul sharif Abarar Tarikhi, Madina, Ƙungiyar Birnin Madina, 1996 M.
- *«الحجرة النبویة.. الملائکة یحفون بالقبر الشریفal-Madina, Tarihin Idarji: 30/07/2021 M, Tarihin Kallo: 05/02/2025 M.
- *«الحجرة النبویة.. قبر الرسول المصطفی و صاحبیه أبوبکر و عمر»،Hukumar Labarai ta Saudiyya, Tarihin Idarji: 10/05/2019 M, Tarihin Kallo: 05/02/2025 M.
- *«الحجرة النبوية، المسجد من الداخل»، Dalilin ku zuwa Madina al-Munawwarah, Tarihin Kallo: 05/02/2025 M.
- Samhudi, Ali bin Abdullah, Wafa' al-Wafa' bi Akhbar Dar al-Mustafa, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, 2006 M.
- Saghir, Muhammad Hussain, Imam Ali(A.S) Siraratuhu wa Kiyadatuhuta Fi Zau'i Al-minhaj Attahlili, Beirut, Ma'aikatar Buga Marifa, 2002 M.
- al-Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Al-Amali, gyarawa da Ma'aikatar Al-Ba'tha, Qom, Dar al-Thaqafa, F1, 1414 H.
- *«العثمانیون. من قصف الکعبة إلی سرقة مقتنیات الحجرة الشریفة»al-Madina, Tarihin Idarji: 26/02/2020 M, Tarihin Kallo: 05/02/2025 M.
- Mufid, Muhammad bin Muhammad bin al-Nu'man, Al-Irshad fi Ma'rifat Hujaj Allah 'ala al-Ibad, Qom, Taron Duniya na Mileniyum na Sheikh al-Mufid, F1, 1413 H.
- Maqrizi, Ahmad ibn Ali ibn Abd al-Qadir, Imta' al-Asma' bi ma li'l-Nabi min al-Ahwal wa al-Amwal wa al-Hafada wa al-Mata', gyarawa da Muhammad Abd al-Hamid al-Numaysi, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyya, F1, 1420 H/1999 M.
- Ya'qubi, Ahmad bin Ishaq, Tarikh Ya'qubi, Beirut, Dar Sadir, F1, 1379 H.
- Pishwayi Mahadi «چرا پیامبر اسلام در خانه خود به خاک سپرده شد؟»،Portal Jam'iyyan Ilimi na Dan Adam, Al'adar Kosar, Lamba 4, 1376 SH.
- Jafarian, Rasul, Aasar Islami Makkah wa Madina, Tehran, Mash'ar, F8, 1386 SH.
- *Saban Suhailu، «مقتنيات الحجرة النبوية الشريفة بموجب تقرير عثماني عام 1326 هـ»al-Madina al-Munawwarah Magazine, Jumada al-Awwal, 1422 H..
- Sabri Pasha, Ayyub, Mawsu'at Mir'at al-Haramayn al-Sharifayn wa Jazirat al-Arab, Al-Qahira, Dar al-Afaq al-Arabiya, 1424 H.