Alamomin Bayyana

Daga wikishia

Alamomin Bayyana (arabic: علامات الظهور) ko kuma ace abubuwan da suke nuni kan bayyana wasu abubuwa ne da za su afku daf da lokacin bayyana ko mikewar Imam Zaman (A.F). wadannan Alamomi sun kasu zuwa kashi biyu: tabbatattu da wanda ba tabbatattu bu, Alamomi Tabbattu sune wanda babu shakka da kokwanto tabbas zasu faru kafin bayyanar Imam Mahadi, misalin Tsawa da karajin Sama, Fitowar Sufyani Mikewar Yamani, Kashe Nafsuz Zakiyya, Kisfewar Baida'u, sai kuma Alamomin wanda suke ba Tabbatattu sune wadanda Imam Mahadi zai iya bayyana ba tare da afkuwarsu ba, a wasu masadir din riwayoyi an cudanya Alamomin Bayyanar Imam Mahadi da Alamomin tashin kiyama. Wasu ba'arin Mufakkirai suna ganin Alamomin Bayyana misalin Sufyani da Dajjal matsayin wani Ramzi. Alal misali Dajjal Ramzi ne na karkata daga barin muslunci, Sufyani kuma Ramzi ne na Karkacewa daga barin al'ummar Musulmi. Masadir din Bayyana wasu hadisai ne cikin litattafan riwayoyi daga bangare biyu Ahlus-sunna da Shi'a. cikin littafi Mai tsarki an ambaci wasu Alamomi game da bayyanar mai ceto, wasu ba'ari cikin wadannan Alamomin sun yi kamanceceniya da Alamomin Bayyanar Imam Mahadi (A.F) sannan wadannan Hadisai an yi tarayya cikinsu a Masadir na Musulmai.

Sanin Mafhumi

Ana kiran abubuwan da faruwarsu ke nuna cewa lokacin bayyanar Imam Mahadi (A.F) ya kusanto da sunan Alamomin Bayyana, an ce ta hanyar faruwar su ne za a banbanci Mahadi (A.F) na gaskiya daga masu da'awar cewa su Mahadi ne bisa karya da kirkire [1]

Zamani da Yanda Za Su Faru

Kan asasin Riwayoyi hakika afkuwar wasu adadi waki'o'u gabanin bayyana zasu kasance damfare da bayyanar wasu adadi daga cikinsu za su yi ta faru tsawon zamanin Gaiba Kubra [2] haka kuma kan asasin riwayoyi da suka zo daga littafin Kamalud-Addini wa-tamam An-i'ima na Saduk Karajin Sama, Fitowar Sufyani, Mikewar Yamani, Kashe Nafsu zakiyya, da kuma Kisfewar Baida duka za su faru gabanin Mikewar Imam Mahadi (A.F) [3] Shaik Mufid ya ambace su da suna Alamomin Mikewar Ka'im [4] kuma ana kiransu Alamomin Mikewar Imam Mahadi (A.F) [5] Wasu ba'arin Alamomin Bayyana sun kama sababin abubuwa da za su faru a kan tsarin dabi'a, amma faruwar wasu ba'arin kamar misalin Karajin Sama faruwarsu kan tsarin dabi'a ba abu ne mai yiwuwa ba, za su faru ne a kan tsarin zirin Mu'ujiza [6]

Tabbatattun Alamomi da Wadanda ba Tabbatattu

Imam Sadiƙ (A.S)

«قَبْلَ قِيَامِ الْقَائِمِ خَمْسُ عَلَامَاتٍ مَحْتُومَاتٍ الْيَمَانِيُّ وَ السُّفْيَانِيُّ وَ الصَّيْحَةُ وَ قَتْلُ النَّفْسِ الزَّكِيَّةِ وَ الْخَسْفُ بِالْبَيْدَاءِ؛

Akwai alamomi guda biyar kafin miƙewar Qaim, dukkansu alamomi ne da babu makawa: Yamani, Sufyani, Saiha, kashe Nafsuz Zakiya, da kisfewar ƙasa ta faɗa cikin rami.

Kulaini, Al-Kafi, bugun shekara ta 1407 h, ƙ, juzu'i 6 shafi na 391, Ibn Qaulawaihi, Kamilul Al-ziyarat, shekarar 1356 h, shamsi, shafi na 106

Alamomin Bayyana sun kasu zuwa kashi biyu tabbatattu da wadanda ba tabbatattu ba [7] Alamomi Tabbatattu wasu abubuwa ne da za su faru da faru ta kasance yankakkiya babu shakka kuma matukar basu faru Hazrat Mahadi (A.F) ba zai bayyana ba. Amma Alamomi wadanda ba tabbatattu ba sune wadanda babu yankewa cikin faruwarsu zai iya yiwuwa Imam Mahadi (A.F) ya bayyana ba tare da faruwarsu ba [8] Kan asasin wata riwaya da Shaik Mufid ya nakalto cikin littafin Al-Irshad ya kebance Fihirisa guda da cikinta ya tattaro Alamomin Bayyana, [9] wasu ba'ari daga ciki sun kasance kamar haka: Kisfewa da Husufi, samun Annobar yawan mace-mace, yawaitar Yake-Yake da Hatsaniya, hudowar Bakaken Tutoci daga Gabas da yawaitar Ruwan sama akai akai babu yankewa [10] wasu ba'ari tare da jingina da jumlar (Allah ne Masani) wacce Shaik Mufid ya kawo a karshen Fihirisarsa [11] sun ce sam babu ma'ana a kawo shakku da kokwanto cikin wadannan Alamomi [12] Kamar yanda ya zo cikin ba'arin wasu Masadir hakika Alamomi wand aba Tabbatattu ba sune kamar haka:

  • afkuwar Sabani tsakankanin Banu Abbas kan shugabancin Duniya da Gushewar Hukumarsu.
  • kashe Sarkin Daular Abbasiyawa na karshe wanda ake kira da Abdullah.
  • Kisfewar Rana a tsakiyar Watan Ramadan sabanin abinda aka saba.
  • Kisfewar Wata a farko ko karshen watan Ramadan, sabanin abinda aka saba gani.
  • Fitowar wani Mutum daga Garin Kazwin wanda sunansa iri daya da sunan daya daga cikin Annabawa zai yawaita zaluntar Mutane.
  • wani sashi daga Masallacin Damashk zai nutse cikin Kasa.
  • wani Kauye daga Kauyukan Sham wana ake kira da suna Kharashna zai nutse cikin Kasa.
  • Rugujewar garin Basara.
  • Kashe wani Mutum da ya yiwa Sufyani tawaye za a kashe shi ne a bayan garin Kufa tare da mutum 7 daga Mabiyansa.
  • Rugujewar Katangar Masallacin Kufa
  • Daga Bakaken Tutoci a wani yanki na garin Kurasan, wannan Runduna masu Bakaken Tutoci za su yaki tare da Rundunar sufyani a wani yanki kusa da garin Shiraz wannan yaki shine farkon shan kasa da sufyani zai fara gani, wannan Bakaken Tutoci za cu cigaba da fifilawa a sama har lokacin da za su isa zuwa Baitul Mukaddas
  • Hudowar Tauraruwa Mai kyalkyala a fuskanin Gabas kai kace Wata mai haskaka, sai kuma geffanta biyu sun lankwashe kai kace zasu hade da juna .
  • Bayyanar ja a sararin sama wanda ke yaduwa a sararin samaniya.
  • yaduwar ruguje mai yawa da Irak da Sham
  • rikici tsakanin gungun Jama'a uku As'hab, Ablak, da kuma Sufyani
  • bayyanar Motsin Tutocin Kaisu a Misra.
  • Fifilawar Bakaken Tutoci daga bangaren Gabashi zuwa ga Haira.
  • Borin Ruwan Kogin Furat har ya kwarara zuwa ga Lungunan Kufa.
  • Fitowar Mutane Goma sha biyu daga tsatson Abu Talib baki dayansu zasu kasance suna kiran mutane zuwa ga Kawukansu.
  • Kone wani Dogon Mutum daga `Yan Shi'ar Banu Abbasi tsakankanin garuruwan Jaula wanda yake akwai nisan Farsaki 7 tsakaninsa da garin Khanikaini.
  • Tasowar Bakar Iska a Bagdad a rana ta farko.
  • karancin abinci da Ganyayyaki da afkuwar fari da rashin Ruwan Sama
  • sabani da rigingimu tsakanin Larabawa da Ajama wanda zai kai ga zubar jini tsakaninsu.
  • Rugurgujewar Garin Rayyu.
  • jirkita Halittar wasu gungun `yan Bidi'a zuwa Birrai da Aladu.
  • Yaki tsakanin Matasan Azebejaniyawa da Armeniyawa.
  • bayyana wani sauti a baki dayan duniya wanda ba a sa ba jin irinsa ba, kowa zai ji shi da yarensa da yake Magana da shi.
  • cikin kowanne Karaji biyar da zasu bayyana kadai na hudu ne tabbatacciyar Alama wanda zai faru a Watan Ramadan, Karaji na farko zai kasance a Watan Rajab zai kasance da wannan yanayi kamar haka
«ألا لعنة الله علی القوم الظالمین»؛

Ku sani lallai Tsinuwar Allah ta tabbata kan Azzalumai.

  • karaji na biyu zai kasance kamar haka:
«یا معاشرالمؤمنین أزفة الآزفة؛

Ya ku Taron Muminai Kiyama (bayyana) ta kusanto

  • Karaji na uku: (zai zo da gangar jiki a bayyane)
«ألا إن الله بعث مهدی آل محمد للقضاء علی‌الظالمین»؛

Ku sani lallai Allah ya turo Mahadi Alu Muhammad (S.A.W) domin kawo karshen Azzalumai.

  • Karaji na hudu wanda zai afku a Watan Ramadan akwai zaton zai afku 23 ga Ramadan daidai lokacin hudar Alfijir kuma Jibrilu zai yi Shi, zai bada shaida kan kariya ga Ahlil-Baiti.
  • Karaji na biyar zai afku daga Shaidan akwai tsammanin zai faru a 23 ga Watan Ramadan tare da goyan bayan Sufyani daidai lokacin faduwar rana, zai tayar da Matattu su fito daga cikin Kaburbura su dawo duniya su ziyarci junansu. [13]

Cudanyar Alamomin Bayyanar Imam (A.F) da na Tashin Kiyama

Cikin ba'arin riwayoyi hakika Alamomin Bayyana sun cudanya da Alamomin Tashin Kiyama, alal misali hudowar Rana daga Yamma wanda ya zo a riwaya a matsayin Alamar Tashin Kiyama [14] haka ya zo a matsayin daya daga cikin Alamomin Bayyanar Imam (A.F) [15] Haka wasu ba'arin Alamomin Bayyana misalin Fitowar Sufyani sun kasance tare da Alamomin Tashin Kiyama misalin Dabbar karkashin Kasa, fitowar Isa, Mikewar Imam Zaman (A.F) hudowar Rana daga Yamma duka sun zo a riwayoyi a matsayin Alamomin tashin Kiyama [16] an ce sakamakon Masadir din addini sun kidaya wasu ba'arin Alamamin Bayyana a Matsayin Alamomi na Tashin Kiyama, [17] hakika mikewar Imam Mahadi (A.S) a Alama ce ta Tashin Kiyama [18]

Shin Alamomin Zuhuri suna Samuwa ta Hakika ko dai wani Samfuri ne

Sayyid Muhammad Sadar wanda ya rayu tsakanin shekaru1322-177 hijiri shamsi daya daga cikin Maraji'an Taklidi a karni Goma sha hudu a cikin mai suna Tarikh Algaiba Alkubra ya bayyana cewa wasu ba'arin Alamomin Bayyana misalign Sufyani da Dajjal Ramzi kawai da Misali. Hakika Dajjali Samfuri ne na karkacewa daga barin Muslunci da al'ummar Musulmi [19] cikin amsar da Malamai suka bashi sun ce ajiye wasu ba'arin Alamomin Bayyana a matsayin samfuri abu ne da sabawa zahirin hadisai, kuma zai zama sababi da zari'a ta rushewar aikin Alamomin Bayyana [20] saboda aikinsu shine taimakawa wajen gano Mahadin Gaskiya da banbance shi daga na Jabu masu da'awar bisa karya [21]

Alamomin Bayyana Mai Tseratarwa a cikin Sauran Addinai

A cikin Addinin Yahudanci da Kiristanci anyi bayani dangane Alamomin bayyanar Mai tseratarwa, wasu daga cikinsu sun yi tarayya da Alamomin Bayyana da suka zo cikin Hadisai, Yahudawa sun yi Imani da cewa Yaduwar yake-yake da rikice-rikice Alama ce ta bayyanar Mashihu [22] Haka a wurin Kiristoci kishiya Almasihu ko Dajjal wani mutum ne ko wasu mutane da suke Inkari ko karyata kasancewar Isa a matsayin Almasihu [23] a Karshen duniya Dajjal zai Yunkura ya tashi a lokacin da Almasihu ya bayyana zai yaki Dajjal y agama da shi [24] da kuma yaduwar barna da yake-yake da rikice-rikice, girgizar kasa, Fari, da kuma bayyanar wasu Alamomi a jikin Rana da wata da Taurari duka abubuwa ne da za su faru gabanin zuwan Isa Almasihu bisa Imanin Kiristoci [25]

Dabbaka Alamomin Bayyana a kan wasu Mutane Banda Imam Zaman

A Daurori daban-daban wasu sun yi kokari Dabbaka Alamomin Bayyana kan wasu abubuwa da wasu mutane, wannan dabbakawa ta faru daga fuskanin wasu Hukumomi bisa kudurori mabambanta, alal misali hudowar Rana daga Yammaci kan kafa Daular Fatimiyya a Misra, da dabbaka Nafsuz Zakiyya kan Muhammad Bn Abdullah Bn Hassan Musanna [26]

Sanin Littafi

Tushen Alamomi Bayyana Hadisai ne da aka nakalto su daga Litattafan Shi'a da Ahlus-Sunna, na'am Malamai sun yi shakku cikin ingancin ba'arin wasunsu, sun ce hakika ba'arin wasu riwayoyi cikinsu basu gangaro daga Ma'asumi ba [27] a cikin littafin Algaibatu Nu'umani [28] Kamalud-Addini wa Tamam An-Ni'ima [29] Algaiba Shaik Tusi [30] da Kitabul Al-Irshad Shaik Mufid [31]sun kebantu da wasu ba'arin riwayoyin Alamomin Bayyana, a cikin Masadirn din Ahlus-Sunna akwai wani sashe da suka sa masa suna (Malahim wa-Fitan) sun Magana a kan wannan mas'ala, haka Ibn Hammad ya rubuta rubuta littafi da wannan suna Malahim wa-Fitan [32] Dangane da rubuce-rubuce da wallafe-wallafe da aka yi kan mas'alar Alamomin bayyanar Mahadi (A.F) hakika wasu ba'arinsu ba komai bane sai tattaro hadisai wasu kuma da Uslubin faifaice bayani, daga jumlarsu akwai:

  • Dirasatu fi Alamat Azzuhur rubutun Jafar Murtada Amili cikin tsarin faifaice bayani da warwara da suka tarea zurfafa bincike [33]
  • Nawa'ib Adduhur fi Ala'im Azzuhur rubutun Muhammad Hassan Mir Jahani an buga shi a shekara 1383.
  • Mi'atani wa-Kamsuna Alamat rubutun Muhammad Ali Tabataba'i cikin wannan littafi ya kawo Alamomi har guda 250, [34]
  • Ta'ammuli dar Nashanahaye Hatmi Zuhur rubutun Nasrullahi Ayati kan Alamomi biyar wanda suke tabbatattu wanda cibiyar Ayande Roshan a shekara 1390 shamsi ta buga shi ta yada [35]

Haka kuma littafin Ikdur Addurar fi Akbaril Almuntazar (A.F), Urful Warid fi Akbaril Almahdi Alaihi Salam, da kuma Alburhanil fi Alamat Mahdi Akiril Azzaman ya na daga talifin Ahlus-Sunna [36]

Bayanin kula

  1. Ayati, Ta'ammuli dar Nashanahaye Zuhur Hatmi,1390, shafi na 15
  2. Salimian, Farhang Nameh Mahdawiyat, Mujalladi na 1, shafi na 445.
  3. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi 650, h7.
  4. Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 368.
  5. Salimian, Farhang Nameh Mahdwiyat, 2008, juzu'i na 1, shafi na 445 (labarai na ƙafa).
  6. Duba Sadr, Tarikh al-Ghaibah Al-Kubra, 1412 AH, shafi na 480.
  7. Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 370.
  8. Salimian, Farhang Nameh Mahdawiyat, 2008, shafi na 446.
  9. Sheikh Sadouq, Kamaluddin, juzu'i na 2, shafi na 650.
  10. Duba Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 368-369.
  11. Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 370.
  12. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 425.
  13. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 429; Sheikh Sadouq, Kamal al-Din, 1395 AH, shafi na 650; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 53, shafi na 182; Tusi, Al-Ghaibah, 1425 AH, shafi na 445.
  14. Siyuti, Addurul Al-Manthor, 1404 AH, shafi na 357; Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 371.
  15. Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 368; Esmaili, "Barasi Nashanahaye Zuhur bayyanar", shafi na 224.
  16. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 436.
  17. Misali duba: Tusi, Al-Ghaibah, 1411H, shafi na 436.
  18. Salimian, Farhang Nameh Mahdawiyat, 2008, shafi na 448.
  19. Sadr, Tarikh Al-Ghaibah Al-Kubra, 1412 AH, shafi na 484.
  20. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2013, juzu'i na 7, shafi na 460.
  21. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 414-415.
  22. Rasulzadeh, “Akiru Zaman wa Hayat Ukrawi dar Yahydiyyat wa Masihiyyat”, shafi na 76. Julius Greenstone ya nakalto, Intizar Masiha dar Ayineh Yahudiyyat, shafi na 62 da Talmud na Babila, Shabbat, 118b.
  23. Nameh Awwal Yohanna Rasul 2:18-20.
  24. Tassalunikawa, 2:8, beh nakali az Panah wa Khawas , “Barasi Fishgyahaye ahdaini darbaraye Kushtare Jam'i Pish aza Zuhur”, shafi na 331.
  25. Luka, 21:5-29.
  26. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 452.
  27. Sadeghi, "Ta'ammuli dar Riwayathaye Ala'imi Zuhur", shafi na 322-323.
  28. Nomani, Al-Ghaibah, 1397 AH, shafi na 247-283.
  29. Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 649-656.
  30. Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 433 zuwa gaba.
  31. Mofid, Al-Ershad, 1413 AH, Juzu'i na 2, shafi na 368-378.
  32. Sadeghi, "Ta'ammuli dar Riwayathaye ala'imi Zuhur", shafi na 322.
  33. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 422.
  34. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 422
  35. <a class="external text" href="http://www.m-mahdi.com/persian/books-252#3">«تأملی در نشانه‌های حتمی ظهور»</a>
  36. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Imam Mahdi, 2014, juzu'i na 7, shafi na 422

Nassoshi

  • Injil tarjame Hezar No..
  • Ismaili, Ismail, "Barasi Nashanahaye Zuhur", Mujallar Hozah bi-bi-biyu, lamba 70, kaka 1374.
  • Ayiti, Nusratullah, Ta'ammuli dar Nashanahaye Zuhur Hatmi, Qum, Aindeh Roshan, 1390.
  • براری، محمد، «منبع‌شناسی روایات علائم ظهور در کتاب الغیبه شیخ طوسی»،Mahdavi yayi bincike, lamba 17, bazara 2015
  • Din Panah wa Khawas, Hassan da Amir,بررسی پیش‌گویی‌های عهدین درباره کشتارهای جمعی پیش از ظهور»،Mashrak Mau'ud, Na 41, 1396
  • Rasul Abbas Zadeh «آخرالزمان و حيات اخروی در یهودیت و مسیحیت» Marifat Adyan shomare 2 bahar 1389 hijiri shamsi
  • Salimian, Khodamorad, farhang Nameh Mahdawiyat, Qum, Mahdi Mououd Cultural Foundation, 1388.
  • Siyuti, Abdur Rahman, Al-Dur Al-Manthur Fi al-Tafseer Balmathur, Kum, Ayatullah Murashi Najafi Publications, bugun farko, 1404H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tamma Al-Naimah, Tehran, Ali Akbar Ghafari, Darul Kitab al-Islamiya, 1395H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hasan, Al-Ghaibah, Ebadullah Tehrani da Ali Ahmad Naseh, suka buga, Qum, Darul Maarif al-Islamiya, 1411H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Ershad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, edited by Al-Al-Bayt Institute, Qum, Sheikh Mofid Congress, 1413 AH.
  • Sadiki Mustapa «تأملی در روایت‌های علائم ظهور»، شماره ۸ و ۹، تابستان و پاییز ۱۳۸۲ش.
  • Sadr, Seyyed Muhammad, Tarikh al-Ghaibah Al-Kubra, Beirut, Dar al-Taraif don bugawa, 1412H.
  • Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam Al-Naimah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, 1395 H.
  • Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah,: Ebadullah Tehrani da Ali Ahmad Naseh, Qum, Darul Maarif al-Islamiyya, 1425H.
  • Nu'mani, Muhammad bn Ibrahim, Al-Ghaibah llan-No'mani, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Gidan Daba'ar Sadouq, 1397H.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad,Daneshnameh Imam Mahdi (AS) bisa ga Alqur'ani (Juzu'i na 7), Hadisi da Tarihi, Qum, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Darul-Hadith, 2013.