Hubbul Waɗani Minal Iman
![]() Zanen rubutun hadisin Hubbul Waɗani da salon rubutun Kufi Sultan | |
Ya Fito Daga | Ana danganta shi ga Annabi (S.A.W) |
---|---|
Ingancin Isnadi | Mursal |
Madogaran Shi'a | Tafsirul Raudul Jinan, A'ayanush Shi'a |
Madogaran Ahlus-sunna | Tafsirul Ibn Arabi |
Mai ƙarfafawa Na Riwaya | "Ummiratul Buldan bihubbil Watan" |
Hadis Silsilatuz Zahab • Hadis Saƙlaini • Maƙbulatu Umar Bin Hanzala • Hadis Ƙurbu Nawafil • Hadis Mi'iraj • Hadis Wilaya • Hadis Wisaya • Hadis Junud Aƙli Wa Jahal • Hadis Shajara |
Hubbul Waɗani Minal Iman, (Larabci: حُبّ الوطن من الإيمان) wannan jumla ce fitacciya wadda ake jingina ta ga Annabi (S.A.W), wasu masu bincike misalin Shaik Makarim Shirazi cewa wannan jumla babu ita a cikin litattafan asali na hadisi, kai wasu ma suna ganin ƙirƙirarta aka yi. Abul Futuh Arrazi ɗaya daga cikin malaman tafsiri a ƙarni na 6 a littafinshi mai suna Raudul Jinan ya ambaci wannan jumla ta san ƙasa imani ne, kuma ya jingina ta ga Annabi (S.A.W) ya ce ya faɗi wannan jumla ne a ya yin da yake barin garin Makka yana hijira zuwa Madina, abin da yake nufi da ƙasa ita ce Makka.
Wasu masu bincike ba su yarda da wannan alaƙa ba tsakanin ƙasa wadda ake kira ƙasa a yau da imani a cikin wannan jumla ta (san ƙasa ɓarayi ne na imani), sai suka yi ta'awilin ma'anar ƙasa a wannan jumla. Wasu suka ce ƙasa a wannan jumla tana nufin ƙasar Muslunci babba, wasu kuma suka ce ita ce aljanna, su kuma masana na muulunci duba da cigaba na ma'anar ƙasa, sai suka ce ita ce duk wata ƙasa da mutum zai sami kwanciyar hankali, kuma ƙasa ta gaskiya ita ce ƙasa maɗaukakiya da kusanci da Allah.
Ingancin Wannan Hadisi
Jumlar San ƙasa wani ɓangare ne na imani ta shahara a matsayin wani shahararren hadisi,[1] kuma an jingina ta ga Annabi Muhammad (S.A.W).[2] Wasu masu bincike irin su Shaikh Makarim Shirazi sun yi imanin cewa wannan jumla ba ta zo a cikin manyan madogaran hadisin Shi'a na asali ba.[3] Wasu kuma sun yi Imani da cewa wannan jumlar ƙirƙiratta aka yi,[4] kuma wannan jumla ta zo a cikin tarjama ta Arabiya ta littafin (Marziba Name) wanda ya rubuta littafin shi ne Marziban Bun Rastam ya rasu a shekara ta 302 hijjira,[5] bisa ra'ayin mai bincike nan ɗan shi'a Murtada Rahimi yana ganin cewa, wannan littafin na Marziban Name shi ne mafi daɗewar littafi da ya kawo wannan jumla a matsayin hadisi na Annabi (S.A.W).[6]
Jumlar son ƙasa yana daga cikin imani ta zo a cikin wasu litattafan Shi'a a matsayin hadisin da aka ruwaito batare da danganashi zuwa ga manzo Allah ba, Abul Futuh Arrazi, ɗaya daga cikin malaman tafsirin a karni na shida a cikin tafsiri na Raudul Jinan ya ambaci wannan jumla cikin hadisan Annabi (S.A.W) a lokacin da yake barin Makka a lokacin da yake hijira zuwa Madina, kuma kamar yadda wannan Hadisi ya nuna, abin da Manzo Allah (S.A.W) yake nufi da ƙasa ita ce Makka.[7] Kazalika wannan jumla ta zo a cikin littafin Safinatul Bihar shi kuma ya samo ta daga cikin muƙaddimar littafin Amalul Amil na Shaik Hurul Amili.[8] cikin waɗanda suke ganin wannan jumlar hadisi ce da aka rawaito daga Annabi akwia Ibn Arabi a cikin tafsirinshi da Sayyid Muhsin Amin cikin littafinshi A'ayanush Shi'a, da Mirza Habibullah Khuyi a cikin sharhin Nahjul Balaga.[9] amma dukkan su ba su kawo sanadin hadisin ba.
An faɗi cewa da yawa daga cikin malaman Ahlus-sunna suna ganinsa mastayin hadisi wanda aka ƙirƙira, kuma sun faɗi matsaloli da yawa a kan shi.[10]
Matsala Kan Alaƙa Tsakanin Imani Da Son Ƙasa
Wasu masu bincike sun tattauna cuɗeɗeniya tsakanin son ƙasa da imani, kuma sun yi tawilin kalamar ƙasa, idan aka ce ita wannan jumla ba zai yi wu a tafi kan zahirinta ba, saboda kafiri da munafuki duk suna son ƙasarsu, alhalin su ba muminai ba ne, saboda haka ba yadda za a yi son ƙasarsu ya zama alamar imaninsu, kazalika muminin da aka haifa kuma ya girma a can ƙasar kafirai kuma yana son ƙasarshi, to zai zamo alaƙanta wannan son na shi da imanishi bai dace da hankali ba,[11] Sayyid Murtada Amili,[12] da Sayyid Murtada Al-askari duk suna daga cikin malaman Shi'a na hadisi da tarihi suna ganin cewa son ƙasa a wannan hadisi so ne wanda yake haɗe da hadafin muslunci maɗaukaki, kuma abin da ake nufi da ƙasa ita ce ƙasar muslunci mai girma.[13]
Tawilin Ma'anar Ƙasa Daga Malaman Irfani
Wasu masu bincike suna ganin ma'anar ƙasa a wannan hadisin yana nufin aljanna, bisa wannan hadisin mumini zai zamo baƙo a wannan duniya, kuma zai zamo yana kwaɗayin komawa ƙasarshi ta hanyar ayyukan alheri,[14] amma malamn Irfani sun faɗaɗa ma'anar ƙasa, inda suka ce ƙasa tana nufin gurin da mutum zai sami nutsuwa, [15] bisa wannan ne suke ganin ƙasa ta gaskiya ita ce samin kusanci ga Allah,[16] kuma suna ganin dalilin da yasa wasu ke fassara ƙasa a wannan hadisi da duniya, ya faru sakamakon son duniya.[17]
Son Ƙasa A Waƙar Larabawa
Wannan jumla ta son ƙasa yanki ne na imani, ta yaɗu da yawa a cikin waƙar larabawa, daga cikin akwai waƙar da Amin Aljundi ya rera;
Tarjama: Lallai soyayyar garin Himsi ya sa ciwo, daga cikin imani akwai son ƙasa.[18]
Fatahullahi Bayiluti Al-halabi ya rera:
Tarjama: Ka gaya wanda ya yi munafunci cikin son ta, htabbas daga cikin imani akwai son ƙasa[19]
Ga kuma abin da Baha'u Din Arrauwas ya rera:
Tarjama: Gurin zamana shi ne gurin zamanku duk inda ba gurin zamanku bane,to nima bazan zauna ba. Gurin da yake baku kariya shi ne gurin da kuke rayuwa (ƙasarku) kuma shi son ƙasa imani ne.[20]
Bayanin kula
- ↑ Makarim al -shirazizi, Nafat al -Wilayat, Vold. 2, shafi 145.
- ↑ Abu Al-Futuh Al-Razi, Rawd Al-jinan, juzu'i na 17, shafi na 299
- ↑ Makarm Al -shirrazi, Payame Amir al -Mu'minin, kundi 15, shafi na 159; Shahidi, Sharhu Masnavi, 1994, kundi 3, shafi. 512; Rahim, "barsi Hadisin Hubbu al -watan ,minal Al -ayman", shafi 219.
- ↑ Makarem Al -shirrazi, Payame Amir al -Mu'minin, juz, 15,shafi 509
- ↑ Marzban Bin Rostam, Marzban Nameh, shafi na 178.
- ↑ Rahim, "Barsi Hadis Hubbul al -watan minal al -iyman", p. 220.
- ↑ Abul Al-Touh al-Razi, Rouz al-jinan, juzu'i na 17, shafi na 299.
- ↑ Al-Qami, Safina Al-Bihar, juzu'i na 8, shafi na 524.
- ↑ Ibn al-Arabi, Tafsirul Ibn al-Arabi, juzu'i na 2, shafi na 329; Al-Amin, Ayan Shi'a, Juzu'i na 1, shafi na 296; Al-Hashemi Al-Khoei, Minhaj al-Baraa', juzu'i na 21, shafi na 394.
- ↑ Rahim, "Barsi Hadis Hubbul Al -watan minal Al -iyman", PP. 221 da 231.
- ↑ Rahim, "Barsi Hadis Hubbul Al -watan minal Al -iyman", PP. 222.
- ↑ Al -amili, Al -sahih min siratin Annabi,(S.A.W), Juz 4, shafi. 153-154.
- ↑ aL-askari, juz 3 shafiu na 242 an ciro daga : rahimi(Hubbul watan minal iman
- ↑ Rahimi, "Barrasi Hadith hubbul watan minal iman," shafi na 224-225.
- ↑ Al-Qushayri, Al-arba'a rasa'il fit tasawwufi, shafi na 59
- ↑ Bali,Sharhu Shathiyyat, 622
- ↑ Al -Khwarzm, Yanbu'ul al -sarr, kundi 2, p. 95
- ↑ [ https://poetry.dctabudhabi.ae/#/poems/78140-%D8%A5%D8%B5%D8%A8%D8%A7%D8%AD-%D8%A3%D9%85-%D8%A8%D8%B1%D9%8A%D9%82-%D8%A3%D9%88%D9%85%D8%B6%D8%A7%7C موقع الموسوعة الشعرية.]
- ↑ موقع الموسوعة الشعرية.
- ↑ [ https://poetry.dctabudhabi.ae/#/poems/60660-%D8%A3%D9%8A-%D9%82%D9%84%D8%A8-%D9%87%D8%A7%D9%85-%D9%81%D9%8A%D9%83%D9%85-%D9%88%D8%B3%D9%83%D9%86%7Cموقع الموسوعة الشعرية.]
Nassoshi
- Ibn Al -Arabi, Moi Al -Din, Tafsirul Ibn al -Arabi, Lebanon, Dar al -al Al -al -umayyah, 1422 ah / 2001.
- Abu Kamarud, Hussein bn ali, ruz al -janan, Mohammad Jafar Yahah al
- Al -amin, Al -sayyaid Mohsen, Ayan Al -shia, Search: Hassan Al-Bamin, Beirut, Dar Al -taarif, DT.
- Baghishan, roozbaan, Sharhu Shathiyyat, Gyara: Henry Kogban, yaren Iran da Al'adu, Rabi'i 1995.
- Al -khavarmzm, Kamaluddin Hussein, Yanbuul al -asarar, Tehran, hada gwiwar al'adu da ayyuka, 2005.
- Rahim, Morteza, "Barrasi Hadis hubbul Al -watan Min AL -iyman", a cikin mujallar: Hadisi
- Sheikh al -shisusharaq, Ras'il Sheikh al -shisusharaq, Tehran, Cibiyar Waldosim, T. 2, 1996.
- Al -amili Ja'afar Maroza, Al -sahih Min siratin Al -Nabi Al -azam, Beirut, Al -alu, Al -suli Al -slai
- Al -QQASHIRI, Abu Al -kahsim Abdul Karim, Abu Arba'a Rasa'il fi Al -tasouf, Baghdad, Al -al -iraqi, 2010 ah.
- Al -qami, Al -bihar Abbas, Safih Al -Bihar da Al -Hakim Vali suna jira, Kin, Dar Al-Al -sawa Lansar, 1414 ah.
- Makarem Al -shirazi, Nasser, Payame Amir Al -Mu'minin, Tehran, Dar Al -Mutab al -Islami, 2007.
- Makarem al -shirazi, Nasser, Al -Wali, Qom, Al -Mam Ali Bin Abi Talib makaranta, T. 2, 1426 AH.
- Marzban Bin Rostam, Marzban Nama, an fassara ta: Ahmad Ibn Muhammad Ibabhah, Beirut, Al -maqshhar Al -âratihar, 1997.
- Nahj al -balagha, gyara: Salifie Saleh, Qom, Dar al -hajji Cibiyar, 1414 ah.
- Al -Hashimi Al -Khawa'i, Habibullah, Manhaj al -bara'a cikin sharhin Nahj al -baleji, Tehran, makaranta na al -ismalili, 4, 1400.