Wikishia
Wikishia wata Mausu'a ilimiya (Wasika ce da take kunshe da ilimi) da take yanar gizo da take dauke da bayanai game da neman sanin Shi'a da sauran Mazhabobin Mabiya Ahlil-baiti (A.S) wannan ilimumuka sun tattaro Akidu, Daidaikun mutane, da misalin ilimun Kalam Tauhidi, Fikihu da Usulul Fikihu, litattafai, wurare, abubuwan da suka faru, bukukuwan addini da Ibada, kungiyoyin Shi'a tarihin shi'anci da dukkanin wani mafhumi da yake da dangantaka da Ahlil-baiti da Mabiyan su, duk kalmomi da sunaye da suka kasance na larura yana zuwa da bayanin su.
A cikin Wiki ShiA ana kawo Tahlili da mahangar mutum a kankin kansa, sannan kuma ana taka tsantsan cikin Mahangar da bata tabbata ba, hukunci kan sabani na ilimi da tarihi yana kan wuyan Masu karatu, Wiki ShiA a wannan mahallin bata da bangare, bisa lura da sabanin Mazhaba, Maginar Marubuta hakika Wiki ShiA suna karbar daga shi'a da Ahlus-sunna, Wiki ShiA suna jingine da Mu'assasar Majma'u Jahani Ahlil-baiti, wannan Wasikar bayanan ilimi zuwa yanzu tana aiki da yaruka daidai har guda goma sha biyar, a iya kadai yaran Farisanci an shigar da Makala 7193
Manufa da Hadafin samar da ita
Cikin wasikun bayanai akwai bayanai masu tarin yawa dangane da muslunci da shi'anci, sai dai cewa Marubutan cikin Wasikun tattara bayanai ko dai basu da ingantaccen sani da ilimi ko kuma dai basu yi imani da muslunci da shi'anci ba, zaka samu cikin rubuce-rubucen su kan muslunci da shi'anci akwai tarin kura-kurai, sakamakon fadaka da lura da wannan matsala mai girma da take cikin dandamalin intanet yanar gizo, sai yan shi'a suka mike tsaye don taimakawa masu bincike dama yan shi'ar da samun kaiwa ga akidun shi'a na asali da muslunci, hakika cibiyar yada al'adu Majma'u Jahani Ahlil-baiti sun taka rawa wajen samar da Wiki ShiA da niyyar zama garkuwa da zata bada kariya ga Maktaba din Ahlil-baiti (A.S).
Takaitaccen tarihi
A daya ga watan Kordad hijira Shamsiyya, zama na farko na samu hadin kai daga Marubutan Wiki ShiA ya kasance, sannan bayan wasu adadin tarurruka na ilimi, har ila yau 28 ga watan Kordar, an yada makala ta farko a cikin Wiki ShiA , sannan a watan Tir shekara 1392 shamsiyya sayit din Wiki ShiA ya sauka ga dukkanin mutane kowa na iya bude shi ya gani ya yi karatu. Wiki ShiA a daya ga watan Tir a lokacin taron Jikan Annabi (S.A.W) da ya kasance a birnin Taharan karkashin Jagorancin Shugaban Kasa Hassan Ruhani an shelanta shi sayit a hukumance. Abubuwan da ya kebantu da su Cikin ba'arin abubuwan da Wiki ShiA ya kebantu da su akwai: Fadaduwar abin da ta kunsa Hakika sayit din Wiki ShiA ya kunshi abubuwa kamar haka: Akidu, daidaikun mutane, ilimummuka, misalin Fikhu, Usululul fikhi, litattafai, wuraren tarihi, abubuwan da suka faru a tarihi, bukukuwan Addini, kungiyoyin da suke imani da Ahlil-baiti, tarihin shi'anci, dama duk wani maudu'i da yake dangantaka da Ahlil-baiti da Mabiyansu, fahimtocin muslunci da suka kasance dukkanin musulmi sunyi imani da su ko kuma wanda suke da alaka da tarihin muslunci suma Wiki ShiA bai manta da su ba an sajjala su ciki. Fahimtoci da suke da dangantaka da sauran kungiyoyin musulmai a lokacin da Wiki ShiA ya bayyana su zai zamana ko dai suna da alaka da Ahlil-baiti ko kuma sun kasance an yawaita amfani da su a ciki. Sa idanu kan abin da Makala ta kunsa. Akwai sa idanu kan abin da ake shigarwa cikin wannan Sayit, domin wannan dandalin wani cibiya ce mai inganci wurin bayanin shi'a. Wasikar bayanai ta Wiki ShiA a zuwa yanzu tana ayyukanta ne a iyakance, amma da yardar Allah nan gaba za ta kasance ta fadadda domin dukkanin yan shi'a da suke da sha'awa da suke da tanadi a basu damar bada gudummawa domin kammaluwarta ilimin makarantar Ahli-baiti (A.S) ya samu damar yaduwa, shiga wannan Wasikar bayanai zai kasance ne da yardar shugabannin ta, wannan bada dama ta shiga Wiki ShiA domin sanya Makala da rubuce rubuce zai kara kimar Makalolin. Majalisar shawara kan tsare-tsare. Majalisar shawara wata gamayya ce ta shugabannin yaruka, da shugabannin ilimi da masana na Wiki ShiA, wannan Majalisa nauyin kula da tsare-tsare a bangarori daban daban na wuyansu. Siyasar rashin daukar bangare Dole ya zamana an kiyaye Siyasar rashin bangaranci a cikin bahasosin tunani cikin Mazhabar Shi'a, sai dai cewa a bayyane yake cewa Wiki ShiA wani sayit ne na yada Maktabar Ahlil-baiti da makaloli tare da hadafin bada kariya ne za a yi rubuce rubuce. Makalolin Wiki ShiA,ba makaloli ne na ilimi da bincike ba, da ma'anar cewa su ba irin rubutu ne a tahkiki na farko farko wanda ba a yada shi ba wanda ba zasu amfanar ba cikin warware matsalolin ilimi, shi asasin Wiki ShiA shi ne nuna bayanai kan asasin tushen da ake da shi , saboda haka bai kamata Marubucin mu ya sanya mahangar tunanin sa cikin abin da zai yada a wannan Sayit ba. Yanke hukunci kan sabani na ilimi ko na tarihi wannan duka suna hannun Masu karatu da bibiyar mu, Wiki ShiA a wannan wuri bata da bangare, bisa lura da la'akari da sabani na Mazhaba, ginin Marubutanmu za su iya kawo abubuwa na fari da aka yarda da su daga manyan kungiyoyi biyu Shi'a da Ahlus-Sunna.
Wasu abubuwa da Wiki ShiA ta kebantu da su
Dama a kowanne lokaci kan warware abubuwan da aka shigo da su. Sabuntawa da kara wasu sabbin bayanai.
- Samar da shafin takaitaccen tarihin Makala. Cikin shafin takaitaccen tarihi duk wani canji da ya kasance a makala zai zama za a ganshi, masu bibiyar mu da Marubutan mu za su iya tsinkaya kan canji da aka samu.
Shafin canje canje na karshe, wannan shafi zai mika karshen canje canje da aka samar cikin dukkanin Wiki zuwa ga masu amfani da wannan Sayit.
- Samun damar kaiwa ga maudu'ai da canje-canjen da suka gabata.
Alakar kofofin shiga tsakanin wannan da wancan,, ta haka Mai karanta makala domin fahimtar kowacce jumla da ta zo cikin matani ba tare da shan wahala bincike ba, kai tsaye zai bude shafin da yake da alaka da wannan abin da yake son fahimta sai ya karanta, wannan hususiya zata taimakawa Mai bibiyarmu ya samu damar karanta kowacce mashiga, cikin sauki dukkanin mafhuman da aka kawo a wannan mashiga zai same su yan kuma kai ga kammalallun bayanai game da maudu'in da yake karantawa. Dangantakar kowacce makala tare da wannan maudu'i cikin wani yaren daban na Wiki. Amfani da raddeha a karshen makala raddeha wani take ne game gari da ake kirga taken makala a kasan sa, Raddeha ba wani abu bane face Fihirisar Wiki.
- Navigations template wani abin kwaikwayo ne da yake tattaro makala ya ajiyeta cikin wani akwatu da yake a Ufuki a kasan Makalar, Navigation wani lokaci yana kasance da surar akwatin Amudi a saman makaloli da yake amfani, dangantaka tsakanin unwanai an ajiye shi cikin wannan jadawali da surar bijira, ma'ana baki dayan unwanai suna kasancewa cikin jelar wani unwani guda da yake tattaro su.
- Akwatun bayanai (Inforbox) wata akwatu ce da take saman makala da take tattare bayanai masu muhimmanci a takaice, tare da leka wanna akwatu ba tare da ka karanta makala ba zaka iya tsinkaya kan bayanai na asali a cikin matanin Makalar .
Shafin bahasi. Kowanne shafi da makala a Wiki suna da shafi bahasi guda daya, amasu amfani da shafin bahasi za su iya bayyanarwa da Marubuci ko mai duba Makala ra'ayin su dangane da makalar, shafin bahasi a hakika wani mahalli ne na tattaunawar Ma'abota ra'ayi a masu alaka da maudu'in makala, hakan zai taimaka kan makalar da aka wallafa. Zuwa yanzu Sayit din Wiki ShiA yana da yaruka 22.