Jump to content

Utlubul Ilma Minal Mahdi Ilal Lahdi

Daga wikishia
Allon rubutun "Utlubul Ilma minal mahdi ilal lahdi, cikin salon rubutun sulusi aikin Majiz Zuhdi shekarar 1994 miladi

Utlubul Ilma Minal Mahdi Ilal Lahdi (Larabci: اُطلُبوا العِلمَ مِنَ المَهدِ إلَی اللَّحْدِ ) Ma'ana ku nemi ilimi tun daga gadon haihuwa har zuwa kabari.

Wata jamla ce data shahara kuma ana jingina ta ga Annabi (S.A.W), amma tare da hakan wannan jumla ba ta zo a cikin littafai na asali ba a gun shi'a da Ahlus-Sunna, Sai dai kuma ma'anar wannan jumla ta inganta, kuma akwai wasu riwayoyi da suka zo da wannan ma'ana.

Shaharar kalmar Larabcin nan "Utlubul Ilma Minal Mahdi Ilal Lahdi" (Ma’ana: Ka nemi ilimi tun daga gadon haihuwa har zuwa kabari) ya sanya ake fassara ta cikin harshen Farisanci da baitin waƙar nan: "ز گهواره تا گور دانش بجوی" (Ma'ana: Ka nemi ilimi daga gadon haihuwa har zuwa kabari). Wannan fassara ta samu shahara a cibiyoyin ilimi na Iran.

Shin Da Gaske Ne Wannan Jumla Daga Hadisi Take

Marubuta a baya-bayanan sun kawo wannan jumla a matsayin riwaya daga Annabi (S.A.W) lalle Abul Ƙasim Fayande mai tarjam kuma marubuci ɗan asalin Iran ya ambaci wannan ruwaya cikin gajerun kalmomi a cikin littafin Nahjul Fasaha (Littafi),[1] kazalika Khajo Nasirid-dini Ɗusi ya kawo ta a cikin littafinshi mai suna Adabul Muta'allimina kuma yace wannan Asar ne Sananne yana nufin ruwaya ce da ta shahara.[2]

Ƙari kan abin da ya gabata Faizul Kashani,[3] da Haj Halifa masani tarihi na ƙarni na 11,[4] da Haƙƙi Albursawi wanda ya rubuta tafsirin Ruhul Bayan,[5] duk sun kawo wannan jumla kuma suka ɗauketa a matsayin riwaya.

Duk da haka akwai masu bincike da suka faɗa ƙarara cewa ba su sami wannan jumla ba a cikin riwayoyi.[6] wasu kuma suka ce wannan jumla ba'a ruwaitota ba a cikin littafan ruwayoyi kuma suna ganin duk marubucin da yake ganin wannan jumlar ruwaya ce to basu da dalili kan hakan kuma basuyi bincike na ilimi ba.[7]

Abin da Jumlar Take Nufi

Wannan jumla ta "اُطلُبوا العِلمَ مِنَ المَهدِ إلَی اللَّحْدِ" bincike ya gudana a kanta ba tare da la'akari da cewa ita riwaya ce ko akasin hakan ba, to ya kamata mu yi bincike kan ma'anarta, ma'anar wannan jumla b ata da wata matsala, akwai wasu ruwayoyi a cikin littafai na hadisi da suke ɗauke da ma'anar wannan jumla, Imam Kazim (A.S) ya rawaito daga Imam Ali (A.S) cewa daga cikin abin da ya keɓanta da mumini shi ne cewa baya ƙoshi da ilimi a zuwa ƙarshen rayuwarshi.[8]

Wannan jumla tashahara a harshan farisanci tana yawo a matsayin Baiti na waƙa.[9] kuma ana rubuta wannan jumla a jikin bango na cibiyoyin ilimi masamman makarantu domin kwaɗaitar da mutane kan neman ilimi.[10]

Bayanin kula

  1. Nahj al-Fasaha wanda Abul Qasim Payandeh ya wallafa, shafi na 218, bugu na shekarar 1382 (Shamsi kalandar)
  2. Adab al-Muta'allimin wanda aka jingina wa Nasir al-Din al-Tusi, shafi na 112, bugu na shekarar 1416 H.
  3. Al-Wafi wanda Al-Faizlul Al-Kashani ya rubuta, Juzu'i na 1, shafi na 126, bugu na shekarar 1406 H.
  4. Kashf al-Zunun wanda Hajji Khalifa (Mustafa bin Abdullah) ya rubuta. Wannan littafi, juz 1 shafi na 51
  5. Tafsir Ruh al-Bayan wanda Isma'il Haqqi al-Burusawi ya rubuta, juz 5 shafi na 274.
  6. Az Aghaz Ta Anjam Dar Goftoguye Do Daneshjoo wanda Ayatollah Montazeri ya rubuta, bugu na shekarar 1388 (Shamsi kalandar), shafi na 29
  7. Daneshnameh Aqaid Islami (Juzu’i na 3, shafi na 15), Al-Ilm wa al-Hikma fi al-Kitab wa al-Sunna na Muhammad Al-Ray Shahri, (Shafuka na 218 da 219), bugu na 1422 H, yana tattauna mahimmancin ilimi da hikima a cikin Al-Qur'ani da Sunnah
  8. Al-Kafi wanda Sheikh Muhammad bin Ya'qub al-Kulayni ya rubuta, Juzu'i na 1, shafi na 19, bugu na shekarar 1407 H.
  9. Hamidreza Fahandejsa'di «آگاهی‌های تازه دربارهٔ «ز گهواره تا گور دانش بجوی» و سرایندهٔ آن»،shafi na 150.
  10. Hamidreza Fahandejsa'di «آگاهی‌های تازه دربارهٔ «ز گهواره تا گور دانش بجوی» و سرایندهٔ آن»،shafi na 150.

Nassoshi

  • Nahj al-Fasaha na Abu al-Qasim Payandeh: Bugu a Tehran, Duniyay-e Danesh, 1382 (Shamsi).
  • Daneshnameh Aqaid Islami: An rubuta ta hannun marubuta daban-daban, bugu a Qum, Dar al-Hadith, 1385 (Shamsi).
  • Kashf al-Zunun na Hajji Khalifa: Littafi kan tarihin adabi, buu a Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi.
  • Tafsir Ruh al-Bayan na Isma'il Haqqi Burusawi: Littafi na tafsirin Al-Qur'ani, bugu a Beirut, Dar al-Fikr.
  • Al-Ilm wa al-Hikma na Muhammad al-Ray Shahri: Bugu a Qum, Dar al-Hadith, 1422 H.
  • Al-Wafi na al-Fayd al-Kashani: Bugu a Isfahan, Maktabat Imam Amir al-Mu'minin Ali, bugu na farko, 1406 H.
  • Al-Kafi na Muhammad bin Ya'qub al-Kulayni: Littafin hadisi, bugu a Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, 1407 H.
  • Nazarin Z Gohvara Ta Gor na Hamidreza Fahandejsa'di: Wani bincike a fannin adabi, bugu na Musim 1400 (Shamsi).
  • Az Aghaz Ta Anjam na Ayatollah Montazeri: Littafi na tattaunawa tsakanin dalibai, bugu a Tehran, Gawahan, 1388 (Shamsi).
  • Nafarin Hadis a Adabi na Muhammad Hasan Natqi: Wani karatun tasirin hadis a cikin adabin Farisa, bugu a shekara ta 1386 (Shamsi).
  • Adab al-Muta'allimin na Nasir al-Din al-Tusi: Littafin ladubban neman ilimi, bugu a Shiraz, Maktabat Madrasat Imam al-Asr, bugu na farko, 1416 H.