Abdullahi Bin Sinan
Cikakken Suna | Abdullahi Bin Sinan |
---|---|
Wurin haihuwa | Shekara 130 bayan hijira |
Wafati | Kusa da shekara 200 bayan hijira |
Mazhaba | Shi'a |
Sahabi | Sahabin Imam Sadiƙ (A.S) |
Ya ruwaito daga Ma'asumi | Imam Sadiƙ (A.S) da Imam Kazim (A.S) |
Inganci | Siƙa |
Talifai | Amalu Yaumin Wa Laila, Assalatul Kabira, haka ya yi talifi cikin sauran babuka daga halal da haram |
Abdullahi ɗan Sinan (Larabci: عبد الله بن سنان) ɗaya ne daga cikin marawaitan hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S), a ƙarni na biyu bayan hijira. Sayyid Khuyi ya ambaci cewa sunan Abdullahi ɗan Sinan ya zo a cikin sanadin riwayoyi guda 1146. An yi imani da cewa ya yi zamani da Imam Baƙir (A.S) da Imam Jawad (A.S). Malaman Shi'a na Rijal sun dauke shi a matsayin Shi'a kuma amintacce, Najashi ya danganta wasu ayyuka ga Abdullahi ɗan Sinan, kuma Shaikh Ɗusi ya ambaci cewa Abdullahi ɗan Sinan ya ruwaito addu'o'i, da ziyarori, da addu'o'in Ranar Ashura, daga Imam Sadiƙ (A.S).
Wane ne Abdullahi Bin Sinan
Babu masaniya da yawa game da Abdullahi ɗan Sinan, tarihi bai kawo lokacin haihuwarshi ba da yadda ya rayu, amma tabbas an kawo lokacin da ya rasu shi ne shekara ta 200 bayan hijira,[1] ansa Abdullahi ɗan Sinan a matsayin bawan Bani Hashim,[2] da Bani Ɗalib,[3] da Ƙuraishawa,[4] da Banu Abbas,[5] kalmar Maula a harshan Larabci, da cikin Isɗilahin na Ilimin Hadisi da ilimin Rijal tana nufin `yantaccen bawa, a wasu lokuta kuma tana nufin abokin ƙawance.[6]
Ahmad ɗan Ali Annajashi ya rawaito daga Abdullahi ɗan Sinan cewa shi Abdullahi mutumin garin Kufa ne, amma ba tare da ya yi nuni cewa shi mazaunin Kufa ne ko an haife shi a Kufa ko ya shahara a Kufa ko ya rasu a Kufa.[7]
Aiki
Najashi da Shaik Ɗusi da Ahmad ɗan Muhammad Albarƙi sun ce shi Abdullahi ɗan Sinan ya kasance mai kula da dukiyar gwamnati, amma akwai bambanci da tsakanin abin da Najashi ya faɗa da na sauran, ya ce shi mai kula da dukiyar gidan gwamanati amma a lokacin Abbasiyawa, da lokacin Mansur da Mahadi da Hadi da Haruna Rashid,[8] Amma Ɗusi da Barƙi sun nuna cewa Abdullahi ɗan Sinan ya kasance mai kula da dukiyar gamnati a lokacin Mansur da Mahdi.[9]
Sunan Mahaifi
Sunan mahaifin Abdullahi ɗan Sinan ba ayi ittifaƙi a kan shi ba a littafan Rijal, Shaiku Ɗusi,[10] da Najashi sun ce sunan mahaifinshi Sinan ɗan Ɗarif,[11] A dai-dai lokacin da Albarƙi ya ce sunan shi Sinan ɗan Sinan, Dawud Alhilli ya ce sunan shi Sinan ɗan Zarif.[12]
Albarƙi ya ce Sinan ɗan Sinan shi ne mahaifin Abdullahi kuma ya kasance bawan Ƙuraishi kuma ɗaya daga cikin Sahabban Imam Baƙir (A.S),[13] Albarƙi ya yi imani cewa Sinan ɗan Ɗarif ya kasance kakan Muhammad ɗan Sinan kuma ya kasance ɗaya daga cikin Sahabban Imam Rida (A.S) da Imam Jawad (A.S),[14] Albarƙi ya ambaci suna guda biyu ga Abdullahi ɗan Sinan, ya nuna cewa sunan mutum na farko ya kasance ɗan wasiɗiya kuma yana cikin sahabban Imam Kazim (A.S),[15] amma na biyun yana cikin sahabban Imam Rida (A.S),[16] amam Sayyid Khuyi yana ganin cewa wannan mutane guda biyu sun shabanban da Abdullahi ɗan Sinan Almaɗlub,[17] kuma shi Sayyid Khuyi yana ganin cewa ra'ayin Albarƙi ya fi kusa da gaskiya kan baban Abdullahi ɗan Sinan.[18]
Matsayin Abdullahi ɗan Sinan A Ilimin Rijal
Najashi ya ce Abdullahi ɗan Sinan yana cikin masu rawaito ruwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) duk da cewa Najashi yana ganin Abdullahi ɗan Sinan a matsayin wanda ya yi rayuwa a lokacin Imam Kazim (A.S) sai dai cewa ba shi da tabbas kan Abdullahi ya rawaito riwaya daga Imam Kazim(A.S),[19] kamar yadda Muhammad Alkasshi yake ganin shi a matsayin masu rawaito ruwaya daga Imam Sadiƙ(A.S),[20] Ayatullahi Khuyi yana ganin Abdullahi ɗan Sinan ya riski lokacin Imam Baƙir (A.S) har zuwa Imam Jawad (A.S) kuma ya rawaito ruwaya daga gare su.[21]
Barƙi da Najashi da Shaik Ɗusi,[22] suna ganin Abdullahi ɗan Sinan a matsayin Siƙa (wanda baya ƙarya) Najashi ya siffanta shi da cewa shi ɗan shi'a ne mai girma da matsayi kuma babu wanda ya yi magana mummuna a kanshi.[23] Bisa wata riwaya da Kashshi ya naƙalto cewa lokacin da Imam Sadiƙ (A.S) ya ambaci sunan Abdullahi ya ce alherinshi yana ƙaruwa gwargwadan ƙaruwar shekarunshi.[24]
Shaik Ɗusi ya kawo riwayoyi guda uku a cikin littafinshi na Al-Fihrisat daga Abdullahi ɗan Sinan,[25] kuma ya kawo wata ruwayar a cikin littafinshi mai suna Misbahul Mutahajjid daga Abdullahi ɗan Sinan daga Imam Sadiƙ (A.S) ruwayar ta ƙunshi addu'a da ziyara da Sallah a Ranar Ashura.[26] Sayyid Khuyi ya sami sunan Abdullahi ɗan Sinan a cikin riwayoyi guda 1146.[27]
Shaik Mufid ya yaba da Abdullahi ɗan Sinan a matsayinshi na malamin Fiƙihu da mai ba da fatawa da hukunce-hukunce.[28] Shaikul Mufid ya kawo ruwaya a cikin littafinshi ta hanyar Abdullahi ɗan Sinan daga ImamSadiƙ( A.S) ita ruwayar tana bayani game da zunubai.[29]
Littafan Abdullahi ɗan Sinan
Bisa abin da Najashi ya kawo Abdullahi ɗan Sinan yana da littafai guda uku na farko ana kiransa da " Amalu Yaumin Wa Laila" (Yana bayani ne kan ayyukan dare da rana) da littafin Salatul Kabir da wani littafi da yake magana kan babuka daban-daban kamar halal da haram,[30] amma Shaik Ɗusi ya ambaci littafi ɗaya ne mai suna "Amalu Yaumin Wa Laila".[31]
Bayanin Kula
- ↑ "Baghdadi, Hadittul Arifin, 1951 M, J1, Sh439."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh 214, Sh558."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh 214."
- ↑ "Barqi, Tabakat Rijal, 1383 H, ."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh 214."
- ↑ "Sajjadi, Rawabit Mawali da Shi'a, 1391 H, Sh 25."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh 214."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh214."
- ↑ "al-Tusi, Ikhtiyar Marifatil Rijal, 1404 H, J2, Sh711; Barqi, Tubarin Mutanen, 1383 H, Sh22."
- ↑ "al-Tusi, Rijal al-Tusi, 1415 H, Sh 221."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh 214."
- ↑ "Hilli, Rijal, 1392 H, J1, Sh 120."
- ↑ "Barqi, Rijal al-Barqi, 1383 H, Sh16 da 18."
- ↑ "Khoyi, Muajam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh6919."
- ↑ "Barqi, Tabakatul Rijal, 1383 H, Sh48."
- ↑ "Barqi, Tabakatul Rijal, 1383 H, Sh 57
- ↑ "Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh6919."
- ↑ Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh6919."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh214."
- ↑ "Al-Tusi, Ikhtiyaru Marifati Rijal, 1404 H, J2, Sh 711."
- ↑ "Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh227."
- ↑ "Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh 226-228
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J 1, Sh 214."
- ↑ "Al-Tusi, Ikhtiyaru Marifati Rijal, 1415 H, J1, Sh412."
- ↑ "Al-Tusi, Al-Fihirsat, 1417 H, Sh166-165."
- ↑ "al-Tusi, Misbah al-Mutahajjid, 1411 H, Sh 782-787."
- ↑ "Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh217."
- ↑ "Khoyi, Mujam Rijalul Hadith, 1413 H, J11, Sh2225."
- ↑ "Mufid, Ikhtisas, 1379 H, Sh238."
- ↑ "Najjashi, Rijal, 1424 H, J1, Sh214."
- ↑ "Al-Tusi, Al-Fihirsat, 1417 H, Sh166."
Nassoshi
- Barqi, Ahmad ibn Muhammad, Rijal al-Barqi, gyara: Sayyid Kazim Musawi Miyamawi, Tehran, Jami'ar Tehran, 1383 H.
- Al-Babani al-Baghdadi, Isma'il ibn Muhammad,"هدية العارفين (أسماء المؤلفين وآثار المصنفين)"Dar Ihya al-Turath al-Arabi, Beirut - Lebanon, 1951 M."
- Khoyi, Sayyid Abu al-Qasim, Mujam Rijalul Hadith, London, Kungiyar Musulunci ta Khoyi, 1413 H/1992 M.
- Hilli, Hasan ibn Dawud, Kitabul Rijal, bita da Sayyid Muhammad Sadiq Bahr al-Ulum, Najaf, Matba'at al-Haidariyya, 1392 H.
- Sajjadi, Sayyid Mohsen, Rawabit Mawali wa Tashayyu, Qom, Ashiyaneh Mehr, 1391 H.
- al-Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Ikhtiyar Ma'rifat al-Rijal (Rijal al-Kashi), Qom, Mu'assasat Al al-Bayt, 1363 H/1404 H.
- al-Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Rijal al-Tusi, Qom, Mu'assasat Nashr Islami, 1373 H/1415 H.
- Al-Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Al-Fihirst, bita da Jawad Qayumi, Qom, Mu'assasat Nashr al-Faqaha, 1417 H/1375 H.
- al-Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Misbah al-Mutahajjid, Beirut, Mu'assasat Fiqh Shia, 1411 H/1991 M.
Mufid, Muhammad ibn al-Nu'man, Kitabul Ikhtisas, bita da Ali Akbar Ghafari, Tehran, Nashr Saduq, 1379 H/1338 H. Najjashi, Ahmad ibn Ali, Rijal al-Najjashi, gyara da Musa Shubayri Zanjani, Qom, Mu'assasat Nashr Islami, 1382 H/1424 H.