Gulmar Da Ta Halasta
Gulmar Da Ta Halasta (Larabci: مُستَثنَيات الغيبة) Ma'ana mutanan da ya halasta ayi da su, daga cikin inda ya halasta ayi Gulma, akwai gurin da yin Gulma ya fi rashin yin ta alfanu, wato idan aka yi Gulma ya fi rashin yin ta amfani, (Da kuma gulamr duk mutumin da yake yin fasiƙanci a bayyane, shi ne mutuman da yake saɓawa Allah ba tare da ya damu ba idan mutane suka sani)
Daga cikin guraran da yin Gulma yafi rashi yinta muhimmanci akwai lokacin shawara, da yayin hani da mummuna da lokacin hana ‘yan bidi'a bidi'arsu da yayin faɗakar da musulmi dan kada ya shiga haɗari da lokacin yinƙurin tabbatar da adalci.
Gulma
- Tushen Ƙasida: Gulma
Gulma ita ce ambaton mutum ɗan uwanka da abin da ba ya so, ita Gulma tana cikin halaye marasa kyau kuma babban laifi ce, ita ce Kur'ani ya siffanta ta da cin naman mutumin da ya mutu,[1] kai ya ma haramta mutum ya saurari Gulma, Gulma tana cikin haƙƙin mutane saboda haka ya zo a riwayoyi cewa tuba daga Gulma yana da sharaɗin neman yafiyarsu.[2]
Wuraran da Gulma ta Halatta
Malamai na fiƙihu da Malam Akhlaƙ) sun yi ittifaƙi cewa Gulma ta halatta a wannan wurare:
- Idan akwai masalahar da ta fi mummanci idan aka yi Gulma.[3]
- Gulma ta halatta kan mutanen da suke bayyana fasiƙanci.[4]
Faɗar aibun mutum bada niyar yaɗawa ba, amma da sharaɗin rashin jin haushin wanda ake magana akan shi.[5]
Halascin Yin Gulma A Wurin da Yin ta Ya fi Barin ta muhimmanci
A musulinci Gulma ta halasta idan ɓoye aibin mutum ya fi zama babban laifi to ya halitta anan ayi Gulma, ga wasu wurare irinsu;[6]
- Neman shawara, idan mutum yana so ya auri wata mace musulma daga wurin mahaifinta, ko wani mutum yana so ya gina kamfani ko wani yana so ya fita zuwa wata ƙasa, sai ya nemi shawar daga wani mutum kan abin da ya dace, to anan ba haramin bane mutum ya faɗi aibin wani mutum, kai amana ma ta hukunta kan wanda aka nemi shawararshi da ya faɗi abu mai kyau da marasa kyau, kuma bai halasta ba yaƙin yin nasiha ga ɗan uwanshi mumini domin tsoran yin Gulma.[7]
- A lokacin hani da mummuna ya halasta ayi Gulma.[8]
- Yayin hana bidi'a ya halasta ayi Gulma.[9]
- Idan mutum yana cikin wani haɗari ko dukiyarshi tana cikin haɗari ko mutuncinshi na cikin haɗari duk saboda wani mutum, kuma shi wannan mutuma musulmi baisan haɗarin da yake ciki ba, to anan ya halasta abashi labarin haɗarin da yake ciki.[10]
- Ko kuma ya zama mutum yana cikin zalinci kuma yana fafutikar neman haƙƙinshi daga wani mutum da ƙoƙarin kawo ƙarshan zalinci, to anan ya halasta ayi Gulma.[11]
Masu Bayyana Fasiƙanci
Idan wani ya yi zunubi a bayyane, bai damu da wasu sun san ya yi wannan zunubi ba, to ya halatta ayi da shi wato ayi Gulmar shi kan lamarin zunubin da ya aikata a bayyane.[12] Wasu suna ganin cewa wannan ba ya cikin gulma ko yi da shi, Domin fasiƙi ba ya jin kunyar bayyanar da zunubi.[13]
Hujjar togaci wannan al-amari, ƙari kan dalilai na hankali, hadisai ne da suke nuna halaccin yin gulma ga irin wannan mutum. An rawaito wani hadisi daga Imam Baƙir (A.S) ya ce: “Mutane uku ba su da wani hurumi da alfarma, mai bin son rai ɗan bidi'a, da azzalumin shugaba, da fasiƙi mai bayyana fasikanci.[14]
Bayyanannun Aibobi
Ambaton aibi na fili kuma sananne da wasu mutane suke dashi, kamar yin (gulma) da makafi, guragu, matukar dai bai yi nufin wulakanta su ba, sai dan ya gabatar da su, kuma ya zamo wanda ake siffantawa da wannan abubuwa ba zai damu ba.[15]
Kafirai da Mushrikai
Ya halatta a yi Gulmar kafirai da waɗanda ba Shi'a imamiyya.[16]
Bayanin kula
- ↑ Al-Jurjani, Ma'ujam al-Ta'arifaat, shafi na 137:
- ↑ Al-Hurr Al-Amili, Wasail Al-Shi'a, juzu'i na 12, shafi na 281:
- ↑ Al-Ansari, Kitab al-Makasib, juzu'i na 1, shafi na 118:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 100:
- ↑ Dastghib, Al-Dhunub Al-Kabira, juzu'i na 2, shafi na 274:
- ↑ Al-Ansari, Kitab al-Makasib, juzu'i na 1, shafi na 118:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 99:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 99:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 99:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 99:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 99:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 101:
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Akhlaq fi Al-Quran, juzu'i na 3, shafi na 101:
- ↑ Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 72, shafi na 253:
- ↑ Dastghib, Al-Dhunub Al-Kabira, juzu'i na 2, shafi na 274:
- ↑ Al-Naraqi, Mi'raj al-Sa'ada, shafi na 453:
Nassoshi
- Al-Qur'ani Mai Girma.
- Al-Ansari, Mortaza, "Kitab al-Makasib," Beirut, Mu'assasat al-A'lamiy lil-Matbu'at, 1415 AH.
- Al-Jurjani, Ali bin Muhammad, "Kitab al-Ta'arifaat," Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyyah, bugu na 1, 1403 AH/1983 AD
- Al-Hurr Al-Amili, Muhammad bin Hasan, "Wasail al-Shi'a," Qom, Mu'assasat Aal al-Bayt (AS) Lil Ihya' al-Turath, bugu na 2, 1416 AH.
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, "Bihar al-Anwar," Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, bugu na 3, 1403 AH/1983 AD.
- Al-Naraqi, Mulla Ahmad, "Mi'raj al-Sa'ada," Qom, Mu'assasat Intisharat Hijrat, 1378 SH.
- Al-Naraqi, Muhammad Mahdi, "Jaami' al-Sa'adaat," Qom, Ismailiyan, Qom, bugu na 7, 1428 AH.
- Dastghib, Abdul Hussein, "Al-Dhunub Al-Kabira," Lebanon, Al-Dar Al-Islamiyya, bugu na 4, 1427 AH/2006 AD.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, "Al-Akhlaq fi Al-Quran," Qom, Madrasat al-Imam