Jump to content

Utlubul Ilma Wa Lau Bis Sin

Daga wikishia
Utlubul Ilma Wa Lau Bis Sin
Maudu'iMuhimmancin Neman Ilimi
Ya Fito DagaAnnabi (S.A.W) Da Imam Ali (A.S)
Ingancin IsnadiHadis Mursal
Madogaran Shi'aMisbahush Shari'a, Da Raudatul Wa'izin,
Madogaran Ahlus-sunnaUkudul Zabarjad
Hadis Silsilatuz ZahabHadis SaƙlainiMaƙbulatu Umar Bin HanzalaHadis Ƙurbu NawafilHadis Mi'irajHadis WilayaHadis WisayaHadis Junud Aƙli Wa JahalHadis Shajara


Ku Nemi Ilimi Ko Da A Birnin Sin Ne (Larabci: اطلبوا العلم ولو بالصين) wani hadisi ne da aka rawaito daga Annabi (S.A.W) da Imam Ali (A.S), wannan hadisi yana ƙarfafa larurar neman ilimi koda hakan zai tilasta yin tafiya mai nisa. Amma Mulla Sadra masanin falsafa da irfani kuma ɗan Shi'a yana ganin wannan hadisin yana nuna kan wajabcin neman ilimi, kuma ya kafa hujja da wannan hadisin kan wajabcin neman ilimi daga wanda ba musulmi ba, mafi daɗewar littafin da wannan hadisi ya zo a cikin shi shi ne Misbahush Shari'a, wannan hadisin ana ɗaukar shi matsayin hadisi mai rauni saboda rashin ambaton silsilar isnadin marawaitan shi, sai dai wasu masu bincike duba da ma'anar hadisin sun tafi kan ingancinshi.

An rawaito daga Imam Ali (A.S) kan ƙarshan wannan hadisi cewa ma'anar ilimi a cikin wannan hadisin yana nufin mutum ya san kanshi kuma haka ne zai sa ya san Allah, amma Ayatullahi Jawadi Amoli malami masanin fiƙihu da tafsirin shi'a yana ganin duk wani ilimi da zai sa mutum ya zama na Allah, to ya shiga ƙarƙashin wannan hadisin, amma Murtada Muɗahhari yana ganin cewa Sin bata taɓa zama cibiyar ilimin addini ba, ba a wancan lokacin ba kuma a waninshi ba, kuma babu wani ƙaidi a cikin hadisin, to lalle ma'anar ilimi ba za ta zamo ilimin addini ba, kai ma'anar ililmi a wannan hadisin yana nufin duk wani ililmi mai amfani kuma wanda zai amfani musulunci da musulmi, Murtada Muɗahhari yana gani dalilin ambatan Sin a wannan hadisin shi ne kasantuwarta mafi nisan gurin daga yankin muslunci da kuma nisan shi daga cibiyoyin ilimi da sana'a a duniya.

Ƙarfafawar Da Muslunci Kan Neman Ilimi

Ku nemi ilimi ko da a Sin ne, wannan hadisi ne da aka rawaito shi daga Imam Ali (A.S) ya zo a cikin littafin Misbahush Shari'a,[1] kuma Fattal Naishaburi (Rasuwa:508 bayan hijira) kuma shi ɗaya ne daga cikin malaman Shi'a ya naƙalto wannan hadisin daga Manzon (S.A.W) a cikin littafin mai suna Raudatul Wa'izin,[2] wannan riwaya ta zo a cikin wasu daga cikin litattafan Ahlus-sunna.[3]

A cikin wannan hadisin akwai ƙarfafa maganar neman ililmi ko da hakan zai kai mutum ya yi tafiya mai nisa a doran ƙasa,[4] kuma ba zai yi wu ba wahalar da mutum zai sha domin neman ililmi, ya zama dalili da zai hana shi neman ililmi,[5] Mulla Sadra (Rasuwa: 1050 bayan hijira) yana ganin wannan hadisi dalili ne kan wajabcin neman ililm,[6] kuma Mulla Sadra ya sanya ililmi mataki-mataki idan mutum ya isa zuwa mataki na ɗaya to wajibi ne ya isa zuwa mataki na biyu,[7] kuma Allama Majalisi (Rasuwa:1110 bayan hijira) ya kawo wannan hadisin a cikin littafinshi mai suna Biharul Al-anwar a cikin babi Wujubul ilmi,[8] amma wasu sun kafa hujja da wannan hadisin kan halascin neman ilimi daga wanda ba musulmi ba ko kuma daga ƙasashan da ba na musulmi ba.[9]

Wasu litattafai ƙarashan wannan hadisin ya zo cewa haƙiƙa neman ililmi wajibi ne kan ko wane musulmi, ku nemi ilimi ko da a birnin Sin ne, saboda shi neman ililmi wajibi ne kan ko wane musulmi.[10] Akwai wata riwayar mai kama da wannan daga Imam Sadik (A.S) tana cewa ku nemi ilimi .... [11]

Bincike Kan Sanadin Wannan Hadisi

Mafi daɗewar littafi daya kawo wannan riwaya shi ne Misubahush Shari'a,[12] kuma Sayyid Ibn Ɗawus (Rasuwa: 664 bayan hijira) yana ɗaya daga cikin malaman ƙarni na bakwai ya jingina wannan littafin ga Imam Sadik (A.S),[13] Muhammad Taƙiyyu Majlisi (Rsuwa:1070 bayan hijira) ɗaya daag cikin malaman hadisi na ƙarni na sha ɗaya ya ce matanin wannan littafi yana nuna cewa jinginashi ga Imam Sadik (A.S) ya inganta,[14] amma a cikin malaman hadisi akwai wanda ya rauanata jingina wannan littafi ga Imam Sadiƙ (A.S) kamar misalin Hurul Amili (Rasuwa: 1104 hijira),[15] kamar yadda rashin ambatan jerin waɗanda suka rawaito wannan hadisi shi ma ɗaya ne daga cikin dalilin rauninshi,[16] sai dai cewa wasu masu bincike suna ganin duba da ma'anar hadisin ya inganta,[17] kuma sun tafi kan yarda da wannan riwaya.[18]

Nazari Kan Abin da Yake Cikin Hadisin

A wajan kammala ma'anar wannan hadisi ya zo a cikin littafin Misbahush Shari'a daga Imam Ali (A.S) cewa ma'anar ilimi a wannan hadisin tana nufin mutum ya san kanshi wanda yin haka ne zai kai shi ga sanin Allah,[19] saboda haka ne wasu suka tafi kan cewa, wannan hadisin bai ƙunshi sababbun ilimummuka ba,[20] sai dai cewa Ayatullahi Jawadi Amoli yana ganin duk wani ilimi da zai sa mutum ya zama na Allah, to zai shiga ciki kamar ililmi Fizik (Physics) ko lissafi ko likitanci ko fiƙihu, to zai iya shiga cikin ma'anar wannan hadisin, amma idan mutum bai kusancin Allah da wannan ilimi ba, to ba su da wata fa'ida,[21] sai dai Allama Murtada Muɗahhari mai tinani masani ɗan Shi'a yana ganin cewa Sin bata taɓa zama cibiyar ilimin addini ba a da da yanzu ba, kuma a hadisin babu ƙaidi, to ma'anar ilimi za ta zamo ba ilimi addini ba, saboda haka ilimi a wannan riwayar da masu kama da ita zai zama duk wani ilimi mai amfani ga muslunci da musulmi kuma ya zamo ba shi da cutarwa.[22]

Sayyid Ali Al-Khamna'i Jagoran juyin-juya hali na Muslinci a Iran, kuma ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi a gun ƴan shi'a, yana kafa hujja da wannan hadisin yana ganin a lokacin neman ilimi da musayar al'ada dole ne ayi amfani da ililmi da hikima, kuma hakan ba yaƙar al'adar mutuane ba ne.[23]

Allama Muɗahhari yana ganin ambatan Sin a wannan hadisin ya faru ne sakamakon tafi nisa ko kuma saboda a ƙarni na ɗaya na muslunci ta zamo wata cibiya ta ilimi da sana'a a duniya,[24] amma al'amarin neman ilimi bai taƙaita da Sin ba kaɗai.[25]

Bayanin kula

  1. "Da aka danganta wa Imam Al-Sadiq عليه السلام, Misbah Al-Shari'ah, shafi na 13."
  2. "Al-Fattal Al-Naysaburi, Rawdat Al-Wa'izin, Juzu'i na 1, shafi na 11."
  3. Haqqi al-Burusawi, Tafsir Ruh al-Bayan, Juzu'i na 2, shafi na 346.
  4. "Shahid Thani, Sharh Misbah al-Shari'ah, shafi na 383."
  5. "Shahid Thani, Sharh Misbah al-Shari'ah, shafi na 383."
  6. "Mulla Sadra, Sharh Usul al-Kafi, Juzu'i na 2, shafi na 76."
  7. "Mulla Sadra, Sharh Usul al-Kafi, Juzu'i na 2, shafi na 5."
  8. "Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, Juzu'i na 1, shafi na 177."
  9. "Nasiri, 'Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 79."
  10. Al-Fattal Al-Naysaburi, Rawdat Al-Wa'izin, Juzu'i na 1, shafi na 11.Al-Tabarsi, Mishkat al-Anwar fi Ghurar al-Akhbar, shafi na 136.
  11. Al-Hulwani, Nuzhat al-Nazir wa Tanbih al-Khatir, shafi na 108.Al-Daylami, A'lam al-Din fi Sifat al-Mu'minin, shafi na 303.
  12. "Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 79."
  13. "Ibn Tawus, Aman al-Akhtar, shafuka na 91-92."
  14. "Al-Majlisi, Rawdat al-Muttaqin, Juzu'i na 13, shafi na 201."
  15. "Al-Hurr Al-Amili, Hidayat al-Ummah, Juzu'i na 8, shafi na 550."
  16. "Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 79."
  17. "Hosseinian, 'Difa'u Az Hadisi', shafi na 21."
  18. Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 79."
  19. "Almansub li Imam Al-Sadiq (A.S), Misbah Al-Shari'ah, shafi na 13."
  20. Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 79."
  21. "Jawadi Amuli, Nasim Andisheh, shafi na 167."
  22. "Mutahhari, Majmu'at Athar, Juzu'i na 1, shafuka na 106-107."
  23. «تبادل فرهنگی یعنی زبده‌گزینی فرهنگی»، "Shafin yanar gizo na Ofishin Kula da Adana da Buga Ayyukan Ayatollah Khamenei.".
  24. "Mutahhari, Majmu'at Athar, Juzu'i na 30, shafi na 106."
  25. Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin', shafi na 80.

Nassoshi

  • Ibn Tawus, Ali bin Musa, Aman al-Akhtar min Akhtar al-Asfar wal-Zaman, Qom, Mu'assasat Al-Bayt, 1409 AH.
  • Al-Hurr Al-Amili, Muhammad bin Al-Hasan, Hidayat al-Ummah ila Ahkam al-A'immah - Mukhtarat al-Masa'il, Mashhad, Majma' al-Buhuth al-Islamiyyah, 1st ed., 1412 AH.
  • Al-Hulwani, Hussein bin Muhammad, Nuzhat al-Nazir wa Tanbih al-Khatir, Qom, Madrasat al-Imam al-Mahdi (A.S.), 1st ed., 1408 AH.
  • Al-Daylami, Hassan bin Muhammad, A'lam al-Din fi Sifat al-Mu'minin, Qom, Mu'assasat Al-Bayt, 1st ed., 1408 AH.
  • Al-Suyuti, Jalal al-Din, Uqud al-Zabarjad ala Musnad al-Imam Ahmad, edited by: Salman al-Qudat, Beirut, Dar al-Jil, 1414 AH.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Sharh Misbah al-Shari'ah, edited by: Jamal al-Khuwansari, Tehran, Payam Haqq, 1st ed., 1377 SH.
  • Al-Tabarsi, Ali bin Al-Hasan, Mishkat al-Anwar fi Ghurar al-Akhbar, Najaf, Al-Maktabah al-Haydariyyah, 2nd ed., 1385 AH/1965 AD.
  • Al-Fattal Al-Naysaburi, Muhammad bin Ahmad, Rawdat al-Wa'izin wa Basirat al-Mutta'izin, Qom, Intisharat al-Sharif al-Radi, 1st ed., 1375 SH.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, 3rd ed., 1403 AH/1983 AD.
  • Mutahhari, Murtadha, Majmu'at Athar, Tehran, Intisharat Sadra, 7th ed., 1384 SH.
  • Mulla Sadra, Muhammad bin Ibrahim, Sharh Usul al-Kafi, edited by: Muhammad Khwajawi, Tehran, Mu'assasat Mutali'at wa Tahqiqat Farhangi, 1st ed., 1383 SH.
  • "Almansub Li Imam Al-Sadiq, Misbah Al-Shari'ah, Beirut, Mu'assasat Al-A'lamy, bugu na farko, 1400 AH."
  • «تبادل فرهنگی یعنی زبده‌گزینی فرهنگی»، "Shafin yanar gizo na Ofishin Kula da Adana da Buga Ayyukan Ayatollah Khamenei, Ranar Dubawa: 26/04/1403 SH."
  • Jawadi Amuli, Abdullah, Nasim Andisheh (Daftar Yekum), edited by: Mahmoud Sadeqi, Qom, Nashr Isra, 3rd ed., 1388 SH.
  • Hosseinian, Mahdi, "Defense of Hadith: Argument for the Theory of Reliability and Credibility of Trusted Narrations", in Samat Quarterly, Issue 2, Summer 1389 SH.
  • Haqqi al-Burusawi, Ismail, Tafsir Ruh al-Bayan, Beirut, Dar al-Fikr, n.d.
  • Nasiri, Mahdi, "Nasiri, Darbaraye Hadis Mashhur Utlubul Ilma wa lau bis Sin',", in Samat Quarterly, Issue 2, Summer 1389 SH.