Mutuwa Ga Amurka

Mutuwa ga Amurka (Larabci: الموت لأمريكا ) wata jumla ce da ake amfani da ita a Iran da wasu ƙasashe domin nuna rashin yarda da siyasar gwamnatin Amurka, amma wasu suna ganin wannan jumla ko take yana daɗa tabbatar da aƙidar da asasi na Juyin juya halin Jumhuriyar muslunci ta Iran, wanda aka yi shi domin barranta kan mulkin mallaka.
Wasu suna kafa hujja kan wannan jumla ko take da ayoyin ƙur'ani waɗanda suke fatan mutuwar kafirai da Mushrikai, a dai-dai lokacin da wasu suke ganin cewa ita wannan jumla tana daɗa tabbatar da aƙidar bara'a, ita aƙidar bara'a ɗaya ce daga cikin Rassan addini, amma shi Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i yana ganin cewa wannan take ko jumlar yana ɗauke da ma'ana mai zurfi a hankalce kuma zai yi wu a kwatantashi da neman tsari daga Shaiɗan da kuma Shirin ko ta kwana domin fuskantar Shaiɗan.
Amma wasu gungun `yan siyasa a Iran suna adawa da wannan take, kuma suna ganin ya kamata a kawar da shi, kuma suna iƙirari cewa marigayi Imam Khomaini Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya yarda da a cire shi a daina aiki da shi a kafafan watsa labarai na gwamnati a tsawon rayuwarshi, amma masu goyan bayan wannan take suna ganin wannan maganar bata da asali ko tushe, kawai yaudara ce, hakan bai tabbata ba, suna ganin yanke shawara yana hannun Waliyul faƙihi, wato abu ne da ya keɓanta da jagoran addini.
Matsayi
Shi wannan take na mutuwa ga Amurka wani sirri ne da hadafi na Jamhuriyar muslunci ta Iran mai hamayya da mulkin mallaka,[1] wasu kuma suna ganin wannan wani take ne na asali da ginshiƙi na juyin juya halin muslunci a Iran.[2] Bai taƙaita da wani lokacin na masamman ba.[3] Babban Malamin falsafan nan na Shi'a Muhammad Taƙiyyu Misbahu Yazdi ya yi imani cewa wannan take Iranawa sun ɗaukeshi da muhimmanci kamar kabbarar da suke yi bayan Sallar Jam'i.[4]
Shugaban Addini babban jagora na juyin juya halin Muslunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i yana ganin wannan take abu ne na hankali, wanda yake nufin kawo ƙarshan siyasar danniya ta Amurka.[5] Kazalika fatan Allah ya ruguza shuwagabanin Amurka a ko wane lokaci.[6] Kuma wannan take ya yi kama da neman tsari da shelanta Shirin ko ta kwana domin fuskantar shaiɗan, kuma ya yi imanin cewa wannan take zai sa mutane su kasance cikin shirin fuskantar masu kwaɗayin danniya da mulkin mallaka.[7]
Dalili na Addini kan Wannan Slogan (Take)
An yi bincike na Kur'ani kan taken "Mutuwa ga Amurka" kuma wannan taken yana da nasaba da ayoyi kamar aya ta 8 a cikin Suratul Muhammad, da aya ta 4 cikin suratul Buruj, aya ta 19 cikin suratul Muddassir, da aya ta 10 cikin suratul Zariyat, waɗannan ayoyi suna fatan mutuwa da halaka ga wasu kafirai da mushrikai ta hanyar amfani da kalmar kashewa.[8] Wasu kuma sun yi imanin cewa taken Mutuwa ga Amurka ana iya ɗaukarsa ɗaya daga cikin rassan addini kuma wani bangare na bara'a.[9]
Yaɗuwar Wannan Slogan A Wasu ƙasashe

Baya ga Iran, ana amfani da taken mutuwa ga Amurka a wasu ƙasashen Asiya, Turai, Afirka da Latin Amurka.[10] Sayyid Ali Khamna'i ya yi la'akari da hakan a matsayin babbar barazana ga Amurka,[11] kuma wata alama ce ta sauyin da babu makawa daga faruwarsa a duniya.[12] Misali wanda ya assasa kuma jagoran harkatu Ansarullahi Yaman ta ƙasar Yaman, Hussaini Al-Husi, a cikin jawabinshi mai taken tsawa a fuskar masu girman kai, ya bayyana cewa taken Allah mai girma, Mutuwa ga Amurka, Mutuwa ga Isra'ila, la'anar Allah kan Yahudawa, nasara ga muslunci shi ne taken Shi'a a wannan yanki.[13]
Adawa Da Wannan Slogan
Wasu mutane a Iran suna kira da a cire taken mutuwa ga Amurka daga cikin adabin siyasar Iran. Irinsu malamin nan kuma dan gwagwarmayar siyasa Muhammad Taƙi Rahbar, wanda ya yi imanin cewa za a iya kawar da taken idan aka ƙulla kawance da Amurka.[14] Shi ma malamin kimiyyar siyasa a jami'ar Tehran Sadiƙ Zibakalam ya yi la'akari da cewa dagewa kan wannan taken zai yi matukar tsada ga Iran.[15] Wasu mutane suna danganta gazawa a fagen ƙasa da ƙasa, kamar ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya sakamakon rera wannan taken da mutane ke yi..[16] Malamin addini da siyasa Akbar Hashemi Rafsanjani ya bayyana a cikin tarihinshi cewa jagoran juyin juya halin Muslunci na Iran Imam Khomaini na farko ya amince da cire taken mutuwa ga Amurka daga kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran.[17]
A ɗaya ɓangaren kuma, wasu kamar Limamin Juma'a na Tehran, Sayyid Ahmad Khatami, suna ganin cewa cire wannan taken yana cikin hurumin waliyul fiƙihu.[18] Dangane da cewa wannan taken yana haifar da gaba da Amurka, Sayyid Ali Khamna'i ya ce: Ma'abota girman kai suna ƙiyayya ga ci gaba da adalci da aka samu a wajen ikonsu, kuma taken ana fakewa da shi ne kawai.[19] Musamman tuni Amurka ta fara ƙiyayya da Iran tin a ranar 6 ga Agusta, 1953, a dai-dai lokacin da babu wani a Iran da ke rera taken Mutuwa ga Amurka.[20] Ya yi imanin cewa muddin Amurka ta ci gaba da mugunta, shisshigi da ƙeta, taken Mutuwa ga Amurka ba zai gushe ba yana fitowa daga bakunan al'ummar Iran.[21]
Tarihin Wannan Slogan
Akwai rahotanni daban-daban game da asalin taken Mutuwa ga Amurka. Wasu na ganin cewa ɗalibai da masu adawa da shugaban ƙasar Iran sun yi amfani da taken a karon farko a ziyarar da ya kai Amurka a ranar 1 ga watan Nuwamban shekarar 1977 miladiyya.[22] Bisa wasu takardu da aka samu daga mamayar ofishin jakadancin Amurka a Tehran, mutane sun yi amfani da wannan taken wajen zanga-zangar da rubuce-rubucen kan bango a shekara ta 1978.[23] Wasu daga cikinsu sun nuna cewa ɗalibai ne suka yi amfani da shi a ranar 22 ga Oktoba, 1978 miladiyya.[24]
Wannan Slogan A CIkin Fasaha Da Kafafan Watsa labarai
Bayan nasarar juyin juya halin Muslunci a Iran, al'amuran wannan take ya ci gaba da haɓɓaka a matsayin ƙasa a kai a kai da kuma duniya, sun hada da yin bajakoli da tarurrukan da suka shafi taken Mutuwa ga Amurka, misali: Ana gudanar da taro na Mutuwa ga Amurka duk bayan `yan shekaru, tare da halartar masu fasaha daga ƙasashe daban-daban na duniya, a fannoni daban-daban kamar ɗaukar hoto, masana a faɗin ƙasa, zane-zane, shirye-shiryen fina-finai da waƙoƙi.[25]
Bugu da ƙari, ana gudanar da musabaƙa ƙasa, irin ta zana Mutuwa ga Amurka a duk fadin ƙasar Iran,[26] da nunin nuna fastoci na taken Mutuwa ga Amurka a harabar jami'u.[27] Kazalika da tarun fasaha na Mutuwa ga Amurka, wanda ake gayyatar wasu fitattun mawaƙan adawa da girman kai na manya ƙasashe a duniya.[28]
A taro na shida na fina-finai an bayan fim ɗin Ammar a matsayin wanda ya lashe lambar yaɓo ta musamman, mai suna Mozabika mauti li Amurka, Ana ba da wannan lambar yaɓo ne a ko wace shekara ga aikin da ya fi nuna kyamar Amurka, kuma an fara ba da ita ga Mahdi Taƙwiyan, daraktan da ya shirya fim ɗin "Al-Ikhwa", wanda ke magana kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa karo na goma a Iran.[29]
Bayanin kula
- ↑ Al-Haidari, Tabyinu gustare Sha'a'ir Ilahi Dar Qur'an ba ruyekerdi tadbiki Shi'arhaye Inkilab Islami, shekara ta 1400 hijiriyya, shafi na 10.
- ↑ جذور شعار "الموت لأمريكا" في تاريخ الحركة الإسلامية، Cibiyar kula da documents na Juyin Juya Halin Musulunci..
- ↑ Mirshkari Soleimani,Dirasatul Khalfiyatil Tarikhiyati Li Shi'arat Sauratil Islamiyya, shekara ta 1398 hijiriyya, shafi na 143.
- ↑ مصباح: كل الناس يعتبرون شعار "الموت لأمريكا" مثل التكبير بعد الصلاة، Gidan Yanar Gizo na Labarai da Nazari na Ensaf.
- ↑ بطاقات شعار "الموت لأمريكا"Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei..
- ↑ بيانات في لقاء مع القادة والعاملين في القوات الجوية للجيش، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei.
- ↑ بيانات في لقاء مع أعضاء جمعيات الطلاب الإسلامية، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei
- ↑ Al-Haidari, Tabyinu gustare Sha'a'ir Ilahi Dar Qur'an ba ruyekerdi tadbiki Shi'arhaye Inkilab Islami, shekara ta 1400 hijiriyya, shafi na 10.
- ↑ لماذا نقول "الموت لأمريكا"؟ / الكتابة عن أمريكا لها عواقب، Kamfanin dillancin labarai na Tasneem.
- ↑ بيانات في لقاء مع الطلاب والطالبات، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei..
- ↑ بيانات في لقاء مع الطلاب والطالبات،Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei.
- ↑ بيانات في لقاء مع أساتذة الجامعات، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei.
- ↑ Alizadeh Mousa, As-sahwatul Islamiyya, shekara ta 1390 hijiriyya, shafukan 208-209.
- ↑ ماذا سيحدث لشعار "الموت لأمريكا"؟، Gidan Yanar Gizo na Nazari da Labarai na Asr Iran..
- ↑ مصير شعار استراتيجي / ماذا يقول مؤيدو ومعارضو "الموت لأمريكا"؟، Khabaru Online.
- ↑ Hidayati،"الموت%20لأمريكا" لماذا يستمر شعار "الموت لأمريكا"، Shafin yanar gizo na Alfu Ikhbari wat tahlili.
- ↑ مصير شعار استراتيجي / ماذا يقول مؤيدو ومعارضو "الموت لأمريكا"؟، Khabaru Online.
- ↑ مصير شعار استراتيجي / ماذا يقول مؤيدو ومعارضو "الموت لأمريكا"؟، Khabar Online.
- ↑ بطاقات شعار "الموت لأمريكا"، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei..
- ↑ بيانات في لقاء مع الطلاب،Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei.
- ↑ بيانات في لقاء مع القادة والعاملين في القوات الجوية للجيش، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei.
- ↑ Mirshkari Soleimani, Dirasatul Alkhalfiyyat Tarikhiyyati Li Shi'arat Sauratil Islamiyya Iraniyya, shekara ta 1398 hijiriyya, shafi na 36.
- ↑ Taron Marubuta, Wasaiq Wakre Attajassusi Amiriki, shekara ta 1386 hijiriyya, shafukan 400 da 403.
- ↑ جذور شعار "الموت لأمريكا" في تاريخ الحركة الإسلامية،Shafin Takardun tarihi na Saura Islamiyya.
- ↑ دعوة للمشاركة في الجائزة الدولية الكبرى الثالثة "الموت لأمريكا"، Shafin yanar gizo na Fastiwarat.
- ↑ تنظيم مسابقة "تايبوجرافي الموت لأمريكا" في تبريز، Hukumar labarai ta Mehr.
- ↑ عرض مجموعة ملصقات "الموت لأمريكا"Shafin Yanar Gizo na Ƙungiyar Ɗaliban Basij a Jami'ar Fasahar Musulunci ta Tabriz..
- ↑ فنانون أمريكيون يقولون "الموت لأمريكا" / دعوة المغنين المناهضين للاستكبار إلى إيران، Hukumar Labarai ta Mehr.
- ↑ الكشف عن الجائزة الخاصة الجديدة لمهرجان عمار، Shafin yanar gizo na Jahan Imruz.
Nassoshi
- بيانات في لقاء مع أساتذة الجامعات، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- بيانات في لقاء مع أعضاء جمعيات الطلاب الإسلامية، موقع مكتب حفظ ونشر آثار حضرة آية الله العظمى الخامنئي، تاريخ الزيارة: 24 خرداد 1403ش.
- بيانات في لقاء مع الطلاب، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Khamenei, ranar wallafa labarin: 11 Aban 1401 hijiriyya, ranar ziyarar: 8 Khordad 1403 hijiriyya.
- بيانات في لقاء مع التلاميذ الطلاب،Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- بيانات في لقاء مع الزوار والمجاورين في حرم الإمام الرضا،Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- Taron Marubuta, Takardun Asirin Jasusancin Amurka, Tehran, Kamfanin Buga Littattafai da Nazarin Siyasa, shekara ta 1386 hijiriyya.
- Taron Marubuta, Al'adun Alamun Juyin Juya Halin Musulunci, Tehran, Cibiyar Kayan Aiki ta Juyin Juya Halin Musulunci, shekara ta 1391 hijiriyya
- لماذا ولد شعار "الموت لأمريكا" في 16 آذر 32؟، موقع وكالة أنباء آنا، تاريخ نشر المقال: 16 آذر 1401ش، تاريخ الزيارة: 8 خرداد 1403ش.
- لماذا نقول "الموت لأمريكا"؟ Rubutawa game da Amurka tana da sakamako, shafin yanar gizo na Tasnim News Agency, ranar wallafa labarin: 17 Aban 1400 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya
- الكتابات على الجدران،Mujallar Nameh Noor, lamba 6 da 7, Bahman 1358 hijiriyya.
- جذور شعار "الموت لأمريكا" في تاريخ الحركة الإسلاميةCibiyar Kayan Aiki ta Juyin Juya Halin Musulunci, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- الكشف عن الجائزة الخاصة الجديدة لمهرجان عمار،Gidan Yanar Gizo na Jahan Emruz, ranar wallafa labarin: 18 Dei 1394 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.*مصير شعار استراتيجي / ماذا يقول مؤيدو ومعارضو "الموت لأمريكا"؟،KhabarOnline, 22 Mehr 1392 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- بطاقات شعار "الموت لأمريكا"، Shafin Yanar Gizo na Ofishin Kiyaye da Yada Ayukan Ayatollah Al-Uzma Khamenei, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
Ali Zadeh, Mahadi, As-sahwatul Islamiyyaعليزاده موسى Matikatul hajji, Tarihin ziyara shekara ta 1390 kalandar Farisa.
- ماذا سيحدث لشعار "الموت لأمريكا"؟، Gidan Yanar Gizo na Nazari da Labarai na Asr Iran, ranar wallafa labarin: 9 Mehr 1392 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- مصباح: كل الناس يعتبرون شعار "الموت لأمريكا" مثل التكبير بعد الصلاة، Gidan Yanar Gizo na Labarai da Nazari na Ensaf, ranar wallafa labarin: 27 Tir 1397 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- الموزاييك بتصميم "الموت لأمريكا" أيضًاMNA News Agency, 13 Bahman 1393 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.
- Mirshkari Soleimani, Razieh, Dirasatul Khalfiyyat Tarikhiyyati Li Shi'arat auratuil Islamiyya Iraniyya, Tehran, Cibiyar Imam Khomeini (RA) da Juyin Juya Halin Musulunci, shekara ta 1398 hijiriyya.
- هHidayati, Ahmad Reza، لماذا يستمر شعار "الموت لأمريكا"،Shafin Yanar Gizo na Labarai da Nazari na Alef, ranar wallafa labarin: 27 Ordibehesht 1397 hijiriyya, ranar ziyarar: 24 Khordad 1403 hijiriyya.