Farwa Bin Naufal Ash'ja'i
Mahallin rayuwa | Kufa |
---|---|
Wafati | Shekara 45 bayan hijira |
Sahabi | Sahabin Imam Ali (A.S) |
Ya ruwaito daga Ma'asumi | Annabin Muslunci (S.A.W) da Imam Ali (A.S) |
Shahara | Ya kasance daga Khawarijawa |
Farwa Bin Naufal Ashja'i (Larabci: Samfuri:Larabci) Marawaicin Hadisi, Ana ɗaukarsa shi ɗaya daga cikin sahabban Imam Ali (A.S), kamar yadda ya halarci yaƙin Siffin da shi, Sai dai ya kasance a ɓangaran Khawarijawa ne bayan sulhu, Bayan ya halarci yaƙin Naharawan, sai ya janye daga fagen fama tare da sahabbanshi ɗari biyar, Bayan shahadar Imam Ali (A.S) ya fita yaƙi da Mu'awiya, amma daga karshe Muawiyah ya ci nasara a kanshi, inda ya yi amfani da Kufawa wajen tunkarar shi. An kashe Bin Naufal a shekara ta 45 bayan hijira.
Wane ne Bin Naufal Da Kuma Matsayinshi
Kamar yadda wasu masu bincike suka ce Farwa ɗan Naufal Al-Ashja'i ya kasance daga mutanen Kufa,[1] kuma mai rawaito hadisi,[2] kuma ɗaya daga cikin Tabi'ai[3]. ya ruwaito hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) da ba'arin sahabbai,[4] akwai ra'ayoyi da maganganu kansu shin ɗan Naufal ana ganin shi cikin sahabban Annabi ne ko kuwa a a?.[5] Kamar yadda wasu bayanai suka nuna cewa Farwa ɗan Naufal yana daga cikin sahabban Imam Ali (A.S) kuma ya kasance cikin sansanin Imam Ali a lokacin yaƙin Siffin, kuma ya yi yaƙi tare da Imam (A.S) a kan Mu'awiya.[6]
Sahabin Imam Ali (A.S) Kuma Shugaban Khawarijawa
Kamar yadda malamin tarihi na Shi'a Rasul Jafariyan ya ce, a cikin mas'alar Tahkim Farwa ɗan Naufal na ɗaya daga cikin waɗanda suka zo wurin Imam Ali, kuma ya neme shi da kada ya zaɓi Abu Musal Ash'ari don yin hukunci.[7] Amma bayan da aka zabi Abu Musal Al-Ash'ari don yin sulhu da abubuwan da suka faru a cikinsa, sai Farwa ya kau da kai daga Imam Ali (A.S), ya koma cikin Khawarijawa, daga baya ya zama ɗaya daga cikin Jagororinsu.[8] Dangane da abin da Al-Balazuri ya ruwaito a cikin Ansab Al-Ashraf, Farwa ɗan Naufal ya yi niyyar barin yaƙin Nahsrawan tare da magoyan bayanshi su 500.[9] Ya bayyana a lokacin cewa bai gane dalilin da ya sa ya fuskanci Imam Ali (A.S) ba, alhalin shi waliyin Allah ne, kuma shi halifan Manzon Allah ne, (S.A.W) wasiyinshi, dan uwanshi,[10] Ya yi imani da cewa suna da zabi biyu, bayan sun isa ga sakamako na karshe: ko dai su yi biyayya ga Ali (A.S), ko kuma su fuskance shi.[11]
Kamar yadda ya zo a cikin littafan tarihi, bayan shahadar Imam Ali (A.S) Farwa ɗan Naufal ya ga cewa lokaci ya yi da za a yi jihadi a kan Mu'awiya bayan Mu'awiya ya karbi halifanci daga Imam Hasan (A.S).[12] Sai Farwa ya tashi a kan Mu'awiya, sai Mu'awiya ya nemi Imam Hassan (A.S) da ya taimaka da ya murkushe boren Farwa da wadanda suke tare da shi, sai Imam Hassan ya ƙi amincewa da bukatarshi, don haka ne aka tilasta wa Muawiya ya haɗa dakaru don tunkarar Naufal, amma ya kasa cin galaba a kanshi.[13] Mu'awiya ya tilastawa mutanan Kufa yaƙar Khawarijawa.[14] Khawarijawa sun sha kashi da rashin nasara ƙarƙashin jagorancin Bin Naufal, kuma an kashe Farwa ɗan Naufal a shekara ta 45 bayan hijira.[15]
Bayanin Kula
- ↑ "Al-Amini, Ashab Amir Al-Mu'minin (a.s) wa ruwat anhu, Juzu'i na 2, shafi na 467
- ↑ "Al-Nuri, Mustadrak Al-Wasa'il, Juzu'i na 4, shafi na 291; Ibn Sa'ad, Al-Tabaqat Al-Kubra, Juzu'i na 2, shafi na 265."
- ↑ "Al-Amini, Ashab Amir Al-Mu'minin (a.s) wa ruwat anhu, Juzu'i na 2, shafi na 467
- ↑ "Nazim Zadeh Qomi, Ashab Imam Ali (a.s), Juzu'i na 2, shafi na 952."
- ↑ "Ibn Hajar, Al-Isabah, Juzu'i na 5, shafi na 280."
- ↑ "Al-Munqari, Waq'at Siffin, shafi na 286."
- ↑ "Ja'fariyan, Hayat Fikri wa Siyasi A'imma (a.s), shafi na 104."
- ↑ "Ja'fariyan, Hayat Fikri wa Siyasi A'imma (a.s), shafi na 104."
- ↑ "Al-Baladhuri, Ansab Al-Ashraf, Juzu'i na 2, shafi na 371."
- ↑ "Ibn A'tham Al-Kufi, Al-Futuh, shafi na 745.
- ↑ "Nazim Zadeh Qomi, Ashab Imam Ali (a.s), Juzu'i na 2, shafi na 952."
- ↑ "Al-Nuwairi, Nihayat Al-Arab fi Funun Al-Adab, Juzu'i na 20, shafi na 272; Ibn Al-Athir, Al-Kamil fi Al-Tarikh, Juzu'i na 3, shafi na 409."
- ↑ "Al-Nuwairi, Nihayat Al-Arab fi Funun Al-Adab, Juzu'i na 20, shafi na 273."
- ↑ Wannan jumla tana nufin "Ibn Al-Athir, Al-Kamil fi Al-Tarikh, Juzu'i na 3, shafi na 409; Nazim Zadeh Qomi, Ashab Imam Ali (a.s), Juzu'i na 2, shafi na 952."
- ↑ "Al-Amini, Ashab Amir Al-Mu'minin (a.s) wa Ruwat Anhu, Juzu'i na 2, shafi na 467."
Nassoshi
- Ibn Al-Athir, Ali bin Muhammad, Al-Kamil fi Al-Tarikh, Beirut, Dar Al-Sadir, 1385 Shamsi.
- Ibn Hajar Al-Asqalani, Ahmad bin Ali, Al-Isabah fi Tamyiz Al-Sahaba, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiya, bugu na farko, 1415 Hijira.
- Ibn A'tham Al-Kufi, Ahmad bin Ali, Al-Futuh, fassara: Muhammad bin Ahmad Mustawi, gyara: Ghulamreza Tabataba'i Majd, Tehran, Kungiyar Fitarwa da Ilimin Juyin Musulunci, 1372 Shamsi.
- Al-Amini, Ashab Amir Al-Mu'minin (a.s) wa Ruwat anhu, Beirut, Dar Al-Kitab Al-Islami, bugu na farko, 1412 Hijira.
- Al-Baladhuri, Ahmad bin Yahya, Ansab Al-Ashraf, Beirut, Dar Al-Fikr, bugu na farko, 1417 Hijira.
- Ja'fariyan, Rasool, Hayat Fikri wa Siyasi A'imma (a.s) (Ruhiyar Ilimi da Siyasa na A'imma), Qom, Ansariyan, bugu na shida, 1381 Shamsi.
- Al-Munqari, Nasr bin Muzahim, Waq'at Siffin, gyara: Abdulsalam Muhammad Harun, Qom, Maktabat Ayatollah Al-Mar'ashi Najafi, bugu na biyu, 1404 Hijira.
- Nazim Zadeh Qomi, Sayyid Asghar, Ashab Imam Ali (a.s), Qom, Bustan Kitab, 1387 Shamsi.
- Al-Nuwairi, Ahmad bin Abdul Wahab, Nihayat Al-Arab fi Funun Al-Adab, Al-Qahira, Dar Al-Kutub wa Al-Watha'iq Al-Qawmiyah, bugu na farko, 1423 Hijira.
- Al-Nuri, Mirza Husayn, Mustadrak Al-Wasa'il, Mu'assasat Ahlul Bayt (a.s) don Raya Al-Adabi, d.t.
- Ibn Sa'ad, Al-Tabaqat Al-Kubra, d.n, 1410 Hijira/1990 Miladiya.