Jump to content

Imamiyya

Daga wikishia
(an turo daga Shi'a Imamiyya)
Wannan wani rubutu ne dangane da Shi'a Isna Ashariyya, domin bayani game da mazhabar shi'a ku duba Shi'a.
Imamiyya
Faɗaɗuwar YankiKo ina a fadin duniya
Muhimman GaruruwaKufa, Ƙum
Wuraren ZiyaraHaramin Imamai, Haramin Annabi (S.A.W), Maƙabartar Baƙi'i
Muhimman AyyukaGaibar Imam Mahadi (A.F)
GwamnatociAlu Buye, Safawiyya, Jamhuriyar Muslunci Ta Iran
Wasu SunayenShi'a Masu Imamai Goma Sha Biyu
Daga RassanMuslunci
AƙiduImamancin Imaman Shi'a
Muhimman LitattafaiKutubul Arba'a


Imamiyya (Larabci; الإمامية) ko shi'a isna ashariyya shi ne mafi girman reshe a mazhabar shi'a. A cewar `yan Shi'ar Imamiyya, shugabancin al'umma bayan Annabi nauyi ne da ke kan Imami kuma Allah ne yake naɗa Imam. A bisa hadisai kamar hadisin Ghadir, `yan Shi'a Imamiyya suna ganin Ali bin Abi Talib a matsayin magajin Annabi (S.A.W) kuma Imami na farko, sun yi imani da imamai goma sha biyu, kuma sun yarda cewa limami na goma sha biyu Mahadi yana raye, sai dai ya bacewa ganin mutane saboda wasu dalilai masu yawa wanda muka sani da wanda Allah ne kaɗai ya barwa kansa sani. Zaidiyya da Ismailiyya, sauran firƙoƙin Shi'a guda biyu, ba su yi imani da dukkan imamai goma sha biyu da `yan Shi'ar Imamiyya suka yi ba, haka nan ma ba sa ganin adadin limamai ya kai goma sha biyu.

Tushen aƙidar shia imamiyya guda biyar ne: kaman ragowar musulmai sun yarda da tauhidi, Annabta, ranar Alƙiyama. Bayan waɗannan guda ukun da duk Musulmai su kai imani da su akwai wasu guda biyun da suka keɓanci ƴan shia su ne adalcin Allah da imamanci. `Yan Shi'ar Imamiyya su na yin abubuwa da dama a rayuwa, daidadi da shari'ar musulinci kamar ibada, mu'amala da kuma biyan haƙƙin Allah kaman zakka da khumusui, kamar yadda tsarin Musulunci ya tanada. Dangane da tunaninsu na tauhidi, fiƙihu, kyawawan halaye da sauransu, suna komawa ne ga Alƙur'ani da hadisan Manzon Allah (S.A.W) da Imamai goma sha biyu, da hankali da ijma'i . Sheikh Ɗusi, Allama Hilli da Shaikh Mortada Ansari na daga cikin fitattun malaman fiƙihu, sannan Shaikh Mufid, Khawaja Nasir al-Din ɗusi da Allama Hilli suna daga mashahuran malaman tauhidi na Imamiyya. A shekara ta 907 bayan hijira Shah Isma'il ya kafa gwamnatin Safawiyya ya sanya mazhabar shi'a Imamiyya a hukumance matsayin mazhaba a ƙasar Iran. Wannan gwamnati ta taka rawar gani wajen faɗaɗa mazhabar Imamiyya a Iran. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce tsarin siyasar kasar Iran a halin yanzu, wanda tsare-tsaren siyasar ƙasar ya ginu ne kan mazhabar Shi'a imamiyya . Ranar Ghadir, haihuwar Imam Ali bin Abu Ɗalib (A.S), ranar haihuwar Sayyida Fatima `yar Manzon Allah (S.A.W), da nisfu sha'aban, su ne bukukuwa mafi muhimmanci na addini musamman ga `yan Shi'ar Imamiyya. Makoki da juyayi ga ma'asumai sha biyu Musamman Imam Husaini binu Ali da sahabbansa a cikin watan Muharram na ɗaya daga cikin muhimman ayyukansu.

Babu dandaƙaƙƙen ƙididdiga na adadin `yan shi'a Imamiyya a duniya, kuma alƙaluman da ake da su sun haɗa da ƴan shi'ar Zaidiyya da `yan Shi'ar Ismailiyya. sai dai kuma wasu alƙaluma sun nuna cewa yawan mabiya Shi'a a duniya yana tsakanin mutane miliyan 154 zuwa 200, daidai da kashi 10 zuwa 13% na musulman duniya, kuma a wasu alkaluma sun haura miliyan 300, wato kashi 19% na al'ummar musulmin duniya. yawancin `yan shi'a, tsakanin kashi 68 zuwa 80 bisa ɗari, suna zaune ne a ƙasashe hudu: Iran, Iraƙi, Fakistan da Indiya.

Takaitaccen Tarihin Samuwar Kalmar Shi'a

Shi'a
Asalan Addini (Aƙidu)
Aƙidu Na Asali TauhidiAnnabtaMa'adAdalcin AllahImamanci
Sauran Aƙidu IsmaIlimin GaibuWilayaMahadawiyyaGaibar Imam Mahadi (A.F)Jiran BayyanaBayyanar Imam Mahadi (A.F)Raja'aBada'u
Rassan Addini (Hukunce-hukuncen Ayyuka)
اHukunce-hukuncen Ibada Umarni Da Kyakkyawa Da Hani Da MunkariWilayaBara'a
Hukunce-hukuncen Da Ba Na Ibada Ba Umarni Da Kyakkyawa Da Hani Da MunkariWilayaBara'a
Madogaran Ijtihadi Kur'aniSunnaHankaliIjma'i
Aklaƙ
Kyawawan Halaye Danne FushiKaramciTawakkali
Miyagun Halaye Girman KaiRiyaAnnamimanciHassada
Madogarai Kur'aniNahjul Al-balaga (Littafi)Sahifa SajjadiyyaSauran Litattafai
Mas'aloli Da Ake tafka Muhawara A Kansu
Halifancin AnnabiCetoTawassuliTaƙiyyaZaman MakokiMutu'aAdalcin Sahabbai
Manyan Mutane
Imaman Shia Imam Ali (A.S)Imam Hassan Mujtaba (A.S)Imam Husaini (A.S)Imam Sajjad (A.S)Imam Muhammad Baƙir (A.S)Imam Sadiƙ (A.S)Imam Kazim (A.S)Imam Rida (A.S)Imam Jawad (A.S)Imam Hadi (A.S)Imam Hassan Askari (A.S)Imam Mahadi (A.F)
Sahabbai Maza
Salmanul FarisiMiƙdadu Bin AmruAbu Zar GifariAmmar Yasir
Mata
Khadijatul Kubra (A.S)Sayyida Faɗima (S)Sayyida Zainab (A.S)Ummu Kulsum Ƴar Imam Ali (A.S)Asma'u Bintu UmaisiUmmu AimanaUmmu Salama Matar Annabi
Malamai اMasana AdabiاMalaman usul • • Malaman RijalMujtahidaiMalaman FalsafaMalaman Tafsiri
Wuraren Ziyara
Masallacin HaramiMasallacin AnnabiBaƙi'iMasallacin Al-AƙsaHaramin Imam AliMasallacin KufaHaramin Imam HusainiHaramin KazimainiHaramin Askariyaini (A.S)Haramin Imam RidaHaramin Ma'asumaHaramin Sayyida Zainab
Bukukuwan Addini
Idul FiɗriIdul ƘurbanIdul GhadirIdul Mab'as
Zaman Makoki
Zaman Makokin MuharramKwanakin Goman Farkon MuharramTasu'aAshuraKwanaki Goman SafarArba'in

Ranakun Fatima

Abubuwan Da Suka Faru
MubahalaWaƙi'ar GhadirWaƙi'ar SaƙifaWaƙi'ar FadakYaƙin JamalYaƙin SiffinYaƙin NaharawanWaƙi'ar Karbala
Litattafai
Al-istibsarAl-kafiTahzibul Al-ahkamMan la yahduruhul Al-faƙihu
Firƙoƙin Shi'a
ImamiyyaIsma'iliyyaZaidiyyaKisaniyya

Akwai ra'ayoyi daban-daban game da tarihin asalin samuwar Shi'a; daga cikinsu ambaci lokacin rayuwar Manzon Allah (S.A.W) bayan waki'ar Saƙifa wasu kuma suna ganin, bayan kashe Usman ne da faruwar waki'ar neman mulki tsakanin banu umayya[1] da banu hashim, abin da ٍ Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i malamin falsafa da tafsiri a shia a ƙarni na 11. . asalin shi'a wanda a farkonsa ake kiransu da "Shi'ar Ali" sun samu ne a zamanin Manzon Allah (S.A.W).[2]

Har zuwa `yan ƙarnoni zuwan muslunci, ba wai kawai ana amfani da kalmar Shi'a ga wadanda suka yi imani da imamancin imamai goma sha biyu bane kadai, A a, masoya Ahlil-baiti da waɗanda suke ganin Imam Ali (A.S) ya fi Usman, su ma ana kiransu da shi'ar Ali (A.S)[3] Mafi yawan sahabban Ahlul Baiti A.S) suna cikin wannan kashi biyun.[4]

An ce tun zamanin Sayyidina Ali (AS), akwai aƙidar Shi'a; ma'ana wasu daga cikin mabiyansa sun yi imani da cewa Allah ne ya naɗa shi Imamanci[5] Tabbas adadin wannan jama'a kaɗan ne.[6] A zamanin Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S) duk da cewa mazhabar `yan Shi'a Imamiyya ya ƙaru, amma har wannan zamani ba su kai ga a kira su da mazhabar addini ba,[7] A zamanin rayuwar Ahlul Baiti akwai ƴan shi'arsu da masoyansu masu yawan gaske. amma wasu hadisai sun nuna cewa adadin waɗanda suke ganin Allah ne ya bawa imamai imamanci basu kai mutum hamsin ba.[8] Daga ƙarshen ƙarni na uku, shi'a Imamiyya ta bambanta da sauran ƙungiyoyin shi'a. Bayan shahadar Imam Hasan Askari (A.S) wasu gungun `yan Shi'a da suka yi imani da cewa kasa ba za ta taba zama babu Imami ba, sun yi imani da samuwar Imami na goma sha biyu, sai dai ba su gan shi a zahiri ba . An san wannan ƙungiya da sunan Shi'a Imamiyya[9] ko shi'a masu Imamai goma sha biyu Daga wannan lokaci a hankali a hankali adadin wannan mazhabar shi'a ya dinga ƙaruwa, Ta yadda a cewar Shaikh Mufid, a zamaninsa wato shekara ta 373 bayan hijira, shi'a Imamiyya wato mai Imamai goma sha biyu ne suka fi yawan mabiya a cikin sauran firƙoƙin shi'a.[10]

Akidu

Ƙa'idojin aƙidar shi'a Imamiyya abubuwa guda biyar ne. Kamar sauran musulmai, sun ɗauki tauhidi da annabci da Ma'ad (Alkiyama) a matsayin Asalai da shika-shikan mazhabar su, haka nan kuma sun yi imani da ƙa'idoji biyu na imamanci da adalci waɗanda suka raba su da Ahlus-Sunna[11] A cewar su, bayan wafatin Annabi (S.A.W), ya wajaba wani mai suna Imami ya maye gurbinsa ya ci gaba da aikinsa. Sun yarda da naɗin Imami a matsayin naɗin da Allah ya yi, kuma suna cewa: Allah yana bayyana imami ga mutane ta hanyar Annabi.[12] Ƴan Shi'a Imamiyya, bisa hadisan da suka kawo daga Manzon Allah (S.A.W) sun yi imani da cewa da umarnin Allah ne ya gabatar da Imam Ali a matsayin halifansa kuma Imami na farko[13] sun yi imani da Imamai goma sha biyu a kan hakan suka kawo Riwayoyi kamar hadisin Lauhu da yake bayyana adadin imamai da Sunayensu[14] kamar haka:

  1. Ali Bin Abi Talib.
  2. Hassan Bin Ali.
  3. Husaini Bin Ali.
  4. Ali Bin Husaini (Imam Sajjad).
  5. Muhammad Bin Ali (Imam Baƙir).
  6. Jafar Bin Muhammad (Imam Sadiƙ).
  7. Musa Bin Jafar (Imam Kazim).
  8. Ali Bin Musa (Imam Rida).
  9. Muhammad Bin Ali (Imam Jawad).
  10. Ali Bin Muhammad (Imam Hadi)
  11. Hassan Bin Ali (Imam Askari).
  12. Hujjatu Bin Hassan (Imam Mahadi).[15]

A cewar shi'a Imami na goma sha biyu Mahadi yana raye kuma yana rayuwa a tsakanin mutane sai dai ba su san shi ba, shi kuma da umarnin Allah ya ɓacewa ganinsu (Gaiba_Kubra) wata rana zai Mike ya tabbatar da adalci a doran ƙasa.[16] Adalcin Allah kamar Imamanci yana ɗaya daga cikin Asalan mazhabar Shi'a, sun yi imanida koda rana ɗaya ta rage ai tashin Alƙiyama Allah ze bayyanashi kuma ze tabbatar da Adalci a doran ƙasa, san nan `yan Shi'a kamar Mu'utazila an kiransu Adliyya saboda imaninsu da adalcin Allah. A bisa aƙidar adalcin Allah, da falala da rahama ko kuma bala'i da ni'ima bisa zati da hali na mutum wanda ya aikata.[17] Raja'a da Bada'u suna daga abin da ƴan Shi'a suka yarda da su,[18] wato bayan bayyanar Imam Mahadi (A.S) wasu muminai daga ƴan Shi'a da masoya Ahlul-Baiti (A.S) da suka mutu, za a tashe su, kuma za a hukunta azzaluman wancan lokacin daidai da abin da suka aikata.[19] Abin da bada'u yake nufi shi ne Allah maɗaukakin sarki saboda wata maslaha yakan bayyanawa Annabawa ko imamai wani ilimi a wani lokaci amma daga baya sai ya canza da wani abun daidai da wannan lokacin,[20] Littattafai kamar Awa'ilul maƙalat, Tas'hihul Iitiƙad, Tajridu Al-Iitiƙad, Kashful Al-Murad, suna daga cikin manya-manyan littafan tauhidi na shi'a Imamiyya,[21] Allama Hilli (Rayuwa: 648-726.h) yana ɗaya daga cikin fitattun malaman tauhidi a Imamiyya.[22] Shaik Mufid (Rayuwa:336 ko 338-423 bayan hijira), Shaik Tusi (Rayuwa:385-460 bayan hijira), Khajo Nasirud-dini Tusi (Rayuwa" 597672 bayan hijira) duka su ma suna daga cikin fitattun malaman akida a shi'a.[23]

Bambancin Shi'a Imamiyya Da Sauran Firƙoƙin Shi'a

Har ila yau kuna iya duba: Zaidiyya da Isma'liyya

Zaidiyya da Isma'iliyya, `yan Shi'a ne da ba su yarda da Imamai goma sha biyu ba. Haka kuma ba su taƙaita adadin imamai zuwa goma sha biyu ba. Zaidiyya sun yi imani da cewa Annabi ya ƙayyade imamancin mutane uku ne kawai, wato Imam Ali (A.S) da Imam Hassan (A.S) da Imam Husaini (A.S)[24] bayan su duk lokacin da wani mutum mai zuhudu ,ƙarfin imani, baiwar hankali da kyauta kuma tsatsan manzon Allah daga ƴarsa Hazrat Zahara (S) ya miƙe da sunan Allah da nemawa mutane adalci daga hannun Azzalumai to shima imami ne.[25] Zaidu Bin Ali, Yahaya Bin Zaidu, Muhammad Bn Abdullahi Bin Hassan (Nafsu Zakiyya), Ibrahim Bn Abdullahi da Shahid Fakh na daga cikin Imaman Zaidiyya.[26] Isma'iliyya ba su yarda da imamancin Imam Hassan Mujtaba (A.S) a matsayin imami na biyu ba,[27] sun yarda da imamancin sauran limaman zuwa Imam Sadiƙ (A.S)[28] dan haka bayan Iimam sadiƙ ɗansa Isma'il da jikansa Muhammad suka yi imani da su[29] A firƙar Isma'iliyya imamanci yana da lokuta daban-daban kuma Imamai bakwai suna jagorantar mutane a kowane lokaci da zamani.[30]

Hukunce-Hukuncen Addini

A mazhabar Imamiyya kamar sauran mazhabobin Musulunci, abubuwa da yawa na rayuwar yauda kullum kamar ibada, mu'amala, haƙoƙin shari'a kamar khumusi da zakka, hajji, aure da rabon gado, wajibi ne a yi su kamar yadda shari'a ta tanada.[31] kur'ani da hadisan Imamai goma sha biyu, sune tushe da majinginar malamai wajan fidda hukunce hukuncen Shari'a a Imamiyya[32] Ana fidda hukunce-hukuncen ne da taimakon ilimin Diraya da Rijal da Usulul fikhi da Fiƙihu.[33] Litattafai misalin sharayi-Islam, Al-Lum'atu al-Dimashkiyya, Sharhu lum'ati, Jawahirul Kalam, Makasib da Al-urwa Al-Wuska su na daga cikin shahararrun littafan fiƙihun Shi'a na imamiyya,[34] Sheikh Tusi,Muhakkik Hilli ,allama hilli,shahid Auwal, shahid sani,kashiful giɗa ,mirza ƙummi da Murtada Ansari suna daga cikin fitattun malaman fikihun wan nan mazahaba ta shia imamiyya.[35]

Marja'in Taƙlidi

Tushen Kasida: Marja'in Taƙlidi

A yau ana rubuta hukunce hukuncen sharia ne a littattafan da ake kira Tauzihul Masa'il , waɗanda maraji'an taƙlidi suka rubuta,[36] marja'in taƙlidi shi ne malami Mujtahidi da ya cika wasu sharuɗɗa wanda mutane suke karɓar fatawoyin addini daga gare shi, Wato suna aiwatar da ayyukansu na addini a bisa ra'ayinsa na fiƙihu (fatawa) kuma shi suke bawa haƙoƙin shari'a ko wakilansa kamar Zakka da Khumusi.[37]

Bukukuwan Addini

Fayil:اربعین.jpg
Hoton taron makokin Arbaeen

Bayan idin ƙaramar sallah da Idin Babbar Sallah da kuma Idin aiko da Annabi (S.A.W) wadanda su ne bukukuwan addini na dukkan Musulmi, Idul Ghadir, Maulidin Imam Ali (A.S), Maulidin Hazrat Fatima (S), da Nisfu Sha'aban su ne muhimman bukukuwan addini na `yan Shi'a Imamiyya. Suna kuma murnar zagayowar ranar haihuwar sauran imamansu.[38] A cikin mazhabar imamiyya, ana son gudanar da ayyuka na musamman na addini a kowane biki; Misali a ranar babar sallah ana son yin ayyuka kamar Wanka, Sallar Idin Babbar Sallah, Layya karanta Ziyarar Imam Husaini (A.S) da addu'ar da ake kira Du'a'u Nudba.[39] A wasu ranaku na shekara, `yan Shi'a na gudanar da zaman makoki domin nuna Kauna ga waɗanda aka kashe daga Imamai, da kuma nuna alhininsu a cikin wahalhalun da suka sha tare da Sahabbansu, Muhimman zaman makoki na `Yan Shi'a ana gudanar da su a kwanaki Goman farkon Watan Muharram, da Goman karshen Watan Safar, Arba'in da kuma kwanakin Fatimiyya.(Shahadar ƴar manzon Allah sayyada Fatima (S)[40] Addu'o'in Ziyarar Manzon Allah (S.A.W) da Ahlul Baiti (A.S) na ɗaya daga cikin manya-manyan ayyukan da Imamiyya suke yi[41] Kuma suna ganin ziyartar ƙabarurrukan ƴaƴan Imamai da sauran manyan malaman addini a matsayin abu mai muhimmanci,[42] a littattafan Riwayoyi na Shi'a an bawa Addu'o'i da Tawassuli muhimmanci sosai, kuma an kawo wasu addu'oi masu girma da falala daga manzon Allah da Ahlulbait,[43] Daga cikin mashahuran addu'o'i da ziyarorin Imamiyyah akwai: Du'a'u Kumaili,[44] Du'a'u Arfa,[45] Du'a'u Nudba.[46] Munajat Sha'abaniyya,[47] Du'a'u Tawassul.[48] Ziyarar Ashura,[49] ziyarar Jami'a kabira[50]da kuma Ziyaratu Aminullahi.[51]

Madogaran Tunani A Wurin `Yan Shi'a Imamiyya

Ƴan Shi'a imamiyya suna dogaro da Alkur'ani, Riwayoyi, Hankali, da Ijma'i, wajan fahimtar iliman tauhidi, fiƙihu, Akhlaƙ da sauran su,[52]

  • Kur'ani
Tushen Kasida: Kur'ani

Ƴan Shi'a Imamiyya sun ɗauki Alƙur'ani a matsayin tushen farko kuma mafi muhimmanci na koyar da ilimin addini. Muhimmancin Alƙur'ani a wajansu shi ne, idan wata ruwaya ta saɓawa Alƙur'ani ba za ta inganta ba,[53] A cewar Muhammad Hadi Ma'arifat, duk Yan Shi'a sun ɗauki Alƙur'anin da yake hannunsu a yau a matsayin daidai kuma cikakke[54]

  • Hadisan Annabi Da Imamai.
Tushen Ƙasida: Hadisi

Imamiyyah kamar sauran mazhabobin Musulunci suna daukar Sunnar Annabi (S.A.W) wato maganarsa da ayyukansa a matsayin hujja.[55] `Yan Shi'ar Imamiyya sun ɗau wasu hadisai kamar Hadis Saƙlaini da Hadis Safina, waɗanda suka yi umarni da a komawa ga Ahlil Baiti (A.S) a bi su sau da ƙafa. Haka nan kuma suna ɗaukar hadisan Ahlul-Baiti a matsayin ɗaya daga cikin manyan tushen tunaninsu na addini.[56] Sun mai da hankali sosai wajen rubuta hadisan Annabi da Imamansu goma sha biyu.[57] Muhimman litattafan riwaya na ƴan Shi'a su ne :AlKafi, Tahzeeb Al-Ahkam, Istibsar da Manla yahdiruhu Alfakihu, waɗanda ake ce wa littattafan Arbaa ko Usul Arba'a.[58]Sauran shahararrun littattafan hadisan Shi'a sun hada da: kutubul Arba'a Al-Wafi, Bihar-Anwar, Wasa'il_Shi'a,[59] Mustadrak, Mizanul Al-Hikma, Jami'u-Ahadis Shi'a, AlHayat da wa Asrarus-Sadiƙain.[60] `Yan Shi'a ba sa ganin kowane hadisi a matsayin ingantacce. Suna la'akari da ma'auni kamar rashin saba wa Alƙur'ani, amincin Marawaita, da Tawatiri, don haka suke amfani da ilimi kamar Diraya da Rijal[61]

  • Hankali
Tushen Makala: Hankali

Hankali ma'auni ne kuma yana da matsayi na musamman a mazhabar Imamiyya. shi'a Imamiyya suna komawa ga hankali don tabbatar da Asalan Aƙidu,[62] Kuma suna amfani da shi wajan fitadda hankali a matsayin tushen hukunce- hukuncen Shari'a,[63]

  • Ijma'i
Tushen Kasida: Ijma'i

Ijma'i yana ɗaya daga cikin tushe hudu na Istinbadi ciro hukunce-hukuncen Shari'a, kuma an yi magana a kai a cikin ilimin Usulul fikihi ta bangarori daban-daban.[64] Malaman Shi'a ba kaman na Ahlus-sunna bane wajan amfani da ijma'i a a matsayin dalilin hukunce hukuncen kaman Alƙur'ani, sai dai suna ɗaukarsa su yi amfani da shi ne a matsayin labarin da ya zo a zamanin ma'asumai cewa malaman wancen lokacin sun haɗu akan wani hukunci kuma Ma'asumi ya yarje musu.[65]

Gwamnatoci

An kafa gwamnatocin Shi'a da dama a Duniyar Muslunci, daga cikinsu akwai gwamnatocin Alawiyyawan Tabaristan, Alu-Buwaihi, Fatimiyya, Isma'iliyya da Safawiyya. Zaidiyawa ne suka kafa gwamnatin Alawi,[66] gwamnatocin Fatimiyyawa da Isma'iliyya na Ale-mauti sun ginu a kan firƙar Isma'iliyya;[67] amma akwai sabanin ra'ayi dangane da Alu-buwaihi. Wasu suna ganin cewa su firƙar Zaidiyya ne, wasu suna ganin Imamiyya ne, wasu kuma suka ce a farkon su ne mazhabar Zaidiyya sannan suka koma ga Imamiyya.[68] Sultan Mohammad Khodabande wanda aka fi sani da Uljayito (wanda ya yi sarauta a shekara ta 716-703 bayan hijira) ana ɗaukarsa a matsayin Sarki na farko da ya ayyana Imamiya a matsayin mazhabar hukumar sa[69] kuma ya yi ƙoƙarin yaɗa shianci a ko'ina, saidai daga baya ya janye daga wannan aiki saboda saɓani daya samu da ƴan sunna Amma duk da haka ya kasance dan shi'a har ƙarshen rayuwarsa.[70] Gwamnatin Sarbadaran a Sabziwar ita ma ana kiranta da gwamnatin Shi'a.[71] Amma daga baya ya tabbata cewa shugabannin wan nan hukumar Sufaye ne, sai dai su ma suna da ɗabi'un Shi'a,[72] duk da haka, Khajo Ali Mu'ayyid, wanda shi ne shugaban Sarbadaran na ƙarshe[73] ya ayyana Imamiyya a matsayin mazhabar gwamnatinsa.[74]

Safawiyyawa

Tushen Kasida: Safawiyya

Shah Isma'il ya kafa gwamnatin Safawiyya a shekara ta 907 bayan hijira,[75]sannan ya ayyana Imamanci a matsayin mazhabar ƙasar Iran a hukuma,[76] sun yaɗa mazhabar Imamiyya a tsakanin Iraniyawa kuma suka mayar da Iran ƙasa ta 'yan Shi'a gaba ɗaya.[77]

Jamhuriyar Muslunci Ta Iran

Tushen Kasida: Jamhuriyar Musulunci ta Iran

An kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne a ƙasar Iran bayan nasarar Juyin juya halin Musulunci na Iran a ranar 22 ga watan Bahman shekara ta 1357(shamsi) ƙarƙashin jagorancin Imam Khumaini.[78] An kafa hukumar kan addinin Musulunci bisa Asalan mazhabar shi'a imamiyya a gwamnatin . Kuma Wilayatul Fakihi,[79] shi ne babban maƙami me faɗa aji a ƙasar[80] kamar yadda kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya tanada, dokokin kasar ba su inganta ba idan ba su dace da addinin Musulunci ba.[81]

Yawan `Yan Shi'a A Duniya

Babu takamammen ƙididdiga na adadin `yan Shi'a Imamiyya a duniya, sai dai kuma alƙaluman da ake da su sun hada da Zaidiyya da `yan Shi'ar Isma'iliyya. A cikin rahoton Pew Religion and Public Life Association, an ƙiyasta adadin `yan Shi'a a duniya tsakanin mutane miliyan 154 zuwa 200, wanda ya kai kashi 10 zuwa 13 na musulmin duniya;[82] amma mai fassara wannan rahoton. ya yi la'akari da wannan ƙididdiga ba gaskiya ba ne, kuma ya ƙiyasta cewa yawan mutanen Shi'a ya haura sama da miliyan dari uku, wato kashi 19% na al'ummar Musulmin duniya.[83]

Yawancin 'yan Shi'a, tsakanin kashi 68 zuwa 80 bisa ɗari, suna zaune ne a ƙasashe hudu: Iran, Iraki, Pakistan da Indiya. 'Yan Shi'a miliyan 66 zuwa 70 ne ke zaune a Iran, wanda ya kai kashi 37 zuwa 40 na dukkan 'yan Shi'a a duniya. Kowace kasa Pakistan, Indiya da Iraki tana da mabiya Shi'a sama da miliyan 16.[84] A ƙasashe hudu , Iran, Azarbaijan, Bahrain, da Iraƙ, `yan Shi'a su ne mafi yawan al'ummar ƙasar.[85] Akwai kuma `yan Shi'a da ke zaune a yankuna irin su Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka, yankin Asiya-Pacific, Turkiyya, Yaman, Siriya, Saudiyya, Amerika, da Kanada.[86]

Bayanin kula

  1. Muharrami, Tarikh Shia, 2013, 43, 44; Sashen Tarihin Jami'ar da Cibiyar Nazarin Hozah, Tarihin Shi'a, 2009, 20-20; Fayyaz, asali da fadada shi'anci, 2002, shafi na 49-53.
  2. Tabatabai, Shi'eh dar Islam 1379, shafi na 25.
  3. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Aagz ta Tulu'i Daulat Safawi, 1390, shafi na 22, 27.
  4. Fayyaz,Faidayesh wa Gustareshe Tashayyu, 2013, shafi na 61.
  5. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Aagz ta Tulu'i Daulat Safawi, 1390, shafi na 30
  6. Fayyaz,Faidayesh wa Gustareshe Tashayyu, 2013, shafi na 61
  7. Fayyaz,Faidayesh wa Gustareshe Tashayyu, 2013, shafi na 63-65
  8. Fayyaz,Faidayesh wa Gustareshe Tashayyu, 2013, shafi na 62
  9. Fayyaz,Faidayesh wa Gustareshe Tashayyu, 2013, shafi na 109-110
  10. Sayyid Morteza, Al-Fusul Al-Mukhtara, 1413 AH, shafi na 321.
  11. Motahari, Majmu'eh Asar, 2009, juzu'i na 3, shafi na 96.
  12. Mesbah Yazdi, Amuzeshe Akayid, 2004, shafi na 14.
  13. Allameh Tabatabai, Shi'eh dar Islam , 1379, shafi na 197, 198.
  14. Allameh Tabatabai, Tashayyu dar Islam , 1379, shafi na 197, 198
  15. Allameh Tabatabai, Shi'eh dar Islam , 1379, shafi na 198, 199
  16. Allameh Tabatabai, Shi'eh dar Islam , 1379, shafi na 230-231
  17. Motahari, Majmu'eh Asar, 2009, juzu'i na 3, shafi na 96.
  18. Rabbani Golpayegani, Dar'amad be Shi'eh Shinashi, 1392, shafi na 273; Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 106.
  19. Rabbani Golpayegani, Dar'amad be Shi'eh Shinashi, 1392, shafi na 273
  20. Tabatabaei, Al-Mizan, 1393 AH, Juzu'i na 11, shafi na 381; Shaykh Mofid, Tahih al-Ithaqad, 1413H, shafi na 65.
  21. Kashfi, Kalam Shia, 2007, shafi na 52.
  22. Kashfi, Kalam Shia, 2007, shafi na 52.
  23. Kashifi, Kalam Shia, 2007, shafi na 52.
  24. Saberi, Tariku Firakul Ilsami , 2008, juzu'i na 2, shafi 86.
  25. Allameh Tabatabai, Shi'eh dar isalm , 1379, shafi na 167.
  26. Saberi, Tariku Firakul Ilsami, 2008, juzu'i na 2, shafi 90
  27. Saberi, Tariku Firakul Ilsami, 2008, juzu'i na 2, shafi 119
  28. Saberi, Tariku Firakul Ilsami, 2008, juzu'i na 2, shafi 110
  29. Saberi, Tariku Firakul Ilsami , 2008, juzu'i na 2, shafi 110
  30. Saberi, Tariku Firakul Ilsami , 2008, juzu'i na 2, shafi 151-156
  31. Makarem Shirazi, Dayiratu Maref Fiqh Makarn, 1427 AH, Mujalladi na 1, shafi na 65-69.
  32. Muzaffar, Uusulu Fikhi, 1430 q., Part 1, shafi na 54, 64.
  33. Makarem Shirazi, Dayiratu Maref Fiqh Makarn, 1427 AH, Mujalladi na 1, shafi na 176. 323-330
  34. Makarem Shirazi, Dayiratu Maref Fiqh Makarn, 1427 AH, Mujalladi na 1, shafi na 261-264
  35. Makarem Shirazi, Dayiratu Maref Fiqh Makarn, 1427 AH, Mujalladi na 1, shafi na 260-264
  36. Yazdani, "Murur Bar Risalahaye Ilmiyyeh", shafi 292, 292.
  37. Rahmansataish, Taklid 1”, shafi na 789.
  38. Musapour, "Jashanahaye Jahan Islam", shafi na 373-376.
  39. Majlesi, Zad al-Maad, 2009, shafi na 426, 427.
  40. Mazaheri, “Azadari”, shafi na 345.
  41. Fuladi da Nowrozi, “Jayigahe ziyarat dar Ayineh Katolik wa Mazhab Shi'eh ", shafi 29, 30.
  42. مفهوم زیارت و جایگاه آن در فرهنگ اسلامی، سایت راسخون، ۱۳ دی ۱۳۹۴ش، دیده‌شده در ۱۶ اردیبهشت ۱۳۹۶ش.
  43. Duba Sheikh Abbas Qomi, Mufatih al-jinan, lissafin littafin.
  44. Hashemi Aghdam, "Asrar al-Arifin Ba-Sharh Du'a'u Kumail", shafi na 32.
  45. Mahalati, "Barasi Tadbiki Du'a'u Arafa Imam Husaini wa Imam Sajjad", shafi na 107.
  46. Ref: Mahdipour, "Ba-Du'a'eh Arafa dar Fagahe Jum'eh"
  47. Heydarzadeh, “Dar Mahdare Munajat Sha'abaniya” shafi na 160.
  48. فضیلت و کیفیت دعای توسل، سایت باشگاه خبرنگاران جوان، ۲۲ آذر ۱۳۹۵، دیده‌شده در ۱۶ اردیبهشت ۱۳۹۶.
  49. Rezaei, "Fajuhi dar Asnad wa-nuskahaye ziyarat Ashura", 153.
  50. Nagareshe Maudu'i bar Ziyaratu Jami'a Kabira shafi na 150
  51. Duba Sheikh Abbas Qomi, Mufatih al-jinan, karkashin Ziarat Aminullah.
  52. Muzaffar, Usulul Fiqhi, 1430 q., Part 1, 51.
  53. Duba Rabbani Golpayegani, Dar-Amad be Shi'eshinasi , 1392, shafi 115, 116.
  54. Ma'arifat Attamhid, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 342.
  55. Duba Rabbani Golpayegani, Dar-Amad be Shi'eshinasi , 1392, shafi na 115- 124
  56. Duba Rabbani Golpayegani, Dar-Amad be Shi'eshinasi , 1392, shafi na 115, 133-135
  57. Mahdavi Rad, “Sairu Intikal Mirase Maktub shieh dar ayineh fihrisat Gadon Shi’a a Aina Fahrist,” shafi na 140.
  58. Moadeb, Tariku Hadis, 2008, shafi na 86
  59. Moadeb, Tarik Hadis, 2008, shafi na 129.
  60. Moadeb, Tarik Hadis, 2008, shafi na 148-156
  61. Allameh Tabatabai, Shi'eh dar Islam, 1379, 128, 129.
  62. Rabbani Golpayegani, Dar'amad Shi'eh, 1392, shafi na 139.
  63. Rabbani Golpayegani, Dar'amad Shi'eh, 1392, shafi na 144-145
  64. Duba Sheikh Ansari, Faraid al-Asul, 1428H, juzu'i na 2, shafi na 179-229
  65. Muzaffar, Usulul Fikhi, 1430 q., juzu'i na 3, shafi na 103.
  66. Chalongar da Shahmoradi,Daultahaye Shi'eh dar Tarik, 1395, shafi na 51.
  67. Chalongar da Shahmoradi,Daultahaye Shi'eh dar Tarik, 1395, shafi na 155-157
  68. Chalongar da Shahmoradi,Daultahaye Shi'eh dar Tarik, 1395, shafi na 125-130
  69. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na 694.
  70. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na
  71. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na 694
  72. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na 777-780
  73. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na 778
  74. Jafarian, Tarik Tashayyu dar Iran aza Agaz ta Tulu'i Daulat SAfawi , 1390, shafi na 781
  75. Hayines, Shi'i, 2009, shafi na 156 da 157.
  76. Foroughi, Karkard Marasim Sogwari Ashura dar Rashmi Shodani Mazhab Shi'eh, 67-68.
  77. Chalongar da Shahmoradi, Daulathayeh Shi'eh dar Tarik, 1395, shafi na 276, 277.
  78. Ghasemi da Karimi, "JamhuriyEH Islami Iran ", shafi na 765.
  79. Ghasemi da Karimi, "JamhuriyEH Islami Iran ", shafi na 768.
  80. Ghasemi da Karimi, "JamhuriyEH Islami Iran ", shafi na 768.
  81. Ghasemi da Karimi, "JamhuriyEH Islami Iran ", shafi na 768.
  82. Anjumaneh Zindagi Umumi PEW Nakashe jam'iyyat Muslimanan Jahan,, 2014, shafi 19.
  83. Anjumaneh Zindagi Umumi PEW Nakashe jam'iyyat Muslimanan Jahan,, 2014, shafi 11
  84. Anjumaneh Zindagi Umumi PEW Nakashe jam'iyyat Muslimanan Jahan,, 2014, shafi 19
  85. Anjumaneh Zindagi Umumi PEW Nakashe jam'iyyat Muslimanan Jahan,, 2014, shafi 20
  86. Anjumaneh Zindagi Umumi PEW Nakashe jam'iyyat Muslimanan Jahan,, 2014, shafi 19-20

Nassoshi

  • Anjumam Zindagi Umunmi Pew Nakashe Muslimaneh Jahan. Mahmoud Taghizadeh Davari ya fassara, Qum,
  • Publications Science na Shi'a, bugun farko, 1393.
  • Ansari, Morteza, Faraed al-Usul, Qum, Majma al-Fikr al-Islami, bugu na 9, 1428H.
  • Jafarian, Rasul, Taril Tashayyu dar Iran Az Agaz Ta Tulu'i Daulat Safawi, Tehran, Alam, bugu na hudu, 1390.
  • Chalongar, Mohammad Ali da Seyyed Masoud Shahmoradi,Daulathayeh Shi'eh dar Tarik, Qom, Cibiyar Bincike na Kimiyya da Al'adun Musulunci, bugu na farko, 1395.
  • Heydarzadeh, Abbas, " Dar Mahdare Munajat Sha'abaniye", Payam Scientific and Cultural Quarterly, No. 106, 2013.
  • Rahmansataish, Mohammad Kazem, "Taklid, Tehran, Islamic Encyclopaedia Foundation, bugun farko, 1382.
  • Rabbani Golpayegani, Ali, Dar-amad Shi'ehshinasi , Qum, Cibiyar Fassara da Buga Al-Mustafa ta Duniya, bugu na 4, 1392.
  • Rezaei, Mohammad Jaafar, Fajuheshi dar Asnad wa-nuskahaye ziyarat Ashura "", Ilimin Hadisi, shafi na 49, 50, 1387.
  • Seyyed Morteza, Al-Fusul al-Mukhtarah Man al-Ayoun da Al-Mahasen, Qom, Al-Khangir al-Alami na Alfiyyah al-Shaykh al-Mufid, bugu na farko, 1413H.
  • Foroughi, Asghar, Karkard Marasim Sowari Ashura dar Rasmi Shodan Mazhab Tashayyu dar zaman Safawiyeh, Mujallar Meshkwah, No. 81, Winter 2002
  • Fuladi, Mohammad, Mohammad Javad Norouzi,Jayigahe zoyarat Katolika wa-Mazhab Shi'eh, Marafet Adian, No. 25, 1394.
  • Fayyaz, Abdullah,Faidayesh wa Gustaresh tashayyu, Seyyed Javad Khatami ya fassara, Sabzevar, Ibn Yamin Publications, bugun farko, 1382.
  • Qomi, Abbas, Mofatih al-Jannan, Kum, Osweh Publishing.
  • Kashfi, Mohammad Reza, Kalam Shi'eh Mahiyat Muktassat wa Manab,Teheran, Cibiyar Buga Al'adun Musulunci da Tunanin Tunani, bugu na 3, 2007.
  • Sashen Tarihin Cibiyar Bincike na Hoza da Jami'a, Tarik Tashayyu, Qom, Cibiyar Gudanarwa na Sherran Theological Seminary, 3rd edition, 2009.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Islamic Publications, bugu na biyar, 1417H.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Shi'eh dar Islam, Qum, Ismailian, bugun farko, 1379.
  • Majlesi, Mohammad Baqer, Zadal Maad, Qom, Jaloh Kamal, 2009.
  • Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar, Tehran, Sadra Publishing House, bugu na 15, 2009.
  • Mazaheri, Mohsen Hossam, "Makoki", Azadari, Tehran, Kimeh, bugu na 1, 1395.
  • Muzaffar, Mohammad Reza, Usul Fiqh, Kum, Islamic Publications, Qum, bugu na biyar, 1430H.
  • Marfat, Mohammad Hadi, Al-Tamhid fi Ulum al-Qur'an, Qom, Al-Nashar al-Islami Foundation, bugu na farko, 1412H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Dayiratu Maref Fiqh Makarin, Qum, Makarantar Imam Ali bin Abi Talib (a.s.), bugu na farko, 1427H.
  • Mehdipour, Ali Akbar, "Ba Du'a Nudba dar Faga Juma'eh", Maud, No. 16, 1378.
  • Najafi, Nafiseh, "Tsarin Jigo na Aikin Hajji na Babban Al'umma", Safina, Mujalladi 26, 2009.
  • Moadeb, Reza, Tarik Hadis, Qom, Al-Mustafa International Translation and Publishing Center, bugu na biyu, 2008.
  • Hashemi Aghdam, Laiya, "Asrar Arifin ba Sharh Du'a Kumail", Littafin Mah Din, shafi 120, 211, 122, 2006.
  • Yazdani, Abbas, “Mururi bar Risalehaye Ilmiyyeh (2)”, Sabon Bincike a Fiqihu, Mujalladi na 15 da 16, 1377.
  • Hallam, Hayines, Tashayyu, Mohammad Taghi Akbari ya fassara, Qom, Adian Publishing House, bugu na biyu, 2009