Ziyarar Imam Husaini (A.S)

Daga wikishia
File:Masallacin Juma'a na Korram shahar

Ziyarar Imam Husaini (A.S) (Larabci: زيارة الإمام الحسين (ع)) tana daga ayyuka mafi falala a wurin ƴan Shi’a, cikin litattafan riwaya an ambaci lada mai yawa tarin kan wannan Ziyara, daga jumlarsu Alfaharin da Allah yake yi da Maziyarta Imam Husaini (A.S) da kuma Addu’ar Annabi (S.A.W) da Imamai ga Maziyartan Imam Husaini, ana iya ziyartar Imam Husaini (A.S) daga nesa cikin Misalin yi masa Sallama da karanta Ziyara ga waɗanda ba su samu halarta inda yake kwance ba, haƙiƙa yin hakan yana cikin ayyukan mustahabbi kuma a bada lada daidai da wanda ya ziyarci ƙabarinsa.

Shaik Hurrul Amili tare da dogara da riwayoyin da aka naƙalto dangane da ziyartar Imam Husaini (A.S) yana ganin ziyartarsa matsayin Wajibi Kifa’i (idan wani ya yi ya sauke saura). An ambaci ladubba masu yawa cikin riwaya dangen da ziyarar Imam Husaini (A.S) kamar misalign; sanin waye Imam Husaini (A.S), Wanka, Sanya tsaftataccen Tufafi, Neman izinin shiga Haraminsa daga wurin Allah da kuma karanta ziyararsa suna daga ladubban da aka ambata, haka zalika ziyartarsa tare da tattakawa ƙafa babu Takalmi shima yana daga ladubban ziyartar Imam Husaini (A.S) da ƙarfafawa kan batunsu ya zo cikin riwayoyin Shi’a, Manya-manyan Malamai misalign Shaik Murtada Ansari da Shaik Jafar Kashiful Giɗa sun kasance suna kiyaye waɗannan ladubba a lokacin ziyarar Arba’in ta Imam Husaini (A.S) a wannan zamani Tattakin Ziyarar Arba’in ya zama ɗaya daga Muhimman Ibadu a wurin ƴan Shi’a, Miliyoyin Mutane suka halartar wannan taro. Cikin Masadir ɗin hadisi na Shi’a an naƙalto ziyarori misalin Ziyaratu Waris da Ziyaratu Nahiya Muƙaddasa da Kuma Ziyaratu Ashura ga Imam Husaini (A.S), an yi wasicci da ziyarar Imam Husaini (A.S) a ranakun Arfa, Ashura, Tsakiyar Sha’aban da kuma ranakun cikin watan Rajab. Kan asasin rahotanni daga Masadir ɗin Tarihi, farkon wanda ya fara tattakawa zuwa ziyartar Imam Husaini (A.S) shi ne Jabir Bn Abdullahi Ansari, ba’arin Halifofin Abbasiya misalin Haruna da Mutawwakil sun yi bakin ƙoƙarinsu cikin hana ziyarar Imam Husaini (A.S) kishiyar haka, haƙiƙa a zamanin Hukumomin Alu Buwaihi da Safawiyya da ƙajariyyawa sun bada umarnin faɗaɗa ginin Haramin Imam Husaini (A.S)\

Matsayi Da Muhimmanci

Ziyarar Imam Husaini (A.S) da hallara cikin Haramin Imam Husaini (A.S) [1] yin wasu ayyukan ibada misalin Sallama da gaisuwa da karanta ziyararsa. [2] na’am wasun lokutan ana iya karanta ziyararsa daga nesa. Kan asasin riwayoyi masu tarin yawa da aka rawaito daga Annabi (S.AW) [3] da Imaman Shi’a [4] haƙiƙa ziyarar Imam Husaini (A.S) a Karbala tana daga mafi falalar ayyukan ibada. [yadasht 1] Ba’arin falalolin ziyarar Imam Husaini (A.S) da aka yi ishara zuwa gare su a cikin riwayoyi sun kasance kamar haka: ladan ziyartarsa daidai da yake da ladan ziyartar Allah a Al’arshi, Alfaharin Allah da Maziyartan Imam Husaini (A.S), Maƙotaka da Annabi (S.A.W) Imam Ali (A.S) da Hazrat Fatima (A.S) Annabi da Imamai (A.S) suna Addu’ar alheri ga Maziyarcinsa, Kyakkyawan ƙarshe, ƙaruwar arziƙi da tsawaitar rayuwa ga Mai ziyartar Imam Husaini (A.S) [5] A ba’arin litattafan hadisi akwai Fasalai da taken wajabcin ziyartar Imam Husaini (A.S) daga jumlar litattafan akwai littafin Al-Mazar talifin Shaik Mufid. [6] Shaik Hurrul Amili Tafsilu Wasa’ilul Shi’a ya kawo riwayoyi kan kasancewar ziyarar Imam Husaini (A.S) Wajibi Kifa’i (idan wasu suka je sun saukewa saura) [7]

Taƙaitaccen Tarihi

Cikin litattafan riwayoyi na Shi’a an kawo rahoto dangane da girmama mahallin da Imam Husaini (A.S) ya yi shahada a cikinsa, an nakalto su tun kafin zuwan Muslunci. [8] kan asasin wata riwaya daga Imam Ali (A.S) lokacin da yake dawowa daga Yaƙin Siffin, ya tunatar da Waƙi’ar Karbala kuma ya yi kuka. [9] Kan asasin rahotannin Tarihi, Mutum na farko da ya fara zuwa Karbala ziyartar Imam Husaini (A.S) tun bayan Shahadarsa ya kasance Jabir Ibn Abi Abdullahi Ansari tare da Aɗiyyatu Ufi bayan kwanaki Arba’in da yin shahadarsa ya taso daga Madina zuwa Karbala. [10] Sayyid Ibn ɗawus cikin littafin Luhuf ya tafi kan cewa Hazrat Zainab (S) tare da Sauran Fursunonin Karbala ta kai kanta Karbala a wannan rana. [11] wasu suna ganin farkon wanda ya fara ziyartar Imam Husaini (A.S) ya kasance Ubaidullahi Bn Hurrul Ju’ufi. [12] A zamanin Umayyawa duk da tsanantawar da suke kan Maziyartan Imam Husaini (A.S) mutane ba su dena zuwa ziyararsa ba. [13] Uƙbatu Bn Amru Sahmi, Mawaƙin Larabawa a ƙarshe-ƙarshen ƙarni na farko ya rera waƙar Makoki da Ta’aziyya ga Imam Husaini (A.S) [14] [yadasht 2] tare da dukkanin tsanantawar Banu Umayya ba su ruguje Hubbaren Imam Husaini (A.S) ba. Amma wasu ba’ari daga Halifofin Abbasiyawa daga jumlarsu akwai Haruna da Mutawakkil sun sa a ruguje Hubbaren Imam Husaini (A.S) Mutawakkil Abbasi bayan ruguje hubbaren da ya yi ya sa an kwarara ruwa kan ƙasar Maƙabarta don sauya wurin zuwa Gonar Noma. [15] kishiyar wannan a zamanin Mulkin Hukumomin Alu Buwaihi, Jallayiran, Safawiyya da ƙajariyyawa sun miƙe kan faɗaɗa ginin Hubbaren. [16] Ibn Baɗuɗa wanda ya rayu tsakanin shekaru 703-779. [yadasht3] ya bada labarin ziyartar ƙabarin Imam Husaini (A.S) da yanda ya ga ana bada abinci ga Maziyarta a gefan Hubbaren da sauran abubuwa da suka haɗa da ladubba da kuma irin girmamawar da ƴan Shi’a suke yi ga Hubbaren. [17] Ibn Sabbag wanda ya mutu shekara ta 855 h ƙamari, shima ya bada labara game da faɗaɗa hubbaren a ƙarni na tara h ƙamari. [18]

Ladubban Ziyara

An yi wasicci cikin riwayoyi dangane da yaya za a yi ziyarar Imam Husaini (A.S), kan asasin waɗannan riwayoyi, akwai sanin Haƙƙin Imam Husaini (A.S), Iklasi, halarto da zuciya da baƙin ciki suna daga ladubban ziyara da kuma Wankan ziyara, [19] Sanya tsaftataccen Tufafi, [20] kada ayi amfani da Turare Mai ƙamshi da kuma Ado, [21] [yadasht 4] kiyayre yin shiru, [22] kamar yanda ya zo cikin littafin Kamilul Az-Ziyarat akwai wani babi ɗauke da taken abubuwa da Makruhi ne kasancewa tare da a hanyar zuwa ziyarar Imam Husaini (A.S) misalin ɗauka ƙayataccen abinci da Alawowi da kayan zaƙi, kan asasin riwayar da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S): kada ku je ziyarar Imam Husaini (A.S) alhalin kuna tare da ƙayataccen abinci, bari dai ku je ziyararsa kuna halin tuburbuɗuwa da ƙasa kanku buɗu-buɗu baku taje ba. [23] a nemi iznin shiga Haraminsa da wurin Allah da Ahlil-Baiti (A.S) [24] haka kuma a karanta ziyarori misalin Ziyaratu Al-Jami’atul Al-Kabira. [25] Kan asasin riwaya daga littafin Kamilul Az-Ziyara, Imam Sadiƙ (A.S) ya yi umarni da yi sallah raka’a biyu kusa da ƙabarin Imam Husaini (A.S), cikin raka’a ta farko a karanta Fatiha da sa suratu Yasin, a raka’a ta biyu kuma a karanta Fatiha da suratu Rahman. [26]

Keɓantattun Lokutan Ziyara

Cikin riwayoyin Shi’a an yi umarni da ziyarar Imam Husaini (A.S) a ranar Arfa, [27] ranar Ashura, [28] Nisfu Sha’aban, [29] da ranakun cikin watan Rajab, [30] dare da ranar Idin Fiɗir [31] da kuma Ziyaratu Arba’in, [32]

Ziyarori

Cikin litattafan Hadisi na Shi’a an kawo Ziyarori dangane da Imam Husaini (A.S) [33] haka kuma akwai Ziyarar Imam Husaini (A.S) da Sahabbansa, [34] Ziyaratu Waris, [35] Ziyaratu Nahiya Muƙaddasa, [36] Ziyaratu Ashura, [37] Ziyaratu Rajabiyya, [38] Ziyaratu Nisfu Sha’aban da Idil Fiɗir da Idil Ad’ha da Ziyarar daren lailatul ƙadri suna daga jumlar ziyorin da suka zo. [39]

Tattakawa Zuwa Ziyara A ƙafa

Asalin Maƙala: Tattakawa Ziyarar Imam Husaini (A.S) ba tare da da Takalmi ba Akwai riwayoyi daban-daban daga Ahlil-baiti (A.S) dangane da ziyarar Imam Husaini (A.S) ƙafa babu takalmi. [40] Riwayoyin Shi’a dangane da ladan zuwa ziyarar Imam Husaini (A.S) a ƙafa babu, daga ciki akwai gafarta zunubai,an naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya fito daga gidansa da niyyar tafiya ziyarar Imam Husaini (A.S) cikin duk taku da ya yi ana rubuta masa lada, [41] Shaik ɗusi cikin littafin Tahzibul Al-Ahkam ya kawo cewa a lokacin dawowar Maziyarci da ƙafa Mala’iku suna faɗa masa daga Alƙawarin Allah, an yafe maka dukkanin zunubaka, sai ka sake sabon aiki. [42] A yanzu tattakin Arba’in ya zama muhimmiyar Ibada a wurin ƴan Shi’a, kowacce shekara a lokacin Arba’in ɗin Imam Husaini (A.S) Milyoyin Mutane suna tattaki zuwa Haraminsa, ya zama babban taron addini na duk duniya. [43]

Ziyara Daga Nesa

An yi wasicci da yin Ziyarar Imam Husaini (A.S) daga nesa kuma tana daga ayyukan Mustahabbi, [44] cikin nau’in wannan ziyarar ma Mustahabbi ne kiyaye ladubba misalin wankan ziyara, sanya tsaftataccen tufafi haka kuma a yi ziyarar a wurare misalin saman rufin gida, [45] haka yin sallar ziyara, kafin ziyarar ko bayan gama karantata duka ya halasta. [46] kan asasin wata riwaya da aka dangantata ga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya yi wanka daga Gidansa ya hau sama sannan ya yi sallama ga Imam Husaini (A.S) daidai yake da wanda ya yi ziyara. [47]

Bayanin kula

  1. Dibace bar ziyarat, 1394, shafi na 11-9; Kargar, hakikat ziyarat, 1391, shafi na 7.
  2. Dibace bar ziyarat, 1394, shafi na 11-9; Kargar, hakikat ziyarat, 1391, shafi na 7.
  3. Dubi Jame Ziyarat al-Masoomin, 2009, juzu'i na 3, shafi na 36-39
  4. Duba Jame Ziyarat al-Masoomin, 2009, juzu'i na 3, shafi na 69-39.
  5. Najafi Yazdi, Asrar Ashura, 1377, juzu'i na 2, shafi na 103-105.
  6. Sheikh Mufid, Al-Mazar, 1413H, shafi na 26, babi Haddi wujubiha fi zaman ala Aginya wal fukara, shafi na 28.
  7. Hurrul Amili, Tafsilu Wasa’ilul Shi’a, 1416 Hijira, Mujalladi 14, shafi na 443-445.
  8. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 4, shafi na 243-244.
  9. Alameh Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 44, shafi na 255-256, h4.
  10. Mohammadi Rishahri, Guzideh shahadat nameh Imam Hossein, 1390, shafi na 839.
  11. Al-Sayyid Ibn Al-Tawoos, Allahuf Fi ƙatali Al-Tufuf, 1417 AH, shafi na 114.
  12. Tabari, Tarikh Tabari, 1967, juzu'i na 4, shafi na 470.
  13. Duba Ibn ƙulawiyya, Kamil al-Ziyarat, 1424H, shafi na 206-203, 242-245.
  14. Amin, Ayan al-Shia, bincike: Hassan Amin, juzu'i na 8, shafi na 146; Mohammadi Rayshahri, Daneshnameh Imam Hussein, Salam bisa Alƙur'ani da Hadisi da Tarihi, Mujalladi na 10, shafi na 243; Al-Hadi, "Muhimmanci da falsafar ziyartar haramin Husaini",shafi na 28-29.
  15. Abul Faraj Esfahani, Muƙatil al-Talbeyin, 1419 AH, shafi na 478-479; Sheikh Tusi, Amali, 1414 AH, shafi na 325-329.
  16. Kalidar, Tarikh Karbala wa Hayer Hosseini, 1389, shafi na 188.
  17. : Ibn Battuta, Rahleh Ibn Battuta, Dar al-Sharƙ al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 168; Al-Hadi, “Ahammiyat wa falsafe ziyarat marƙad Husaini”, shafi na 28.
  18. Al-Hadi, “ahammiyat wa falsafe ziyarat markad Husaini”, shafi na 28.
  19. Mohammadi Rayshahri, Daneshanameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 435
  20. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 435.
  21. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 435.
  22. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 436.
  23. Ibn ƙolwayh ƙomi, Kamel al-Ziyarat, 1356, juzu'i na 1, shafi na 130.
  24. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 436
  25. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 10, shafi na 437
  26. Mohammadi Rayshahri,Daneshnameh Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 11, shafi na 169
  27. Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424H, shafi na 316.
  28. Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424H, shafi na 323.
  29. Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424H, shafi na 333.
  30. Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424H, shafi na 338
  31. Ibn ƙulawiyya, Kamel al-Ziyarat, Al-Nasher Muƙatah al-Sadooƙ, shafi na 188.
  32. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 329.
  33. Duba: Mohammadi Rishahri, Daneshnameh na Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 11, shafi na 257.
  34. Duba Mohammadi Rishahri, Daneshnameh na Imam Hossein, 1430H, juzu'i na 11, shafi na 281.
  35. Muhaddi, Farhang Ashura, 1374, shafi na 213.
  36. Muhaddi, Farhang Ashura, 1374, shafi na 210.
  37. Muhaddi, Farhang Ashura, 1374, shafi na 207.
  38. Muhaddi, Farhang Ashura, 1374, shafi na 206.
  39. ƙommi, Sheikh Abbas, ziyarat Imam Hussain (a.s) dar shahayae ƙadri, wa nisfu mahe Sha'aban, Id Fitr da ƙur'ani.
  40. .Misali, duba Ibn ƙulawiyya, Kamil al-Ziyarat, 1424H, shafi na 134; Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424H, shafi na 187; Ibn ƙolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1424, shafi na 132
  41. Ibn ƙolwayh, Kamel al-Ziyarat, 1356, juzu'i na 1, shafi na 133.
  42. Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1365, juzu'i na 6, shafi na 43.
  43. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.lemonde.fr/proche-orient/article/2014/12/13/affluɗ-record-pour-un-pelerinage-chiite-en-irak_4540151_3218.html">گزارش روزنامه فرانسوی لوموند از مراسم اربعین در کربلا</a>
  44. Farhang Fiƙh, 1389, juzu'i na 4, shafi na 329.
  45. Farhang Fiƙh, 1389, juzu'i na 4, shafi na 329.
  46. Farhang Fiƙh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 329
  47. Farhang Fiƙh, 2009, juzu'i na 4, shafi na 329

Nassoshi

  • Ibn Battuta, Rahleh Ibn Battuta, dab'i n Al-Sharƙ al-Arabi.
  • ابن قولویه، Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, binciken Sheikh Jaɓad ƙayyumi, ƙum, bugun Al-Fiƙahah, 1424H.
  • Abul Faraj Esfahani, Ali bin Hossein, Muƙatil al-Talbeyin, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1419 AH/1998 Miladiyya.
  • Amin, Seyyed Mohsen, Ayan al-Shia, Bincike: Hasan Amin, Bija, Bita.
  • Jame Ziyarat Al-Masoomin, Imam Al-Hadi (AS), ƙum, Payam Imam Hadi (AS)/Etidam, 2009.
  • Har Amili, Muhammad bin Hasan, bayanin hanyoyin da ‘yan Shi’a suke bi wajen nazarin mas’alolin Shari’a, ƙum, Mu’assasa ta Al-Baiti ta Rayar da al’ada, 1416H/1374H.
  • Gabatarwa kan aikin hajji: Amsa shubuhohin Wahabiyanci daga mahangar malaman Shi'a da Sunna, ƙum, Payam Imam Hadi Publications, 1394.
  • Zare Khormizi, Mohammad Reza, "Arba'in na Jini: Duban wasu hare-hare na zubar da jini a bikin Arbaeen na Hosseini a wannan zamani", a cikin Farhang Ziarat ƙuarterly, lamba 19 da 20, rani da kaka na 2013.
  • Al-Sayyid Ibn Taɓus, Allahuf fi ƙatali al-Tufuf, ƙum, Anwar al-Hadi, 1417H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Amali, Kum, Dar al-Thaƙafeh, 1414H.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Numan, Al-Mazar, ƙom, Sheikh Mofid World Hazara Congress, 1413 AH.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Tabari, Beirut, Dar al-Tarath, 1967.
  • Allamah Majlisi, Muhammad Baƙir bin Muhammad Taƙi, Bihar al-Anwar al-Jamaa shugaban Akhbar al-Imam al-Athar, editan Muhammad Baƙir Mahmudi da sauransu, Beirut, Mu'assasar Al-Wafa, 1403H/1983 miladiyya. .
  • Alaɓi, Seyyed Adel, "Karfafa Tafiya don Hajjin Marasa Lafiya", wanda Hossein Shahrashtani ya fassara, a cikin Farhang Ziarat ƙuarterly, No. 19 da 20, bazara da kaka na 2013.
  • Farhang fiƙhu bisa addinin Ahlul-Baiti (a.s), Cibiyar Ilimin Fikihu ta Musulunci, ƙum, Cibiyar Encyclopaedia ta Shari’a, 1389 ta yi bincike kuma ta hada shi.
  • Kargar, Rahim, Haƙirat Ziarat, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi, 1391.
  • Kalidar, Abdul Jaɓad, Tarihin Karbala da Haer Hosseini, Muslim Sahibi, Tehran, Mashaar, 1389 ya fassara.
  • Mohaddisi, Jaɓad, Farhang Ashura, ƙom, sanannen bugu, 1374.
  • Mohammadi Roimhari, Muhammad, Kundin ilmin Imam Hossein bisa alkur'ani da hadisi da tarihi, wanda Abdul Hadi Masoudi ya fassara, juzu'i na 10, ƙum, Darul-Hadith, 1430H/1388.
  • Mohammadi Roimhari, Mohammad, daga cikin shedar Imam Hossein bisa ingantattun majiyoyi, ƙum, Dar al-Hadith Scientific and Cultural Institute, 1390.
  • Najafi Yazdi, Seyyed Mohammad, Asrar Ashura, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1377.
  • Al-Hadi, Jafar, "Muhimmanci da Falsafar Aikin Hajji zuwa Haramin Hosseini", a cikin Farhang Ziarat ƙuarterly, No. 19 da 20, Summer and Fall of 2013.