Haramin Askariyaini (A.S)

Daga wikishia
Haramin Askariyaini (A.S)

Haramin Askariyaini (arabic: حرم الإمامين العسكريين (ع)) ko Haramin Imamai guda biyu Askariyaini ya kasance makwancin Imam Hadi (A.S) wanda ya yi shahada a shekara ta 254 h ƙamari, da ɗansa Imam Hassan Askari (A.S) wanda ya yi shahada shekara ta 260 h ƙamari, wannan makwanci na su ya na garin Samarra ƙasar Iraƙ, ya kasance ana ƙidaya shi daga cikin muhimman wuraren ziyara a wurin ƴan Shi’a a ƙasar Iraƙ, Narjis Khatun Matar Imam Hassan Askari (A.S) kuma Mahaifiyar Imam Mahadi (A.F) da Hakima ɗiyar Imam Jawad (A.S) da wasu adadi daga Sharifai da kuma Malamai suna cikin waɗanda aka binne a wannan wuri. Imam Hadi (A.S) a Shekara ta 254 h ƙamari, da kuma Imam Hassan Askari (A.S) a shekara ta 260 h ƙamari aka binne su a cikin gidansu, a shekara ta 328 h ƙamari, aka fara ɗora ƙubba ta farko a kan ƙaburburansu su biyu, bayan nan kuma a daurori daban-daban da suka zo daga baya an yi gyare-gyare da ƙara faɗaɗa wannan wuri da sabunta gininsa, a shekarun 1384 da 14386 h shamsi, wani yanki daga wannan Harami ya ruguje sakamakon hare-haren ta’addanci da ƴan Ta’addan Da’ish suka kawo kai, bayan wannan hari, hukumar sabunta gine-ginen Haramai tare da taimakon ofishin Ayatullahi Ali Sistani an sake sabunta gine-gine ƙaburburan da Haramin.

Matsayin Da Wuri

Haramin Askariyaini Makwanci ne na Imamai guda biyu kuma yana cikin jerin wuraren ziyara ga ƴan Shi’a a ƙasar Iraƙ, wannan wuri yana garin Samarra gari ne d ayake da nisan kilomita 120 da arewacin Bagdad, [1] cikin riwayoyin Shi’a an yi wasicci da ziyartar Makwancin Imamai guda biyu, [2] cikin kowacce shekara yan Shi’a daga sassan duniya suna zuwa ziyartar ƙabarin Imam Hadi (A.S) da Imam Askari (A.S) da suke garin Samarra.

Taƙaitaccen Tarihi

Hasumiyar Haramin Askariyaini (A.S)

Imam Hadi (A.S) da Imam Hassan Askari (A.S) Imami na goma da Imam na goma sha ɗaya a wurin yan Shi’a, bayan shahadarsu an binne su a cikin gidansu da yake garin Samarra. [3] Imam Hadi ya sayi wannan gida daga Hannun Dalilu Bn Yaƙub Nasrani, [4] a cewar Zabihullahi Mahallati gidan da a cikinsa aka binne Imam Hadi da Imam Hassan Askari (A.S) ya kasance a yanda yake tun farko har zuwa shekara ta 328 na’am an kafa wata taga jikinsa, wasu ba’arin mutane sun kasance suna ziyartar Imamai biyu (A.S) daga wajen gida [5] Malam Mahallati tare da jingina da waƙar Muhammad Samawi wanda ya rayu a tsakanin shekaru 1292-1370 h ƙamari, Nasirul Daula Hamdani wanda ya rayu tsakanin shekaru 323-356 h ƙamari, ɗaya daga Sarakunan Alu Hamdan shin ne farkon wanda ya fara gini cikin wannan gida ya gina ƙubba kan ƙaburburansu a shekarar 328 h ƙamari,. [6] bayan nan an yi ta sabunta ginin Haramin Askariyaini a daurori daban-daban da bayaninsu zai zo a ƙasa:

• Mu’izzul Daula [7] da Adhadhul Daula Dailami [8] daga Sarakunan Alu Babawaihi wanda suka yi Mulki tsakanin shekaru 322-448 h ƙamari.
• Arsalan Basasayir wanda ya rasu shekara 451 h ƙamari. [9]
• Sulɗan Barkiyariƙ wanda ya mutu shekara ta 498 h ƙamari, daga sarakun Salajuƙiyan. [10]
• Ahmad Al-Nasir Lidinilahi wanda ya rasu shekara ta 622 h ƙamari, [11] da Almustansir billahi wand aya rasu shekara ta 640 h ƙamari, [12] daga cikin Halifofin Abbasiyawa.
• Sulɗan Hassan Jalayari wanda ya rasu shekara 776 h ƙamari, [13]
• Sulɗan Husaini Safawi wanda ya rayu tsakanin shekaru 1105-1135 h ƙamari, [14] daga sarakunan Safawiyya
• Ahmad Khan Dunbuli, [15]
• Hasanƙali Khan Dunbuli wanda ya rasu shekara ta 1297 h ƙamari, [16]

Nasir-dini Shah ƙajari wanda ya rayu tsakanin shekaru 1264-1313 h ƙamari.

• Mirza Shirazi wanda tsakanin shekaru 1230-1312 h ƙamari. [17]

Dukkaninsu suna cikin mutanen da suka bada umarnin gina wannan wuri ko sabunta gininsa.

Rugujewar Haramin Askariyaini Sakamakon Harin Ta’addanci Kansa

Asalin Maƙala: Ruguje Haramin Askariyaini (A.S)

Haramin Askariyaini a shekaru 1384-1386 ya fuskanci hare-hare daga ƙungiyoyin ƴan Ta’addan takfiri lamarin da ya haifar da tarwatsewarsa, wannan ta’addanci ya fuskanci zazzafan martani daga Maraji’an Taƙlidi da kuma ƴan Shi’a daga Sassan duniya, dasa wannan nakiya da yan ta’adda suka yi ƙubbar kan Haramin da Adon da aka yi masa da ruwan zinariya duk sun rushe, sai dai cewa ƙafafun ƙubbar ba su taɓu ba, [18] hukumar kula da sabunta gine-ginen Haramai ta ƙasar Iran tsakanin shekara ta 1389-1394 hijri sun sabunta ginin wannan Harami, [19] cikin sabunta ginin an cancaɗawa ƙubbar Ado da ruwan Zinariya. [20] haka kuma an sabunta ginin Hubbaren ƙarƙashin kulawar wakilin Ayatullahi Sistani a ƙasar Iran Sayyid Jawad Shahristani. [21]

Tsarin Gine-Gine

Haramin Askariyaini an gina shi daga sassa daban-daban ba’arinsu sun kasance: ƙubba: ƙubbar Haramin Askariyaini faɗinta ya kai 200 sƙuare Meter ta kasance mafi girman ƙubbar da take kan Haramin Imaman Shi’a. [22] Manara: cikin geffa biyun ƙubbar akwai Manara guda biyu waɗanda an yiwa samansu ado da ruwan zinare. [23] ƙabari: anyi amfani da kilo gram ɗari biyar na Azurfa cikin ginin katangogin da suke kewaye da ƙabarin da kuma kilo gram 70 daga zinare. [24] Filin Farfajiyar Harami: Haramin Askariyaini cikinsa akwai filin Farfajiya guda ɗaya wanda faɗinsa ya kai girman mita 77 zurfinsa kuma mita 78, akwai filin da ake sallah da tsayinsa ya kai mita 50 faɗinsa kuma mita 40, sannan akwai Filin Gaiba da yake da zurfin mita 64 da kuma faɗin mita 61. [25]

Mutanen Da Aka Binne Cikinsa

Asalin Maƙala: Fihirisar Mutanen Da Aka Binne Cikin Haramin Askariyaini (A.S)

A cewar Zabihullahi Mahallati cikin littafin Ma’asir fil Al-Kubara fi Tarikh, a cikin Haramin Askariyaini akwai ƙabarin Narjis Mahaifiya Imam Mahadi (A.F) da ƙabarin Hakima ƴar Imam Jawad (A.S) da ƙabarin Mahaifiyar Imam Hassan Askari (A.S) da kuma Husaini Bn Ali ɗan’uwan Imam Hassan Askari (A.S) DA Jafar Al-Kazzab da Abu Hashim ɗaya daga cikin jikokin Jafar Al-ɗayyar. [26] da kuma ƙabarin Samanatu Magribiyya mahaifiyar Imam Hadi (A.S) [27] Ahmad Khan Dunbali wanda ya rasu shekara 1200 h ƙamari da ɗan Husainiƙali Khan Dunbali [28] da Agha Rida Hamadani wanda ya rasu shekara 1322 h ƙamari Almajirin Mirzaye shirazi dukkanin an binne cikin wannan Harami. [29]

Bayanin kula

1. Qaidan, Atbat Aliyat Iraq, 2007, shafi na 193.
2. Misali, duba Sheikh Tusi, Tahzeeb al-Ahkam, 1407 AH, juzu'i na 6, shafi na 93.
3. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 315.
4. Khatib Baghdadi, Tarikh Bagadad, 1422 Hijira, juzu'i na 13, shafi na 518.
5. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 317.
6. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 318
7. Mahalati, Al-Kabra Ma'ather, 1384, juzu'i na 1, shafi na 321
8. Mahalati, Al-Kabra Ma'ather, 1384, juzu'i na 1, shafi na 324.
9. Mahalati, Al-Kabra Ma'ather, 1384, juzu'i na 1, shafi na 344.
10. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 347-348.
11. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 350.
12. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 366-365.
13. Mahalati, Al-Kabra Ma'ather, 1384, juzu'i na 1, shafi na 377.
14. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 389-379.
15. Mahalati, Al-Kabra Ma'ather, 2004, juzu'i na 1, shafi.386.
16. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 393.
17. Saheti Sardroudi, Guzideh SImaye Samarra, 2008, shafi na 67.
18. Khameyar, Ziyaratgahaye Islami dar Kishwarhaye Arabi, 2014, shafi na 29 da 30.
19. «تخریب و بازسازی حرم امامین عسکریین(ع)»
20. «تخریب و بازسازی حرم امامین عسکریین(ع)»
21. «ساخت ضریح مطهر امامین عسکریین»
22. «تخریب و بازسازی حرم امامین عسکریین(ع)»
23. «گلدسته‌های حرم امامین عسکریین(ع) از تخریب تا طلاکاری»
24. «ساخت ضریح مطهر امامین عسکریین»
25. Qaidan, Atbab Aliyat Iraq, 2008, shafi na 208.
26. Mahalati, Ma'ather al-Kubra, 1384, juzu'i na 1, shafi na 315.
27. Qaidan, Atbat Aliyat Iraq, 2007, shafi na 206
28. Qaidan, The Honours of Iraq, 2007, shafi na 218
29. Qomi, Al-Fawa'id Al-Rezawieh, 2005, juzu'i na 2, shafi.382.

Nassoshi

• «تخریب و بازسازی حرم امامین عسکریین(ع)»، خبرگزاری فارس، درج مطلب، ۴ آذر ۱۳۹۹ش، مشاهده ۳۱ مرداد ۱* Khame Yar, Ahmad,Takribi Ziyaratgahaye Islami dar Kishwarhaye Arabi , Qom, Darul-Ilam na Madrasa Ahl al-Bait (AS), 2013.
• Khatib al-Baghdadi, Ahmed bin Ali, Tarikh Bagdad, Bashar Awad, Beirut, Dar al-Gharb al-Islami, ya yi bincike, bugu na farko, 1422H/2002 Miladiyya.
• Qaidan, Asghar, Atbat Aliayat Iraq, Tehran, Mash'ar, 2007.
• Qomi, Sheikh Abbas, al-Fawad al-Razwiyyah a cikin sharuddan malaman addinin al-Jaafari, Qum, Bostan Kitab, 1385.
• Sahti Sardroudi, Mohammad, Guzideh Simayi Samarra Sinai Se Musa, Mashaar, Tehran, 2008.
• Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marifah Hajjullah Alal al-Ibad, edita ta Mu’assasa Al-Bait, Qum, Sheikh Mofid Congress, bugu na farko, 1413H.
• Tusi, Muhammad bin Hasan, Tahzeeb al-Ahkam, Hasan Mousavi Khorsan, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya ya yi bincike, bugu na 4, 1407H.
• «ساخت ضریح مطهر امامین عسکریین»، صداوسیمای مرکز قم، مشاهده ۳۱ مرداد ۱۴۰۱ش.
• «گلدسته‌های حرم امامین عسکریین(ع) از تخریب تا طلاکاری»، مشرق‌نیوز، درج مطلب ۲ خرداد ۱۴۰۰ش، مشا

۴۰۱ش.هده ۳۱ مرداد ۱۴۰۱ش.

• Mehlati, Zabihullah, Ma'sir al-Kubra fi tarikh Samarra, Kum, al-Maktab al-Haydariyya, 1384/1426H.