Ganin Allah
Ganin Allah (arabic: رؤية الله) wata mas’ala ce ta ilimin Kalam da ake bahasi kan yiwuwar ganin Allah da idanu, Malaman ilimin Kalam na Imamiyya da Mu’utazilawa sun yi Imani kan cewa ba zai taba yiwuwa idanu su ga Allah ba duniya da lahira, a mahangarsu ganin Allah da kwayar idanuwa yana lazimtawa Allah gangar jiki, hakika sun kasance kishiyar sauran Mazhabobin Kalam na Ahlus-sunna daga Ash’ariyya, Ahlul-hadis,(Mujassima), Karamiyya, Salafiyya, wadanda suka tafi kan yiwuwar ganin Allah. Gabatuwar mas’alar ganin Allah a Muslunci tana komawa ne zuwa ga Karni na biyu na hijira, a mahangar wasu ba’ari wannan mas’alar ta shigo makarantar muslunci ta hannun wasu Munafukan musulmi wanda a hakika Yahudawa ne da Kiristoci da suka boye kafircinsu suka bayyanar da muslunci, hakika wannan mas’ala kari kan ilimin Kalam anyi bahasi kanta cikin Alkur’ani da Irfani, akwai rubuce-rubuce da akayi masu tarin yawa kan mas’alar daga ciki: Ruyatullahi fi Dau’i Kitabu was-Sunna wa Aklil Sarihi, wallafar Ayatullahi Jafar Subhani.
Mafhumi da Matsayi
Ganin Allah mas’ala ce ta ilimin Kalam dangane da cewa shin zai yiwu idanu su ga Allah ko kuma ba zai yiwu ba.[1] a cikin ayoyin Kur’ani Magana ta zo game da ganin Allah, misalin aya 22-23 cikin suratul Alkiyama da kuma aya ta 15 cikin suratul Mudaffifin da aya ta 16 cikin suratu Yunus da aya 11-13 cikin suratul Najamu da kuma ba’arin wasu ayoyi; Haka kuma cikin aya ta 103 cikin suratul An’am da aya 143 cikin suratul A’araf da aya ta 55 suratul Bakara, da aya ta 153 cikin suratul Nisa’i da aya ta 21 suratul Furkan.[2] sannan kuma cikin Masadir din shi’a da sunna riwayoyi masu tarin yawa sun zo da suke Magana kan yiwuwar ganinsa da rashin yiwuwar.[3] Cikin Malaman tafsiri akwai wanda suka yadda za a gan shi wasu kuma suka kore ganinsa, karkashin wadannan ayoyi an faifaice bahasi dangane mas’alar ganin Allah.[4] Sakamakon kasantuwar Sufaye a koda yaushe suna neman samun hanya alaka da Allah kai tsaye sai ya zamana wannan mas’ala ta ganin Allah ta bijira cikin Sufanci da Irfani, kusan za a iya cewa dukkanin Manyan Malaman Sufanci dabaka ta farko misali Ibrahim Adham sun yi Magana kan wannan mas’ala.[5]
Takaitaccen tarihin Mas’alar
Mas’alar ganin Allah tana da gabatuwa a muslunci mas’ala ce ta aka fara bijira kanta tun karni na biyu.[6] a wannan karni Firkoki biyu Mu’utazila da Jahamiyya sun yi inkarin ganin Allah da idanu, amma a farkon karni na uku ganin Allah ya wayi gari wata sananniyar akida ga Ahmad Bn Hanbal, haka kuma sauran Firkokin Ahlus-sunna daga Asha’ira,Maturidiyya, Mujassima, Mushabbaha,Karamiyya,Salafiyya.[7] duka sun yarda cewa za a iya ganin Allah da idanu.[8] Wasu ba’arin Malaman Kalam na misalin Jafar Subhani wanda yake raye a wannan karni na 14 h kamari ya yi Imani da cewa fikirar ganin Allah ta shigo cikin musulmai ne ta hannun wasu Yahudawa da Kiristoci da suka nuna sun muslunta suka boye kafircinsu misalin: Ka’abul Ahbar mutumin da ya kutsa cikin rawaito hadisai da bahasin muslunci.[9] a ra’ayin Jafar Subhani baki dayan hadisan da suke Magana kan ganin Allah sun gangaro ne daga hannun musulmai Yahudawa da Kirista da suka bayyana muslunci a zahiri suka boye kafircinsu.[10]
Ganin Allah a Sauran Addinai
Gabanin muslunci mas’alar ganin Allah ta bijira cikin At-Taura da Linjila.[11] a cikin Attaura littafin Mai tsarki a wurin Yahudawa Allah ya yi Magana da Hazrat Musa (A.S): (ba zaka iya ganin fuskata ba ; saboda mutumin da ya gan ni ba zai rayu ba).[12] sanann cikin wata ayar Magana zuwa ga Musa (A.S) ya ce: zan `dage hannuna don ka ga keyata amma fuskata ba za ka iya ganin ta ba.[13] a wata ayar daga littafin Linjila ya zo cewa: masu tsarkin zuciya za su ga Allah.[14] amma kuma a wata ayar ance: babu wanda ya taba ganin Allah.[15]
Mahangar Mazhbobin Muslunci dangane da ganin Allah
Akwai mahangu uku dangane da mas’alar ganin Allah: Mujassima da Karamiyya daga Firkokin Kalam na Ahlus-sunna sun tafi kan yiwuwa ganin Allah a duniya da lahira, saboda suna ganin Allah matsayin gangar jiki da yake da bigire.[16] Sauran Firkokin Kalam na Ahlus-sunna daga Asha’ira.[17] da Ahlul-hadis.[18] sun tafi kan cewa kadai dai za a iya ganin Allah a ranar lahira da idanu; duk da cewa su basu yi Imani da cewa Allah yana da gangar jiki ba.[19] Imamiyya[20] da Zaidiyya[21] da Mu’utazila[22] sun kore batun yiwuwar ganin Allah a duniya da lahira, a wannan mas’ala suna da ittifakin mahanga.[23]
Dalilansu kan yiwuwar ganin Allah a lahira
Wanda suka yadda za a ga Allah sun kawo dalilai[24] na hankali da nakali kan tabbatar da da’awarsu, su ne kamar haka:
- wanda yake iya ganin kansa da ganin sauran abubuwa, akwai yiwuwar shima a gan shi, sakamakon Allah yana ganin kansa yana ganin abubuwa, akwai yiwuwar ya bamu dama da iko mu gan shi.[25]
- halittu daban-daban za a iya ganinsu yiwuwar ganinsu ya dogara da zatin samuwarsu, saboda haka a nan tun da shima Allah samamme ne dole ya zamana za a iya ganin sa.[26]
Dalilai na nakali
Dalilan nakali sun tattaro ayoyin Alkur’ani da riwayoyi: Daga cikin jumlar ayoyin Alkur’ani akwai aya ta 143 cikin suratul A’araf da Annabi Musa (A.S) ya nemi Allah ya bashi izini ya gan shi, amma sai Allah ya ba shi amsa da cewa ba zaka iya gani na ba. kafa Hujja da wannan aya da ace ganin Allah ya koru ba zai yiwu ba da Hazrat Musa (A.S) ba zai taba neman izinin haka daga Allah ba.[27] Sun kafa hujja kan halascin ganin Allah da aya ta 44 cikin suratul Ahzab da aya 22 cikin suratul Alliyama da aya 15 cikin suratul Mudaffifin[28] da aya 103 cikin suratul An’am.[29] Kan yiwuwar ganin Allah a lahira kuma sun kafa hujja da riwayoyi da aka nakalto da Annabi (S.A.W)[30] misalin hadisi Annabi[31] (zaku ga ubangijinku kamar yanda kuke ganin wata a daren sha hudu.[32]
Dalilai kan kore yiwuwar ganin Allah
Wanda ba su yadda da ganin Allah ba sun jingina da dalilan hankali da nakali kan haka: Dalilan Hankali Jafar Subhani: asasin dalilan hankali sun tafi kan cewa ganin Allah yana lazimta masa gangar jiki ko siffar jiki.[33] wasu ba’arin dalilan hankali suna tabbatara da cewa: 1 gani da kwayar idanu ta zahiri yana lazimta cewa Allah yana sa sasanni bigire da zamani, daidai lokacin da ya tsarkaka daga wadannan siffofi.[34] a ra’ayi Allama Hilli hukuncin wajabcin samuwar Allah na na wajbata masa koruwar gangar jiki da koruwar bigire da zamani, tare da kore wadannan abubuwa ganin Allah da kwayar idanu tana koruwa.[35] 2 ko dai Allah ya zama da baki dayan zatin sa za a iya ganinsa ko kuma da wani yanki zatinsa, sura ta farko tana faruwa ne da kaddara masa iyakantuwa da karewa, sura ta biyu tana lazimta masa tarkibi, da bigire kuma dukkanin surori biyun korarru ga zatinsa tsarkakka, saboda haka ba zai yiwu a gan shi.[36]
Dalilai na Nakali
Littafin Ruyatullahi wallafar Ayatullahi Jafar Subhani, daga cikin dalilan masu kore ganin Allah aya ta 143 cikin suratul A’araf wacce masu da’awar ganinsa suka kafa hujja da ita cikin wannan aya Allah yana cewa Musa (A.S) lallai kai ba zaka gan ni ba
Har abada ba zaka gan ni ba. Korewa ta har ababa domin ita (lan tarani) tana nuni zuwa ga korewa ta har abada.[37] Sai kuma ayar:
Idanu ba za su riske shi kuma shi yana risker idanu.[38] A mahangar Malaman Kalam na Imamiyya da Mu’utazila ayar tana nuni da cewa ba a za ga Allah da idanu ba.[39] Riwayoyin da aka nakalto daga Imaman Shi’a suma suna nuni da cewa ba za a ga Allah da idanu ba,[40] cikin wata riwaya wani mutum ya tambayi Imam Ali (A.S) shin ka ga Allah, sai ya bashi amsa ni bana bautawa ubangijin da ban gan shi ba, amma ni na gan shi da hakikar Imani bawai da kwayar idaniya ba.[41] a ra’ayin wanda suke kore ganin sa riwayar da masu da’awar ganinsa suke jingina da ita idan an kaddara ingancinta tana shiryarwa kan sanin ubangiji bawai ganinsa da idanu ba, saboda idan ya zama ana nufin ganinsa da idanu to ana lazimta masa bigire wanda abu ne korarre cikin hakkin Allah.[42]
Fihirisar Littafi
An fadada bahasi kan mas’alar ganin Allah cikin litaffan Kalam da Tafsiri da ba’arin litattafan Irfani da riwaya,kari kan haka akwai litattafai masu cin gashin kansu da suka kawo wannan bahasin wanda su ne kamar:
- Kalimatu Haula Ruya, wallafar Sayyid Abdul Husaini Sharafud Addini, wannan littafi ya wallafa shi ne karkashin mahangar shi’a kan kore yiwuwar ganin Allah.[43] wannan littafi a juz na 4 mai taken (Mausu’atu Imam Assayid Sharafuddini Abdul Husaini) wanda cibiyar Markazul Ulum was Sakafati Islamiyya ta tsara shi, sannan kuma Intisharatu Darul Mu’arrik Arabi suka buga karkashin binciken Mahadi Ansari Qummi da taken (Ruyatullahi wa Falsafa Misaki Islamiyya).
- Ruyatullahi fi dau’I kitabu was sunna wa Aklul Sarihi, na Jafar Subhani. A cikin wannan littafi ya dauki ganin Ubangiji a matsayin ka'idar da aka shigo da ita daga yahudawa tare da kokarin karyata wannan ka'idar da kare mahangar Shi'a da hujjoji na hankali da na Kur'ani da na ruwaya.
• Ruyatullahi Jal wa Ala, wallafar Ali bin Umar Darqutani, daya daga cikin mashahuran malaman hadisi kuma malaman karni na hudu. A cikin wannan littafi, domin tabbatar da halaccin ganin Allah an tattaro ayoyi da ruwayoyin da suka shafi ganin Allah[44] Wannan littafi yana tare da hadisai guda biyu, Ruyatullahi tabaraka wata’ala” wanda Ibni ya rubuta. Nahas da "Abdu' al-Sari, Ili Ma'rafah Ruya Al-Bari" Dar al-Kitab al-Alamiya buga ta Abishameh Moghdisi. Haka kuma an buga shi a matsayin shafi ga “Al-Musbah al-Munir fi Ruyya al-Rab al-Khibir” da “Al-Muhlaq al-Dhafi mana a cikin littafin al-Ruya al-Wafi” wanda Abu Awais ya rubuta. al-Kurdi a gidan buga littattafai na Ibn Taimiyyah. Daga cikin wasu ayyuka game da ganin Ubangiji akwai: Ruyatullahi baina Tanziyyah wa Tasbiyyah, Abdulkarim Behbahani, Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya; Ganin wata a sararin sama: nazarin tarihi na matsalar saduwa da Allah a Tauhidi da Sufanci, Nasrullah Purjawadi, Cibiyar Buga Ilimi; Ruyutullahi? A nan duniya da ma duniya, Sayyid Abdul Mahdi Tawakkul, karkashin kulawar Nasser Makarem Shirazi, Imam Ali bin Abi Talib.
Bayanin kula
- ↑ Subhani, Ruyatullahi fi dau'i kitabu wa sunna wa Aklil Sarihi, shafi na 26 da 27; Subhani, Ilahiyat, 1412q, juzu'i na 2, shafi 127; Bahbhani, Ruyatullahi baina Tanzihi wa Tashbihi, 1426Q, shafi.
- ↑ zakiri wa Digaran Ruyatullahi sha na 799-802
- ↑ duba riwayoyin Shi'a, duba Kulainy, Al-Kafi, Islamiyyah, 1407 AH, Babin Abtal al-Ruyyah, Mujalladi na 1, shafi na 110-95; Sheikh Sadouq, Al-Tauhidi, 1398 AH, Babin Ma Ja'a fi al-Rawiya, shafi na 107-122; Nahj al-Balagha, editan Sobhi Saleh, hadisi na 91, shafi na 124, hadisi na 185, shafi na 269 da hadisi na 186, shafi na 273; Sharaf al-Din, Ruyatullahi wa Falsaf Al-misthaq wa Al-Walaiya, 1423 AH, shafi na 81-53. Domin hadisai Ahlus-Sunnah, duba Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 Hijira, juzu'i na 1, shafi 115, juzu'i na 6, shafi na 139, juzu'i na 9, shafi na 127-129; Darqutani, Ruyatullahi Jal wa Ala, 1426 Hijira, shafi na 94-7.
- ↑ Domin neman fassarar masu adawa da ganin Allah, alal misali, duba Tusi, Al-Tabayan, Darahiya al-Tarath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 249-253, juzu'i na 10, shafi na 197-199; Tabatabai, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 8, shafi na 243-237; Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 141; Juzu'i na 2, shafi na 151-157; Misali, duba Fakhr Razi, Tafsir Kabir, 1420H, Juzu'i na 3, shafi na 519-520, Mujalladi na 14, shafi na 354-358, Mujalladi na 30, shafi na 730-733.
- ↑ Duba Zakiri wa Digaran, Ruyat, shafi na 810.
- ↑ SObhani. Ruyatullahi fi dau'i Kitab wa Sunna wa Aklil Sarihi shafi na 24-25, Zakiri wa Digaran,Ruyatullahi, shafi na 804
- ↑ Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah, 1406Q, Part 2, shafi na 316, 329-349, Part 3, shafi na 341, 344, 347.
- ↑ zakiri wa Digaran,Ruyatu Koda shafi na 804
- ↑ Duba Subhani, Al-ilaHiyat, 1412q, juzu'i na 2, shafi na 138 da 139; Subhani, duba Ruyatullahi fi dau'i kitabu wa sunna wa Aklil Sarihi, shafi na 15-24; Bahbhani, Roya Allah bin al-tanziyah wa al-tashbiyah, 1426q, shafi na 99 da
- ↑ Subhani, duba Ruyatullahi fi dau'i kitabu wa sunna wa Aklil Sarihi shafi na 16
- ↑ Zakiri w digaran, Ruyatu Koda, shafi 799
- ↑ Kitabu Mukaddas,Safru Kuruji, babi 33 aya ta 20
- ↑ Kitabu Mukaddas,Safru Kuruji, babi 33 aya ta 23
- ↑ Kitabu Mukaddas, Injilu Matta babi na 5 aya ta 8
- ↑ Kitabu Mukaddas.Injilu Yuhana babi na 1 aya 18
- ↑ Sobhani, Ilahiyat, muassaseh Imam Sadiq (a.s.), Mujalladi na 2, shafi na 125; Fakhr Razi, Al-Arbain fi Usul al-Din, 1986, Mujalladi na 1, shafi na 266 da 267; Behbahani, Ruyatullahi baina Tanziyyah da Al-Tashbiyyah”, 1426H, shafi na 15.
- ↑ Shaari, Al-Ibanah an usulid diyana Asalin, 1397 q.p., shafi na 25 da 51;
- ↑ Ruyatullahi fi dau'i Kitab wa sunna wa Aklil Sarihi sha na 27
- ↑ Sobhani, Ilahiyat, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 125.
- ↑ Allameh Hali, Kashf al-Morad, 1382, shafi na 46; Sobhani, Ruyatullahi fi dau'i kitab wa sunna wa Aklil Sarihi, shafi na 27; Javadi Amoli, Tauhid dar kur'ani, 1395, shafi na 256 da 257.
- ↑ Subhani,Ruyatullahi fi dau'i kitab wa sunna wa Aklil Sarihi, shafi na 27; Ash'ari, Maqalat al-Islamiyn, 1426q, juzu'i na 1, shafi.
- ↑ Qazi Abdul Jabbar, Al-Mukhtasar fi Usul al-Din, 1971, shafi na 190; Shahrashtani, Millam da Al-Nahl, 1364, juzu'i na 1, shafi na 57 da 114.
- ↑ Ash’ari,Makalat Al-Islamiyya, 1426 Hijira, juzu’i na 1, shafi na 131 da 172; Amadi, Ghaya Al-Maram, 1413 AH, shafi na 142; Shahrashtani, Al-Milal da Al-Nahl, 1364, juzu'i na 1, shafi na 5; Sobhani, Tauhidi, Cibiyar Imam Sadik (AS), juzu’i na 2, shafi na 125.
- ↑ Duba Ash'ari, Al-Ibanah an usulid diyana, 2018, shafi na 35-5.
- ↑ Duba Ash'ari, Al-Ibanah an usulid diyana, shafi na 53
- ↑ Amadi, Ghaya Al-Maram, 1413 AH, shafi na 142 da 143; Shahrashtani, Milal wa Al-Nahl, 1364, juzu'i na 1, shafi na 113.
- ↑ Waka, Al-Ibanah an usulid diyana, 2018, shafi na 41; Razi, Al-Arba'in fi Asool al-Din, 1986, juzu'i na 1, shafi.
- ↑ Duba Ash'ari, Al-Ibanah an usulid diyana, 2018, shafi na 35, 45 da 46; Fakhr Razi, Al-Arba'in fi Asool al-Din, 1986, juzu'i na 1, shafi 292-2
- ↑ Fakhr Razi, Tafsir Kabir, 1420 AH, juzu'i na 13, shafi na 97.
- ↑ Duba: Darqutani, Ruyyat Allah Jal wa Ala, 1426 AH, shafi na 94-7.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 115, juzu'i na 6, shafi na 139, juzu'i na 9, shafi na 127-129.
- ↑ Al-Ash’ari, Al-Ibanah an usulid diyana, 1397 s, shafi 49; Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah, 1406Q, Part 2, shafi na 332, Part 3, shafi na 341.
- ↑ Sobhani, Ilahiyat, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 128.
- ↑ Javadi Amoli, Tauhid dar kur’ani, 1395, shafi na 257.
- ↑ Allameh Hali, Kashf al-Morad, 1382, shafi na 46 da 47.
- ↑ Sobhani, Ilahiyat, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 127.
- ↑ Sobhani, Ruyatullahi fi dau'i kitab wa sunna wa AklilSarihi, shafi na 64-66
- ↑ suratu An'am aya ta 103
- ↑ Javadi Amoli, Tauhidi dar Kur’an, 1395, shafi na 258; Sobhani, Ruyatullahi fi dau'i kitab wa sunna wa Aklil Sarihi, shafi na 55; Qazi Abdul Jabbar, sharhu Usul al-Khumsa, 1422H, shafi na 156.
- ↑ Duba: Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, Babin Abtal al-Ruyyah, Mujalladi na 1, shafi na 110-95; Sheikh Sadouq, Al-Tauhidi, 1398 AH, Babin Ma Ja'a fi al-Ru'uya, shafi na 107-122.
- ↑ Nahj al-Balaghah, Jaab Dar al-Kitab al-Lebanese, Kashi na 1, shafi na 258, Huduba ta 179.
- ↑ Qazi Abdul Jabbar, Al-Mukhtasar fi Usul al-Din, 1971, shafi na 191 da 192.
- ↑ Aminipour, "Nime Niha be unwanihaye Mausu'atu Imam al-Sayyid Abdul Hossein Sharaf al-Din", shafi na 25 da 26.
- ↑ Duba Darqutani, Ruyyat Allah Jal wa Ala, 1426 AH, shafi na 7; Nafisi, “Darqutani, Abul Hasan Ali Ibn Omar”, shafi na 755.
Nassoshi
- Allameh Hali, Kashf al-Murad fi Sharh Tajrid al-Itqad Qasm al-Hiyat, Gabatarwa da Kammalawar Jafar Sobhani, Qum, Cibiyar Imam Sadiq (AS), bugu na biyu, 1382.
- Amadi, Saif al-Din, Ghaya al-Maram fi Alam al-Kalam, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, bugu na farko, 1413H.
- Aminipour, Abdullah, “Rabi-duba taken littafin mausuatu Imam al-Sayyid Abd al-Hossein Sharaf al-Din”, a cikin Mujallar Littattafan
- Musulunci, shafi na 22 da 23, fall da hunturu 2004.
- Ash'ari, Abul Hasan Ali bin Ismail, Al-Ibanah an Usulul Diyanah, Bincike na Fuqiyah Hossein Mahmud, Alkahira, Darul Ansar, bugu na 1, 1397H.
- Ash’ari, Abul Hasan Ali bin Ismail, Makalat islamiyya wa iktilaf musallin, Naeem Zarzour, Mazhabar Asriya, bugun farko, 1426 Hijira-2005 Miladiyya.
- Behbahani, Abdul Karim, Fai Rehab Ahl al-Bait (a.s): Ruyatullahi baina Tanziyyah wa Al-Tashbiyyah, Qum, Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya, bugu na biyu, 1426H.
- Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahih Bukhari, binciken Muhammad Zuhair bin Nasser al-Nasser, Dar Taq al-Najah, bugun farko, 1422H.
- Darqutani, Ali Ibn Umar,Ruyatullahi Jal wa Ala wa Yaliyyah Ruyatu Allah Tabarak wa Ta’ala da Hasken Al-Sari ga Ilimin hangen Al-
- Bari, Ahmad Farid al-Muzhesi ya yi bincike. Beirut, Darul Kutb al-Alamiya, bugu na farko, 1426 AH-2005 AD.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Al-Arabain fi Usul al-Din, Cairo, Al-Azhari School of Alcoholism, bugun farko, 1986.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Tafsir Kabir, Beirut, Darahiya al-Taraq al-Arabi, bugu na uku, 1420H.
- Ibn Taimiyyah, Ahmed Bin Abdul Halim Minhaj Sunna, fi nakadi kalam shia kadariya, bincike na Muhammad Rashad Salem, Imam Muhammad
- Bin Saud Islamic Society, bugun farko, 1986-1406 Miladiyya.
- Javadi Amoli, Abdullah, Tauhid dar Kur'ani (Tafsirin Kur'ani Mai Girma), Kum, Gidan Buga Isra'i, bugu na 8, 1395.
- Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
- Mohammadi, Ali, sharh Kashf al-Morad, Qom, Dar al-Fikr, bugu na 4, 1378.
- Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Kum, Hijira, bugun farko, 1414H.
- Qazi Abd al-Jabbar, Bayanin Usul al-Khumsa, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugun farko, 1422H.
- Qazi Abdul Jabbar, Al-Mukhtasar fi Usul al-Din, Mohammad Amara, Beirut, Daral Hilal, ya yi bincike, 1971.
- Shahrashtani, Muhammad bin Abdul Karim, Millam wa al-Nahl, bincike na Muhammad Badran, Kum, Sharif Razi, bugu na uku, 1364.
- Sharafuddin, Abdul Hossein, Ruyatullahi wa falasafe misak wa Al-Walaiya, Bincike na Mahdi Ansari Qomi, Qom, Loh Mahfuz, 1423H.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali Ibn Babouyeh, Al-Tauheed, Qum, Jamia Modaresin, bugun farko, 1398H.
- Sobhani, Ja’afar, ruyatullahi fi dau'i al-Kitab wa Sunnah wa Al-Aql, Kum, Al-Marqar Al-Alami na Ilimin Musulunci, bugu na uku, 1412H.
- Subhani, Ja'afar, Ruyatullahi ala hudal kitab wa sunna.
- Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Scientific Institute, bugu na biyu, 1390H.
- Zakari, Mustafa, Mohammad Zare Shirin Kandi and Babak Abbasi, "Vision", in Islamic World Encyclopedia, vol.20, Tehran, Islamic Encyclopedia Foundation, 2014.
- Zamakhshari, Mahmoud bin Omar, Al-Kashaf, Mustafa Hossein Ahmad, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, bugu na uku, 1407 AH.
http://ensani.ir/fa/article/187403/
- http://rch.ac.ir/article/Details?id=9000&&searchText= cikin Daneshname Jahan islam juz na 16 , Tehran Bunyad dayire Ma'aref Islami, 1393 shamsi