Sahifa Sajjadiyya

Daga wikishia
Sahifa Sajjadiya Kamila

Sahifa Sajjadiyya (Larabci: الصحيفة السجادية) wani littafi ne da ya tattaro Addu’o’in Imam Sajjad (A.S) wadanda ya shifta su zuwa ga ƴaƴansa biyu, Imam Baƙir (A.S) da Zaidu Bn Ali, wannan littafi bayan Alkur’ani da Nahjul Al-balaga yana daga mafi muhimmanci litattafan Shi’a, ana kuma kiran wannan littafi da sunaye misalin dan’uwan Alkur’ani da kuma Linjilal Ahlil-Baiti (A.S) Sahifa Sajjadiyya da farko dai ta tattaro Addu’a guda 75 sai dai cewa ba’arin wasu Addu’o’in sun bata bat bayan shudewar Daurorin zamani kadai guda 54 suka rage.

Sahifa Sajjadiyya littafi da ya samu karbuwa hatta wurin ba’arin wasu Malaman Ahlus-sunna, hakika ba’arin Malamansu sun nakalto wasu daga cikin Addu’o’in cikin Sahifa, ba’arin Turawan Yammacib Turai Masu bincike kan Muslunci sun yi Imani da cewa Sahifa Sajjadiyya tana nuna wa mutum sabuwar fuska daga muslunci , Imam Sajjad (A.S) cikin Sahifa cikin zirin Addu’a da Munajati ya yi bayani Asalan kyawawan dabi’u da kuma tsarin rayuwar zamantakewa da siyasa, a cewar Masu zurfafa bincike, kasancewar Imam Sajjad (A.S) a lokacin rayuwarsa ya kasance ne yana rayuwa cikin Takiyya sai ya yi amfani da Addu’a matsayin hanyar isar da wannan sako da bayaninsa. Mas’alar Imamanci daya daga cikin muhimman bahasosi ne na siyasa da Addini da aka bijiro da su cikin Sahifa da kuma tona aisirin wadanda suka yi kwacen Halifanci, yada manufofin jagorancin A’imma, jaddada karfafa kariya ga Alfarmar addini, bada kariya ga wadanda aka zalunta da kalubalantar Azzalumai, duka suna daga Mas’aloli da aka bijiro da su cikin wannan littafi. Wannan littafi ne da ya shahara a wurin ƴan Shi’a tare da samun karbuwa, ba’arin Masana hadisi suna cewa wannan littafi ya kai matsayin Mutawatiri, na’am wasu ba’arin Malaman fikihu sun yi ishkali da suka kan wasakar (Amana) Mutawwakil Bn Haruna, saboda haka basu ganin ingancin dogara da baki dayan shafukan littafin Sahifa Sajjadiyya. An tarjama littafin Sahifa Sajjadiyya zuwa Harshe daban-daban daga misalin Farisanci, Turanci, Faransanci, Indunusanci, Turkanci, Urdu, Sifaniyanci, Bosniyanci, Albaniyanci, da Tamil, an rubutu gomomin Sharhi kan wannan littafi mafi shahararsu shi ne Sharhin Riyadul As-Salikin, talifin Sayyid Ali Khan Kabir, wasu ba’arin masu bincike sun tattaro sauran Addu’o’in Imam Sajjad (A.S) da suka zo a wasu litattafan daban.

Mafi Muhimmancin Littafin Shi’a Bayan Littafin Nahjul Al-Balaga

Sahifa Sajjadiyya ta kasance mafi muhimmancin littafi kuma mafi shahara a wurin ƴan Shi’a bayan Nahjul Al-Balaga. [1] wannan littafi ya tattaro Addu’o’in da aka nakalto daga Imam Sajjad (A.S) [2] a cewar Ibn ShahreAshub wanda ya mutu shekara ta 588 h kamari, hakika Sahifa Sajjadiyya ta kasance cikin litattafai na farko-farko da aka rubuta a bayan bayyanar Muslunci [3] Murtada Mutahhari Masanin Muslunci daga bangaren ƴan Shi’a, yana ganin Sahifa matsayin dadadden littafin Shi’a bayan Al-Kur’ani , Malamin ya yi Imani cewa Addu’o’in da suke cikin Sahifa Sajjadiyya suna da matukar inganci daga bangaren Isnadi da mataninsu, [4] ya ce Sahifa ita kadai ce littafi da ya zo da surar liitafi guda daya mafi ingancin littafin da yake hannunmu a karshe-karshen karni na farko. [5]

Agha Buzurg Tahrani, Masanin Litattafan Shi’a ya rubuta cewa Hakika Sahifa Sajjadiyya ta kasance Uktu Al-Kur’ani (Yar’uwar Alkur’ani) kuma Linjilar Ahlil-Bai(A.S), Zaburar Alu Muhammad (A.S), ana mata lakabi da Sahifa Kamila. [6] Izzud-Dini Jaza’iri ya ce: wannan littafi ana koyar da shi a Hauza Ilimiyya ta kasar Indiya. [7]

Wani bangare daga maganar Imam Khomaini game da Sahifa Sajjadiya ciki hashiyar Sahifar da yayi kyauta ga Sayyid Ali Khamna'i:

Sahifa Kamila Sajjadiyya, wani Samfuri ne da yake matsayin kwaikwayo da Misalin Al-Kur’ani Mai girma, kuma tana cikin Mafi girman Munajati na Irfani da Makebantar da halwar debe haso wacce hannu ya gaza kaiwa ga samun Albarkokin cikinta, Sahifa Kamila wani littafi ne da ya fito daga mabubbugar hasken Allah, kuma ya kasance hanyar sulukin Manya-manya Waliyyai da Wasiyyai Masu girman Sha’ani da suke koyar Ma’abota kebantuwa da Allah, wannan tsarkakakken littafi shima kamar dai Alkur’ani ya kasance littafin Allah wanda cikinsa akwai dukkanin ni’imomi, kowanne mutum zai amfanu da shi gwargwadon tanadin sha’awarsa ta ma’anawiyya

Imam Khomaini cikin Saihafatu Imam bugun shekara ta 1389 j 21 sh 209.

Wani Sunan Daban na Sahifa Kamila

A ra’ayin Sayyid Ali Khan Kabir daya daga cikin wadanda suka rubuta Sharhi kan Sahifa, kasancewa wadatarwar wannan littafi cikin biyan bukatun duniya da na lahira ko kuma kasantuwar ya tattaro duk wata hususiyar kammalallen littafin Addu’a, ana kiransa da Sahifa Kamila, [8] haka kuma akwai tsammanin cewa ana kiransa da wnanan suna sakamakon banbantuwar Kwafin da yake hannun Imamiya da na Hannun ƴan Zaidiyya; saboda suma ƴan Zaidiyya suna da na su Kwafin Sahifa Sajjadiyya a hannunsu wacce kusan rabin Kwafin da Imamiyya suka nakalto ce. [9]

Adadin Addu’o’in Da Suke Cikin Sahifa Sajjadiyya

Da farko adadin Addu’o’in da ta tattaro ya kai 75 Addu’o’i ne da Imam Sajjad (A.S) ya shifta su zuwa ga ƴaƴansa guda biyu, ma’ana Imam Baƙir (A.S) da Zaidu Bn Ali, daga dai wannan kwafi na farko ne ya shifta kwafi daidai ga kowannensu [10] Yahaya Bn Zaidu ya bada kwafin da Mahaifinsa ya rubuta zuwa ga Mutawakkil Bn Haruna Balakhi, shi ne ya kasance Farkon Marawaicin Sahifa Sajjadiyya, [11] haka kuma Mutawakkil ya dauki wannan kwafi ya kai shi wurin Imam Sadiƙ (A.S) ya kiyastata shi da kwatanta shi da kwafin da Imam Baƙir (A.S) ya rubuta ba a samu kowanne irin banbanci ba a tsakaninsu, [12] sai dai cewa kuma Addu’o’in da suka rage a hannun ba su wuce 64 da hudu ba a lokacin , [13] sannan wannan 64 suma ba su cirata ba zuwa sauran daurorin zamani da suka zo daga baya, da wannan dalili ne ma ya zamana cikin kwafin da yake hannu a yanzu iya Addu’o’i 54 suka rage. [14] `dan gidan Mutawakkil shi kadai ne wanda ya nakalci Sahifa Sajjadiyya daga Mahaifinsa, sauran Marawaitanta 1 Ahmad Bn Muslim Mutahhari, 2 Aliyu Bn Nu’uman A’alam, Muhammad Bn Salihu, 4 Husaini Bn Ashkib Maruzi, 5 Ubaidullahi Bn Fadhal Nabhani, Aliyu Bn Hammad Bn Ula’i sun nakalto daga dansa Mutawwakil, [15] Sahifa Sajjadiyya tana da riwayoyi masu yawan gaske, sai dai cewa riwayar Baha’u Bn Sharaf ita aka fi sani kuma ita tafi shahara daga sauran. [16]

Shaharar Sahifa

A cewar Masana hadisi, hakika Sahifa Sajjadiyya a zamanin Majlisi na farko ma’ana Muhammad Takiyu Majlisi, ta samu shahara sosai, [17] ta hanyar Mafarki da mukashafa da kuma haduwa da Imam a wancan zamani ya samu kwafi daya daga Sahifa, kamar yanda ta yadu hakika a gidajen Mutane kari kan Alku’arni to za ka samu su na ajiye da Sahifa, [18] a cewar Muhammad Takiyu Majlisi rabin Mutanen garin Isfahan sun samu dacewa da amsa Addu’a Albarkacin Sahifa Sajjadiyya. [19]

Mahangar Ahlus-sunna Da Kuma Masu Bincike Kan Muslunci

Wani Ɓangare daga Wasikar Ɗanɗawi zuwa ga Ayatullahi Mar'ashi Najafi:
Hakika yana daga cikin tsiyatarmu ace har zuwa yanzu hannun bai kai ga wannan ilimi dawwamamme mai girman daraja da kima ba wanda ya kasance daga Gadon Annabta, duk sanda na yi tunani sai na samu wannan littafi yana sama da Magana dukkanin abin halitta kasa kuma da maganar mahalicci.

[20]

Muhamnmad Zakiyyu Mubarak wanda ya rayu tsakanin shekaru 1310-1379 h kamari, Mutumin Misra, cikin littafin At-Tasawwuful Islami wal Adabu wal Akhlaku, ya ce: Sahifa Sajjadiyya ta yi kama da Linjila ta Asali da ta sauka wurin Hazrat Isa (A.S) bawai Linjila da take hannun Kiristoci a yanzu ba, ya kuma rubuta cewa ita Sahifa wata Faila ce daga Allah da ya zartar da ita a kan harshen Imam Zainul Abidin. [21] Ibn Jauzi wanda ya mutu shekara ta 654 mawallafin littafin Tazkiratu Khawas ya yi Imani cewa Imam Sajjad yana da hakkin koyar da Musulmai a fagen ta yaya za a yi Magana da Ubangiji da bijiro masa da bukatu a fadar Allah, saboda ya koyawa mutane ya yin Istigfari yaya za a yi Magana da Ubangiji, haka kuma lokacin neman saukar ruwan sama ta yaya za roki Allah ya saukar da Ruwan Sama, sa’ilin da ake cikin tsoro daga Makiya yaya za a nemi mafaka gurin Ubangiji. [22] Sulaiman Bn Ibrahim Kanduzi wanda ya mutu shekara 1294 h kamari daya daga cikin Malaman Ahlus-sunna cikin littafinsa mai suna Yanabi’ul Muwadda ya ambaci sunan Sahifa Sajjadiyya ya kuma nakalto wani sashi daga Addu’o’in da suke cikinta, [23] Tantawi Jauhari mawallafin littafin Al-Jawahir fi Tafsiril Al-Kur’anil Al-Kareem, bayan samun kwafin Sahifa Sajjadiyya daga hannun Mar’ashi Najafi a shekara ta 1385 h kamari ya yabi Sahifa da kalmomin (Maganganu ne da suke saman maganganun halittu suke kuma kasan maganganun Mahalicci). [24] Wiliyam Citik Ba’Amirike Mai binkice kan Muslunci ya ce: galibin Mutanen Yammacin Turai babu abin da suka sani daga Addinin Muslunci illa Jumudi da kuma zahirinsa da rashin dokarsa, Amma Sahifa Sajjadiyya na iya nuna sababbin Fuskoki da ra’ayi ga masu sauraro tare da bayyana wadancan fahimtocin Dan Adam wadanda suka kasance sharadin tabbatuwar Hadafin Musulunci. [25]

Ingancin Littafin

A rahotan Masu bincike kan Hadisi, hakika Sahifa Sajjadiyya a kodayaushe ta kasance shahararren Littafi a wurin ƴan Shi’a da suka aminta da shi, Malamai misalin Shaik Tusi, Kudbuddini Rawandi, Shahid Awwal da Kaf’ami sun nakalto Addu’o’I daga Sahifa sun zuba su cikin litattansu, [26] Muhammad Baƙir Majlisi Mawallafin littafin Bihar-Anwar, [27] haka ma Agha Buzurg Tahrani suna ganin Sahifa Sajjadiyya ta kai Matsayin Tawatiri a mahangar Isnadi, saboda Marawaitanta cikin dukkanin Dabakoki da Daurori sun samu iznin Nakalinta. [28] Muhammad Takiyyu Majlisi ya rubuta cewa Sahifa Sajjadiyya tana da isnadi fiye da miliyan daya, [29] Muhammad Baƙir Majlisi ya ce wannan littafi hatta wurin Zaidiyya ana kirga shi cikin Mutawatiri, [30] a ra’ayin Malamin tare da la’akari da kasancewa Matanin Sahifa ya kure Fasaha da kuma kewayar kan Ilimin sanin Ubangiji babu shakka kuma da ta rage kan cewa lallai wannan littafi daga wajen Imam Sajjad (A.S) ya fito, [31] wasu ba’ari tare da dogara da Maganar Baƙir Majlisi suna ganin Sahifa littafi ne da taka matsayin mustafiz ko kuma mutawatiri [32] Tare da haka wasu ba’ari daga masu bincike bisa wasu adadin dalilai da suke da su suna ganin rashin ingancin da’awar tawatiri kan wannan littafi, [33] Abu Kasim Kuyi shima yana ganin rashin samun yakini kan Wasakar (aminci) Mutawakkil Bn Haruna wanda shi ne Asalin Marawaicin Sahifa Sajjadiyya, [34] a ra’ayin Imam Khomaini, duk da cewa Sahifa ta kunshi kololuwar balaga da kololuwar ma’anoni da hakan yake nuna cewa Asalin littafin daga Imam Sajjad (A.S) ya gangaro amma tare da haka ba zamu iya jingina baki dayan jumlolin da ta tattaro ba zuwa ga Imam Sajjad (A.S) kuma mu rike su hujja ba, [35] Malaman Fikihu da Malaman Tafsiri cikin litattafai da dalilansu sun dogara da wasu shafukan Sahifa Sajjadiyya, [36] Abu Ma’ali Kalbasi wanda ya mutu shekara ta 1315 h Kamari ya rubuta Risala guda kan sanadan Sahifa Sajjadiyya, [37] wannan Risala an buga ta cikin Risalolin Ilmin Rijal. [38]

Kwafi da Bugu

Shafin farko na mafi tsufa kwafin Sahifa Sajjadiyyah

Sahifa Sajjadiyya tana cikin litattafai da take da tarin kwafin rubutun hannu, [39] a iya kasar Iran kadai akwai kwafin rubutun hannu har guda dbu uku. [40] daya daga cikin dadaddun kwafin Sahifa an rubuta shi tun shekara 695 h Kamari, yana nan ajiye da Dakin Nazari na Ayatullahi Mars’ashi Najafi. [41] lokacin da ake kara sabunta ginin Haramin Imam Rida (A.S) a Shekara ta 1348 h shamasi an ci karo da wani dadadden tsohon kwafin rubutun hannu na Sahifa wanda tarihinsa yake komawa zuwa ga shekara 416 h Kamari, [42] kuma baki dayan Marawaitan Kwafin sun kasance daga Ahlus-sunna. [43] Haramin mai tsarki na Imam Rida (A.S) sun buga wannan kwafi tare da bai kasance kammalallen Kwafi ba. [44] An nakalto daga Sayyid Murtada Nujumi daga daya daga danginsa cewa Kwafin da ya kasance da rubutun Alkalamin Zaidu Bn Ali, an ganshi a Dakin Nazari (Library) na Batikan. [45] akwai tsammanin cewa kwafin da Imam Baƙir (A.S) ya rubuta da hannunsa yana nan a wurin Imam Zaman (A.F). [46] A karon farko an buga Sahifa Sajjadiyya a Birnin Kalkuta na Kasar Indiya a shekarar 1248. [47] a zamanin da suka zo daga baya an tarjama wannan littafin zuwa harsuna daban-daban tare da sharhi kuma an buga a wannan dai gari na kasar Indiya. [48] haka kuma an buga shi Kasar Iran a shekara 1262 h Kamari, an buga kasar Misra shekara ta 1322 h Kamari, a kasar Siriya kuma a shekara ta 1330 h Kamari, da kuma kasar Irak shekara ta 1352 h Kamari. [49]

Abin da Ta Tattaro

Imam Sajjad (A.S):
Ya Allah ka yi Salati kan tsarkakakku daga Ahlil-Baiti Muhammad (S.A.W). wadanda ka zabe su domin shugabanci, Ma’adanan Iliminka kuma Masu bada Kariya ga Addininka kuma Halifofinka a kasa Hujjarka kan Bayinka, wadanda da iradarka ka tsarkake su daga dukkanin Kazantar Sabo, wadanda ka zabe su tsani zuwa ga Aljannarka Madawwamiya

Sahifa Sajjadiyya, Addu’a Lamba ta 47 Sh 56.

A cewar Ba’arin masu bincike, yawanci abin da Sahifa take kunshe da su madalib ne na tauhidi sannan jigonsu da jagabansu ya kasance Kankan da Kai da kaskanta a gaban Allah da magiya gabansa. [50] Imam Sajjad cikin Sahifa ya yi bayanin Asalan Akhlak da tsarin rayuwar zamantakewa da siyasa a cikin zirin Addu’a da Munajati. [51] cikin yanayin da idan mutane suka karanta wannan Addu’a za su samu fahimtar tsari da uslubin siyasar Imam Sajjad (A.S). [52] dalilin da ya sanya Imam ya zabi bayanin wannan Ma’arifi da ilmi cikin tsari da zirin Addu’a ba komai bane sai yanayin da ya samu kansa a zamaninsa, musammam ma lokacin mulkin Sarki Abdul-Malik Bn Marwan, [53] wanda a lokacin Imam ya kasance yana rayuwa cikin Takiyya. [54] cikin wannan Sahifa kadai cikin yan tsirarun Addu’o’I ne zaka samu ba ayi Salati ba. [55] a cewar Rasul Jafariyan yin salati ga Muhammad (S.A.W) da Iyalansa yana daga gayar muhimmanci cikin bayanin Akidun Shi’a. [56] Mas’alar Imamanci daya daga cikin muhimman bahasosi ne na siyasa da addi da aka bijiro da su a cikin Sahifa. [57] sannan kuma Imam Sajjad (A.S) kari cancantuwar Imaman Shi’a cikin Halifanci ya bijro da kasancewarsu tare da Isma da ilmin Annabawa da kuma. [58] tare da tona asirin masu kwacen halifanci da kuma yada manufofin A’imma, karfafa kariya ga hurumin Addini da kalubalantar karya da bata da kuma kariya da goyan bayan wadanda aka zalunta da kalubalantar Azzalumai, suna daga sauran Mas’lolin da Sahifa ta bijira a kansu, [59] Jafar Subhani ya rubuta cewa Sahifa Sajjadiyya ta kunshi bayani kan wasu ba’arin mujizozin ilimi wadanda ba a tsinkaya da gano su ba a wancan zamani. [60] misalin yaduwar Annoba ta hanyar ruwa kamar yanda ya zo cikin wannan Addu’a:

«اللَّهُمَّ وَ امْزُجْ مِیاهَهُمْ بِالْوَبَاءِ

Ya Allah ka cudanya ruwayensu da Annoba. [61]

Fihirisar Jerin Addu'o'in Da Suke Cikin Sahifa Sajjadiyya

Wasu daga cikin addu’o’in Sahifa Sajjadiya ana kebe su ne ga wasu ranaku (kamar Addu'ar Ranar Arafa, Addu'ar bankwana da watan Ramadan, da Addu'ar ganin jinjirin wata) wasu kuma addu’o’in ba su kebantu da karanta su a wata rana ba ta musamman kadai ba,[62] Sahifa Sajjadiyya tana tattare da Addu'o'i guda 54, ga Fihirisar jerin sunayensu kamar haka:

1. Addu'ar Godiya ga Allah 2. Addu'ar Gaisuwa ga Annabi 3. Addu'ar Makusantan Mala'iku 4. Addu'ar Mabiya Annabawa 5. Addu'a ga Kai da abokai 6. Addu'ar Safiya da yamma 7. Addu'ar neman Saukin Matsala da wahala 8. Addu'ar neman tsarin Allah daga Mummunan halaye 9. Addu'ar Neman gafara 10. Addu'ar Neman tsari ga Allah 11. Addu'ar Kyakkyawar Ƙarshe 12. Addu'ar Furuci da tuba 13. Addu'ar Neman biyan bukatu 14. Addu'ar kai Kara gurin Allah kan zalunci 15. Addu'a Lokacin rashin lafiya 16. Addu'ar Neman gafara 17. Addu'ar Neman tsari daga Sharrin Shaidan 18. Addu'ar Tunkude Bala'i 19. Addu'ar Neman ruwan sama 20. Addu'ar Makarim al-Akhlaq 21. Addu'ar Bakin ciki kan aikata kurakurai 22. Addu'a a Lokacin wahala 23. Addu'ar Neman Lafiya 24. Addu'a ga Iyaye 25. Addu'a ga ƴaƴa 26. Addu'ar Makwabta da abokai 27. Addu'ar Masu tsaron kan iyaka 28. Addu'ar Neman tsari daga Allah 29. Addu'ar Neman Arziki 30. Addu'ar Biyan bashi 31. Addu'ar Tuba 32. Addu'a a cikin sallar dare 33. Addu'ar Neman Alheri. 34. Addu'ar yayin ganin wanda suka fada cikin Tarkon zunubi 35. Addu'ar Yarda da hukuncin Allah 36. Addu'a a lokacin tsawa 37. Addu'ar neman uzuri kan Karancin godiya 38. Addu'ar Neman uzuri bisa gazawa cikin Sauke Hakkin Allah 39. Addu'ar Neman Afuwa da rahama 40. Addu'ar Tunawa da mutuwa 41. Add'uar neman lullube zunubi 42. Addu'ar Khatamar Alqur’ani 43. Addu'ar Ganin jinjirin wata 44. Addu'ar Shiga Ramadan 45. Addu'ar Babkwana da Ramadan 46. Addu'ar Eid al-Fitr da Juma'a 47. Addu'ar Arafa 48. Addu'ar Eid al-Adha da Juma'a 49. Addu'ar Kawar da dabarar makiya 50. Addu'ar Tsoron Allah 51. Addu'ar Tawali’u ga Allah 52. Dagewa akan Addu'a 53. Tawali’u ga Allah 54. Cire bakin ciki

Tarjamomi

Tarjamar littafin Sahifa Sajjadiya da yaren Malay na Jalalud-dini Rahmat

An buga littafin Sahifah Sajjadiya a cikin harsuna daban-daban kamar Farisanci, Ingilishi, Faransanci, Indunisiyanci, Turkanci, Urdu, Sifaniyanci, Bosniyanci, Albaniyanci da Tamil [63] Wasu daga cikin waɗannan fassarorin sun kasance kamar haka:

Tarjamar Farisanci, Abolhasan Shearani; [64] Tarjamar Farisanci, Abdul Mohammad Aiti; [65] Mehdi Elahi Qomshaei ya yi tarjamar Farisanci; [66] tarjamar Farisanci wanda Mohammad Mehdi Foladvand ya rubuta, mai suna "Pishawaye Chehere bar Khak Sayendagan" [67] Tarjamar Faransanci daga Farida Mahdavi Damghani mai suna "Les Psaumes De L'islam";[68] Fassarar Tajik, Mullah Marouf Stroushni; [69] Tarjamar Azari, Rasul Ismailzadeh; [70] Tarjama zuwa harshen Malay ta Jalaluddin Rahmat mai taken "Shahifah Sajjadiyya, Gita Suci Keluarga Nabi." [71]

Sharhi, Ta’aliki Da Takmila

Littafin Riyadh As-Salikin Sharhi kan Sahifi Sajjadiyya, talifin Sayyid Ali Khan Asalin Makala: Fihirisar Sharhin Sahifa Sajjadiyya Agha Buzurg Tahrani cikin littafin Al-Zari’a ya kawo sunayen litattafai har guda 70 da aka rubuta su kan sharhin Sahifa Sajjadiya. [72] Mafi shaharar Sharhin da aka yi shi ne Riyad As-Salikin, talifin Sayyid Ali Khan, kuma yana cewa mafi dadewar sharhinta da yake hannunmu a yanzu shi ne littafin Al-Fawa’id Ash-Sharifatu fi Sharh As-Sahifatu, tare da Alkalamin Kaf’ami. [73] daga cikin sauran Sharhi da aka yi kanta za su iya kasancewa kamar haka:

  • Tarjume wa Sharh Sahifa Kamila Sajjadiya, talifin Sayyid Ali Nakiyyu Faizul Islam. [74]
  • Tafsir wa Sharh Sahifa Sajjadiyya, talifin Husaini Ansariyan. [75]
  • Shuhud wa Shenakt, tallifin Hassan Mamduhi Kemanshahi, [76]
  • Riyadul Al-Arifin fi sharh Sahifa, talifin Muhammad Bn Muhammad Darabi. [77]
  • Sharh As-Sahifatu As-Sajjadiyya, talifin Sayyid Muhammad Husain Husaini Jalali. [78]

An samu gurguzun wasu Addu’o’i daga Imam Sajjada (A.S) da suka ninninka adadin Addu’o’in da suke cikin Sahifa Sajjadiyya. [79] ba’arin Malamai sun yi bakin kokarinsu cikin tattaro sauran Addu’o’in Imam Sajjad (A.S) daga sauran Masadir, an kuma dawwana su da yada su cikin littafi guda, [80] ana kiran wadannan litattafan da sunaye kamar haka As-Sahifa As-Sajjadiya As-Saniya talifin Hurrul Amili, As-Sahifatu As-Sajjadiyya As-Salisa talifin Abdullahi Bn Isa Afand, As-Sahifatu As-Sajjadiyya Ar-Rabi’atu tare da Alkalimin Muhaddisul Qummi, As-Sahifatu As-Sajjadiyya Al-Khamisatu rubutun Sayyid Muhsin Amin, As-Sahifatu As-Sajjadiya As-Sadisatu, talifin Muhammad Salihu Mazandarani. [81] Sayyid Muhammad Baƙir Aftahi cikin wani rubutunsa mai taken Sahifa Sajjadiya Kamila ya tattaro Addu’o’i guda 272 daga Imam Sajjad (A.S) [82] Muhammad Baƙir Majlisiya shima ya tattaro wasu addu’o’in daban daga Imam Sajjad (A.S) ya kara a karshen Sahifa Sajjadiyya ana kiransu da sunan Mulhakat Sahifa, [83] a Aksarin Kwafin rubutun hannu sun tattaro da Karin wadannan Mulhakat. [84]

Rubuce-rubuce Da Suke Da Alaka Da Sahifa

Littafin Ridad Salikin Sharhu Sahifa Sajjadiya na Sayyid Ali Khan Kabir

Littafin Al-Mu’ujamul Al-Mufaharisu Li Al-Faz As-Sahifati Al-Kamila, fihirisa ce ta Maudu’i da aka rubuta ta kan Sahifa Sajjadiya, tareda Alkalamin Sayyid Ali Akbar Karashi. Sannan dangane da Sanin Littafin Sahifa Sajjadiya an rubuta litattafai daga jumlarsu za a iya kidaya Fajuhesh Nameh Sahifa Sajjadiyya, talifin Majid Gulami Jalise da kuma littafin Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifa Sajjadiyya wa Risaleh Hukuk, talifin Salmanu habibi da Muktar Shamsud-dini, [85] haka kuma cikin fagen rubutun fihirisar Maudu’an Sahifa an wallafa litattafai da sunayen wasu ba’ari cikinsu zai zo a kasa:

  • Ad-Dalilu Ila Maudu’atil As-Sahifati As-Sajjadiyya, rubutun Muhammad Husaini Muzaffar: cikin wannan rubutu ya Ambato dukkanin Maudu’an da suke da alaka da Sajifa Sajjadiyya, cikin surori 19 a gamammen babi da karshensu ya bijiro da juzu’an Maudu’ai da na Reshe, [86] an yada wannan littafi a cibiyar Daftare Intisharat Qum a shekara ta 1402, [87]
  • Farhang Nameh Maudu’i Sahifa Sajjadiyya, talifin Sayyid Ahmad Sajjadi da taimakon wasu marubuta: wannan littafi wanda Maudu’ansa suka kasance cikin tsarin jerin Haruffan Alphabet cibiyar Mu’assaseh Farhangi Mutala’ati Az-Zahra Qum Suka Yada shi mujalladi 3 a shekarar 1385 h shamsi. [88]
  • Namaye Nameh Maudu’i Sahifa Sajjadiyya, rubutun Mustapa da wasu: wannan littafi an buga shi cikin Mujalladi biyu karkashin tallafin Markaz Mutala’ati wa Madarik Ilmi Iran a Birnin Tehran. [89]
  • Hadis Bandagi, rubutun Kazim Arfa’u: Marubucin wannan littafin ya tsara shi cikin jerin Alphabet. [90] cibiyar Intisharat Faizul Kashani Tehran ta buga shi a shekarar 1388 h shamsi. [91]
  • Al-Mu’ujamul Al-mufaharisu Li Al-Faz As-Sahifati Al-Kamila, Talifin Sayyid Ali Akbar Karashi: an yada wannan littafi da kokarin cibiyar Intisharat darul At-tablig Qom a shekarar 1343 h shamsi. [92]
  • Al-Mu’ujamul Al-mufaharisu Li Al-Faz As-Sahifatu As-sajjadiyya, talifin Fatima Ahmadi: cibiyar Intisharat Uswe ta buga shi shekarar 1394 h shamsi. [93]

Bayanin kula

  1. Pishvai, Sireh Pishvayan, 2017, shafi na 281.
  2. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, Mujalladi na 15, shafi na 18-19.
  3. Ibn Shahr Ashub, Maalem Ulama, 1380H, shafi na 2.
  4. Motahari, Falsafeh Akhlak na xa'a, 1390, shafi na 36.
  5. Motahari, Falsafeh Akhlak na xa'a, 1390, shafi na 36
  6. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, Mujalladi na 15, shafi na 18-19.
  7. Jazayeri, Sharh al-Sahifah Al-Sajadiyeh, 1402 AH, shafi na 19.
  8. Madani, Riyad al-Salikin, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 100.
  9. Hakim, Elamul Al-hidaya, 1425 AH, Juzu’i na 6, shafi na 211.
  10. Tabatabai, Tarikh Hadisul Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 134.
  11. Mukaddimeh Sahifah Sajjadiyeh,
  12. Mukaddimeh Sahifah Sajjadiyeh
  13. Mukaddimeh Sahifah Sajjadiyeh
  14. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 134.
  15. Emadi Haeri, "Sahifah Sajjadiyeh", shafi na 394-395.
  16. Sadraei Khoei, Fehrestegan Nuskeh Kaddi 2002, juzu'i na 9, shafi.456.
  17. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 136.
  18. Majlisi, Raudatul Al-Mutaqiin, 1406 Hijira, juzu'i na 14, shafi na 421.
  19. Majlesi, Rawdat al-Mutaqiin, 1406 Hijira, juzu'i na 14, shafi na 421-422.
  20. Balaghi, tarjameh Sahifah Sajjadiyeh, 1369H, shafi na 249-252, ya nakalto daga Hosseini Tehrani, Imam Shinasi, 1425 AH, juzu'i na 15, shafi na 41.
  21. Zaki Mubarak, Al-tasawwuf Islami wal Adab wal Akhlak, 2004, juzu’i na 2, shafi na 65.
  22. An ɗauko daga: Mukaddimaeh Mar'ashi bar Sahifeh, shafi na 43-45.
  23. Duba: Kundozi, Yanabiyyah al-Moudah, 1422 AH, juzu'i na 3, shafi na 411-430.
  24. Balaghi, tarjameh Sahifah Sajjadiyeh, 1369H, shafi na 249-252, ya nakalto daga Hosseini Tehrani, Imam shinasi, 1425 AH, juzu'i na 15, shafi na 41.
  25. Chittik, “Mukaddameh bar Sahifeh Sajjadiyyah”, shafi na 85-86.
  26. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 134.
  27. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 107, shafi na 59.
  28. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, Mujalladi na 15, shafi na 18-19.
  29. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 107, shafi na 50.
  30. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 107, shafi na 59.
  31. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 107, shafi na 59.
  32. Tabatabaei, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 137.
  33. Tabatabaei, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 137.
  34. Khoei, Majam Rijal al-Hadith, Al-Khoei Islamic Foundation, juzu'i na 15, shafi na 185.
  35. Khomeini, Al-Makasab al-Muharmah, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 481
  36. Misali: Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiyah, 1410 AH, juzu'i na 2, shafi na 273; Bahrani, Hadaeq al-Nadrah, 1405 AH, juzu'i na 16, shafi.390; Najafi, Javaher al-Kalam, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 11, shafi na 158; Ansari, Kitab al-Makasab, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 338; Mashhadi, Tafsirin Kanz al-Daqaq, 1368, juzu'i na 2, shafi.237; Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH,juzu'i na 1, shafi.409
  37. Kolbasi, Ar-Rasa'ilul Al-Rajaliyah, 1422 AH, shafi na 624-559.
  38. Duba: Kolbasi, Al-Rasailul al-Rajliyyah, 1422 AH, shafi na 624-559.
  39. Tabatabai, Tarikh HadisShi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 136.
  40. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 136.
  41. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 136
  42. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 136
  43. Hosseini Tehrani, Imam Shinasiy, 1425 AH, juzu'i na 15, shafi na 110.
  44. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 137
  45. Fahri Zanjani, Sharh wa Tarjamaeh Sahifah Sajjadiyeh, 1388, juzu'i na 1, shafi na 20
  46. Fahri Zanjani, Sharh wa Tarjamaeh Sahifah Sajjadiyeh, 1388, juzu'i na 1, shafi na 20
  47. Jaliseh, Negahe Ijmali bar cafe Shifaeh Sajjadiyeh dar Daureh Qajar wa Pahlawi”, shafi na 307.
  48. Jaliseh, Negahe Ijmali bar cafe Shifaeh Sajjadiyeh dar Daureh Qajar wa Pahlawi”, shafi na 307
  49. Jaliseh, Negahe Ijmali bar cafe Shifaeh Sajjadiyeh dar Daureh Qajar wa Pahlawi”, shafi na 308
  50. Emadi Haeri, "Sahifah Sajjadiyeh", shafi na 392.
  51. Sobhani, farhang Akayid wa Mazahib islami, 1395, juzu’i na 6, shafi na 406.
  52. Jafarian, hayat wa Fikri Siyasi Imamaneh Shi'a, 2007, shafi na 274.
  53. Ansari, Ahlul Baiti (AS), 1428H, shafi na 279.
  54. Khalji, Asrar Kushoshan, 2003, juzu'i na 1, shafi na 127.
  55. Jafarian, hayat wa Fikri Siyasi Imamaneh Shi'a, 2007, shafi na 274.
  56. Jafarian, hayat wa Fikri Siyasi Imamaneh Shi'a, 2007, shafi na 274.
  57. Jafarian, hayat wa Fikri Siyasi Imamaneh Shi'a, 2007, shafi na 275.
  58. Misali duba: Sahifah Sajjadiyeh, du'a ta 47, sakin layi na 56; Addu'a ta 48, sakin layi na 9-10; Da Du'a 34
  59. Torabi, Imam Sajjad (a.s.) Jamal Niyaishgaran, 1373, shafi na 286-287.
  60. Sobhani, Farhang Akayid wa Mazahib Islami, 1395, juzu’i na 6, shafi na 407.
  61. Sahifah Sajjadiyeh, Du'a 27.
  62. Emadi Haeri, "Sahifah Sajjadiyeh", shafi na 392.
  63. Habibi da Shams al-Dini,Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyyah da Risalah al-Haqq, 1394, shafi na 273-293.
  64. Shearani, Sahifeh Sajjadiyeh, 1393.
  65. Aiti, Sahifah Sajjadiyeh, 1375.
  66. Elahi Qomshaei, Sahifah Sajjadieh, 1389
  67. Fouladvand, Psihawaye Cheherr Bar Khak Sayendigan, 1379.
  68. مهدوی دامغانی، Les Psaumes De L'islam، الهدی.
  69. Habibi da Shams al-Dini,Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyyah da Risalah al-Haqq, 1394, shafi na 289.
  70. Habibi da Shams al-Dini, Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyyah da Risalah al-Haqq, 1394, shafi na 289.
  71. Habibi da Shams al-Dini, Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyyah da Risalah al-Haqq, 1394, shafi na 293.
  72. Aghabozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, juzu'i na 3, shafi na 345-359.
  73. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 138.
  74. Faiz al-Islam,Tarjame wa Sharh Sahifa Kamila Sajjadiyeh, 1376.
  75. Ansariyan, Tafsir wa Sharh Safiha Sajjadiyeh, 2013.
  76. Mamdohi,shuhud wa shenakt, 2008.
  77. Darabi, Riyad al-Arifin fi Sharh Saifah Seyyed al-Sajdin, 1421H.
  78. Hosseini Jalali, Sharh al-Sahifa al-Sajadiyeh, 1436H.
  79. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 134.
  80. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, Mujalladi na 15, shafi na 19-21.
  81. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1403H, Mujalladi na 15, shafi na 19-21.
  82. Mohd Abtahi, Sahifa Al-Sajadiyyah Al-Kamalah, 1413 AH.
  83. Sadraei Khoei, Feherestegane Nuske Kaddi Hadis, 2002, juzu'i na 9, shafi.456
  84. Sadraei Khoei, Feherestegane Nuske Kaddi Hadis, 2002, juzu'i na 9, shafi.456
  85. Duba: Gholami Jaliseh, fajuhesh Nameh bar Sahifah Sajjadieh, 2013;Habibi da Shams al-Dini,Kitabe Shinasi Imam Sajjad, Sahifah Sajjadiyeh da Risaleh al-Haqq, 1394.
  86. Duba: Muzaffar, al-Dalil Ila maudu'at al-Sahifa al-Sajadiyeh, 1403H.
  87. Duba: Muzaffar, al-Dalil Ila maudu'at al-Sahifa al-Sajadiyeh, 1403H.
  88. Sajjadi wa digaran, Farhang nameh Sahifah Sajjadieh, 2005.
  89. Draiti wa Digaran, Namaye Nameh Maudu'i Sahifah Sajjadiyeh, 1377.
  90. Arfa, Hadith Bandagi, 2008
  91. Arfa, Hadith Bandagi, 2008
  92. Qurashi, al-Mu'ajm Al-Mufars for Al-Faz Sahifa Al-Kamalah, 1343.
  93. Ahmadi, Al-Mujajm Al-Mufars Lalfaz Sahifa Al-Sajadiyeh, 1394.

Nassoshi

  • Safiha Sajjadiyeh.
  • Aghabuzur Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhari'a al-Tsanif al-Shia, Beirut, Dar al-Azwa, 1403 A.H.
  • Aiti, Abdul Mohammad, fassarar Sahifah Sajjadieh, Tehran, Soroush, 1375.
  • Ibnshahrashoob, Muhammad bin Ali,Ma'alim al-Ulama a cikin jerin littafan shi'a da sunayen masu ajujuwa da suka hada da tsofaffi da hadisai, Najaf, Al-Matabah Al-Haydariyyah, 1380H.
  • Ahmadi, Fatemeh, Al-Mujajm Al-Mufhars Lalfaz Al-Sahifa Al-Sajadieh, Tehran, Osweh Publishing House, 2014.
  • Arfa, Seyyed Kazem, Hadith Bandagi, Tehran, Faiz Kashani, 2008.
  • Elahi Qomshaei, Mahdi, tarjameh Sahifah Sajjadiyeh, Qom, Tobay Mohabbat, 1389.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini (RA), 1389.
  • Ansari, Muhammad, Ahlul Baiti (a.s), Kum, Majmael al-Fikr al-Islami, 1428H.
  • Ansari, Morteza, Kitab al-Makasab, Qum, Majalisar Dinkin Duniya na tunawa da Sheikh Azam Ansari, 1415H.
  • Ansarian, Hossein, Tafsir wa Sharah Safiha Sajjadiyeh, Qom, Dar al-Irfan, 2013.
  • Bahrani, Yusuf bin Ahmad, Hadaiq al-Nadrah fi Haqam al-Utrah al-Tahira, Qum, Islamic Publications Office, 1405 AH.
  • Peshwai, Mehdi, Sireh Peshwaiyan, Qum, Imam Sadiq Institute (AS), 1397.
  • Torabi, Ahmad, Imam Sajjad (a.s.) Jamal Niayeshgaran, Mashhad, Islamic Research Foundation, 1373.
  • Jazayeri, Ezzeddin, Sharh al-Sahifa al-Sajadiyeh, Beirut, Dar al-Taraif don bugawa, 1402H.
  • Jafarian, Rasoul,Hayat Fikri wa Siyasi Imamaneh Shi'a, Kum, Ansari, 2007.
  • Jaliseh, Majid, "neagahi Ijmali bar cafahaye Sahifa dar Daure Qajar wa Pahlavi", Aineh Research, Ofishin yada farfagandar Musulunci na Seminary na Kum, 187, Farvardin da Ardibehesht 1400.
  • Chittick, William, “mukaddimeh bar Sahifeh Sajjadiyyah”, wanda: Safari, Vahid, ya fassara a cikin Journal of Sciences Hadith, No. 41, Fall 2006.
  • Habibi, Salman da Mukhtar Shamsuddin Mutlaq, kitabe shinasi Imam Sajjad (a.s.), Sahifah Sajjadiyyah kuma risasi a kan haqqoqi, Qum, Majalisar Ahlul Baiti ta Duniya, 1394.
  • Hosseini Jalali, Muhammad Hossein, Sharh al-Sahifa al-Sajadiyya, Karbala, Al-Utaba al-Husainiyya al-Maqdisa, 1436H.
  • Hosseini Tehrani, Seyed Mohammad Hossein, Imam shinasi, Mashhad, Allameh Tabatabai Publications, 1425 AH.
  • Hakim, Seyyed Munzer, wa Digaran, Elamul Al-Hudaiya, Qum, Majalisar Ahlul Baiti (AS), 1425H.
  • Khalji, Mohammad Taghi, Asrar Kushumshan, Proto Khurshid, Qom, 2003.
  • Khumaini, Sayyid Ruhollah, Al-Makasib al-Muharmah, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini (RA), 1415H.
  • Khoi, Seyyed Abulqasem, ALmujamu Rijal al-Hadith wa tafsil Dhabakat Tabaqat Al-Rawat, Kum, Al-Khoei Al-Islami Foundation, Bita.
  • Darabi, Mohammad, Riyaz al-Arifin fi Sharh Saifah Seyyed al-Sajdin, Tehran, bugun Osweh, 1421H.
  • Draiti, Mustafa, wa digaran, Namaye Nameh Maudu'i Sahifah Sajjadiyeh, Tehran, Center for Scientific Information and Documents of Iran, 1377.
  • Zaki Mubarak, Muhammad,At-Tasawwuf Islami wal Adab wal Akhlak, Al-Kahira, Al-Muktaba al-Thaqafi al-Diniya, 2004.
  • Sobhani, JafarFarhang Akayid wa Mazahib Islami, Qum, Tauhidi, 1395.
  • Sajjadi, Seyed Ahmad, da sauransu, Namaye Nameh Maudu'i Sahifah Sajjadieh, Qum, Al-Zahra Cultural Studies Institute, 2005.
  • Shearani, Abolhassan, Tarjame Sahifah Sajjadieh, Tehran, Kamfanin Bugawa na Duniya, 2013.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda al-Bahiyyah fi Sharh al-Lama' al-Damashqiya, margin: Kalanter, Seyyed Muhammad, Qom, Davari Publications, 1410 AH.
  • Sadraei Khoei, Ali, Kataloji na Rubuce-rubucen Hadisi da Kimiyyar Hadisin Shi'a, Kum, Dar al-Hadith 2002.
  • Tabatabaei, Sayyed Mohammad Kazem, Tarikh Hadith Shi'a, Tehran, Smit, 2008.
  • Tabatabaei, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Al-Nashar al-Islami Est., 1417H.
  • Emadi Haeri, Sayyid Muhammad, "Sahifah Sajjadiyeh", in Islamic World Encyclopedia, Juzu'i na 29, Tehran, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1400.
  • Gholami Jaliseh, Majid, Fajuhehs Namneh Sahifah Sajjadieh, Qom, Dalil Ma, 1390.
  • Foulavand, Mohammad Mahdi, Pishawaye cehere bar Khak sayandegan, Tehran, Suratu Mehr, 1379.
  • Fahri Zanjani, Ahmad, Sharh Sahifah Sajjadiyeh, Tehran, Osweh Publishing House, 2008.
  • Faiz al-Islam, Sayyid Ali Naqi, Tasir wa sharhin Safiha Kamila Sajjadiyeh, Tehran, Faqih, 1376.
  • Qurashi, Sayyid Ali Akbar, Al-Mujajm Al-Mufars na Al-Faz Sahifa Al-Kamaleh, Qom, Dar Tabligh Islami, 1343.
  • Kundozi, Suleiman bin Ibrahim, Yanabi Al-Moudeh, bincike: Ali Jamal Ashraf, Tehran, Osweh Publishing House, 1422 AH.
  • Kalbasi, Muhammad bin Muhammad Ibrahim, Al-Rajali al-Rajaliyah, Qum, Dar al-Hadith, 1422H.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar shugaban Akhbar al-Imam al-Athar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Majlesi, Mohammad Taqi, Al-Mutaqeen Ruda, Qum, Kushanpur Islamic Cultural Institute, 1406 AH.
  • Madani, Ali Khan Bin Ahmad, Riaz Al-Salkin a cikin bayanin littafin Seyyed Al-Sajdin, Al-Nashar al-Islami Foundation, bincike na Mohsen Hosseini Amini. 1409 AH
  • Mashhadi, Mohammad bin Mohammad Reza, Tafsirin Kanz al-Daqaeq, Tehran, Kungiyar Buga da Buga ta Ma'aikatar Shiryar Musulunci, 1368.
  • Motahari, Morteza, Falsafe Aklhlak, Tehran, Sadra, 2013.
  • Muzafar, Mohammad Hossein, Al-Dalil Ila maudu'at Sahifa al-Sajadiyya, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1403H.
  • Mamdohi, Hassan, shuhud wa shenakt, Qom, Bostan Kitab, 2008.
  • Mohd Abtahi, Sayyid Muhammad Baqir, Sahifa Al-Sajadiyyah Al-Kamalah, Qum, Imam Mahdi Institute (AS), 1413H.
  • Mahdavi Damghani, Farideh, Les Psaumes De L'islam, Tehran, Al-Hadi, 2009.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shariah al-Islam, Beirut, Dar Ihya al-Tarath al-Arabi, B.T.A.