Jump to content

Gafarta Zunubai

Daga wikishia

Gafarta zunubai (Larabci: غفران الذنوب ) yana nufin cewa Allah maɗaukaki yana yafewa ma'abota zunubi da saɓo, yana kawar da tasirin saɓon da suka aikata daga gare su. Ya zo a cikin riwayoyi na muslunci da litattafai na akhlaƙ da na tafsiri, bayanin hanyoyi da ake samun gafara da yafe zunubai daga cikinsu akwai; yin Istigfari (Neman gafara) da son iyalan gidan manzo (S.A.W) da neman ceto da yin tawassuli da biyayyar iyaye da ziyarar kaburburan Imaman Shi'a (A.S) da zuwa aikin Hajji da yin umara da kuma sadar da zumunci da raya dare da ibada da yin dubiya marar lafiya da ciyarwa da nuna hali na gari da kai ziyara ga Imam Husaini (A.S) da yin kuka kan musibar Imam Husaini(A.S) da hidimtawa iyali da taimakon matarka da yin sadaka da yayewa mumini baƙin ciki da zuwa akiyar mamaci maƙabarta da koyan karatu.

Daga cikin abubuwan da suke sawa a yafewa mutum zunubai ƙari kan abin da ya gabata, akwai kasancewar mutum a wasu gurare kamar, kasancewa a filin Arafa, kuma ana gafarta zunubai a wasu lokuta, kamar a watan Ramadan da watan Rajab da daren nisfu Sha'aban da kuma Allah ya jarabci mutum da wani Ibtila'i a dunitiya.

Akwai wasu zunubai da ba a yafewa, kamar shirka da bidi'a, da cin haƙƙin mutane (Idan mutum ya ci ba tare da yardarsu ba) da aikata saɓo a bainar jama'a.

Matsayi Da Ma'ana

Abin da ake nufi da gafarta zunubi, shine yin afuwa kan lefin da mutum ya aikata,[1] kuma yin haka shi ne zai sa mutum ya tsira daga azabar Allah da wutar Jahannama a ƙarshe ya sami rabauta da shiga aljanna.[2] Batun gafara zunubi ya zo a cikin aya ta 53 cikin suratul zumar.[3] da cikin wata addu'a da ta zo a Sahifa Sajjadiyyaاللَّهُمَّ يَا مَنْ بِرَحْمَتِهِ يَسْتَغيثُ الْمُذْنِبُون. Ma'ana, ya ubangiji kai ne wanda da rahamarka masu zunubi suke neman ɗauki.[4] Ibni Fahad Hilli malamin fiƙihu da hadisi a ƙarni na tara yana ganin cewa idan Allah ya gafartawa mutum zunubinshi to tasirin wannan zunubin zai gushe, da hakan mai zunubin zai zamo kamar wanda bai taɓa aikata wani saɓo ba kwata-kwata.[5]

Akwai wasu zunubai da suka zo a cikin ayoyin kur'ani da hadisi waɗanda ba a yafe su, daga cikinsu akwai shirka[6] da ƙirƙirar wani abin da babu shi a cikin addini[7] da cin haƙƙin mutane ba tare da yardar su ba[8] da aikata zunubi a gaban mutane.[9]

Hanyoyin Samun Gafara

Sayyidina Muhammad (S.A.W)Cikin Addu'ar Dare Na 20 Watan Ramadan'
Ina neman gafarar Allah akan laifukana na baya wadanda na manta amma an rubuta su gareni. Ina neman gafarar Allah akan zunubai masu halakarwa. Ina neman gafara a gare shi a kan mafi girman zunubai da munana. Ina neman gafararSa a kan abin da ya wajabta mini, kuma na yi sakaci wajen cika shi. Ina neman gafara a gare shi saboda manta abubuwan da suka nisanta ni daga Ubangijina.

[10]

Akwai hanyoyi na neman gafara da yafiya da suka zo a cikin ruwayoyin muslinci da litattafai na akhlaƙ da na tafsiri,kamar son iyalan gidan manzo (S.A.W)[11] da ceto[12] da addu'ar mutane ga mai aikata zunubi.[13] ga wasu kamar haka:

Zamani, da matsalolin duniya:

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Al-Mazhari, Saire Wa Suluk, shafi. 140.
  2. Al-Mazhari, Saire Wa Suluk, shafi. 155.
  3. Suratul Zumar, aya ta:53.
  4. Al-Sahifah Al-Sajadiya, Al-Dua 16, sakin layi na 1.
  5. Ibn Fahad Hilli, Uddatad al-Da'i, shafi. 327.
  6. Makarem al-Shirazi, Walatarin Bandigani, shafi na. 155.
  7. Al-Saduq, Sawabul A'amal Wa Iqabu; A'amal, shafi na. 258.
  8. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, Juz. 6, shafi na 29-30.
  9. Al-Bahrani, Awalim Uloom, vol. 11, shafi. 280.
  10. Mohammadi Rayshahri, Nahj al-Dhikr, 2008, juzu'i. 4, shafi. 309.
  11. Daylami, Irshadul Qulub, 1992, juzu'i. 2, shafi. 253.
  12. Mazaheri, Saire sulok, 2011, shafi. 275.
  13. Tabarsi, Majma'ul al-Bayan, 1372, juzu'i. 5, shafi. 403.
  14. Nuri, Mustadrak al-Wasail, 1408 AH, juzu'i. 12, shafi. 118.
  15. Ansari, Tafsir Wa Sharhu Sahifa Sajjadiya, 2004, juzu'i. 12, shafi na 308-310.
  16. Qomi, Maqamat al-Aliyah, 2010, shafi. 474.
  17. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 74, shafi. 290.
  18. Duba: Shahid Awwal, Al-Arba’un Haditha, 1407H, shafi. 91; Sheikh Saduq, Thawab al-A'mal, 1364 AH, shafi na 56-58; Mohammadi Rayshahri, Nahj al-Dhikr, 1387 AH, Juz. 4, shafi. 120.
  19. Mamaqani, Siraj Al-Shari'a, 2009, shafi. 809.
  20. Dastghayib, Gunahane Kabireh, 2009, juzu'i. 1, shafi. 122.
  21. Ibn Tavus, Falah Al-Sa'eel, shafi. 167.
  22. al-Tabarsi, Majma al-Bayan, Juz. 2, shafi. 658.
  23. Al-Sadooq, Sawabul A'amal, shafi na 56-58.
  24. Ibn Qolwayh, Kamel al-Ziyarat, shafi. 129.
  25. Ibn Qolwayh, Kamel al-Ziyarat, shafi. 104.
  26. Al-Kulayni, Al-Kafi, Juz. 4, shafi. 64.
  27. Al-Sha’iri, Jami'ul Akhbar, shafi. 75.
  28. Al-Fattal Al-Nishapuri, Rawdat Al-Wa’izin, shafi. 195.
  29. Al-Saduq, Sawabul A'amal, shafi. 2.
  30. Ansarian, Irfane Islami, Juz. 6, shafi. 99.
  31. Al-Maliki al-Tabrizi, Asrarul Salawat, shafi na. 254.
  32. Al-Sha’iri, Jami'ul Akhbar, shafi. 166.
  33. Qara'ati, Gunashanasi, shafi. 270.
  34. Al-Sha’iri, Jami'ul Akhbar, shafi. 69.
  35. Mohammadi Ray shahri, Nahj al-Dhikr, Juz. 2, shafi. 433.
  36. Al-Mashkini, Tahririul Mawa'iz Al-adadiyya, shafi. 683.
  37. Al-Mashkini, Tahririul Mawa'iz Al-adadiyya, shafi. 683.
  38. Al-Kulayni, Al-Kafi, Juz. 2, shafi. 100.
  39. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, Juz. 72, shafi. 461.
  40. Al-Kulayni, Al-Kafi, Juz. 4, shafi. 52.
  41. Al-Mamaqani, Siraj al-Sharia, shafi na 212-213; Al-Sha’iri, Jami’ al-Akhbar, shafi na 68-69.
  42. Mohammadi al-Rayshahri, Nahaj Addu'a, Juz. 1, shafi. 350.
  43. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 454.
  44. Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, Juz. 101, shafi. 132.
  45. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 454.
  46. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 454.
  47. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 454.
  48. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i. 86, shafi. 283.
  49. Mohammadi al-Rayshahri, Nahj al-Dhikr, JUz. 2, shafi. 376.
  50. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 2, shafi. 513.
  51. Muhammadi Reshahri, Nahj al-Dua’, 1389 AH, JUz. 1, shafi. 330.
  52. Mohammadi al-Rayshahri, Nahajud Addu'a, Juz. 1, shafi 279.
  53. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 452.
  54. Al-Mamaqani, Siraj al-Sharia, shafi. 874.
  55. Ansari, Tafsir Wa Sharhe Sahifa Sajjadiyya, Juz. 7, shafi. 230.
  56. Shahid Thani, Maskan Al-Fouad, Laburare Basarati, shafi. 21.
  57. Muhammadi Al-Rishahri, Hekmatnameh Piyambar Azam (PBUH), Juz. 8, shafi. 449.
  58. Ansari, Tafsir Wa Sharh Sahifa Sajjadiyya, 1383H, juzu'i. 7, shafi. 230.

Nassoshi

  • Qur'ani mai girma.
  • Ibn Tawus, Ali bn Musa, Falahul Sa'il Wa Najahul Masa'il Qum, Mu'assasa Daba'ar Musulunci, 1st ed., 1406H.
  • Ibn Fahd al-Hilli, Ahmad ibn Muhammad, "'Uddat al-Da'i," Tehran, Darul Kutub al-Islamiyya, 1407H.
  • Ibnu Quluwayh, Ja’afar bn Muhammad, “Kamil al-Ziyarat,” edita kuma ya gyara shi ta hanyar Abd al-Husayn al-Amini, Najaf al-Ashraf, Darul-Murtadawiyya, 1st ed, 1356H.
  • Bahrani al-Isfahani, Abdullah, "Awalimul Ulumi Wal-Ma'arif Wal Ahwal minal Ayat Wal Akhbar Wal Aqwal," Qum, Mu'assasa Imam Mahdi, 1sted, 1413H.
  • Al-Daylami, Hasan bn Muhammad, "Irshadul Qulub," Qum, Al-Sharif Al-Radi, 1st ed., 1412 AH.
  • Al-Sha'iri, Muhammad bn Muhammad, "Jami' Al-Akhbar," Najaf Al-Ashraf, Al-Haydariyya Press, 1st ed., n.d.
  • Al-Shahid Al-Awal, Muhammad bn Makki Al-Amili, "Arba'una Hadisan," Qum, Mazhabar Imam Mahdi, 1st ed, 1407H.
  • Al-Shahid Al-Thani, Zayn Al-Din bn Ali Al-'Amili, Musakkinul Fu'ad Inda Faqdil Ahibba Wal Aulad," Qom, Laburaren Basirati, N.d.
  • Al-Saduq, Muhammad bn Ali bn al-Husayn, "Sawabu; A'amal Wa Iqabul A'amal," Qum, Darul Sharif al-Radi Publishing House, 2nd ed, 1406 AH.
  • Al-Tabarsi, al-Fadl bn al-Hasan, "Majma'ul al-Bayan fi Tafsiril Quran," Hashim Rasuli da Fadlullah Yazdi, Tehran, Nasir Khusraw,, 1372H.
  • Al-Fattal al-Nishapuri, Muhammad ibn Ahmad, "Rawdat al-Wa'izin," Qom, Dalil Ma, 1381H.
  • Al-Qummi, Abbas, “Maqa,mat Aliyya Fi Mujibatis Sa'ada Abadiyya (Da’a da xabi’u),” Qom, Nur Mataf, 1389H.
  • Al-Kulayni, Muhammad ibn Ya’qub, Al-Kafi, edita na Ali Akbar al-Ghafari da Muhammad al-Akhoundi, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyyah, 4th ed., 1407H.
  • Al-Mamaqani, Abdullah, Siraj al-Shari'ah Qom, Risalat Ya'qubi, 1388H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, 3rd ed, 1403 AH/1983 AD.
  • Al-Mishkini, Ali, "Tahrir al-Mawa'iz al-Adadiyyah," Qom, Nashr al-Hadi, 1382H.
  • Al-Mazhari, Hussein, Saire Wa Suluk , Isfahan, Cibiyar Nazarin Al-Zahra', 1390H.
  • Al-Maliki Tabrizi, Javad, "'Asrarul Salat", Tehran, Payam Azadi, 1372H.
  • Al-Nuri, Hussein bn Muhammad, "'Khatimatu Mustadrakil Wasa'il", Qum, Mu'assasa ta Ahlul-Baiti ta Farfado da Gado, 1st ed., 1408H.
  • Ansarian, Husaini, "'Tafsiru Wa Sharhu Al-Sahifa al-Sajjadiyya'", Qum, Darul Irfan, 1383H.
  • Ansarian, Hussein, Irfan Islami, D.N., Dar Al-Irfan, D.T.
  • Dastghib, Abdul Hussein, Az-Zunubul Kabira, Qum, Mu'assasar Buga Musulunci, 1388H.
  • Karatuna, Mohsen, Gunahe-Shahnasi, Tehran, Farhangi Darshahi Ez-Qur'an Center, 1386 AH.
  • Mohammadi Al-Rishahri, Muhammad, Hikmatnameh Payambar A'azam (S.A.W), Qom, Al-Ilmi Farhangidar Al-Hadith Foundation, 1387 A.H.
  • Mohammadi Al-Rishahri, Muhammad, Nahaj Addu'a Qom, Al-Ilmi Farhangidar Al-Hadith Foundation, 1389 A.H.
  • Mohammadi Al-Rishahri, Muhammad, Nahj Al-Zikr, Qom, Al-Farhangidar Al-Hadith Foundation, 1387H.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Walatarin Bandegan, Qom, zuriyar Javan, 1383H.