Shaiɗan
- Wannan wani rubutu ne da aka yi shi game da mafhumin shaiɗan da shaiɗanu, domin sanin ma'ana shaiɗan wanda ya ƙi yin sujjada ga Adam ku dubu ƙasida mai taken Iblis.
Shaiɗan (Larabci:شيطان) suna ne da ake amfani da shi kan duk wata halitta ma'abociyar sharri da girman kai, shaiɗan (Ko Iblis) wani keɓantaccen take ko keɓantaccen suna na wata halitta da ta ƙi yin sujjada ga Adam sakamakon haka aka kore shi daga fadar ubangiji, game da mece ce haƙiƙar shaiɗan mene ne shi akwai saɓanin tsakanin malamai, sai dai cewa galibin malaman tafsiri sun tafi kan cewa shaiɗan ya fito ne daga jinsin aljanu.
Kalmar shaiɗan ko shaiɗanu ta zo wuri 88cikin kur'ani, a wurare da dama ta zo ne ma'anar Iblis. Bisa ayoyi, haƙiƙa shaiɗan bayan ya nuna girman kai cikin bin umarnin Allah dangane da yin sujjada ga Adam, sakamon haka ne aka kore daga muƙaminsa, bayan nan ne sai ya roƙi alfarma a wurin Allah da ya bashi dama har zuwa tashin alƙiyama, sai Allah ya ɗaga masa ƙafa tare da shi dama zuwa wani ayyanannen lokaci, cikin adadin ayoyi ubangijin ya nusantar da mutum kan girman hatsarin shaiɗan, ya kuma nemi mutum ya nemi tsarin Allah daga waswasin shaiɗan don gudun ka da ya fitar da shi daga hanyar ibadar da bautar Allah.
Cikin riwayoyi an yi magana game da batutuwa daban-daban daga jumlarsu labarin yadda ta kasance tsakanin shaiɗan da ba'arin Annabawa da Imamai, hanyoyin da ake nesantar shaiɗan da kuma siffofi da halayensa. Bisa koyarwar muslunci, shaiɗan iya abin da zai iya shi ne ya jefa waswasi cikin mutum da kuma kwaɗaitar da shi kan aikata saɓo, bai da wani tasiri da ƙarfi kan mutum fiye kiransa zuwa saɓo, ba zai iya tilasta mutum kan aikata zunubi ba. Sannan wuta ita ce za ta kasance ƙarshe da makomar shaiɗan da mabiyansa.
Matsayi Da Muhimmanci
Cikin al'adun muslunci shaiɗan gama garin suna ne da ake amfani da shi kan duk wata karkatacciyar halitta mai girman kai gaban Allah, wannan halitta za ta iya kasancewa mutum ko kuma aljani. Cikin kur'ani mai girma, an bayyana shaiɗan matsayin dawwamammen maƙiyin ga mutane da yaƙe baƙin ƙoƙarinsa wajen ɓatar da su.[1] an yi amfani da kalmar shaiɗar karo 88 cikin kur'ani, karo 70 kalmar ta zo ne da shakalin mufradi, karo 18 kuma ta zo da surar jam'i ma'ana shaiɗanu.[2] Allama majlisi cikin littafin Biharul Al-anwar ya naƙalto riwayoyi guda 177 daga Ma'asumai (A.S) suke magana kan shaiɗan (Ko Iblis).
Ayatullahi Jawadi Amoli Masanin Hikima da Ilimin Akida:
Mu na da wani makiyi da ake kira shaidan kuma baya yarda da sulhu matukar dai bai maishe mu bayinsa ba, to fa ba zai taba kyale mu ba, zamu yi ta dauki ba dadi da shi, wani lokaci mutum ya kan yi nasara kan shaidan, wani lokaci kuma ya sha kasa, wani lokaci ya wayi gari daurarre, malaman kyawawan halaye sun ce: haka al'amarin yake cikin yaki da son rai da biye zuciya, wani lokaci mutum ya kan yi shahada a fafatawa da zuciya, ma'ana dai wannan mutumi har zuwa karshen numfashinsa ya sallamawa Ahlil-baiti (A.S) baya gazawa ko gajiya, saboda haka ne bisa riwayoyi idan wani tare da tsananin bege da soyayya Ahlul-baiti ya rasu a kan gadonsa hakika ya mutu shahidi, saboda ya rasu alhalin yana filin daga filin jihadul akbar (mafi girman jihadi) ko har numfashinsa na karshe bai sallama ba ya mikawa wuya ga son rai. wani lokaci mutum yana samun nasarsa fagen jihadul akbar yana daure shaidan da sasari, wani lokacin kuma Allah ya tsare ya kiyaye faruwar hakan, shaidan yana galaba kansa ya daure shi matsayin fursunansa.
https://javadi.esra.ir/fa/w/دعای-آیت-الله-العظمی-جوادی-آملی-برای-زائرین-اربعی
Allama ɗabaɗaba'i cikin Tafsirul Al-mizan, samuwar shaiɗan wanda yake kiran mutum tare da kwaɗaitar da shi zuwa ga saɓo yana ganinsa matsayin ɗaya daga rukunan samuwa da yake hikaya kan zaɓin da mutum yake da shi da kuma tabbatar da cewa tafiyarsa tana cikin hanya ta neman kamala.[3] filin da shaiɗan yake sukuwa ya kasance fagen shari'a, ba na halitta ba, saboda koyarwar muslunci ta nuna cewa kaɗai shaiɗan yana da iko ne cikin jefa waswasi da kwaɗaitar da mutum zuwa ga saɓo, bai da wani ƙarfi da iko fiye haka, bai da wani iko kan mutum.[4]
Dangantaka Tsakanin Shaiɗan Da Iblis
Kalmar shaiɗan an yi amfani da ita kan Iblis kamar dai yadda muka gani cikin labarin halittar Adam da yadda Shaiɗan ya yi girman kai kan umarnin yi masa sujjada, da kuma yadda ya bi sahun sauran shaiɗan cikin ɓatar da mutane.[5] kalmar shaiɗan an yi amfani da ita kan Iblis kamar yadda ya zo a cikin aya ta 36 suratul baƙara, a wasu wuraren kuma kamar aya ta 121 suratul an'am an yi amfani da ita kan runduna da mabiyan Iblis.[6] a cewar Allama ɗabaɗaba'i daga binciken da aka yi kan wuraren da aka yi amfani da wannan kalma a cikin kur'ani da kuma maganganun malaman tafsiri za a fahimci cewa a mafi yawan wurare abin da ake nufi daga kalmar shaiɗan shi ne dai wannan Iblis.[7] wasu ba'ari sun fayyace magana ƙarara cewa galibi wurare kalmar shaiɗan tana aiki ne kan Iblis.[8] sakamakon yawan amfani da kuma aiki da wannan kalma kansa sai aka wayi gari ta zama suna ga Iblis wace da shi ne ake saninsa.[9]
Shaiɗanun Cikin Mutane Da Aljanu
Cikin matanan litattafan muslunci daga kur'ani da hadisai sun nuna cewa halittar shaiɗan bai da wata keɓantacciyar mahiya, shaiɗan wata halitta ce mai ɓatar da mutane daga da zai iya kasancewa daga jinsin aljanu, kamar yadda Iblis zuriyarsa suka kasance haka, haƙiƙa mutane su ma za su iya kasancewa tare da waɗannan siffofi da halaye na shaiɗan. Allama ɗabaɗaba'i cikin tafsirin « مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ» yana cewa wannan jumla ta kasance ne cikin bayanin «خناس» kuma ishara ce kan cewa wasu mutane an risker da su da shaiɗanu suna cikin gayyarsu, kamar dai yadda a aya ta 12 suratul an'am ubangiji yace cewa:
Shaiɗanun Aljanu da Mutane.[10]
Halaye
Cikin adadin ayoyin kur'ani an siffanta shaiɗan matsayin bayyanannen maƙiyin mutum.[11] a bayyane ya kasance yana ɓatar da mutum (مُضِلٌ مُبین) mai ɓatarwa mabayyani.[12] kuma ya kasance (خَذول) wanda yake watsi da mutum a lokacin da shi mutum ɗin yake tsananin buƙatuwa da taimakonsa.[13] yana ma mutane alƙawari na ƙarya cewa zai cika musu burace-buracensu,[14] yana kiransu zuwa ga jahannama.[15] haka kuma a cikin kur'ani an siffanta shaiɗan da shaiɗanu cewa sun kasance masu butulci,[16] saɓo,[17] taurin kai da girman kai,[18] jefaffe korarrare, [19], [20] ɗan fitina mayaudari,[21] sannan makomarsu ta ƙarshe ta kasance wuta da faɗawa cikin fushin Allah.[22]
Dabarun Yaudara Da Shaiɗan Yake Amfani Da su Kan Mutum
Kur'ani ya yi bayani salo da hanyoyin da shaiɗan yake bi cikin ɓatar da mutum; daga jumlarsu: samar da ƙiyayya,[23] nesanta mutum daga ambaton Allah da tunawa da shi musammam sallah,[24] tsorata mutum da talauci da sauran musibun duniya.[25] ƙayata zunubi da kyawun fuskokin gurɓatattun tunani da ayyuka,[26] kyawuntar da fuskokin ni'imomin duniya da cusa soyayyar mata, ƴa'ya da dukiya,[27] motsa dogon buri,[28] yaɗa fasadi da alfasha da munkari,[29] suna daga sauran hanyoyi da salon shaiɗan da yake amfani da su cikin halakar da mutane kamar yadda suka zo a kur'ani.
Cikin wasu ayoyi daga kur'ani mai girma, an siffanta tasirin shaiɗan matsayin iyakantacce kuma raunanna;[30] shaiɗanu ba za su tsinkaya kan duniyoyin gaibu da ɓoyayyun al'amura ba, kuma sun gaza samun ikon tsinkaya kan sirrikan sammai.[31] duk wanda ya kasance kan hanyar bautar Allah shaiɗanu ba za su taɓa samu iko kansa ba; kaɗai suna samun iko ne kan mutanen da suke biyayya ga shaiɗanu.[32] Allama ɗabaɗaba'i da Makarim shirazi sun tafi kan cewa shaiɗanu suna iya bayyana cikin kowacce irin sura da shakali in banda sura da shakalin Annabawa da Wasiyyai.[33]
Hanyoyin Yaƙar Shaiɗan
Kan asasin hadisai da Allama majlisi ya naƙalto daga ma'asumai cikin Biharul Al-anwar, haƙiƙa ambaton Allah da karanta bismilla cikin farkon kowanne aiki misalin cin abinci,[34] tafiya aiki hajji,[35]alwala.[36] sallah,[37] yayin kusantar iyali[38] abu ne da yake nesantar da shaiɗan.
Dalilin Halittar Shaiɗan Da Ikonsa
Malaman tafsiri sun ba da amsa game da me yasa Allah ya halicci shaiɗan, sannan me ya say a bashi ƙarfi da iko kan bayinsa har yake halakar da su.[39] Kan asasin kur'ani, idan ya zama abin da ake nufi da shaiɗan shi ne dai Iblis, haƙiƙa bayan korarsa daga fadar ubangiji sakamakon saɓawa umarnin ubangiji kan yin sujjada ga Adam, ya nemi Allah ya ɗaga masa ƙafa ya jinkirta masa har zuwa ranar tashin alƙiyama, sai dai cewa Allah ya jinkirta masa zuwa wata ayyananniya kafin tashin alƙiyama.[40] saboda a asalin Allah bai halicci Shaiɗan a lalatacciya gurbatacciyar halitta ba, kamar yadda ya kasance yana bautar Allah tsawon shekaru dubu shida, ya kuma kasance cikin mala'iku da ma'abota ibada, amma sakamakon girman kai gaban Allah, sai ya faɗa cikin ɗagawa aka kore shi daga rahamar Allah.[41] bisa abin da Allama ɗabaɗaba'i ya tafi kansa cikin Tafsirul Almizan, haƙiƙa samuwar shaiɗan ba ta kasance zallan sharri ba, bari ya kasance cuɗanye da alheri.[42]
Hanyar Jarrabawar Mutum
Kan asasin kur'ani haƙiƙa halittar Iblis ta kasance domin jarraba bayin Allah.[43] haka nan Allah ya sanya shawarwarin shaiɗan matsayin jarrabawa ga masu tsatsar zuciya da bushashun zukata.[44]
Bayanin kula
- ↑ Suratul Zukhruf, aya ta 62; Suratul Yusuf, aya ta 5; Suratul Kahf, aya ta 50; Suratul Isra, aya ta 53; Suratul Baqarah, aya ta:168.
- ↑ Asgari, "MNa'ana shinasi nawin wajeh Shaidan", shafi na 214.
- ↑ Allameh Tabatabai, Al-Mizan, 1374, juzu'i na 8, shafi na 38.
- ↑ و ما کان لی علیکم من سلطان الا ان دعوتکم فاستجبتم لی (سوره ابراهیم، آیه ۲۲).
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1375 AH, juzu'i na 29, shafi 192
- ↑ Asgari, “Ma'ana shinasi Wajeh shaidan,” shafi na 214.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i na 7, shafi na 321.
- ↑ Alusi, Ruh Al-Maani, 1417 AH, juzu'i na 4, shafi na 202
- ↑ Shabestari, A`lam Al-Qur’an, 1379 AH, shafi na 83.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, manshurat Ismailian Publications, juzu'i na 20, shafi na 397.
- ↑ Suratul Yaseen, aya ta 60; Suratul Kahf, aya ta 50; Suratul Fatir, aya ta 6; Suratul Baqarah, aya ta 208 da ta 168; Suratul An'am, aya ta 142; Suratul Yusuf, aya ta 5.
- ↑ Suratul Qasas, aya ta 15; Suratul Sad, aya ta 82.
- ↑ Suratul Furqan, aya ta:29.
- ↑ Suratul Nisa’i, aya ta:120
- ↑ Suratul Lukman, aya ta 21.
- ↑ سوره اسراء آیه ۲۷.
- ↑ Suratul Maryam, aya ta 44.
- ↑ Suratul Safat, aya ta 7; Suratul Nisa’i, aya ta:117.
- ↑ Suratul Takwir, aya ta 25; Suratul Nahal, aya ta:98. aboki
- ↑ Suratul Nisa’i, aya ta 38.
- ↑ Suratul A'araf, aya ta 7, 22 da 27; Suratul Taha, aya ta 20 da ta 120.
- ↑ Suratul S, aya ta 84 da ta 85; Suratul Isra, aya ta 63.
- ↑ إِنَّما یریدُ الشَّیطَانُ أَن یوقِعَ بَینَکم العَدَ وةَ والبَغضَاءَ فِی الخَمرِ والمَیسرِ و یصدَّکُم عَن ذکرِاللهِ و عَن الصَّلوَةِ فَهل أَنتم مُنتهونَ (آیه ۹۱ سوره مائده).
- ↑ إِنَّما یریدُ الشَّیطَانُ أَن... یصدَّکُم عَن ذکرِ اللهِ و عَن الصَّلَوةِ (آیه ۹۱ سوره مائده)؛ استَحوذَ عَلیهِمُ الشَّیطَانُ فأَنسَهُم ذِکرَاللهِ أُولَلِکَ حِزبُ الشَّیطَانِ أَلا إِنَّ حِزبَ الشَّیطَانِ همُ الخَسِرونَ (سوره مجادله، آیه ۱۹)؛ مَا أَنسَنِیهُ إلاَّ الشَّیطَانُ (سوره کهف، آیه ۶۳)؛ سوره یوسف، آیه ۴۲.
- ↑ الشَّیطَنُ یعدِکُم الفَقَر (سوره بقره، آیه ۲۶۸).
- ↑ قَالَ ربِّ بِما أَغویتَنِی لاَُزَیننَّ لَهم فِی الأَرضِ (سوره حجر، آیه ۳۹).
- ↑ Suratul Al Imrana, aya ta 14.
- ↑ (Suratul Nisa’i, aya ta 119). Fakhr Al-Razi, Al-Tafsir Al-Kabir, 1411 BC, juzu'i na 11, shafi na 38-39; Tabari, Jami’ al-Bayan, 1415 BC, juzu’i na 4, shafi na 381.ولاَُضِلَّنَّهم ولاَُمنِّینَّهم
- ↑ و مَن یتَّبِع خُطُوتِ الشَّیطَانِ فإِنّهُ یأمرُ بِالفَحشاءِ والمُنکَرِ (Suratul Nur, aya ta 21).
- ↑ إِنَّ کَیدَ الشَّیطَنِ کانَ ضَعیفاً (Suratul Nisa’i, aya ta 76).
- ↑ و حَفظنها مِن کلِّ شیطن رجیم إِلاَّ مَنِ استَرقَ السَّمعَ فَأَتبَعَهُ شِهابٌ مُبِینٌ (Suratul Hijir, aya ta 17 da 18). Suratul Safat, aya ta 6-10; Suratul Malik, aya ta 5.
- ↑ إِنَّ عِبادِی لَیسَ لَکَ عَلیهِم سُلطَنٌ إِلاَّ مَنِ اتَّبَعکَ مِن الغَاوینَ (سوره حجر، آیه ۴۲)؛إِنَّ عِبادی لَیسَ لَکَ عَلیهِم سُلطَنٌ و کَفَی بِربِّکَ وَکِیلا (سوره اسراء، آیه ۶۵)؛ سوره نحل، آیه ۹۹.
- ↑ Allama Tabatabai, Al-Mizan, 1374 AH, juzu'i na 8, shafi na 62; Makarem Shirazi, Tafsir Namuna, 1375 AH, juzu'i na 7, shafi na 202.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 60, babin ambaton Shaidan da labaransa, shafi na 203, na 25 da 26.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 60, babin ambaton Shaidan da labaransa, shafi na 201-202, mujalladi na 21.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 60, babin ambaton Shaidan da labaransa, shafi na 203, juzu'i na 27.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 60, babin ambaton Shaidan da labaransa, shafi na 202, juzu'i na 24.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 60, babin ambaton Shaidan da labaransa, shafi na 201, juzu'i na 19; shafi 202, h. Shafi na 207, H42.
- ↑ Allama Tabatabai, Al-Mizan, 1374 AH, juzu'i na 8, shafi na 54-69.
- ↑ قَالَ رَبِّ فَأَنظِرنِی إِلَی یومِ یبعثونَ قَالَ فَإِنّکَ مِن المُنظَرینَ الی یوم الوقت المعلوم (سوره حجر، آیه ۳۶ و ۳۷).
- ↑ Nahj al-Balagha,tas'hihu Subhi Saleh, hadisi na 192, shafi na 285-286.
- ↑ Allama Tabatabai, Al-Mizan, 1374 AH, juzu'i na 8, shafi na 37
- ↑ و مَا کَانَ لهُ عَلیهم مِن سُلطَن إِلاَّ لِنعلمَ مَن یؤمنُ بِالأَخرةِ مِمّن هُوَ مِنها فِی شَکّ (سوره سبأ، آیه ۲۱).
- ↑ لِیجعَلَ مَا یلقِی الشَّیطَنُ فِتنةً لِلَّذینَ فِی قلوبِهم مَرضٌ والقَاسِیةِ قُلوبُهم (سوره حج، آیه ۵۳).
Nassoshi
- Ahmed bin Mohammad Ghazali, majmu'eh asare Farsi n Press, 1376.
- Ain al-Qadah Hamdani, Tamhidat, tare da gabatar da gyara daga Afif Asiran, bugu na 7, Tehran, Buga Manochehri, 2006.
- Allameh Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Jamia Modaresin, 1374.
- Alqur'ani mai girma.
- Asgari, Ansieh, "Ma'ana shinasi wajeh Shaitan", a cikin Mujallar Qobsat, No. 64, Winter 2009.
- Baghli, Rozbahan, Sharah Shathyat, editan Henry Carbone, bugu na uku, harshe da al'adun Iran, Tehran, bazara 1374.
- Beizawi, Naseruddin, Anwar al-Tanzil wa Asrar al-Tawil, Beirut, Dar al-Fakr, Bita.
- Fakhr al-Razi, Muhammad bin Umar, Al-Tafsir al-Kabir ko Mufatih al-Ghaib, juzu'i na 11, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1411 AH/1990 AD.
- Gonabadi Sultan Muhammad, Tafsir Bayan al-Saada fi Maqamat al-Ibadah, bugu na biyu, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1408 AH.
- Hallaj Hossein bin Mansour, Tawasin, littafin Mahmoud Behfrozi, bugu na farko, Alam Publications, 2004.
- Hassanzadeh Amoli Hassan,Hezarro yek kaleme, Juzu'i na 4, Fitowa Na Uku, Gidan Bugawa na Kitab, Qum, 2001.
- Ibn Arabi Mohi al-Din, Tafsirin Ibn Arabi, wanda Samir Mustafa Rabab ya yi bincike, bugun farko, Beirut, Dar Ahya Al-Tarath al-Arabi, 1422H.
- Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1403H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuna, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1375.
- Meybodi Rashiduddin, Kashf al-Asrar wa Uddatil al-Abrar, wanda Ali Asghar Hekmat ya yi bincike, bugu na biyar, Tehran, Amir Kabir Publishing House, 1371.
- Mulla Sadra, Muhammad, Tafsir Kur'an al-Karim, Muhammad Khajawi ya yi bincike, bugu na biyu, Kum, Bidar Publications, 1366.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Jami al-Bayan an Tawil Ayye Qur'an, tare da kokarin Jamil Attar Sedqi, Beirut, Darul Fikr, 1415H.
- Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Publisher: Ismailian Manifesto, Bita, Bija.
- Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, ya gyara shi, 1980.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tabian fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Beita.
- Hassanzadeh Amoli Hasan, ittihadu Akilu be makul, bugu na biyu, Tehran, gidan buga littattafai na Hekmat, 1366.
- https://javadi.esra.ir/fa/w/دعای-آیت-الله-العظمی-جوادی-آملی-برای-زائرین-اربعی