Shekara Ta 8 Hijira
Appearance
Shekara 9 Hijira Ƙamari Shekara 7 Hijira Ƙamari | |
| 629 da 630 miladiyya | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Annabtar Sayyidina Muhammad (S.A.W) | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Muhammad Bin Abdullah (S.A.W) A Madina | (Hukuma:1-11 hijira ƙamari) |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Yaƙin Mu'utata | |
| Fatahu Makka | |
| Yaƙin Hunainu | |
| Haihuwa da mutuwa | |
| Ibrahim Ɗan Manzon Allah | |
| Wafati/Shahada | |
| Zainab Ƴar Annabi (S.A.W) | |
| Shahadar Jafar Bin Abi Ɗalib | |
| Shahadar Zaidu Bin Harisa | |
| Shahadar Abdullahi Bin Rawaha | |
| Halimatus Sa'adiyya | |
Shekara ta 8 hijira ƙamari,( Larabci: سنة 8 للهجرة) ita ce shekara ta takwas a jerin lissafin kalandar hijira.
Rana ta farko a wannan shekara tana kasancewa ɗaya ga Muharram wanda ya yi daidai da ranar Dushambe 14 ga watan Urdibeheshti shekara ta 8 kalandar Farsi kuma 4 ga watan Mayu shekara ta 629 miladiyya. Rana ta ƙarshen shekarar hijira ko shekarar Muslunci tana kasancewa 29 Zil-Hijja, daidai da ranar Panjishanbe (Ranar Alhamis) 1 ga watan Urdibeheshti shekara ta 9 kalandar Farsi kuma daidai da 22 Afrilu shekara ta 630 miladiyya.[1]
Yaƙin Mu'utata, Fatahu Makka, Yaƙin Hunainu da haihuwar Ibrahim Ɗan Annabin Muslunci (S.A.W) da kuma dai rasuwar Zainab Ƴar Annabi (S.A.W) suna cikin abubuwan da suka faru a wannan shekarar.
Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Wannan Shekara
- Yaƙin Mu'utata a ranar 5 Jimada Al'ula tsakanin sojojin Musulmi da Rum.[2]
- Sariyya Zatil Salasil cikin martani ga harin wasu ƙabilu misalin ƙuza'atu.[3]
- Saukar suratul Adiyyat game da bayanin jarumtakar Imam Ali (A.S) a lokacin yaƙin zatil salasil.[4]
- Fatahu Makka a ranar 18 Ramadan da Musulmi suka yi nasara.[5]
- Bai'a tare da Annabi (S.A.W) bayan Fatahu Makka.[6]
- Yaƙin Hunainu a Shawwal tsakanin Musulmi da ƙabilun Hawazan da Saƙif.[7]
- Yaƙin Ɗa'if a watan Shawwal[8]
- Yaƙin Sariyya Galib Bin Abdullah domin tunkarar ƙabilar Bani Al-Maluhi a yankin Kadid da Sariyya Khabaɗ domin tunkarar ƙabilar Juhaina.[9]
- Musluntar Abu Sufyan bayan Fatahu Makka.[10]
- Musluntar Amru Bin Asi Sahami daga masu adawa da Sayyidina Ali (A.S) kuma wakilin Mu'awiya a lokacin yin Tahkim.[11]
Haihuwa
- Haihuwar Ibrahim Ɗan Annabin Muslunci (S.A.W) ranar 7 Zil-Hijja.[12]
Rasuwa
- Rasuwar Zainab Ƴar Annabi (S.A.W).[13]
- Shahadar Jafar Bin Abi Ɗalib a yaƙin Mu'utata[14]
- Shahadar Zaidu Bin Harisa a yaƙin Mu'utata.[15]
- Shahadar Abdullahi Bin Rawaha a yaƙin Mu'utata.[16]
- Rasuwar Bishru Bin Barra, sahabin Annabi (S.AW) wanda ya ci guba a yaƙin Khaibar.[17]
- Rasuwar Halimatus Sa'adiyya, uwa da shayar da Annabi (S.A.W) nono.[18]
Bayanin kula
- ↑ سایت تبدیل تاریخ هجری
- ↑ Waqidi, Al-Magazi, 1409 AH, Juzu'i na 2, shafi na 755-761.
- ↑ Tabari, Tarikh Al’umam Wal Muluk, 1387H, juzu'i. 2, shafi. 32.
- ↑ Tabarsi, Majma'ul al-Bayan, 1367, juzu'i. 10, shafi na 802-803; Makarem Shirazi, Tafsir al-Numno, 1374, juzu'i. 27, shafi. 240.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiya, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 389.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i. 3, shafi. 61.
- ↑ Waqidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 892.
- ↑ Tabarsi, I'ilam al-Wara, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 233; Bayhaqi, Dalail al-Nubuwwa, 1405 AH, juzu'i. 5, shafi. 156.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i. 3, shafi. 27.
- ↑ Waqidi, Al-Magazi, 1409 AH, Juzu'i na 2, shafi na 817-818.
- ↑ Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i. 3, shafi. 1185.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 1, shafi. 108.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i. 3, shafi. 28.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 198.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 473.
- ↑ Ibn Hajar Asqalani, al-Isabah, 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 72.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1410H, juzu’i. 3, shafi na 429-430; Ibn Abdul-Barr, Al-Isti'ab, juzu'i. 1, shafi. 167.
- ↑ Ibn Athir, Al-Kamil, 1385H, juzu'i. 1, shafi. 460.
Nassoshi
- Ibn Athir, Ali bn Abi al-Karam, Al-Kamil fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sader, 1385.
- Ibn Abdul-Barr, Yusuf bn Abdullah, Al-Isti’aab fi ma’rifat al-Ashab, wanda Ali Muhammad al-Bajawi ya yi bincike a Beirut, Dar al-Jil, 1412H.
- Ibn Hisham, Abdul-Malik, Al-Sirat al-Nabawiyya, Beirut, Dar al-Mara’if, Beta.
- Ibn Hajar Asqalani, Ahmad bn Ali, Al-Isabah fi tam’iz al-Sahaba, Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah, 1415H.
- Baladzuri, Ahmad bn Yahya, Jamal min Ansab al-Ashraf, Suhail Zakkar da Riyad Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, Beirut, 1417 bayan hijira.
- Bayhaqi, Abu Bakr Ahmad bn Husayn, Dalail al-Nubuwwah wa ma’rifat ahwal sahib al-Shari’ah, bincike na Abdul-Mu’ati Qalaji, Beirut, Dar al-Kutb al-Ilmiyah, 1405H.
- Tabarsi, Fadl bn Hassan,I'ilam al-Wara bi-A'alam al-Huda, Qum, Aal al-Bayt Foundation (AS), 1417H.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir Alqur'an, wanda Muhammad Jawad al-Balaghi ya buga da sauransu, Beirut, Darul-Marfa, 1367H/1408H.
- Tabari, Muhammad bn Jarir, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, Beirut, Darul-Turat, 1387H.
- Amili, Sayyid Jafar Murtaza, Sahih min Sirat al-Nabi al-Azam, Kum, Darul-Hadith, 1426H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Numno, Tehran, Darul Kutb al-Islamiyya, 1374H.
- Waqidi, Muhammad bn Omar, Kitab al-Magazi, Beirut, Al-Alami Foundation, bugu na uku, 1409H.