Jump to content

Zabura

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne da aka yi game da Littafin Annabi Dawud. domin sanin Zaburar Alu Muhammad, ku duba shafin Sahifa Sajjadiyya.

Zabura, (Larabci:الزبور) littafin Allah ne wanda aka saukar wa Annabi Dawud (A.S). Zabura ba ta ƙunshi sababbin dokoki da hukunce-hukunce ba, amma tana ɗauke da nasihohi da addu'o'i da munajati. Kamar yadda ayoyin kur'ani suka nuna, Annabi Dawud ya fi wasu annabawan daraja saboda ba shi Zabura da Allah ya yi, Kamar yadda wasu ruwayoyi suka nuna, Zabura na ɗaya daga cikin alamomin imamanci kuma an ambaci sunan Manzon Allah (S.A.W).

A cewar wasu masu bincike, Zabura a cikin littafin kiristoci na bible, akwai wasu ayoyi da ake kira mazamir wanda aka ce daga Zabura ta Annabi Dauda suke, waɗanda suka tsira daga ɓacewa, wato su ba a neme su an rasa ba, Zabura da Attaura suna cikin amintattun tushen addini da al'adun Yahudawa. Duka sun haɗa da littattafai biyar da mazmur 150, daga cikinsu mazmur 73 aka jingina ga Annabi Dauda. An ce aya ta 105 a cikin suratun Anbiya ita ce kawai abin da aka naƙalto daga Kur'ani acikin Attaura, wanda har yanzu yana nan a cikin ɓangaran mazamir.

Gabatarwa da Muhimmanci

Kamar yadda wasu ruwayoyi suka ce, Zabura tana ɗaya daga cikin litattafai na sama guda 104[1] da cikin Ramadan 18 aka saukar wa Annabi Dawud (A.S),[2] kuma ba ta da wasu sabbin dokoki da sharia, sai Addu'oi da munajati,[3] Zabura ɗaya ne daga cikin ajiyoyin imamanci kuma an ajiye ta a Jafru Abyad.[4]

Kamar yadda aka ruwaito daga Sayyiduna Muhammad (S.A.W) a cikin Zabura an ambaci sunan Annabin Musulunci da sunan "Mahi" wanda ke nufin mai shafe ƙasa daga bautar gumaka[5] A wasu hadisai an ce, sunan Imam Ali (A.S) ma ya zo,[6] hakanan wasu hadisai suna cewa Allah ya ba Annabin Musulunci surorin Masani (Baƙara da Alu Imran) maimakon Zabura,[7] Wasu littafai kamar Sahifa Sajjadiya da wasu Masnawi na Aɗɗar Nishaburi, ana kiransu Zabura saboda sun ƙunshi addu'a da kyawawan ayyukan da ya kamata ɗan Adam ya dinga yi,[8] Ma'anar kalmar Zabura yana nufin "Rubutacce".[9]

Ayoyin Da Suke Da Alaƙa Da Zabura a Cikin Al-Kur'ani

Rubutun Aya ta 105 Suratu Anbiya jikin Haramin Imam Husaini (A.S)

An ambaci kalmar Zabura sau uku a cikin Alƙur'ani cikin aya ta 163 cikin suratul Nisa'i da aya ta 55 a cikin suratul Isra'i, an bayyana ta a matsayin kyauta ga Annabi Dawud,[10] Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i mawallafin littafin Almizan Fi Tafsiril Kur'an, ya yi nuni da aya ta 163 a cikin suratun Nisa'i da cewa dalilin ɗaukakar Annabi Dawud a kan wasu annabawa ya kasance ne sakamakon saukar masa da Zabura da aka yi,[11] A cikin aya ta 196 cikin suratul Shu'ara, Zabura ta zo a jam'i (Zabur) kuma tana nufin littafan sama waɗanda aka saukar wa annabawan da suka gabace shi, musamman littafin da aka saukar wa Dawud ba.[12]

An ambaci kalmar "Zabura" a cikin ayar (Kuma mun rubuta a cikin Zabur bayan ambato, bayina salihai ne za su gaji ƙas),[13] duk da an ambaci kalmar zabur a cikin ayar, sai dai an kawo tafsirai daban-daban game da hakan; Sai dai kuma Allama Ɗabaɗabai, ya yi nuni da wasu ayoyi, akan cewa littafin Annabi Dawud shi ne ake nufi a wannan ayar,[14] Wasu masu bincike suna ganin aya ta 105 a cikin suratul Anbiya a matsayin ɗaya tilo da aka naƙalto daga kur'ani kai tsaye a littafin bible.[15] Muhammad Sadiƙi Tehrani da Nasir Makarim Shirazi, wasu daga cikin malaman tafsirin ƙarni na 15, sun yi bincike da nazari a mazamir da suka zo a cikin Attaura, sun cimma matsayar cewa jigon wannan ayar an kawo shi a cikin mazamir na bible.[16]

Ɗabbaqa Zabura Kan Wasu Ɓangaren Littafi Mai tsarki (Bible)

Hoton mafi kyawun kwafin Zabura na Dauda, ​​na ƙarni na 4 AD, an adana shi a cikin Gidan Tarihi na 'yan Kibɗawa na Misra.[17]

Wasu malaman tafsiri kamar Makarim Shirazi da Sadiƙi Tehrani, sun ɗabbaƙa Zabura na Annabi Dawud a kan wasu sassa na bible (Mazamir ɗin bible), amma sun yi imani da cewa a cikin wannan ɓangare na bible ɗin ma an tafka ta'adi wajan goge wasu abubuwan da canza wasu da ƙara wasu.[18] Tabbas Sadiƙi Tehrani ya yi imani da cewa bayan Alƙur'ani, babu wani littafi na sama da ya tsira daga jirkita kamar Zabura, wato gurɓatashin da aka yi kaɗan ne,[19] a faɗin wasu masu bincike akwai kama sosai tsakanin Alƙur'ani da Zabura, kamar wasu misalai iri ɗaya ko wasu kalmomi masu nauyin ma'ana waɗanda suke nuni da cewa daga tushe ɗaya suka fito,[20] mazmur na 45 ya yi magana kan Annabin Musulunci da sahabbansa.[21]

Jimillar mazamir litattafai guda biyar ne.[22] wan da suke ƙunshe da mazmur 150.[23] daga cikinsu mazmur 73 an jingina su ga Annabi Dawud,[24] wasu an jingina su ga Annabi Sulaiman, wasu kuma an jingina su ga wasu mutane da aka sani ko waɗanda ba a sani ba.[25] mazamir ɗin bible anyi musu tsarin waƙa,[26] kuma suna ɗaya[27] daga cikin amintattun tushen addini da al'adun Yahudawa,[28] kuma babu wasu daga cikin littattafai masu tsarki da suke karantawa inka ɗauke bible, kamar Zabura.[29]

Ku Duba Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Duba: Sheikh Sadouq, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 524.
  2. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 157
  3. Makarem Shirazi wa digaran, Payam Qur'an, 2006, juzu'i na 7, shafi na 348.
  4. Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 186.
  5. Sheikh Sadouq, Ilalul Al-Shara'i, 1385, juzu’i na 1, shafi na 128.
  6. Duba: Sheikh Sadouq, Ma'ani Al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 59; Ibn Shazan Qomi, Al-Fadael, 1363, shafi na 175.
  7. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 601.
  8. Izanlo, da Khandaghabadi, "Zobor", shafi na 254.
  9. Asadi, "Zobor", shafi na 288.
  10. Duba: Suratu Nisa, aya ta 163; Da kuma Suratul Isra’i aya ta 55.
  11. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 Hijira, juzu'i na 13, shafi na 120.
  12. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 Hijira, juzu'i na 15, shafi na 320.
  13. Suratul Anbiya, aya ta:105.
  14. Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 14, shafi na 329.
  15. Izanlou, wa Khandaghabadi, "Zobor", shafi na 251.
  16. Sadeghi Tehrani, al-Furqan, 1406 AH, juzu'i na 19, shafi na 379-382; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 13, shafi na 566.
  17. فرحات، «مزامیر داوود»
  18. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 13, shafi na 520; Sadeghi Tehrani, al-Furqan fi Tafsirin Kur’ani, 1365, juzu’i na 17, shafi na 230.
  19. Sadeghi Tehrani, Al-Furqan fi Tafsiril Kur’ani, 1365, juzu’i na 17, shafi na 230.
  20. Sadeghi Tehrani, Al-Furqan fi Tafsiril Kur’ani, 1365, juzu’i na 17, shafi na 230.
  21. Balaghi, Qasas Kur'an, 1381, shafi na 375.
  22. Mr. Hawkes, Qamus Kitabe Mukqaddas, 1377, shafi na 796.
  23. Balaghi, Qases Kur'an, 1381, shafi na 375.
  24. Khazaeli, I'lam Kur'an, 1371, shafi na 347.
  25. Mr. Hawks, Qamus Kitabe Muqaddas, 1377, shafi na 797.
  26. Izanlo, wa Khandaghabadi, "Zobor", shafi na 249.
  27. Asadi, “Zobor”, shafi na 291.
  28. Asadi, “Zobor”, shafi na 291.
  29. Mr. Hawks,Qamus Kitabe Muqaddas, 1377, shafi na 799.

Nassoshi

  • Alqur'ani Kareem.
  • Balaghi, Sadr al-Din, Qases Qur'an, Tehran, Amir Kabir, 1381.
  • Ibn Shazan Qomi, Al-Fadael, 1363, shafi na 175. * Asadi, Ali, "Zobor", dar Dayiratul Almarif Qur'an Kareem, juzu'i na 14, Qom, Bostan Kitab, 1395.
  • Khazaeli, Mohammad, I'lam Kur'an, Tehran, Amirkabir, 1371.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Darul-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1374.
  • Makarem Shirazi, Nasser, wa digaran, Payam Qur'an, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1386.
  • Malam Hawks, Qamus Kitabe Muqaddas, Tehran, Asatir, 1377.
  • Sadeghi Tehrani, Mohammad, Al-Furqan fi Tafsirin al-Qur'an with the Qur'an and Sunnah, Qum, Islamic Farhang Publications, 1365.
  • Sheikh Mofid, Muhammad bin Nu'man, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid (RA), 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Al-Khisal, Qum, ofishin yada labaran Musulunci, 1362.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ilalul Shara'i, Qum, Davari, 1385.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bn Ali, Ma'ani Al-Akhbar, Qum, ofishin da'a na Musulunci, 1403H.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsiril Qur'an, Qum, Islamic Publications Office, 1417 AH.
  • Izanloo, Ramzanali, and Hossein Khandaqabadi, «زبور»، A cikin Encyclopedia na Duniyar Musulunci, Vol. 21, Tehran, Islamic Encyclopedia Foundation, 2016.
  • Farhat, Fatima,«مزامیر داوود»،A gidan yanar gizon Mujallar Hafen, kwanan watan shiga: Oktoba 31, 2019, kwanan wata: Janairu 1, 1402 AH.