Itikafi
Itikafi, (Larabci: الإعتكاف) zama a masallaci (Mafi ƙarancinsa kwanaki uku) cikin halin azumi, itikafi bai da keɓantaccen lokaci, sai dai kuma cewa ya zo cikin hadisi mafi alherin lokacin yin itikafi shi ne kwanakin goman ƙarshen watan ramadan. Akwai keɓantattun hukunce-hukunce da ladubba yadda ake zama a masallaci da kuma fita.
A ƙasar Iran ana shirya itikafi a fararen ranaku (kwanakin 13, 14, 15) ga watan rajab cikin manyan masallatai a galibin garuruwan ƙasar. Bisa abin da ya zo daga hadisai an kwatatanta itikafi da zuwa aikin hajji da umara, sannan kuma yana sanya gafarta zunubai da kuɓuta daga shiga wutar jahannama.
Muhimmanci Da Falala
Itikafi, ibada ce ta mustahabbi wace cikin hadisai da aka naƙalto daga Imamai ma'asumai (A.S) sun kwatanta shi da zuwa aikin hajji da umara.[1] itikafi yana matsayin sunnar Annabi (S.A.W) zaka samu mafi yawan ƙasashen musulmi suna shirya yin sa.
Ma'ana
Fiƙihun muslunci ya bayyana itikafi da zama cikin masallaci tsawaon kwanaki uku ko fiye da haka da niyyar ibada neman kusanci da Allah tare da wasu ayyuka na musamman. Sannan ana kiran mutumin da ya shiga itikafi da suna mutakif.[2] an ciro kalmar اعتکاف (itikafi) daga «عکف» (Akafa) wace a harshen larabci take ɗaukar ma'anar karkata ga wani abu da girmama shi.[3] haka nan cikin kur'ani kalmar «عاکف» (Akifu) ta zp da ma'ana mazauni.[4] sannan kuma «معکوف» (Ma'akufu) tana da ma'ana abin da aka yi hani kansa da wanda aka tsare.[5]
Itikafi A Mahangar Irfani
A isɗilahin irfani, itikaf yana nufin karkaɗe zuciya daga barin duk wani abu wand aba Allah ba tare da sallama zuciya zuwa ga majiɓicin al'amarinta.[6] Allama majlisi yana ganin haƙiƙanin itikafi da fuskantuwar bawa zuwa ga ɗa'ar ubangiji da kuma lazimtar muraƙaba da taka tsantsan.[7] haka nan malamin yana ganin kamalar itikafi cikin tattaro zuciya da hankali da sauran gaɓoɓin jiki kan aikata ayyuka nagargaru tare da taka tsantsan daga gafala da kuma yi wa kai dabaibayi da umarnin Allah, da tabbatuwar iradar Allah da nesanta duk abin da ba Allah ba daga dukkanin samuwar bawa.[8]
Ladubba Da Hukunce-hukunce
Lokaci
Babu ayyanannen lokaci ga itikafi, sai dai kuma bisa abin da ya zo daga hadisin Manzon Allah (S.A.W) haƙiƙa ya kasance yana itikafi a watan ramadan.[9] da wannan dalili ne mafi alherin lokacin yin itikafi shi ne watan ramadan, musammam goman ƙarshen ramadan.[10] a wannan zamani a ƙasar Iran ana shirya zaman itikafi a fararen kwanaki (ranakin 13, 14. 14) a watan rajab, haka nan wasu ƙasashen suna shirya itikafi.[11] a waɗannan ranaku..[12]
Tsawon Lokaci
A ra'ayin malaman fiƙihu na shi'a mafi ƙarancin kwanakin itikafi shi ne kwanaki uku, bayan ƙarshen rana ta biyu haƙiƙa itikafi rana ta uku yana kasancewa wajibi.[13] lokacin itikafi yana fara daga hudowar alfijir na ranar farko zuwa faɗuwar rana ta uku.[14] na'am a ra'ayin Malik ɗan Anas,[15] da Shafi'i[16] daga cikin shuwagabannin mazhabobi huɗu na ahlus-sunna, suna ganin mai itikafi wajibi ne gabanin faɗuwar rana ya kai kansa mahallin itikafi.[17]
Mahalli
Ba'arin riwayoyi, haƙiƙa sun tafi kan cewa mahallin yin itikafi ya keɓanta da masallacin harami, masallacin annabi, masallacin kufa da masallacin juma'a na basra, sai dai kuma akwai wasu riwayoyin da suka bayyana cewa za a iya yin itikafi a duk wani babban masallacin juma'a na gari ko wani masallaci da adalin limami yake jagorantar sallar juma'a a cikinsa ko sallar jam'i.[18] da wannan dalili ne mafi yawan malaman fiƙihu daga magabata suka tafi kan cewa kaɗai ana yin itikafi ne a masallatai guda huɗu.[19] amma kuma Shahidul Awwal da Shahidul Sani sun ce, maganar keɓantuwar itikafi a masallatai huɗu magana ce mai rauni.[20] galibin malaman fiƙihu a ƙarni na goma sha huɗu hijiri, suma sun tafi kan ingancin yin itikafi cikin masallatan juma'a da suke a garuruwa.[21] ba'ari suna ganin babu matsala yin itikafi a sauran masallatai (daga na juma'a da wanda ba na juma'a ba) koma bayan masallatai huɗu da niyyar fatan samun lada..[22]
Sharaɗin Kasancewa Tare da Azumi
Daidai da fiƙihun shi'a, azumi yana daga rukunan itikafi;[23] da wannan dalili ne wanda ba zai iya yin azumi ba; daga misalin matafiyi, mara lafiya da mace mai haila, itikafinsu ba ya inganta.[24] ya halasta ƙulla niyyar azumin ramuwa da bakance a cikin itukafi.[25] Muhammad ɗan Idris Shafi'i da Ahmad ɗan Hanbal daga shuwagabannin mazhabobi huɗu na ahlus-sunna basa ganin wajabcin yin azumi lokacin itikafi.[26] amma a fiƙihun malikiyya a maganar da ta shahara a mazhabar hanafiyya ba zai yi wu a yi itikafi ba tare da azumi ba.[27]
Rashin Fitowa Daga Masallaci
Tsawon lokacin zama a itikafi, fitowa daga masallaci domin wasu buƙatu na larura misalin nemo abin ci, ko kuma wasu al'amura da suke tattare da maslaha kamar dai misalin sallar juma'a, raka jana'iza, bada shaida da dubiyar mara lafiya duka waɗannan abubuwa sun halasta a fita domin su. Na'am hatta cikin waɗannan wurare wajibi ne mai itikafi ya wadatu da iya haddin larura cikin su bai kamata ya je ya zauna a wani wuri ba, idan har ma zai yi wu ka da ma ya bi hanyar da take da inuwa.[28] Sayyid Kazim ɗabaɗaba'i Yazdi cikin littafin Al-urwatul Al-wusƙa yana ganin halascin fitowa daga masallacin da mutum yake yin itikafi domin biyan wata buƙata ta larura al'adance da shari'a da take tattare da maslaha (maslahar tana da alaƙa da mutumin da yake itikafin ne ko kuma wani daban).[29] haka nan bisa rahotanni da suka zo daga littafin Biharul Al-anwar daga Uddatu Ad-da'i an naƙalto cewa, Imam Hassan Al-mujtaba (A.S) ya kasance yana yanke ɗawafinsa domin biyan bashin ɗaya daga cikin ƴan shi'arsa, yak an raka shi har ya sauke biya masa bashin.[30][Tsokaci 1]
Abubuwan Da Suka Haramta
A cewar malaman fiƙihu, haramun lokacin itikafi a shafa turare, rigima da jidali kan al'amuran duniya, saye da sayarwa (In banda cikin halin larura), istimna'i, jima'i (hatta sumbata), kuma yin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa yana lalata itikafi.[31] haka kuma duk wani abu da yake lalata azumi yana lalata itikafi.[32]
Falsafa Da Tasiri
Bisa abin da ya zo daga riwayoyi, yin itikafi yana sanya samun gafarta zunubai.[33] nesantuwa daga jahannama,[34] haka kuma yana samar da kyakkyawan yanayin tunani, damar yin addu'a da ibada, samar da damar tuba, dukkanin waɗannan abubuwa ana lissafa su daga falsafa da hikima itikafi.[35]
Tarihinsa
Musulmai sun koyo hanyar yadda ake itikafi daga sunnar Annabi (S.A.W).[36] bisa wata riwaya, tun kafin muslunci akwai itikafi.[37] Rahotan da aka bayar game da itikafin Annabi yana da alaƙa ne da zamanin hijirarsa zuwa madina a lokacin watan ramadan, ya kasance ana kafa masa tanti cikin masallaci annabi.[38] a wannan zamani da muke ciki a cikin masallacin Annabi bangaren dama akwai wata matokara sutunul tauba da ake kira da “sariru" (gado) an ce kwanakin itikafi Annabi (S.A.W) yana yin shimfiɗa kusa da wannan matokara ya zauna itikafi.[39] Annabi muslunci lokacin watan ramadan a shekara ta biyu bayan hijira sakamakon yaƙin badar bai samu damar yin itikafi ba; da wannan dalili ne shekarar da ta zago, sai ya shiga itikafin kwanakin ashirin cikin watan ramadan, kwanaki goma na wannan shekara sauran goman kuma ramuwar shekarar da ta gabata.[40] cikin madogaran riwaya an naƙalto itikafin Imaman shi'a daga jumlar su Imam Hassan Al-mujtaba (A.S)[41] da Imam Sadiƙ (A.S).[42]
Itikafin A Zamanin Mulkin Masarautar Safawiyya Da Pahlawi Bisa rahotan Shaik Luɗfullahi Misi (Wafati: shekara 1035 hijiri) a zamanin mulkin safawiyya a garin ƙazwin da isfahan ya kasance ana shirya itikafi.[43] ba'arin rahotanni sun kawo cewa a lokacin mulkin gwamnatin Shah Pahlawi, itikafi ya yi matuƙar ƙaranta kuma ana yinsa kaɗai cikin garuruwan masu riƙo da addini.[44]
Nazari
An yi rubuce-rubuce daban-daban cikin harshen farisanci da larabci game da itikafi, ba'arin waɗannan rubuce-rubuce su ne kamar haka:
- "Kitabul Al-Itikaf" na Muhammad ɗan Idris Shafi'i da Dawud Isfahani[45] haka nan Shaik Saduƙ da Abu Fazli Sabuni su ma sun wallafa littafi da wannan take.[46]
- Al-Itikafiyya, na Mu'in Badrud-dini Salim ɗan Badran basri.[47]
- Al-Itikafiyya Ya Ma'ul Al-hayat Wa Safi Al-furat, na Shaik Luɗfullahi Misi (Wafati:1033. hijiri) wanda bisa ƙoƙarin Rasul Jafariyan aka buga shi a shekara 1377 shamsi cikin mujalladi ta hannun kamfanin Miras Islami Iran ƙum.
- Al-kafaf Fi Masa'il Al-itikaf, na Muhammad Jafar Astir'abadi (Wafati:1263. hijiri)akwai kwafin wannan littafi a ɗakin nazari na Ayatullahi Mar'ashi Najafi.[48]
- Al-Itikafiyya, na Sayyid Muhammad Ali Shaharistani (Wafati:1290. Hijiri) wanda Agha Buzurg Taharani ya bada rahotan samuwar kwafin littafin.[49]
A shekarun nan na ƙarshe-ƙarshe tare da yaɗuwar sunnar itikafi, an buga gomman litattafan da suka ƙunshi batun itikafi.[50]
Bayanin kula
- ↑ Sheikh Sadouq, Man la Yahzara al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 188; Ibn Tavus, Iqbal al-Amal, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 195
- ↑ Mu’assasa Dayiratu Al-marif Al-Fikih Al-islami, Farhang fikh farsi, 1382H, juzu’i na 1, shafi na 598.
- ↑ Rageb, Mufradat, 1392 BC, shafi na 355.
- ↑ Suratul Hajji, aya ta:25.
- ↑ Suratul Fath, aya ta 25.
- ↑ Jurjani, Al-Tarifat, 1357H, shafi na 25.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 4.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 98, shafi na 150.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1401 BC, juzu'i na 4, shafi na 175.
- ↑ Misali, duba: Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiya, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 149; Jeziri, Fiqhu Ali al-Mahabh al-Arba, 1406 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 582.
- ↑ «تاریخچه اعتکاف»، خبرگزاری تسنیم.
- ↑ «مراسم اعتکاف در کشورهای جهان»، خبرگزرای ایرنا؛ «استقبال چشمگیر جوانان»، شیعه نیوز.
- ↑ Mohaghegh Hilli, Shara’i al-Islam, 1389 AH, juzu’i na 1, shafi na 216.
- ↑ Tabatabai, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1420 AH, juzu'i na 3, shafi na 671.
- ↑ Malik, Al-Muwatta’, 1406 BC, juzu’i na 1, shafi na 314.
- ↑ Shafi’i, Al-Umm, Dar Al-Ma’rifah, juzu’i na 2, shafi na 105.
- ↑ Ibn Rushd, Bidayat al-Mujtahid, 1406 BC, juzu'i na 1, shafi na 314.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1401 BC, juzu'i na 4, shafi na 176; Mufid, Al-Muqnia, 1410 AH, shafi na 363.
- ↑ Duba: Sadouq, al-Muqna, 1404 AH, shafi na 18; Duba kuma: Said Morteza, Al-Entisar, 1391 AH, shafi na 72; Tusi, Al-Khilaf, 1407H, juzu'i na 2, shafi na 272.
- ↑ Shahid Sani, al-Rawda al-Bahiyya, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi 150.
- ↑ Khomeini, Tahrir al-Wasila, Dar al-Alam, juzu'i na 1, shafi na 305; Golpayegani, Jami'ul al-Masa'il, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 175; Safi Golpayegani, Jame al-Ahkam, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi 144; Behjat, Esfatataat, 1428H, juzu'i na 2, shafi 442.
- ↑ «مکان اعتکاف»، پایگاه اطلاعرسانی حوزه.
- ↑ Malik, Al-Muwatta’, 1406 BC, juzu’i na 1, shafi na 315; Muhaqqiq Hilli, Sharia’ul-Islam, 1389H, juzu’i na 1, shafi na 215.
- ↑ Naraghi, Mustanad al-Shia, 1415 AH, juzu'i na 10, shafi na 546.
- ↑ Naraghi, Mustanad al-Shia, 1415 AH, juzu'i na 10, shafi 545.
- ↑ Duba: Shafi'i, Al-Alam, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 107; Ibn Habirah, al-Ifsah, 1366 AH, juzu'i na 1, shafi na 170; Duba kuma: Morozi,Ikhtilaful Al-Ulama, 1406 AH, shafi na 75.
- ↑ Duba: Samarkandi, Tohfa al-Fuqaha, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi.372; Sheikh Nizam al-Din, Al-Fatawi al-Hindiya, 1323 AH, juzu'i na 1, shafi na 211.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1401 BC, juzu'i na 4, shafi na 178; Ibn Rushd, Bidayat al-Mujtahid, 1406 BC, juzu'i na 1, shafi na 317; Muhaqqiq Hilli, Sharia’ul-Islam, 1389H, juzu’i na 1, shafi na 217.
- ↑ Tabatabai, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1420 AH, juzu'i na 3, shafi na 686.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 94, shafi na 129.
- ↑ Ibn Hubayra, Al-Afshah, 1366 BC, juzu'i na 1, shafi na 171; Muhaqqiq Hilli, Sharia’ al-Islam, 1389 AH, juzu’i na 1, shafi na 219-220; Jaziri, Fikihu Akan Rukunan Hudu, 1406 BC, juzu'i na 1, shafi na 585-587.
- ↑ Khomeini, Tahrir Al-Wasila, Dar Al-Ilim, juzu'i na 1, shafi na 305.
- ↑ Suyuti, Jami’ al-Saghir, 1401 BC, juzu’i na 2, shafi na 575.
- ↑ Al-Tabarani, Al-Mu’jam Al-Awsat, 1415 BC, juzu’i na 7, shafi na 121.
- ↑ «اعتکاف و فلسفه آن»، وبگاه راسخون.
- ↑ Malik, Al-Muwatta’, 1406 BC, juzu’i na 1, shafi na 314.
- ↑ Bukhari, Sahihul Bukhari, Sashen Buga Al-Maniriyyah, juzu'i na 3, shafi 105-110; Ibn Majah, Sunan Ibn Majah, 1952-1953, juzu'i na 1, shafi na 563.
- ↑ Kulayni, Al-Kafi, 1401 BC, juzu'i na 4, shafi na 175.
- ↑ H, shafi na 226. Al-Manqari, Wafaa Al-Wafa Akhbar Dar Al-Mustafa, Publisher: Ayatullah Al-Marashi Al-Najafi
- ↑ Sheikh Saduq, Min La Hadrahu Al-Faqih, 1413 Q, juzu’i na 2, shafi na 184.
- ↑ Sheikh Saduq, Min La yahdrahul Al-Faqih, 1413 Q, juzu'i na 2, shafi na 190.
- ↑ Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 47, shafi na 60.
- ↑ Miras Islami Iran, Daftare Awwal, Risaleh Itikaf, bincike na Ahmad Abedi Razvanshahri, 317-320, Laburaren Ayatollah Marashi.
- ↑ «مراسم اعتکاف قبل از انقلاب»، پایگاه اطلاعرسانی دفتر آیت الله خامنهای.
- ↑ Duba: Ibn Nadim, Al-Fihrast, 1350, shafi na 264-271.
- ↑ Duba: Najashi, Rijal, 1407 AH, shafi na 375-389.
- ↑ Duba: Agha Bozur, Al-Dhari'a, Dar al-Awtah, Juzu'i na 2, shafi na 230.
- ↑ Duba: Agha Bozur, Al-Dhari'a, Dar al-Audha, juzu'i na 2, shafi na 229; Madrasi Tabatabai, Mukadimeh bar fikihi Shia, 1368, shafi na 338.
- ↑ Agha Bozur, Al-Dhari'a, Dar al-Audha, Juzu'i na 2, shafi na 229-230.
- ↑ «لیست کتابها».
Tsokaci
- ↑ Ibn Abbas ya bada rahoto cewa Imam Hassan (A.S) yayin da ya shagaltu da dawadi cikin masallacin harami, sai wani mutum daga `yan shi'arsa ya zo ya nemi ya taimakon kudi daga gare shi, sai Imam Hassan (A.S) ya yanke dawain da yake yi, ya fito suka tafi tare da wannan mutumi, sai na ce amsa ka manta kana itukafanu ne? sai ya bani amsa da cewa a a, amma na ji daga babana shi ma ya ji daga bakin Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk wanda ya ya biya bukatarsa daidai yake da wanda ya yi ibada shekara dubu tara yana azumu da tashi tsayuwar dare. «من قضى أخاه المؤمن حاجةً كان كَمَن عَبَد الله تسعة آلاف سنة صائماً نهاره قائماً ليله.» مجلسی، بحارالانوار، ۱۴۰۳ق، ج۹۴، ص۱۲۹. 1
Nassoshi
- Aghabozur Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhariyyah ila Tasaneef al-Shi'a, Beirut, Dar al-Al-Adat, Bita.
- Al-Tabarani, Suleiman bin Ahmad, Al-Mu'jam al-Awsat, bincike: Abu Mu'az, Tariq bin Awadullah, Alkahira, Darul-Harameen, 1415H.
- Allameh Hilli, Hasan bin Yusuf, Tazkira al-Fuqaha, Qum, Al-Bait Institute (A.S.), bugun farko, 1414H.
- Alqur'ani mai girma.
- Balkhi, Sheikh Nizam al-Din, Al-Fatawi al-Hindiyya (Al-Fatawi al-Alamkiriya), Alkahira, 1323H.
- Behjat, Mohammad Taqi, Istiftaat, Ofishin Sayyidina Ayatullah Behjat, Qum, bugun farko, 1428H.
- Bukhari, Muhammad bn Ismail, Sahih Bukhari, Alkahira, Al-Maniriya Mabuba, Beta.
- Golpaygani, Seyyed Mohammad Reza, Majmam al-Masail, Darul Qur'an al-Karim, Qum, bugu na biyu, 1409H.
- Ibn Habirah, Yahya, Al-Ifsah an Ma'ani al-Sihah, tare da kokarin Mohammad Ragheb Tabakh, Aleppo, 1366H.
- Ibn Majah, Muhammad, Sunan Ibn Majah, na Muhammad Fouad Abd al-Baqi, Alkahira, 1952.
- Ibn Nadim, Muhammad, Al-Fahrest, ta kokarin Reza Toddjd, Tehran, 1350.
- Ibn Rushd, Muhammad Ibn Ahmad, Al-bidayatul Al-Mujtahid wa Al-nihayat Al-Maqtasad, Beirut, 1406 Hijira.
- Ibn Tavus, Ali Ibn Musa, Iqbal Al-Amal. Tehran, Darul Katb al-Islamiyya, bugu na biyu, 1409H.
- Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, Qum, Dar Alam Press Institute, bugu na farko, beta.
- Jaziri, Abdur Rahman, Fiqhu Ali al-Mahabh al-Arba, Beirut, 1406H.
- Jurjani, Ali bin Muhammad, Al-Tarifat, Alkahira, 1357H.
- Kulaini, Muhammad, Al-Kafi, na Ali Akbar Ghafari, Beirut, 1401H.
- Madrasi Tabatabaei, Hossein, Mukaddima bar Fiqh Shi'a, wanda Mohammad Asif Fikart ya fassara, Mashhad, 1368.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
- Malik bin Anas, al-Muwatta, bisa kokarin Muhammad Fouad Abd al-Baqi, Beirut, 1406H.
- Marozi, Muhammad bin Nasr,Ikhtilaful Al-ulma, na Sobhi Samrai, Beirut, 1406H.
- Mohagheq Hali, Jafar bin Hasan, Shara'e al-Islam, na Abdul Hossein Muhammad Ali, Najaf, 1389 AH.
- Najashi, Ahmad bin Ali, Rijal al-Najashi, bisa qoqarin Musa Shabiri Zanjani, Qum, Jama'at al-Madrasin fi Al-Hawza Al-Alamiya, 1407H.
- Naraghi, Molly Ahmad bin Muhammad Mahdi, Mustanad al-Shia fi Ahkam al-Sharia, Qom, Al-Al-Bayt Institute (A.S.), bugu na farko, 1415H.
- Safi Golpayegani, Lotfollah, Jame Al-Ahkam, Hazrat Masoumeh (AS) Publications, Qum, bugun 4, 1417 AH.
- Samarkandi, Aladdin, Tohfa al-Fuqaha, Beirut, 1405 AH/1985 miladiyya.
- Shafi'i, Muhammad, Al-Umm, ta kokarin Mohammad Zohri Najjar, Beirut, Dar al-Marafa, Bita.
- Shahidi Thani, Zain al-Din, al-Rawzah al-Bahiyeh, ta kokarin Mohammad Kalanter, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1403H.
- Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Al-Juma'a al-Fiqhiyyah (Al-Muqnaq), Qum, 1404H.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Man la Yahduruhul al-Faqihu, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na biyu, 1413H.
- Sheikh Tusi, Abu Jafar Muhammad bin Hassan, al-Khilaf, mai bincike kuma mai gyara: Khorasani, Ali, Shahrashtani, Seyyed Javad, Taha Najaf, Mahdi, Iraqi, Mojtabi, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, bugu na farko, 1407H.
- Siyuti, Jalal al-Din, Jame al-Saghir, Beirut, Darul Fikr, bugun farko, 1401H.
- Syed Morteza, Ali, Al-Intisar, bisa kokarin Mohammad Reza Khorsan, Najaf, 1391H.
- Mofid, Muhammad bin Muhammad Numan, Al-Muqni'a, Qum, Islamic Publication Institute, 1410 AH.
- Ragheb Esfahani, Hossein, Mufradat Al-faz Al-kur'an, bisa qoqarin Nadim Marashli, Alkahira, 1392H.
- «استقبال چشمگیر جوانان»، شیعه نیوزتاریخ نشر: ۲۷ فروردین ۱۳۹۶ش، تاریخ بازدید: ۱۶ بهمن ۱۴۰۱ش..
- «اعتکاف و فلسفه آن»، وبگاه راسخون، تاریخ نشر: ۲۷ خرداد ۱۳۸۹ش، تاریخ بازدید: ۱۶ بهمن ۱۴۰۱ش.
- «تاریخچه اعتکاف»، خبرگزرای تسنیم، تاریخ بازدید: ۱۵ بهمن ۱۴۰۱ش.
- جرجانی، علی بن محمد، التعریفات، قاهره، ۱۳۵۷ق.
- «مراسم اعتکاف قبل از انقلاب»، پایگاه اطلاعرسانی دفتر آیت الله خامنهای، تاریخ نشر: ۲۵ اردیبهشت ۱۳۹۲ش، تاریخ بازدید: ۱۶ بهمن ۱۴۰۱ش.
- «مراسم اعتکاف در کشورهای جهان »، خبرگزرای ایرنا، تاریخ نشر: ۱۸ فروردین ۱۳۹۵ش، تاریخ بازدید: ۱۶ بهمن ۱۴۰۱ش.
- «مکان اعتکاف»، پایگاه اطلاعرسانی حوزه، تاریخ نشر: ۳۰ فروردین ۱۳۹۵ش، تاریخ بازدید: ۱۵ بهمن ۱۴۰۱ش.
- «نگاهی به اهمیت و فضیلت اعتکاف»، وبگاه آیین رحمت، تاریخ بازدید: ۱۵ بهمن ۱۴۰۱ش.