Sayyida Faɗima Ma'asuma (A.S)

Daga wikishia
Hubbaren Sayyida Fatima Ma'asuma (A.S)

Sayyida Ma'asuma (A.S), (Larabci: السيدة فاطمة المعصومة سلام الله عليها) Faɗima shi ne asalin sunanta na yanka, ta kasance ƴa ga Imam Kazim (A.S), ƴar'uwa ga Imam Rida (A.S) ta kasance mafi falala da fifiko cikin ƴaƴa mata ga Imam Kazim (A.S), an ce cikin ƴaƴan Imam Kazim (A.S) bayan Imam Rida (A.S) ba ta da tsara ko kwatankwaci, cikin madogaran tarihi na shi'a ba so kawo kammalallen rahoto game da ita daga jumla tarihin rayuwarta da wafatinta, haka nan game da rahotan aurenta, amma dai abin da ya shahara shi ne cewa ba ta yi aure ba.

Ma'asuma, Karimatu Ahlul-baiti (A.S) su ne shahararrun laƙubbanta, cikin hadisin Imam Rida (A.S) an ambace ta da Ma'asuma. Sayyida Ma'asuma a shekara ta 201 bayan hijira ƙarƙashin buƙatar ɗan'uwanta Imam Rida (A.S) ta taso daga madina zuwa ƙasar Iran domin ganin ɗan'uwanta, sai dai cewa ta kamu da rashin lafiya a kan hanya, bisa roƙo da gayyatar mutanen garin ƙum ta sauka wannan gari ta zauna a gidan wani mutum da ake kira Musa ɗan Kazraj ash'ari, bayan kwanaki 17 sai ta rasu. An binne ta a wata maƙabarta da ake kira babilan (Haraminta a yanzu haka). Sayyid Jafar Murtada Amili (Wafati:1441.h.ƙ) ya yi amanna an cewa an shayar da ita guba ne a garin sawa, wannan guba ce musabbabin shahadarta. ƴan shi'a su na matuƙar girmama Faɗima Ma'asuma (A.S). sun imani da zuwa ziyara tare da girmama ta. Haka nan an naƙalto wata riwaya game da ita da take magana kan ceton da za ta yi, da kuma samun ladan aljanna ga wanda ya ziyarce ta. An ce baya ga Sayyida Faɗima (S) ita ce kaɗai mace da aka rawaito hadisi game da zuwa ziyararta.

Ƙarancin Rahoto Game da Sayyida Ma'asuma

A cewar Zabihullahi Mahallati cikin littafin Rayahinul Ash-shari'a, babu cikakken rahoto game da rayuwar Sayyida Ma'asuma; daga jumlars ranar haihuwarta da wafatinta, shekarunta, yaushe ta taso daga madina zuwa ƙasar Iran, shin tun kafin shahadar Imam Rida (A.S) ta rasu ko kuma bayan shahadarsa, duka babu cikakken rahoto a kansu.[1]

Dangi

Faɗima ta kasance ƴa ga Imam Kazim (A.S) ƴar'uwa ga Imam Rida (A.S) ana mata laƙabi da Ma'asuma. Shaik Mufid cikin littafin Al-Irshad ya kawo sunayen ƴaƴa mata ga Imam Kazim (A.S) waɗanda su ne Faɗima Kubra da Faɗima Sugra, sai dai cewa bai tantance wace ce Sayyida Ma'asuma ba daga cikin su biyun.[2] Ibn Jauzi daga malaman ahlus-sunna a ƙarni na shida bayan hijira, ya kawo ƴaƴan Imam Kazim (A.S) waɗanda duk sunansu Faɗima, sai dai cewa shi ma bai ayyana wace ce Faɗima Ma'asuma daga cikinsu ba.[3] a cewar Muhammad ɗan jarir, marubucin littafin Dala'iul Al-imama, ya ambaci cewa Najma khatun ita ce mahaifiyar Sayyida Ma'asuma da Imam Rida (A.S).[4]

Tarihin Ranar Haihuwa Da Wafati

Cikin daɗaɗɗun madogaran shi'a, babu bayani game da tarihin haihuwar Faɗima Ma'asuma da wafatinta, a cewar Rida Ustadi, littafi na farko da ya kawo tarihin haihuwarta da wafatina ya kasance littafin Nurul Al-afaƙ na Jawad Shah Abdul-azimi.[5] wanda ya fito a shekarar 1344 bayan hijira.[6] cikin wannan litttafi an bayyana 1 ga watan zil ƙa'ada shekara ta 173 bayan hijira ranar da aka haifeta, sannan ta bar duniya a ranar 10 ga watan rabi'u sani shekara ta 201 bayan hijira, daga wannan littafin ne sauran litattafai suka naƙalta.[7] sai dai cewa wasu ba'arin malamai misalin Ayatullahi Mar'ashi najafi,[8] Ayatullahi Shubairi zanjani,[9] Rida Ustadi[10] da Zabihullahi Mahallati,[11] ba su amince da wannan magana da Shah Abdul-azimi ya kawo ba, sannan tarihin da ya ambata game da lokacin haiuwarta da wafatinta suna ganin cewa ƙirƙirarriyar magana ce. Cikin kalandar jamhuriyar muslunci ta Iran ranar 1 ga watan zil ƙa'ada an sanya mata suna ranar ƴa mace.[12]

Laƙubba

Ma'asuma da Karimatu Ahlul-baiti (A.S) suna daga mafi shaharar laƙubban Faɗima ɗiyar Imam Kazim (A.S).[13] malaman sun ce “Ma'asuma” an ciro wannan laƙabi ne daga wata riwaya da ake dangantawa ga Imam Rida (A.S).[14] cikin wannan riwaya wacce a ka kawo ta a cikin littafin Zadul Al-ma'ad na Muhammad Baƙir Majlisi, ya zo cewa, Imam Rida (A.S) ya kirata da sunan Ma'asuma.[15] Faɗima Ma'asuma (A.S) a wannan zamani ana kiranta da laƙabin “Karimatu Ahlul-baiti”.[16] malamai suna cewa wannan laƙabi nata ya jingina da wani mafarki da Sayyid Mahmud Mar'ashi Najafi baban Ayatullahi Mar'ashi Najafi ya gani, cikin wannan mafarki ya ga ɗaya daga cikin Imamai (A.S) yana kiran Faɗima Ma'asuma (A.S) da Karimatu Ahlul-baiti.[17]

Aure

Kamar yadda mai littafin Rayahinul Ash-shari'a ya kawo, babu labari shin ta yi aure ko ba ta yi ba, tana da ƴaƴa ko ba ta da su.[18] na'am mashhur sun tafi kan cewa ba taɓa aure ba har ta bar duniya,[19] tare da kawo dalilai kan tabbatar da hakan; daga jumlarsu sun ce: sakamakon rashin samun kufu'i da tsaranta ya sanya ba ta yi aure ba.[20] haka nan Yaƙubi malamin tarihi a ƙarni na uku bayan hijira, ya rubuta cewa Imam Kazim (A.S) ya yi wasiyya da cewa ka da ɗaya wata daga cikin ƴaƴansa ta yi aure,[21] sai dai cewa malamai sun yi suka da sanya alamun tambaya kan wannan magana da ya kawo, tare da kafa hujja da cewa wannan magana ba ta zo ba cikin wasiyya da Kulaini ya kawo a littafin Al-kafi wacce ya naƙalto daga Imam Kazim (A.S),[22] samsam ba ta zo ba a ciki.[23] ba'ari daga masu dandaƙe bincike su na ganin rashin yin auren Sayyida Ma'asuma (A.S) da sauran ƴan'uwanta mata ya samo asali sakamakon takurawar da gwamnatin Abbasiyawa suka yi kansu musammam ma sarki Haruna rashid da Mamun.[24]

Tafiya Zuwa Iran Da Shiga Garin ƙum Da Kuma Wafatinta

Kan asasin abin da littafin Tarikh ƙum ya kawo, a shekarar ta 201 bayan hijira Faɗima Ma'asuma (A.S) ta taso daga Madina zuwa ƙasar Iran.[25] bisa naƙalin Baƙir Sharif ƙarashi masanin tarihi a shi'a, ya kawo daga littafin “Jauharatul Al-kalam fi Madahi As-sadatil Al'alam” dalilin tasowar ta daga madina zuwa Iran wata wasiƙa ce da Imam Rida (A.S) ya aika mata cikin wannan wasiƙa ya nemi ta zo Khurasan wurinsa[26] Imam Rida (A.S) a wannan lokaci ya kasance “Waliyul Ahad” (Mai jiran mulki) ga Mamun halifan abbasiyawa, yana zaune a Khurasan, a kan hanyarta ta zuwa wurinsa ne ta kamu da rashin lafiya ta rasu.[27] bisa abin da Sayyid Jafar Murtada Amili ya yi amanna da shi, yana ganin lallai an shayar da Sayyida Ma'asuma (A.S) guba a garin Sawa, sakamakon shan wannan guba ta yi shahada.[28]

Game da dalilin zuwanta garin ƙum akwai rahotanni guda biyu, bisa abin da ya zo daga rahoto na farko, ta kamu da rashin lafiya a garin Sawa, sai ta nemi ƴan rakiyarta su kaita garin ƙum.[29] kan asasin rahoto na biyu wanda marubucin tarihin ƙum ya yi amanna cewa shi ne rahoto mafi inganci, ya bayyan cewa mutanen garin ƙum ne da kansu suka nemi ta zo garinsu.[30]

Sayyida Ma'asuma bayan shigarta garin ƙum ta sauka a gidan wani mutum da ake kira da Musa ɗan kazraj ash'ari, bayan kwanaki 17 da sauka ne Allah ya karɓi ranta.[31] an binne jana'izarta a wata maƙabarta da ake kira Babilan wanda nan ne haraminta a yanzu.[32] Alu Sa'ad sun samu saɓani tsakanin juna kan binne ta, daga ƙarshen dai sun yanke shawara ƙadir wani tsoho hadimi mutumin kirki shi ne wanda zai shirya jana'izar binneta; sai dai cewa kwatsam an ga bayyana waɗansu mutane da fuskarsu ta kasance lulluɓe suna ta gaggawa suka kan jana'izarta suka sallaceta suka binneta, bayan kammala binne ta ne sai waɗannan mutane suka hau dokunansu suka yi tafiyarsu ba tare da sun yi magana da kowa ba.[33] an naƙalto daga Fadil Lankarani (Wafati:1386.h.shamsi), babu mamaki waɗannan mutane biyu mahaya dawakai da suka sun kasance daga Imamai (A.S).[34]

Kyakkyawan zanen rubutu na kan tayil cikin Haramin Imam Sayyida Ma'asuma

Matsayinta A Wurin ƴan Shi'a

Malaman shi'a suna bawa Sayyida Ma'asuma (A.S) matsayi mai matuƙar girma, sun naƙalto riwaya game da matsayinta da ziyararta, Allama majlisi cikin littafin Bihar Al-anwar ya yi bahasi kan wani hadisi da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S), cikin wannan hadisi an bayyana cewa duk ƴan shi'a za su shiga aljanna ta hanyar ceton Sayyida Ma'asuma (A.S).[35] cikin wata gaɓa daga ziyarar Faɗima Ma'asuma (A.S), sakamakon matsayin da take da shi a wurin Allah, an roƙeta cetonta.[36][Tsokaci 1]

Muzaharar makoki a ranar Ashura a farfajiyar hubbaren Sayyidina Ma'asuma

Muhammad Taƙiyyu Shushtari a ƙarni na goma sha huɗu a cikin littafin ƙamusul ar-rijal an rubuta cewa cikin ƴaƴan Imam Kazim (A.S) masu yawa, bayan Imam Rida (A.S) babu wani ko wata da take kwatankwacin Faɗima Ma'asuma (A.S).[37] Shaik Abbas ƙummi yana ganin Faɗima Ma'asuma (A.S) matsayin mafi fifita cikin ƴaƴan Imam Kazim (A.S) daga mata.[38] haka nan yana ganin ta tana daga cikin ƴaƴan Imamai da ta kasance mai girman matsayi, kuma tabbas tana daga cikin ƴaƴan Imam Kazim (A.S), kuma tabbas a wannan harami dai da yake garin ƙum aka binne ta.[39]

Kan asasin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S), Imam Kazim (A.S) da Imam Jawad (A.S) aljanna ta kasance ladan wanda ya ziyarci Faɗima ƴar Imam Kazim (A.S).[40] na'am a wasu riwayoyin ya zo da ƙarin cewa: aljanna ce ladan wanda ya ziyarce ta yana mai sanin haƙƙinta.[41]

Marubucin littafin Zindigani Karime Ahlul-baiti (A.S) ya naƙalto daga Mahmud Ansari ƙummi (Wafati:1377.h.shamsi) da Sayyid Nasrullahi Musntanbiɗ malamin shi'a (Wafati:1364.h.shamsi) a cikin littafin rubutun hannu na Kashful Alla'ali na Salihu ɗan Arandas Hilli, malamin shi'a a ƙarni na tara, ya yi tuntuɓe da wani hadisi wanda cikinsa Imam Kazim (A.S) yake magana zuwa ga Sayyida Ma'asuma yace: “Babanta ya fansheta”. Kan asasin wannan naƙali jumlar da ta biyo bayan ta farko cikinta yace Sayyida Ma'asuma itace ta baiwa ƴan shi'a amsoshin tambayoyinsu a lokacin da Imam ba ya nan, kuma amoshi ne da suka kasance masu inganci, marubucin littafin Zindigani Karime Ahlul-baiti (A.S) ya ce: wannan hadisi babu inda aka naƙalto sai anan ba zaka same shi ba cikin sauran litattafan hadisai.[42]

Ziyara

Abdullahi Jawadi AMoli Daga Maraji'an Taklidi
Daga Littafin ziyara na Sayyida Masoumeh, ya bayyana cewa samuwa mai albarka ta Fatimah Masoumeh Karimatu Ahlul Baiti (A.S) ya kasance ne cikin sislisalr Annabawa da waliyyai, ma'ana lokacin silsilar Annabawa da waliyyai amincin Allah ya tabbata a garesu, ta kare, sai layi ya zo kan almajiransu mai kwazoda kebantattun sahabban imamai, samuwar mai albarka na Ma'asuma (A.S) wace ta kasance magajiyar iliminsu da ma;arifa, karimatu gidna tsarkaka da sani, zuhudu, ilimi, hankali da sauran kyawawan halaye da suka ksance tare da almajiran imamai da sahabban imama.da suka samar.

[43]

Tushen ƙasida: Ziyarar Sayyida Ma'asuma (A.S)

Allama majlisi cikin litattafan Zadul Al-ma'ad, Biharul Al-anwar da Tuhufatul Al-za'ir, ya kawo ziyara ta Faɗima Ma'asuma da aka naƙalto daga Imam Rida.(A.S)[44] na'am cikin Tuhufatul Al-za'air ya bayyana cewa akwai tsammanin matanin wannan ziyara bai kasance daga hadisin Imam Rida (A.S) ba, ya da cewa[45] malamai sun ce: Sayyida Faɗima Zahara (S) da Sayyida Ma'asuma suka kaɗai mata da suke da ziyara da isnadi da sanadinta yake isa ga Imami Ma'asumi.[46]

Tsarkakken Haramin Sayyida Ma'asuma

Tushen ƙasida: Haramin Sayyida Ma'asuma (A.S)

An gina ƙubba da Inuwa kan makwancin Sayyida Ma'suma (A.S) da yake garin ƙum.[47] wannan makwanci an faɗaɗa shi matuƙar faɗaɗawa wanda a yanzu baya ga haramin rida shi ne mafi kyawun da shaharar hubbare a ƙasar Iran.[48] Haramin Faɗima Ma'asuma, ya ƙunshi hubbarenta, gine-gine, waƙafofi, ofishoshin gudanarwa masu alaƙa da wannan haramin waɗanda akasarinsu suna cikin garin ƙum.[49]

Taron Majalisar Girmamawa Da Fim Na Sinima

A shekarar 2015 an shirya taron majalisar girmama Sayyida Ma'asuma (A.S) da kuma matsayin al'adu a ƙum ƙarƙashin umarnin Ali Akbar Mas'udi Khomaini, shugaban haramin Sayyida Ma'asuma (A.S).[50] cikin wannan taro da aka shirya a cikin haramin Ma'asuma, maraji'an taƙlidi misalin Nasiri Makarim shirazi da Abdullahi Jawadi Amoli sun yi bayani.[51]

Ahmad Abidi sakataren wannan majalisa ya bada rahoto game da buga litattafai guda 54 da suka ƙunshi batutuwa game da Sayyida Ma'asuma (A.S) haraminta, hauzar ƙum da juyin juya halin muslunci na Iran.[52]

Fim Mai ɗauke Da Suna ƴar uwar Rida

Fim da aka shirya mai suna Uktul Rida, riwaya ce game da tafiyar Sayyida Ma'asuma (A.S) daga madina zuwa ƙum, wannan fim ya fito a 24 ga watan rabi'u awwal, daidai da 10 ga watan oktoba 2023, shekara ta 1445 bayan hijira daidai da 18 ga watan mihir hijira shamsi.[53] [53]

Fihirisa

Ba'arin litattafai da aka rubuta game da Faɗima Ma'asuma (A.S) sun kasance kamar haka:

  • Hazrat Ma'asuma Faɗima Dubom, na Muhammad Muhammadi Ishtihardi.
  • Portuyi az rawa Doste, Isma'il Kermanshahi.
  • Zindigani Hazrat Ma'asuma wa Tarikh ƙum, na Sayyid Mahadi Sahafi.
  • Hazrat Ma'asuma wa Shahre ƙum, Muhammad Karimi.
  • Hayat wa Karamat Faɗima Al-ma'asuma, na Sayyid Muhammad Ali Husaini Baƙa'i Lubnani.
  • Banuye Malakut, Ali Karimi Jahrami.
  • Amme Sadat, na Sayyid Abu ƙasim Hamidi.

Bayanin kula

  1. Mahalati, Riyahin al-Sharia, 1373, juzu'i na 5, shafi na 31.
  2. Mufid, Al-Irshad, 1403 BC, juzu'i na 2, shafi na 244.
  3. Ibn Jawzi ne ya rawaito shi, Tazkirat al-Khawas, shafi na 315.
  4. Tabari, Dala'ilul Imama, 1413 BC, shafi na 309.
  5. Malamina, “Ashnay Ba Hazrat Abdul Azim Masadir Sharh Hal Aw,” shafi na 301.
  6. Malamina, “Ashnay Ba Hazrat Abd al-Azeem Masadir Sharh Hal Aw,” shafi na 297.
  7. Malamina, “Ashnay Ba Hazrat Abd al-Azeem Masadir Sharh Hal Aw,” shafi na 301.
  8. Mahallati, Riyahin Al-Sharia, 1373 AH, juzu'i na 5, shafi na 32.
  9. Shabiri Zanjani, Jur’ah Ya Az Darya, 1394 AH, juzu’i na 2, shafi 519.
  10. Ashnay Ba Hazrat Abd al-Azeem Masadir Sharh Hal Aw,” shafi na 301
  11. Mahallati, Riyahin al-Sharia, 1373 AH, juzu'i na 5, shafi na 31 da 32.
  12. Shura Markaz Taqwim Muassaseh Geophysics Daneshgahe Tehran, kalandar hukuma ta kasar ta shekara ta 1398H, shafi na 9.
  13. Mehdipour, Karime Ahlul Baiti (S), 1380, shafi na 23 da 41; Haka nan kuma a duba Asghari-Najad, " Nazre bar asameh wa alkab hazrat Sayyida Fatimah Masoumeh (A.S)".
  14. Mahdipur, Karime Ahlul-Bait (S), 1380, shafi na 29.
  15. Majlesi, Zad al-Ma'ad, 1423H, shafi na 547.
  16. Duba Mehdipour, Karima Ahl al-Bait (A.S), 2013, shafi na 41 da 42.
  17. Mahdipur, Karima Ahlul Baiti (S), 1380H, shafi na 41 da 42.
  18. Mahallati, Riyahin Al-Sharia, 1373 AH, juzu'i na 5, shafi na 31.
  19. Mahdipur, Karima Ahl al-Bait (S), 1380 AH, shafi 150.
  20. Mahdipur, Karima Ahlul Bait (S), 1380H, shafi na 151.
  21. Yaqubi, Tarikh Yaqubi, 1413 BC, juzu'i na 2, shafi na 361.
  22. Kulaini, Kitab al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 317.
  23. Qurashi, Hayat al-Imam Musa bin Jafar (a.s.), 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 497.
  24. Hosseini, “Raz az adame izdiwaje Hazrat Masoumeh (A.S),” shafi na 103-104.
  25. Qomi, Tarikh Qum, Tus, shafi na 213.
  26. Qurashi, Hayat al-Imam al-Reza (a.s.), 1380, juzu'i na 2, shafi na 351.
  27. Qomi, Tarikh Kum, Tos, shafi na 213.
  28. Ameli, Hayat al-Siyasiya li Imam Riza (AS), 1403 AH, Juzu'i na 1, shafi na 428. ↑
  29. Qomi, Tarikh Kum, Tos, shafi na 213.
  30. Qomi, Tarikh Kum, Tos, shafi na 213.
  31. Qomi, Tarikh Kum, Tos, shafi na 213.
  32. Qomi, Tarikh Kum, Tos, shafi na 213.
  33. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 60, shafi na 219.
  34. Mohammad Beigi, Foroughi az Kausar, 2007, shafi na 35.
  35. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 99, shafi na 267.
  36. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 99, shafi na 267; Majlesi, Zad al-Maad, 1423 AH, shafi na 548-547.
  37. Shushtri, Tavarikh al-Nabi da al-Al, 1391 AH, shafi na 65.
  38. Qomi, Mantehi al-Amal, Juzu'i na 2, shafi na 378.
  39. Qomi, Mufatih al-Janan, shafi na 562.
  40. Duba Ibn Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 536; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 99, shafi na 265-268.
  41. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 99(102), shafi na 266.
  42. Mahdipur, Zandaghani, Karimeh Ahlul Baiti (A.S), 1384 AH, shafi na 52-54.
  43. «جایگاه حضرت معصومه سلام الله علیها و لزوم معرفت به آن حضرت»، پرتال بنیاد اسراء.
  44. Duba Majlesi, Zad al-Maad, 1423 AH, shafi na 548-547; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 99, shafi na 266-267; Majlisi, Tohfa Al-Zaer, 2006, shafi na 664.
  45. Majlisi, Tohfa Al-Zaer, 2006, shafi na 666.
  46. Mehdipur, Karima Ahlul Bait (S), 1380 AH, shafi 126.
  47. Qomi, Tarihin Qum, Tus, shafi na 213; Sajjadi, “Hazrat Masoumeh Astana”, shafi na 359.
  48. Sajjadi, “ Astana Hazrat Masoumeh,” shafi na 358.
  49. Sajjadi, “Astana Masoumeh ,” shafi na 358.
  50. Congress Buzurdashte Sayyida Fatima Masoumeh, tarin labarai, 2004, juzu'i na 1, shafi na 2.
  51. Sharaft, "Congress Buzurgdashte Sayyida Fatima Masoumeh (A.S) da Wurin Al'adun Kum", shafi na 139-145.
  52. Sharaft, "Congress Buzurgdashte Sayyida Fatima Masoumeh (A.S) da Wurin Al'adun Kum", shafi na 142.
  53. «اکران فیلم سینمایی «اخت‌الرضا در سینماهای سراسر کشور»، خبرگزاری مهر.

Tsokaci

  1. یا فاطِمَةُ اِشْفَعی لی فِی الْجَنَّهِ فَاِنَّ لَکِ عِنْدَاللهِ شَأْناً مِنَ الشَّأْن

Nassoshi

  • Ameli, Sayyid Jafar Mortada, Hayatul Al-Siyasiyati Imam Riza (A.S), Qum, Lujnatu Jamiat-e Modarreen, 1403 BC.
  • Ibn Jozi, Tazkira Al-Khwas, Kum, Manshurat al-Sharif al-Razi, 1418H.
  • Ibn Qolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, Najaf, Dar al-Mortazwieh, bugun farko, 1356.
  • Kongireh Buzurdasht, Sayyida Fatima Masumeh, Majmu makalat, Qom, Bazi, Babi na Daya, 1384 Hijira.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, wanda: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhunandi suka buga, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
  • Mahallati, Zabihullah, Riyahin al-Sharia, Dar al-Kutub al-Islamiyya, Tehran, Beta.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bahar al-Anwar, edited by: Collected by Muhaqqan, Beirut, Dar Ihya’ al-Tarath al-Arabi, pdf: Dom, 1403 BC.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Tuhfat al-Za’ir, wanda cibiyar Imam Hadi, Kum, ma'ajin Imam Hadi, babi na farko, 1386H.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Zadul al-Maad, editan: Alaa al-Din Ilmi, Beirut, Ilmi Publications Foundation, 1423 BC.
  • Mehdipur, Ali Akbar, Karima Ahlbayt (S), Qum, Wallafar Haziz, babin farko, 1374H.
  • Mehdipur, Aliakbar, Zandaghani Karima Ahlabit (amincin Allah ya tabbata a gare shi)], Kum, Wallafar Haziz, 1384H.
  • Muhammadbeghi, Ilyas, Foroughi Az Mo'assir. Qom, Bugawa Buga, 1387 AH.
  • Qomi, Hasan bin Muhammad, Tarikh Qum, edited by: Jalaluddin Tahrani, Tehran, Tus, Beta.
  • Qomi, Sheikh Abbas, Muntaha al-Amal fi Tarikh al-Nabi wal-Ahl, Qom, Jami'ar Malamai, 1422 BC.
  • Qurashi, Baqar Sharif, Hayat Al- mam Musa bin Jaafar, Nazari da Nazari, Beirut, Dar Al-Balagha, Babin Dom, 1413 BC.
  • Qurashi, Baqursharif, Hayat Al-Imam Riza (A.S), Qum, Saeed bin Jubair, 1380H.
  • Sajjadi, "Astana Hazrat Masoumeh", Dayrat al-Ma'arif Bozorg Islami, juzu'i na 1, Tehran, Darat al-Ma'arif Bozorg Islami Center, 1367 AH.
  • Shabiri Zanjani, Sayyid Musa, Jarah Iz Darya, Qum, Mu’assasa Kitabshinasi Shi’a, Qum, 1394H.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bn Muhammad bn Numan, Al-Irshad fi Ma’rifat Hujajillahi ala ibad, Beirut, Dar Al-Mufid, 1414 BC.
  • Shorai Markaz Taqwim Muassaseh Geophysic Daneshgah Tehran, kalandar hukuma ta shekara ta 1398H.
  • Shushtari, Muhammad Taqi, Tarikh Annabiyi wa Al, Tehran, 1391 BC.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Dala'ilul Imama, Qum, 1413 BC.
  • Yaqubi, Ahmad bin Abi Yaqubi, Tarikh Al-Yaqubi, edited by Abdul Amir Muhanna, Beirut, Al-Alami Publications Institution, babin farko, 1413 BC.
  • «جایگاه حضرت معصومه سلام الله علیها و لزوم معرفت به آن حضرت»، پرتال بنیاد اسراء، تاریخ درج مطلب: ۱۶ آذر ۱۳۹۸ش، تاریخ بازدید: ۳ آبان ۱۴۰۳ش
  • «اکران فیلم سینمایی «اخت‌الرضا» در سینماهای سراسر کشور»، خبرگزاری مهر، تاریخ درج مطلب: ۱۸ مهر ۱۴۰۲ش، بازدید: ۲۰ مهر ۱۴۰۲ش.
  • استادی، رضا، «آشنایی با حضرت عبدالعظیم و مصادر شرح‌حال او»، نور علم، ش۵۰و۵۱.
  • اصغری‌نژاد، محمد، «نظری بر اسامی و القاب حضرت فاطمه معصومه(س)»، فرهنگ کوثر، ش۳۵، ۱۳۷۸ش.
  • حسینی، سید جواد، «راز عدم ازدواج حضرت معصومه(ع)»، فرهنگ کوثر، ش۶۹، فروردین ۱۳۸۶ش
  • شرافت، امیرحسین، «کنگره بزرگداشت حضرت فاطمه معصومه(س) و مکانت فرهنگی قم»، وقف میراث جاوید، ش۵۲، ۱۳۸۴ش.