Sallar Idi

Daga wikishia
Wannan ƙasida wani rubutu ne suffatau da aka yi game da wani mafhumi na fiƙihu, ba za iya zama ma'auni ba game da ayyukan addini, ko koma zuwa ga wasu madogaran domin ayyukan addini
Sallar Idin Fitri Da Limancin Abdul-Karim Ha'iri yazdi A Haramin Sayyida Ma'asuma (S) Qum Farkon Shekarar Karni Na 14

Sallar idi ko sallar idi biyu, (Larabci: صلاة العيد) wata sallah ce da musulmai suke taruwa su yi a ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah, musulmi masu tarin yawa ne suka taruwa musammam a ranar idin ƙaramar sallah. Bisa fatawar malaman fiƙihu na shi'a a lokacin hallarar Imami ma'asumi sallah idi tana kasancewa wajibi, kuma wajibi ne a yi ta cikin tsarin jam'i, haka nan wannan sallah mustahabbi ce a zamanin fakuwar Imami, duk da cewa malamai sun yi saɓani kan yinta cikin jam'i ko ɗaiɗaiku.

Bisa abin da ya zo a tarikh ɗabari, sallar idi ta farko da aka fara ta kasance a shekara ta biyu bayan hijira. Imam Rida (A.S) lokacin daurar halifa mai jiran gado a zamanin halifancin Mamun Abbasi, ya amince da buƙatar Mamun kan ya jagorancin sallar idi, ya shira duk wani shirye-shirye na wannan sallah, sai dai kuma daga bayan Mamun ya yi nadama. A shekarar 1357 hijirar tafiyar rana, a ƙasar Iran an yi wata sallar idi ƙarƙashin jagorancin Muhammad Mufatteh tare da lacca daga ɓangaren Muhammad Jawad Bahonar wacce bayan idar da sallah al'umma suka hau kan titi suna masu jerin gwano na nuna rashin amincewa da gwamnatin Pahalawi. Sallar idi bayan nasarar juyin juya halin muslunci a ƙasar Iran wace aka yi babban birnin Tehran, Sayyid Ali Khamna'i ne ya kasance limami a galibin sallolin idin da aka bayan nasara juyin juya halin muslunci a Iran. Sallar idi raka'a biyu ce; cikin raka'a ta farko ana yin ƙunun guda biyar, a raka'a ta biyu kuma a yi ƙunun guda huɗu. Haka nan sallar idi tana huɗuba guda biyu da ake yi bayan idar da sallah, lokacin tsayar da wannan sallah yana farawa daga hudowar rana zuwa zawali (Azuhur ta shari'a). sallar idi tana da ladubba da hukunce-hukunce, daga jumlarsu an fi buƙatar tsayar da ita a fili inda babu rufin sama, kuma ana son karanta keɓantacciyar addu'a cikin alƙunut ɗin da ake yi a sallar.

Matsayi Da Muhimmanci

Sallar idi sallah ce da musulmi suke tsayar da ita a ranar idin ƙaramar sallah da babbar sallah, wannan sallah a cikin madogaran riwaya ana kiranta da sunan «صلاة العیدین» (Sallar idi guda biyu).[1] a cewar Muhammad ɗan Jarir ɗabari, malamiin tarihi a ƙarni na uku bayan hijira, Annabin muslunci (S.A.W) karon farko ya fara tsayar da sallar idi a watan shawwal shekara ta biyu bayan hijira.[2] musulmi masu yawan gaske suke zuwa sallar idi musammam ma idin ƙaramar sallah, suna yin wannann sallah a bakiɗayan wurare masu tsarki a wurin musulmi da ƴan shi'a.[3] a wurare da yankunan daban-daban ne a ƙasar Iran tare da halartar dubban gurguzun masallata ana tsayar da wannan sallah bisa tsarin jam'i a bayan limami..[4] A garin Mashad na ƙasar Iran a duk shekara ana yin wannan sallah a cikin hubbaren Imam Rida (A.S).[5] bisa rahotanni haƙiƙa zamanin mulkin ƙajar ana yin wannan sallah a mashad da masallaci.[6] a garin Najaf na ƙasar Iraƙi ana yinta a cikin Haramin Imam Ali (A.S)[7] a Kufa sana shirya wannan sallah a masallacin juma'a na kufa.[8] a garin Karbala kuma ana yinta a bainal haramaini.[9]

Mamun Abbasi Ya Hana Imam Rida (A.S) Jagorantar Sallar Idi

Kan asasin riwaya wace aka naƙalto daga littafin Al-kafi, Mamun Abbasi bayan zaɓar Imam Rida (A.S) da ya yi matsayin halifa mai jiran gado a bayansa, sai ya nemi Imam ya fito ya jagorancin sallar idi, bayan dagewa da Mamun ya yi sai Imam Rida ya yarda zai yi, amma da sharaɗin cewa sallar za ta kasance bisa yadda take a sunnar Annabi (S.AW).[10] tare da haka kan asasin waccan riwaya da aka ambata, Fadlu ɗan Sahal wazirin Mamun Abbasi, lokacin da ya fahimci yadda mutane suka yi maraba da wannan shawara Mamun sai ya cewa da Mamun, matuƙar Ali ɗan Musa ya je filin da za a yi sallar idi, lallai mutane za su yaudaru da shi, da wannan dalili ne Mamun tare da aika da ɗan aikensa wurin Imam Rida (A.S) ya umarce shi da ya dagatar da wannan sallah ya dawo gida.[11] a cewar Murtada Muɗahhari, dalili na asali da ya sanya Mamun hana Imam Rida (A.S) jagorantar sallar idi ya kasance hatsari da ya ji tsoro, da kuma yadda mutane suka yi maraba suka fito kwansu da kwarkwata don yin sallah a bayan Imam, saboda yayin da Imam ya fito, ya fito da shiga saɓanin wace sarakunan Abbasiyawa suka saba yi, ya fito sanye da gama garin tufafi, sannan mutane suka masa babbar tarba da maraba.[12]

Sallar Idi A Rabat Babban Birnin Maroko

Sallar Idul Fiɗri(Idin ƙaramar sallah) a Shekarar 1357.H.Shamsi

Sallar idul Fiɗri a babban birnin Tehran a shekarar 1357 hijira shamsi, ranar 13 ga watan shahriwar ƙarƙashin limancin Muhammad Mufatteh tare da lacca daga Muhammad Jawad Bahonar daga malaman addini masu adawa da gwamnatin Pahalawi a wancan zamani, an yi wannan sallah a tsaunin ƙaiɗariyya Tehran.[13] daga ƙarshe aka shirya jerin gwano na adawa da gwamnatin pahalawi.[14] bisa rahotannin jaridar ittila'at, a cikin ƙasar Iran kusan mutum miliyan uku ne suka shiga jerin gwanon da aka yi ranar idin ƙaramar sallah.[15] an ce wannan jerin gwano shi ne ya haifar da zanga-zangan ranar 17 ga watan shawariwar shekarar 1357 tare da kashe masu zanga-zanga ta hannun jami'an tsaron hukumar pahalawi.[16]

Sallar Idi Karamar Sallar Tare da Limancin Sayyid Khamna'i Shekarar

Sallar Idi Tare da Limancin Jagoran Jamhuriyar Muslunci Iran

Bayan fara jagorancin Sayyid Ali Khamna'i a Iran shekarar 1368. Ya jagorancin sallar idin ƙaramar sallah. Haka shima Imam Khomaini ya kasance limamin juma'a a masallacin Tehran.[17] daga shekarar 1361 zuwa 1368 hijira shamsi ya kasance shi ne yake jagorantar sallar idan ƙaramar sallah.[18] a shekarar 1360 Akbar Hashimi Rafsanjani ya jagoranci sallar idul fiɗri a babban birnin Tehran.[19]

Tsawon lokaci ya kasance ana sallar idi a cikin jami'ar Tehran, daga shekarar 1362 shamsi wanda ya yi daidai da 1403 hijira ƙamari.[20] an fara sallar idul fiɗri a babban masallacin juma'a na birnin Tehran. An dagatar da taron sallar idul fiɗri a tsawon shekarun biyu a jere daga 1399-1401 sakamakon yaɗuwar annobar cutar shaƙe numfashi da ake kira da korona (Corona).[21]

Addu'ar Alƙunut

«اَللّهُمَّ اَهْلَ الْکبْرِیاءِ وَالْعَظَمَةِ وَاَهْلَ الْجوُدِ وَالْجَبَروُتِ وَاَهْلَ الْعَفْوِ وَالرَّحْمَةِ وَاَهْلَ التَّقْوی وَالْمَغْفِرَةِ اَسْألُک بِحَقِّ هَذَا الْیوْمِ الَّذی جَعَلْتَهُ لِلْمُسْلِمینَ عیداً وَ لِمـُحَمَّد صلی الله علیه وآله ذُخراً وَشَرَفاً وَ کَرامَةً وَمَزیداً أَنْ تُصَلِّیَ عَلی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ اَنْ تُدْخِلَنی فی کُلِّ خَیرٍ أدْخَلْتَ فیهِ مُحَمَّداً وَآلَ مُحَمَّد وَ أَنْ تُخْرِجَنی مِنْ کلِّ سوُءٍ اَخْرَجْتَ مِنْهُ مُحَمَّداً وَ آلَ مُحَمَّد صَلَواتُک عَلَیهِ وَ عَلَیهِمْ اَللّهُمَّ إنّی اَسْألُکَ خَیرَ ما سَألَکَ بِهِ عِبَادُکَ الصَّالِحوُنَ وَأَعوُذُ بِکَ مِمَّا اسْتَعَاذَ مِنْهُ عِبَادُکَ الْمـُخْلَصوُنَ

Ya Allah ya ma'abocin girma, ma'abocin kyauta da iko, ma'abocin afuwa da rahama, ma'abocin takawa da gafara, ina rokonka da hakkin wannan rana da ka sanya ta idi ga musulmi, ka sanya ta ajiya da daukaka da karamci da karuwa ga muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa), ina rokonka ka shigar da ni cikin duk wani alheri da ka shigar da Muhammad da iyalansa. ina kuma rokonka ka fitar da ni daga duk wani mugun abu da ka fitar da Muhammad da iyalansa, (tsira amincinka ya tabbata a garesu.) daga cikinsa. ina rokonka mafi alherin abin da bayinka nagargaru suka roke ka. ina neman tsarinka daga abin da tsarkakkun bayinka suka nemi tsarinka daga gare shi.

Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), 1378 AH, Juzu'i na 1, shafi na 296

Hukunce-hukence Da Ladubban Sallar Idi

kan asasin fiƙihuyn shi'a, sallar idi wajibi ce a lokacin hallarar Imami Ma'asumi.[22] kuma wajibi yinta da tsarin jam'i.[23] amma a zamanin fakuwa da gaibar Imami ma'asumi tana kasancewa mustahabbi,[24] tare da haka akwai saɓani cikin yin wannan sallah a jam'i lokacin gaiba.[25] bisa fatawar Imam Khomaini, idan waliyul faƙihi ko kuma mutumin da ya samu izini daga gare shi ya yi niyyar jagorantar limancin sallar idi ko kuma da niyyar muna fatan samun lada, cikin wannan hali babu matsala, saɓanin haka bisa ihtiyaɗi na wajibi shi ne kada a yi ta da tsarin jam'i.[26]

sallar idi raka'a biyu ce, cikin kowacce raka'a bayan karatun fatiha ana karanta wata sura daga kur'ani. An ce yafi lada a raka'a ta farko bayan fatriha a karanta suratul shamsi, a raka'a ta biyu a karanta suratul gashiya, ko kuma a raka'a ta farko a karanta suratul a'ala ta biyu a karanta suratul shamsi. haka nan a raka'a ta farko bayan karatun sura ana yin kabbara guda biyar tare da alƙunut biyar, a raka'a ta biyu kuma bayan karatun sura ana yin kabbarori guda huɗu tare da alƙunut huɗu, cikin alƙunut za a iya yin kowanne zikiri da addu'a, amma dai an fi so a karanta addu'a ko zikiri na musammam wanda ya zo a hadisi misalin addu'a wannan addu'a «اللّهُمَّ اَهْلَ الْکبْرِیاءِ وَالْعَظَمَةِ...».[27]

huɗuba

sallar idi kamar misalin sallar juma'a ce tana da huɗubobi guda biyu, tare da ɗan ƙaramin bambanci tsakaninsu, ksancewa ita huɗubar idi ana yinta bayan idar da sallah.[28] kan asasin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Rida (A.S) wace a littafin Jawahirul Al-kalam ta zo, wannan bambanci ya kasance sakamakon ita sallar juma'a ana yinta duk sati, kuma idan aka ce za adinga yin huɗuba bayan idar da sallah lallai mutane za su gaji za su dinga tafiya ba tare da sauraren huɗubar ba, amma ita sallar idi sakamakon karo biyu kacal aka yinta a shekara mutane suna jira su saurara har zuwa ƙarshen huɗuba.[29] haka nan game da kasancewarta wajibi ko mustahabbiu akwai saɓani tsakanin malaman fiƙihu.[30]

lokaci

a cewar Sahibul Jawahir, kan asasin ra'ayin mashhur daga malaman fiƙihu na shi'a, lokacin sallar idi yana farawa ne daga farkon hudowar rana zuwa zawali (Azuhur ta shari'a),(31) idan ba a yita kan lokacinta ba shikenan ta wuce ba za a rama ba,[31] bisa fatawar Imam Khomaini mustahabbi ne yin sallar idi bayan ɗagowar rana.[32] haka nan sahibul jawahir ya naƙalto daga littafin madarikul al-ahkam cewa malamai sun yi ittifaƙi kan kasancewar sallar idin ƙaramar sallah mustahabbi tare da jinkiri kaɗan cikin yinta daga babbar sallar layya, saboda a idin ƙaramar sallah mustahabbi ne masu sallah su ci abinci gabanin tsayar da sallar, amma a idin babbar sallah mustahabbi ne a yi a fara buɗa baki da naman da aka yi layya bayan idar da sallar idin.[33]

Sallar Idi A Bainal Haramaini Karbala

ladubba

  • Faɗin zikirin: «اَللهُ اَکبرُ اَلله اَکبرُ، لا اِلهَ اِلّا اللهُ وَاللهُ اَکبرُ، اَلله اَکبرُ وَلِله الحَمدُ، اَلله اَکبَرُ عَلی ما هَدانا» bayan idar da sallar idi.[34]
  • Sallar idi babu kiran sallah da iƙama a cikinta, amma mustahabbi ne ladan ya maimaita faɗin “Assalat” sau uku.[35]
  • Makaruhi ne yin sallar idi a wuri mai rufi.[36] an arawaito cewa Imam Ali (A.S) tun daga fitowa daga gidansa har zuwa wajen garin kufa wurin da ake yin sallar idi ya kasance yana maimaita kabbara.[37] haka nan an naƙalto daga Abdullahi ɗan Umar cewa Annabi (S.A.W) yana tattaki daga gida zuwa filin sallar idi, haka bayan idar da sallah yana tattaki ya dawo gida.[38] an naƙalto daga Abu Rafi'i cewa Annabi (S.A.W) idan zai dawo yana canja hanya saɓanin hanyar da ya bi yayin zuwa wurin sallar idi.[39]
  • Wajibi wanda zai je sallar idi ya fara bayar da zakka fidda kai gabanin sallar idi, ko kuma bisa fatawar ba'arin malamai ya fitar da zakkar ya wareta daga cikin dukiyarsa,[40] saboda bisa abin da ya zo a riwaya, abin da ake nufi daga «تزکی» و «فَصَلَّیٰ» در cikin ayoyin «قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَکیٰ» [41] da «وَذَکرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّیٰ»[42] ya kasance bada zakkar fidda kai da tsayar da sallar idi.[43]
  • Mustahabbi ne masu sallah su fara yin wanka kafin sallah, tare da karanta addu'o'i da zikiri da ake yi kafin sallar da bayanta.[44]
  • Mustahabbi ne masu sallah su ɗora goshinsu kan ƙasa lokacin da suke yin sallah,[45] yayin kabbara ana son a ɗaga hannuwa sama tare da ɗaga murya cikin karatun zikirin sallah.[46]
  • Cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya yi umarni da sanya mafi kyawun tufafi a ranar idi tare da amfani da mafi kyawun turare.[47]

Bayanin kula

  1. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 333.
  2. Tabari, Tarikh al-Tabari, Beta, juzu'i na 2, shafi na 418.
  3. «باشکوه‌ترین نمازهای عید در کجا برگزار می‌شود؟»، خبرگزاری ایرنا.
  4. «نماز عید فطر در سراسر کشور اقامه شد»، خبرگزاری ایرنا.
  5. «جزئیات نماز عید فطر در حرم مطهر رضوی»، پایگاه حوزه‌نیوز.
  6. «عید فطر آستان قدس رضوی در آیینه تاریخ»، خبرگزاری ایرنا.
  7. «نماز عید فطر در حرم امام علی»، پایگاه خبری شفقنا.
  8. «نماز عید در مسجد جامع کوفه»، پایگاه خبری شفقنا.
  9. «نماز عید در بین الحرمین»، خبرگزاری ابنا.
  10. Kulayni, Al-Kafi, 1407 BC, juzu'i na 1, shafi 489.
  11. Kulayni, Al-Kafi, 1407H, juzu'i na 1, shafi 490.
  12. Mutahari, Majmu'eh Athar, 1390 AH, juzu'i na 17, shafi na 174-176.
  13. Nikbakht, "Ramadan 1357 da Masjudu Quba", shafi na 60.
  14. Nikbakht, "Ramadan 1357 da Masjudu Quba", shafi na 60.
  15. «حواشی متفاوت آخرین نماز عید فطر زمان شاه»، پایگاه اطلاعات آنلاین.
  16. «نماز و راهپیمایی عید فطر شهریور 1357 به روایت اسناد ساواک»، سایت مرکز بررسی اسناد تاریخی».
  17. Khumaini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 12, shafi na 116.
  18. «نماز عید فطر در دهه ۶۰»، خبرگزاری خبرآنلاین.
  19. Hashemi Rafsanjani, Ubur Bahran, 1378 AH, shafi 224
  20. Hashemi Rafsanjani, Aramesh wa Chalash, 1386 AH, shafi na 145
  21. «پایان سه‌ سال وقفه»، خبرگزاری خبرآنلاین.
  22. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 333.
  23. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 824.
  24. Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362, juzu'i na 11, 333.
  25. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 824
  26. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 824
  27. Khumaini, Tahrir Al-Wasila, Mu’assasa Tanzimu Asar Imam Khumaini, juzu’i na 1, shafi na 227.
  28. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 337-338.
  29. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 338.
  30. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 337-338.
  31. Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 11, shafi na 355.
  32. Bani Hashemi Khomeini,Tauzihul Al-masa'il (Marajis), Ofishin Intisharat Islami, Juzu'i na 1, shafi na 824.
  33. Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 11, shafi na 354-355.
  34. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji'u), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 827.
  35. Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362, juzu'i na 11, shafi na 374.
  36. Khumaini, Mu’assaseh Tanzimu wa nashar asar Imam Khumaini, juzu’i na 2, shafi na 228.
  37. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 BC, juzu'i na 88, shafi na 118; Mutqi al-Hindi, Kanz al-Ummal, 1413 BC, juzu'i na 7, shafi na 88.
  38. Mutqi al-Hindi, Kanz al-Ummal, 1413 BC, juzu'i na 7, shafi na 88.
  39. Mutqi al-Hindi, Kanz al-Ummal, 1413 BC, juzu'i na 7, shafi na 88.
  40. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji'u), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 827.
  41. سوره اعلی، آیه ۱۴.
  42. سوره اعلی، آیه ۱۵.
  43. Tabatabaei, Al-Mizan, Jamia Modaresin Publications, juzu'i na 20, shafi.269.
  44. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji'u), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 826
  45. Najafi, Jawahirul al-Kalam, 1362, juzu'i na 11, shafi na 374.
  46. Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il (Maraji'u), Ofishin Intisharat Islami, juzu'i na 1, shafi na 826
  47. Qazi Nu'man, Da'aim al-Islam, 1385 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 185.

Nassoshi

  • باشکوه‌ترین نمازهای عید در کجا برگزار می‌شود؟، خبرگزاری ایرنا، تاریخ درج مطلب: ۲ اردیبهشت ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۴ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • بنی‌هاشمی خمینی، محمدحسن، توضیح المسائل (مراجع)، قم، دفتر انتشارات اسلامی، بی‌تا.
  • «پایان سه‌ سال وقفه»، پایگاه خبرآنلاین، تاریخ درج مطلب: ۱ اردیبهشت ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۱ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • «حواشی متفاوت آخرین نماز عید فطر زمان شاه»، پایگاه اطلاعات آنلاین، تاریخ درج مطلب: ۳ اردیبهشت ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۴ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Tehran, Imam Khomeini Works Editing and Publishing Institute, Beta.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, 1378.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Jamia Modaresin Publications, Beta.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Tabari, bincike: Mohammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, B.T.
  • Qazi Noman Maghrib, Da'aim al-Islam, bincike na Asif Faizi, Qum, Cibiyar Al-Bait, 1385H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, bugun Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • «گزارش نماز عید فطر سال ۱۳۵۷ در مرکز بررسی اسناد تاریخی»، تاریخ درج مطلب: ۲۹ فروردین ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۲ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • Motaghi al-Hindi, Ali bin Hussam, Kanz al-ummal fi Sunan al-Aqwal wa al-Afal, Beirut, Al-Rasalah Est., 1413 AH.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Darahiya al-Trath al-Arabi, 1403H.
  • Motahari, Morteza,majmu asar, Tehran, Sadra, 1390.
  • Najafi, Mohammad Hasan bin Mohammad Baqir, Javaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, wanda Abbas Qochani ya yi bincike a Beirut, Dar Ihya Al-Tarath al-Arabi, bugu na 7, 1362.
  • «نماز عید فطر در دهه ۶۰»، پایگاه خبرآنلاین، تاریخ درج مطلب: ۲۵ خرداد ۱۳۹۷ش، تاریخ بازدید: ۲ اردیبهشت ۱۴۰۲ش.
  • نیکبخت، رحیم، «رمضان ۱۳۵۷ و مسجد قبا»، ماهنامه زمانه، شماره ۲۶، آبان ۱۳۸۳ش.
  • Hashemi Rafsanjani, Akbar, Aramesh wa Chalish: Karname da Tunanin Hashemi Rafsanjani, 1362, tare da kulawar Mehdi Hashemi, Tehran, Enghelab Ma’arif Publishing Book, 1386 AH.
  • Hashemi Rafsanjani, Akbar, Amid wa Dilawabsi: Karname da Tunanin Hashemi Rafsanjani, 1364, tare da sha'awar Sara Lahouti, Tehran, Enghelab Ma’arif Publishing Book, 1387 AH.
  • Hashemi Rafsanjani, Akbar, Pas Az Bahran: Karname da Tunanin Hashemi Rafsanjani, 1361, tare da kulawar Fatemeh Hashemi, Tehran, Littafin Bugawa Enghelab Ma’arif, 1386 Hijira.
  • Hashemi Rafsanjani, Akbar,Ubur Bahraini: Karname da Tunanin Hashemi Rafsanjani, 1360, Yasser Hashemi, Tehran, Littafin Bugawa Enghelab Ma’arif, 1378 Hijira.