Shekara Ta 3 Hijira
Appearance
Shekara 4 Hijira Ƙamari Shekara 2 Hijira Ƙamari | |
| 624 da 625m | |
|---|---|
| Imamanci | |
| Annabtar Sayyidina Muhammad (S.A.W) | |
| Hukumomin ƙasashen Muslunci | |
| Muhammad Bin Abdullah (S.A.W) a Madina | (Hukuma:1-11 hijira) |
| Muhimman abubuwan da suka faru | |
| Yaƙin Uhudu | |
| Yaƙin Hamra'ul Asad | |
| Sariyyatu Zatu Irƙi | |
| Yaƙin Buhran | |
| Auren Annabi (S.A.W) tare da Hafsa Ƴar Umar Bin Khaɗɗab | |
| Haihuwa da mutuwa | |
| Imam Hassan Mujtaba (A.S) | |
| Wafati/Shahada | |
| Shahadar Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib | |
| Shahadar Mus'ab Bin Umair | |
| Shahadar Hanzalatu Bin Abi Amir | |
Shekara ta 3 hijira ƙamari, (Larabci: سنة 3 للهجرة) ita ce shekara ta uku a jerin lissafin hijira ƙamari.
Rana ta farko tana kasancewa 1 Muharram daidai da Yekshanbe 6 ga watan Tir shekara ta uku kalandar Farsi, kuma daidai da 27 Yuni shekara 624 miladiyya, rana ta ƙarshen wannan shekara tana kasancewa 29 Zil-Hijja, wanda ya yi daidai da Ceharshanbe 25 ga watan Khordad kalandar Farsi shekara ta 4 kalandar Farsi, daidai da 16 Yuni shekara ta 625 miladiyya.[1]
Haihuwar Imam Hassan (A.S), rashin nasarar Musulmi a yaƙin Uhudu da shahadar Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib, kawun Annabi (S.A.W) da Hanzala Bin Abi Amir, suna cikin muhimman abubuwan da suka faru a wannan shekara.
Muhimman Abubuwa Da Suka Faru
- Faruwa yaƙin Uhudu daga shahararrun yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W) tare da mushrikan Makka (7 Shawwal[2] a wata maganar kuma 15 Shawwal[3]/23 Maris 625m)
- Yaƙin Hamra'ul Asad bayan yaƙin Uhudu domin hana mushrikai sake kawo hari a 8 Shawwal.[4]
- Sariyyatu Zatul Irƙi wanda ya faru sakamakon rashin zaman lafiya da kuma hana ayarin ƴankasuwar ƙuraishawa tafiya a watan Jimadus Sani.[5]
- Yaƙin Buhran dan warware makircin ƙabilar Bani Salim.[6]
- Afkuwar sariyyatu Abu Salma Bin Abdul-Asad domin warware hatsarin mushrikan ƙabilar Bani Asad.[7]
- Auren Annabi (S.A.W) tare da Hafsa Ƴar Umar Bin Khaɗɗab a watan Sha'aban.[8]
- Auren Annabi (S.A.W) tare da Zainab Ƴar Khuzaima.[9] Ɗabari yana ganin wannan aure ya kasance a shekara ta 4 hijira[10]
Haihuwa
- Haihuwar Imam Hassan Mujtaba (A.S)(15 Ramadan)[11] Shaik Kulaini a cikin Al-Kafi tare da naƙalin wata riwaya ya ba da rahoton haihuwar Imam a shekara ta 2 hijira.[12]
- Haihuwar Hudainu Bin Munzir Raƙƙashi daga sahabban Imam Ali (A.S) kuma marawaicin hadisi,[13]
- Haihuwar Sa'ib Bin Yazid Kindi daga sahabban Annabi kuma alƙalin Madina a lokacin mulkin Umar da Usman.[14]
Wafati
- Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib.[15]
- Shahadar Hamza Bin Abdul-Muɗɗalib kawun Annabi (S.A.W) a lokacin yaƙin Uhudu.[16]
- Shahadar Mus'ab Bin Umair a yaƙin Uhudu.[17]
- Mutuwar Ka'ab Bin Ashraf daga manyan garin Madina masu adawa da Annabi (S.A.W).[18]
Bayanin kula
- ↑ سایت تبدیل تاریخ هجری
- ↑ Wagedi, Al-Maghazi, 1966, juzu'i. 1, shafi. 199.
- ↑ Ibn Ishaq, Al-eyar Wa Al-Magazi, 1398H, shafi na 324.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiya, 1355 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 107-108.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 1, shafi. 374.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Sirah Al-Nabawiya, 1355 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 50.
- ↑ Masoudi, Al-Tanbih wa al-Ashraf, Alkahira, shafi. 212.
- ↑ Ibn Qutaybah, Al-Ma'arif, 1960, shafi. 158.
- ↑ Ibn Hajar, Al-isaba, 1415 AH, juzu'i. 8, shafi. 157.
- ↑ Al-Tabari, Tarikh al-Umam Wa al-Muluk, 1387H, juzu'i. 2, shafi. 545.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i. 2, shafi. 537; Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 3; Arbeli, Kashful al-Ghumma, 1421 AH, juzu'i na 2, shafi.80; Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 141.
- ↑ Al-Kulaini, Al-Kafi, 1401, juzu'i. 1, shafi. 461.
- ↑ Amin, Ayan al-Shi'a, 1403 AH, juzu'i. 6, shafi. 194.
- ↑ Ibn Asakir, Tarikh Madinati Demashƙi, 1415H, juzu'i. 20, shafi na 109, 112.
- ↑ Vagadi, Al-Maghazi, 1966, juzu'i. 1, shafi. 199.
- ↑ Baladhari, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i. 9, shafi. 408.
- ↑ Ibn Abdul Bar, Al-Isti'ab, 1412 AH, juzu'i. 1, shafi. 381.
- ↑ Ibn Sa’ad, Al-Tabaqat al-Kubra, 1405H, juzu’i. 2, shafi. 3233.
Nassoshi
- Ibn Ishaq, Muhammad, As-Siyar wa al-Magazi, bugun Suhail Zakkar, Damascus, 1398H.
- Ibn Hajar, Ahmad bn Ali, Al-Isaba fi Tamyiz al-Sahaba, Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah, 1415H.
- Ibn Sa’d, Muhammad, Al-Tabaqat al-Kubra, Beirut, Darul Sadir, 1405H.
- Ibn Abd al-Barr, Yusuf bn Abdullah, Al-Isti'ab fi Ma’arifati al-As'hab, Beirut, Dar al-Jil, 1412H.
- Ibn Asakir, Ali bn Hassan, Tarikhul Madinatul Damashƙi, wanda Ali Shiri ya yi bincike a Beirut, 1415 bayan hijira.
- Ibn Qutaybah Dinwari, Abdullahi bn Muslim, Al-Ma’arif, Alkahira, Tharwat Ukasha Publishing House, 1960H.
- Ibn Hisham, Abdul Malik, Al-Sirat al-Nabawiyya, Mustafa Sakka, Ibrahim Abyari, da Abdul Hafiz Shalabi, Alkahira, 1355H suka yi bincike.
- Arbali, Ali bn Isah, Kashful Gumma Fi Ma'arifatil A'imma, Qum, Razi Publishing House, 1421H.
- Amin, Sayyid Mohsen, A'ayan al-Shi’a, Beirut, Dabul-Ta’rif Publishing House, 1403H.
- Baladzhari, Ahmad bn Yahya, Jamal min Ansab al-Ashraf, Suhail Zakkar da Riyad Zarkali suka yi bincike a Darul Fikr, Beirut, 1417 bayan hijira.
- Khatib Baghdadi, Ahmad ibn Ali, Tarikh al-Baghdad, Mustafa Abdulqadir Atta, Beirut, Muhammad Ali Baydoon Publications ya yi bincike, 1417 AH.
- Sheikh Mufid, Muhammad ibn Muhammad, Al-Irshad fi Ma’rifat al-Hujajullahih ‘ala al-Ibad, Qum, Sheikh Mufid Congress, 1413 AH.
- Tabari, Muhammad bn Jarir, Tarikh al-Tabari, Beirut, Darul-Turat, bugu na biyu, 1387H.
- Kulayni, Muhammad bn Ya'qub, Al-kafi, Tehran, Islamiya, 1362H.
- Masoudi, Ali bin Hossein, al-Tanbihu wa al-Ishraf, Abdullah Ismail al-Sawi, Alkahira, Dar al-Sawi, Bita ya gyara.