Jump to content

Bayyanar Da Ƙin Yin Azumi Da Gangan

Daga wikishia


Ƙin yin azumi da gangan a watan Ramadan (Larabci: المجاهرة بالإفطار) magana ce game da ƙin ɗaukar azumi da gangan ba tare da wani dalili a shari'a ba, wannan abu haramin ne a addinin Muslunci, kai bari ma wannan abu yana daga cikin manyan laifuka, kuma wajibi ne ga wanda ya sha azumi da gangan ya rama azumin da ya sha da kuma ƙarin bada kaffara.

Bisa fatawar malaman fiƙihu hukuncin wanda ya sha azumi da gangan a karo na farko ko na biyu shi ne bulala 25. Wasu daga cikin malaman sun tafi kan cewa idan aka yi mishi hukunci na bulala 25 sau biyu, to idan ya ƙara karya azumi karo na uku, hukuncinshi shi ne kisa.

Kamar yadda malaman fiƙihu suke gani cewa mai shan azumi a gaban mutane, koda yana da uziri a shari'a to haramun ne, kuma wanda yake aikata hakan ya cancanci uƙuba. A wasu ƙasashe na Muslunci ƙin yin azumi a bainar jama'a laifi ne a doka, kuma yin hakan yana iya sa mutum ya yi zaman gidan yari (Gidan gyaran hali) da yin bulala da kuma biyan tara ta kuɗi

Ma'anar Bayyana Shan Azumi Da Muhimmancinshi

Shan azumin watan Ramadan yana nufin ƙin yin azumi da gangan ba tare da wani uzuri ba.[1] Yin hakan haramun ne a Muslunci kuma babban laifi ne.[2] Ya zo a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) wanda Kulaini ya kawo a cikin littafinshi na Al-Kafi cewa, duk wanda ya karya azumi da gangan, to ya fita daga addini.[3]

Daga cikin hukunce-hukunce ada suka zo cikin litattafai na fiƙihu, akwai cewa duk wanda yaƙi yin azumi da gangan a watan Ramadan kuma ya san hukuncin yin hakan kuma ya yi imanin cewa abin da ya aikata halas ne, to irin wannan mutuman ana ɗaukarshi a matsayin wanda ya yi ridda, kai ko dama bai karya azumin ba, amma ya yi imani da cewa halas ne ya ƙi yin azumi a watan Ramadan, to lalle za a yi mishi hukuncin cewa ya yi ridda.[4] Bisa fatawar malaman fiƙihu, wajibi ne ga wanda yaƙi yin azumi ya rama azumin da ya sha kuma ya ƙara da ba da kaffarar azmin da ya karya da gangan.[5]

Malaman fiƙihu suna ganin duk wanda ya karya azumi da gangan, amma ba tare da ya yi imanin cewa hakan halas ba ne, to irin wannan mutumin ya cancanci ladabtarwa da Hakimul shar'i' ya ga ya dace da shi. An ambaci hukuncin mai karya azumi da gangan, a karon farko da na biyu za a yi wa mutum bulala 25.[6] Bisa abin da wasu malaman fiƙihu suka tafi akai idan ya maimaita shan azumi bayan yi mishi hukunci sau biyu, to hukuncinshi a karo na uku shi ne a kashe shi, duk da wasu malaman ba su yarda da wannan ra'ayin ba.[7] Wajibi ne ga wanda ya sha azumi, daɗi kan yi mishi hukunci dole ne ya rama azumin kuma ya ba da kaffara.[8]

Shan Azumi A Bayyane da Hukuncinshi

Malaman fiƙihu na Shi'a da Ahlus-Sunna suna ganin bai halatta ba mutum ya bayyana baya azumi a bainar jama'a a watan Ramadan, kuma ko da yana da wani uziri a shari'a.Suna ganin wanda yake nuna baya azumi da gangan a cikin mutane ya cancanci a yi mishi uƙuba.[9] Tabbas ya tabbata cewa shan azumi a cikin mutane laifi ne a wasu daga cikin ƙasashan Muslunci.[10] Ta yadda suke hukunci a kanshi da hukunce-hukunce da suka ƙunshi zaman gidan gysran hali, ko kora ko bulala ko tara, kai hadda hukuncin kisa a wasu lokutan.[11] Alal misali bisa hukunci na uƙuba a Muslunci a Iran duk wanda ya sha azumi a cikin mutane hukuncishi shi ne zaman gidan gyaran hali zuwa kwana 10 ko 20 ko hukuncin yin bulala 74.[12] Kazalika wanda ba Musulmi ba da yake rayuwa a Jamhuriyyar Muslunci za a hanashi ci da sha a guraran da mutane suke taruwa a watan Ramadan, saboda doka ana aiki da ita ne ga dukkan mazauna ƙasar.[13]

Sharuɗɗan Zartar Da Hukuncin Shan Azumi A Bainar Jama'a

Daga cikin shariɗɗan yin hukuncin kan wanda yaƙi yin azumi a watan Ramadan da gangan, ya zama ya yi hakan a bayyane kuma a cikin mutane.[14] Kamar yadda aka ce duk wanda yake bayyana ƙin yin azumi a inda mutane suke taruwa, ya kamata a miƙa shi ga kotu domin yi mishi hukunci.[15]

Bayanin kula

  1. Salihi، معارف إسلامي، ج27، ص15.
  2. Dastgheeb, Al-Zunub Al-Kabira, Juz. 1, shafi. 27; Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-Wasilah, Kungiyar da ke fayyace ayyukan Imam Al-Khamini, Vol. 1, shafi na 258-259.
  3. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, Juz. 2, shafi. 278.
  4. Mu'assasatu Da'irati Ma'arif Al-fiqhi Al-Islami, Farhange Fiqh (Mausu'atu Al-fiqhi Al-Islami Tibqan Li MazhabAhlil-Bati), 2013, juz. 5, shafi na 145-146; Al-Imam Al-Khomaini, Tauzihul Masa'il (Al-Mahashi), 1424H, Juzu'i na 2, shafi na 494 da 495.
  5. Al-Najfi, Jawahir al-Kalam, 1404 AH, juzu'i. 16, shafi. 226; Al-Khoyei, Mausu'atu Al-Imam Al-Khoyei, 1418 AH, juzu'i. 21, shafi. 305.
  6. Al-Tabataba’i Al-Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthqa, 1420 AH, Juz. 3, shafi na 521-522.
  7. Al-Tabataba’i Al-Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthqa, 1420 AH, Juz. 3, shafi na 522.
  8. Imam Khomaini, Tauzihul Masa'il (Al-Mahashi), 1424H, Mujalladi. 1, shafi. 926; Mu'assasatu Da'irati Ma'arif Al-fiqhi Al-Islami, Farhange Fiqh (Mausu'atu Al-fiqhi Al-Islami Tibqan Li MazhabAhlil-Bati), 1385 AH, Juz. 4, shafi. 169.
  9. Al-Allamah Al-Hilli, Muntaha Al-Matlab, Juz. 9, shafi na 174-175; Al-Sarakhsi, Al-Mabsut, 1414 AH, Juz. 24, shafi na 32-33.
  10. Zaki Zakka da Salman Pour, "Bazkhwani fiqhi Wa Huquqi Jurme Inkari Tazahur Beh Ruzeh Khori Dar Qanun Majazat Islami Iran Wa Kode Jazaye Afganistan," shafi. 60.
  11. "Majazate Rozeh Khori Dar Iran Wa Sayire Kishwarhaye Islami," wanda aka buga a cikin shafin labarai na Gabas da gidan yanar gizon nazari.
  12. Qanun Majazate Islami Iran, Kitabe Panjom, an amince da ita a shekara ta 1375.
  13. Qanun Majazate Islami Iran, Kitabe Panjom, an amince da ita a shekara ta 1375.
  14. Mousavi Azadeh Wa hamkaran., "Ta'ammuli Bar Ruze Khori Dar Ruye Qazayi, Fi'ili Mujrimaneh Ya Fi'li Haram?", shafi. 544.
  15. Mesavi Kalbaykani, Majma'ul al-Masa'il, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 215.

Nassoshi

  • Imam Al-Khomaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Tehran, Kungiyoyi da Buga Ayyukan Imam Al-Khamini, D.T.
  • Al-Imam al-Khomeni, Sayyid Ruhollah, Tauzihul Al-masa'il (Al-Mahashi), ta kokarin Mohammad Hosseini Al-Hashemi Al-Khamini, Qum, Islamic Publications, D.T.
  • Al-Khoei, Sayyid Abul-Qasim, Mausu'atu al-Imam Al-Khoyei, Qum, Mu'assasa ta Farfado da Ayyukan Imam Al-Khoei, Juzu'i na 1, 1418 Hijira.
  • Dastgheeb, Seyyed Abdul Hossein, Al-Zonoub al-Kabeira, Qom, ofishin wallafe-wallafen Musulunci.
  • Zaki Zaki, Ahmad da Abbas Salmanpour«بازخواني فقهي و حقوقي جرم انگاري تظاهر به روزه خواري در قانون مجازات إسلامي ايران و كد جزاي افغانستان»، Jaridar Kwatakwata ta Kwatancen Nazarin Shari'ar kasashen Musulunci, lamba 3, 1402H.
  • Al-Sarakhsi, Muhammad bin Ahmad, Al-Mabsut, Beirut, Dar Al-Marafah, 1414H.
  • Salehi, Nad Ali,Ma'arif Islami, Qum, ofishin yada farfagandar Musulunci na Al-Hawza Al-Elamiya Qum, D.T.
  • Tabatabai Al-Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-urwa Al-Wuthgha, Qom, Al-Nashar Islamic Institute, 1420H.
  • Allamah Al-Hali, Hasan bin Youssef, Mantaha al-Matalib a cikin binciken addini, Mashhad, Majalisar bincike ta Musulunci, 1412H.
  • Qanun Majazate Islami Jamhuriye Islami Iran, Cibiyar Nazari Ta Majalisa, ta amince da ita a shekara ta 2012.
  • Al-Kulaini, Muhammad bin Yaqoob, Al-Kafi, gyara: Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kutb al-Islami, 1407H.
  • «مجازات روزه‌ خواري در إيران و ساير كشورهاي إسلامي », wanda aka haɗa a cikin gidan labaran Sharq, wanda aka buga: Mayu 31, 2019, duba: Maris 3, 2024.
  • Mu'assasatu Da'irati Al-ma'arif al-Fiqhil Islami, Farhang Fiqh (Mausu'atual-Fiqhil Islami Tibqan Li Mazhab Ahlil-Baiti), Qum, Mu'assasar Shari'a ta Musulunci, 1387.
  • Mousavi Azadeh, Seyed Reza, Iman Esfandiar, Seyed Hamed Razavi,«تأملي بر روزه خواري در رويه قضائي؛ فعل مجرمانه يا فعل حرام؟»،Jaridar Kwata-kwata ta Wayewar Shari'a, Na 11, 1401 AH.
  • Al-Muusawi Al-Kaykani, Sayyid Mohammad Reza, Majma'ul Al-Masa'il, Qum, Darul Qur'an al-Karim, 1409H.
  • Al-Najafi, Muhammad Hassan, Jawahirul al-Kalam Fi Sharhi Shara'i'il Islam, Abbas Quchani da Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihiya al-Tarath al-Arabi, Juzu'i na 7, 1404H.