Jump to content

Aiki Na Gari

Daga wikishia

Aiki na gari (Larabci: العمل الصالح) Aiki na gari yana nufin aiki mai kyau, bayan imani da Allah, ana la'akari da aiki na gari matsayn sharaɗi domin dacewa da rabauta, Kur'ani ya siffata muminai waɗanda suke aiki na gari a matsayin mafifta a cikin halittu, bisa abin da ya zo a Kur'ani a ranar ƙiyama ƴan wuta za su yi fatan komawa duniya domin su yi aiki na gari, a cikin Kur'ani sakamakon aiki na gari da kuma imani shi ne rayuwa mai kyau, dukkan mutane suna cikin asara face muminai waɗanda suka yi aiki na gari.

Aiki na gari ya ƙunshi aikin mutum ɗaya da kuma aiki mutane da yawa wanda ya dace, daga cikin ma'anar aiki na gari, akwai bin Allah da ciyarwa, da aikata nauyin da ya hau kan mutum da bari abin da ya haramta da neman ilimi da bautawa Allah da duk wani aiki wanda yake kai wa ga ci-gaban al'umma. Malamai masana ilimin Kur'ani suna cewa akwai alaƙa ta tasirantuwa tsakanin imani da aiki na gari kuma ko wane ɗayansu yana cika ɗayan ne, imani shi kaɗai baya tseratar da mutum kazalika aiki na gari shi ma haka. Kuma su waɗannan masana suna ganin cewa wanda yake da imani, to tsiranshi zai zamo gwargwadon imanishi da aikinshi.

Matsayi

Allah Ta'ala Ya ce:

فَمَنْ كانَ يَرْجُوا لِقاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلاً صالِحاً وَ لا يُشْرِكْ بِعِبادَةِ رَبِّهِ

Wanda yake fatan gamuwa da Ubangijinsa, to, ya aikata kyawawan ayyuka, kuma kada ya yi shirka cikin ibadar Ubangijinsa.

[1]

A cikin Kur'ani tare da imani an ambaci aiki na gari a matsayin sharaɗi na tsira ga ɗan Adam.[2] Umarni ya zo a cikin ayoyi da yawa kan aikata aiki na gari da cewa sakamakon duk mutumin da yake aiki na gari shi ne aljanna,[3] kamar yadda ambaton aiki na gari ya zo sau 87 da yanayi daban-daban a cikin Kur'ani.[4] Bisa abin da ya zo a cikin Kur'ani, duk wanda yake aiki na gari[5] a yayin da yake mumini, to sakamakonshi shi ne gidan aljanna.[6] Malaman tafsiri sun ƙarfafa cewa abin da yake da muhimmanci a addini kuma yake sa dacewa da karama ga ɗan Adam shi ne imani da aiki na gari.[7] An bada labari cewa alaƙa ta gaskiya da Allah tana bayyana ne a imani da aiki na gari, saɓani haka zai zama mutum yana yaudarar kansa ne kawai.[8]

Ma'ana Da Kuma Wane Abu Ne Aiki na Gari

Ana la'akari da aiki na gari a matsayin abin da ya ƙunshi abubuwa da yawa,[9] ana cewa ya ƙunshi duk wani aiki na gari, shin aiki ne na mutum ɗaya ko na mutane da yawa ko na addini ko na siyasa,[10] daga cikin abubuwan da ake lissafa su a aiki na gari akwai biyayya ga Allah maɗaukaki,[11] jihadi,[12] bin Annabi,[13] aikata duk abin da yake wajibi ne da kuma barin aikita haramun,[14] yin ibada, sadaka, neman ilimi da duk wani aiki na gari wanda zai kai ga ci-gaban al'umma a fagage daban-daban.[15]

Alaƙa Tsakanin imani Da Aiki Na Gari

Allah Ta'ala Ya ce:

مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً ۖ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ

Duk wanda ya aikata aiki na gari, namiji ko mace, kuma yana mumini, to, za mu rayar da shi da rayuwa mai kyau, kuma za mu saka masa da mafi kyawun abin da ya aikata

[16]

Bisa abin da Jafar Subhani ya faɗa, mafi yawan guraran da Kur'ani yake ambatar aiki na gari to zaka samu yana ambaton imani da Allah.[17] a ra'ayinshi akwai alaƙa ta tasiri tsakani imani da aiki na gari kuma akwai cuɗeni in cuɗeka.[18] Izutos masanin ilimin Kur'ani ɗanƙasar Jafan ya ce wannan alaƙa mai ƙarfi a tsakanin imani da aiki na gari, ta kai cewa imani yana bayyana aiki na gari kazalika aiki na gari yana bayyana mene ne imani.[19] Malaman tafsiri sun kai ga sakamako bisa wasu ayoyi cewa, kaɗai aikin da yake karɓaɓɓe shi ne wanda aka yi shi tare da imani,[20] kazalika ana cewa shi aiki na gari, sakamako ne na imani da raba-rabenshi.[21]

Sakamakon Aiki Na Gari

Bisa abin da ya zo a Kur'ani, cewa sakamakon aiki na gari ana ganinshi a duniya da lahira.[22] Duk wanda yake da imani kuma ya yi aiki mai kyau, to zai kai ga wani matsayi gwargwadon aikinshi.[23] A cikin aya ta 7 cikin suratul bayyina an siffanta muminai waɗanda suke aiki na gari a matsayin waɗanda suka fi dukkan halittun Allah.[24] A cikin aya ta 10 suratul faɗir ana la'akari da cewa ma'anar kalimuɗ ɗayyub ita ce aƙida ingantacciya amma aiki na gari abu ne da ake kusantar Allah da shi.[25] Ya zo a cikin ayoyi da yawa na Kur'ani,[26] cewa `yan wuta za su yi fatan dawowa duniya domin aikata aiki na gari,[27] muminai da suke aikata aiki na gari an yi musu alƙawarin babban matsayi a aljanna.[28] Kur'ani yana ganin cewa dukkanin mutane suna cikin asara face muminai waɗanda suka yi aiki na gari.[29]

Bayanin kula

  1. Suratul Kahf, aya ta:110.
  2. Makarem Shirazi, Al-Amthal Fi Tafsiril Kitabillahil Munazzal, j 3, shafin na.465 da j 20, shafi na 437; Montazeri, Islam dinil Fitra, shafi na. 211; Mutahhari, Majmu'eh Asar J 22, Shafi na 96.
  3. Suratul Faatir (35:10, 37), Suratul Nahl (16:97), Suratul Taghabun (64:9), Suratul Asr (103:3), Suratul Nur (24:55), Suratul Tauba (9:120), Suratul Jathiya (45:15), Suratul Hajj (22:14, 23, 56), Suratul Muhammad (47:12), Suratul Taha (20:75), Ja'far Al-Subhani, Manshur Jawed, Juzu'i na 14, shafi 338 da 34
  4. Al-Subhani, Manshor Javid, vol. 14, 338.
  5. Akhlaq Islami fi Nahj al-Balagha (Khutbat al-Muttaqin)" na Ayatollah Naser Makarem Shirazi, J 1 shafi na 520
  6. Kara'ati, Tafsirin An-Nur, Vol. 2, ku. 160.
  7. Makarem Shirazi, Tafsirin Al-Amthal, Vol. 1, p. 249; Karaati, Tafsirin Al-Nur, Vol. 1, p. 127.
  8. Al-Madrasi, Tafsirin Hidayat, j 1, shafi na 514.
  9. Al-Subhani, Manshor Javid, vol. 14, 339.
  10. Al-Tabataba’i, Al-Mizan, J 20, sh 357; Makarem Shirazi, Nafhat Al-Quran, j 6, sh 138; Al-Kashani, Minhajus Sadikin Fi Ilzamil Mukhalifin, J 10, Sh 314.
  11. Kashf al-Asrar wa 'Uddat al-Abrar" na Abu al-Fadl Rashid al-Din al-Maybudi, J 6, sh 468.
  12. Al-Tabataba’i, Al-Mizan, J 9, sh 403.
  13. Manhaj al-Sadiqin fi Ilzam al-Mukhalifin, J 3 sh 375
  14. Khoshdel Mofard, "Barsi Hauze ma'anayi amalil salihi dar Qur'an," shafi. 17.
  15. Makarim Shirazi, Al-Amthal, J 20, sh 436.
  16. Suratul Nahl, aya ta:97.
  17. Al-Sabhani, Manshor al-Javid, J 14, shafi na 340 da 341.
  18. Al-Sabhani, Manshor al-Javid, J 14, Sh 338.
  19. Toshihiko Izutsu, Mafahim Akhlaqi wa Dini dar Qur'an Majid, shafi na. 415.
  20. Karaati, Tafsirin An-Nur,J 4, sh 577.
  21. Makarem Shirazi, Nafhat al-Quran, J 6, sh 136; al-Subhani, Manshur Javid, J 14, Sh 346.
  22. Al-Subhani, Rubutun Javid, J 14, sh 344.
  23. Misbah Al-Yazdi, Restagaran, sh 144.
  24. Makarim Shirazi, Al-Amthal, J 20, sh 365.
  25. Makarim Shirazi, Al-Amthal,J 14, sh 33; Al-Subhani, Manshur Javid, J 14, sh 348.
  26. Suratul Mu'uminun, aya ta 100; Suratul Sajdah, aya ta 12; Suratul Fatir, aya ta 37.
  27. Abu al-Fath al-Razi, Rawdat al-Janan wa Ruh al-Janan, J 14, Sh 51; Makarim al-Shirazi, al-Amthal, J 14, Sh 98.
  28. Al-Tabataba’i, Al-Mizan, J 14, Sh 183.
  29. Makarim Shirazi, Al-Amthal, J 20, Sh 437.

Nassoshi

  • Al-Qur'ani Mai Girma.
  • Abul Futuh al-Razi, Husayn bn Ali, Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan fi Tafsir al-Quran, Mashhad, Islamic Journal of Astan Quds Razavi, 1408 AH.
  • Subhani, Ja'afar, Manshur Javid, Qum, Mu'assasa Imam Sadik (A.S), 1st ed., 1383H.
  • Tabataba'i, Muhammad Husayn, Al-Mizan fi Tafsirin Al-Qur'an, Beirut, Al-A'lami Publications Foundation, 2nd., 1390 AH.
  • Kashani, Fathullah, Tafsir Manhaj al-Sadiqin fi Alzam al-Mukhaleefin. Tehran, Muhammad Hasan Elmi Library, 1336 AH.
  • Modarresi, Mohammad Taqi, Tafsiru Hidayat, Mashhad, Astan Quds Razavi, Mu'assasar Nazarin Musulunci, 1377H.
  • Motahhari, Morteza, Majmu'eh Asar. Qom, Sadra Publications, 7th, 1389 AH.
  • Maybadi, Rashid al-Din, Kashf al-Asrar wa-Uddat al-Abrar, bisa tafsirin Khawaja Abdullah Ansari, Tehran, Amir Kabir Publications, 1371 AH.
  • Izutsu, Toshihiko, Mafahim Akhlaki dini dar Qur'an", wanda Fereydoun Badre-e Ay, Tehran, Farzan-e Ruz, ya fassara, 1394H.
  • Khoshdel Mofrad, Hossein, Barsi Hauzeh Maanayi Amalil Salihi dar Qur'an Jaridar Ilmi da Ilmi, Na 4, Kaka 1388 Hijira.
  • Qarati, Mohsen, "Tafsir al-Nur," Beirut, Dar al-Mu'arikh al-Arabi, 1st ed., 1435 AH/2014 AD.
  • Misbah Yazdi, Mohammad Taqi, "Rastegaran," wanda Mohammad Mahdi Naderi Qomi ya rubuta kuma ya rubuta, Kum, Kum, Buga Cibiyar Ilimi da Ilimin halin dan Adam ta Imam Khomeini, n.d.
  • Makarim Shirazi, Naser, Akhlaw Islami Fi Nahj al-Balagha (Khudubatul Mauttaqeen)," Akbar Khadim al-Dhakirin, Qom, Nesle-e Javan, 1385H. *Makarim Shirazi, Nasser, "Al-Amsal Fi Tafsiril Kitabillail MNunazzal, Qum, Mazhabar Imam Ali (A.S), 1st ed, 1426H.
  • Makarim Shirazi, Nasser, Nafhatul Al-Qur'ani, Qum, Mazhabar Imam Ali bn Abi Talib (a.s), 1st ed, 1426H.
  • Montazeri, Hossein Ali, Al-Islam dinil Fitra," Qom, Arghavan Danish, 1429H.