Jaharu

Daga wikishia
Wannan labarin labari ne mai bayyanawa game da ra'ayi na fikihu kuma ba zai iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. Koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini
Risala Ilmiyya

Jaharu (Larabci: الجهر) ko Bayyanar da Karatun Sallah, bisa ra’ayin Mashhur ɗaga murya a lokacin karatun Fatiha da sura wajibi ne kan Masu sallah cikin sallolin Asubahi da raka’o’i biyu na farkon sallolin Magariba da Isha, bayyanar da karatun cikin babukan sallah da hajji da diyya yana da hukunce-hukunce da suka kebance shi, wasu jama’a daga Malaman fiƙihu suna ganin ma’auni cikin bayyana karatu shi ne bayyanuwar gundarin sauti, sannan ayanna shi yana komawa ga mutane, bayyanar da karatu a wurare misalin sallar ayoyi, sallar Juma'a, sallolin Idi guda biyu, sallar roƙon ruwa, Alƙunut da talbiyar maza duka malamai suna ganin mustahabbbi ne bayyana da karatu a cikinsu, a ra’ayin mashhur ɗin Malaman fiƙihu cikin sauran wurare da ake zikiri da tasbihi bayyanar da sauti makruhi ne kan Mamu, na’am cikin tasbihatul arba’a wajibi a yi karatu a ɓoye. Duk wanda ya jiwa wani ciwo ta kai haddin da sakamakon wannan ciwo ba zai iya bayyanar da karatu ba wajibi ne ya biya shi cikakkiyar diyya.

Sanin Mafhumi

Bayyanar da karatu kishiyar ɓoye karatu ne wanda yake n ufi ɗaga murya da bayyana sauti [1] wasu jama’a daga Malaman fiƙihu suna ganin ma’aunin bayyanar da karatu shi ne bayyanuwar gundarin sauti, [2] kuma shi zayyane gundarin sauti yana komawa ga mutane, [3] a cewar Malaman fiƙihu cikin kiyaye bayyana karatu bai kamata sauti ya ƙetara haddin tsakatsaki ba ya zama misalin ihu da kururuwa, [4] wannan maudu’i ya zo cikin ɓangaren bahasin Sallah, Hajji, [5] Diyya, [6] Isɗilahin Jaharu (Bayyanar da murya)a cikin ilimin Tajweed kuma ana amfani da kalmar Jaharu wajen kame shakar numfashi da sakinsa kwatsam, yayin furta wasu haruffa, [7]haruffa 18 daga haruffa 28 a harshen Larabci haruffan da suka kasance kan wannan siffa ana kiransu da sunan (Huruful Mahajura) kishiyar (Huruful Mahamusa) waɗanda suke ishara kan sauran haruffan guda goma da suka rage. [8]

Hukunce-hukuncen Jaharu

Malaman fiƙihun Shi’a sun yi bayanin wuraren wajabci yin Jaharu da na Mustahabbi da Makruhi. Wuraren da ake Jaharu (bayyana murya) sun kasance kamar haka: Kan ra’ayin Mashhur Jaharu a cikin karanta fatiha da sura idan mai sallah ya kasance Namiji wajibi ne yin jaharu a lokacin sallolin Asubashi da raka’o’i biyu na farkon magariba da Isha, [9] ance an yi ijma’i kan wajabcin bayyanar bismilla cikin sallolin Asuba Magariba da Isha da juma’a, da kuma kan mustahabancin yin haka a sallolin da ake ɓoye karatu, [10] a ra’ayin Malaman fiƙihu idan mai sallah cikin ganganci yaƙi kiyaye wurin da wajibi a ɓoye karatu ko bayyana shi to sallarsa ta ɓaci, amma idan ya zamana cikin mantuwa ko rashin sani hakan ta kasance to sallarsa ta inganta. [11] Idan wani ya cutar da wani zuwa haddin da wanda ya cutar ba zai iya bayyana karatun sallah ba a inda bayyana shi ya zama wajibi, to wajibi ya biya shi cikakkiyar diyya. [12]

Wurare da bayyanar da karatu yake kasancewa mustahabbi da mubahi. Jaharu bayyanar da karatu mustahabbi ne a wuraren da za su zo a ƙasa Sallar Ayoyi [13] Sallar Juma'a [14] Karatun Fatiha a sallar azahar ta ranar Juma’a ga maza [15] Sallar Idi (Eid al-Fitr da Eid al-Adha) [16] Sallar neman ruwan sama. [17] Sallar mustahabbi ta dare. [18] Ambaton ƙunut bisa Mashhur. [19]

Bismilla cikin wuraren da wajibi ne a ɓoye karatu hatta tare da zaɓar karanta fatiha maimakon tasbihatul arba’a. [20] kabbarar haramar sallar jana’iza wajibi ne kan limami ya bayyanar da karatu. [21] Kabbarar haramar kan limamin sallar jam’i. [22] Cikin talbiya wajibi ce kan maza. [23] Haka kuma halal ne bayyanar da ita wurare da za su zo a ƙasa, kuma mai sallah zai iya karatun a bayyane ko a ɓoye: Karatun fatiha da sura cikin sallolin Asubahi, Magariba da Isha idan mai sallaha mace ce idan ya zama wani wanda muharraminta ba zai ji muryarta tana karatu ba. [24] Zikiri da suke sallah banda Fatiha da sura da tasbihatul araba’a. [25] Sallar ɗawafi. [26] Jaharu (Bayyana murya) na Makruhi Mashhur daga Malaman fiƙihu bayyanar da murya cikin zikirin cikin sallah banda fatiha da sura da tasbihatul arba’a yana zama makruhi ga mamu mai bin liman sallah. [27]

Bayanin kula

  1. Mu'assaseh Da'iratul Almarif Fikh Islami, Farhanga Fikh Farsi, 1426 AH, juzu'i na 1, shafi na 113; Daga,Luggatnameh Dehkhoda, ƙarƙashin kalmar
  2. Misali, duba: Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha (Mohashi), 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 510.
  3. M26; Khomeini, Tahrir al-Wasila, Dar al-Alam, juzu'i na 1, shafi na 166, M11.
  4. خویی، موسوعة الإمام الخوئی، ۱۴۱۸ق، ج‌۱۴، ص۴۰۲<a class="eɗternal teɗt" href="https://www.sistani.org/persian/ƙa/0873/">«جهر و اخفات در نماز»</a>پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله سیستانی.
  5. Duba Mu'assaseh Da'iratul Almarif Fikh Islami, Farhnag Fiƙh Farsi, 1426H, juzu'i na 1, shafi na 113
  6. Tabatabaei Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha (Mohashi), 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 511.
  7. Alami, Fajuheshi dar Ilmi Tajweed, 2013, shafi na 137.
  8. Alami, Fajuheshi dar Ilmi Tajweed, 2013, shafi na 137.
  9. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 9, shafi na 364-365; Khumaini, tauzihul Al-Masa'il (Mohashi), 1424H, juzu'i na 1, shafi na 549.
  10. Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1407H, Mujalladi na 1, shafi na 331-332; Mohammadi Rishahri, Daaneshnameh ƙuran wa Hadith, 1391, juzu'i na 13, shafi na 308.
  11. Khomeini, tauzihul Almasa'il (Mohashi), 1424 AH, Juzu'i na 1, shafi 550, 1995
  12. Khomeini, Tahrir al-Wasila, Darul Alam, juzu'i na 2, shafi na 593.
  13. Najafi, Jawairul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 11, shafi na 457.
  14. Hakim, Mustamsak Al-urwa, 1416 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 203.
  15. Khumaini, Tahrir Al-Wasila, Cibiyar Gyara da Buga Ayyukan Imam Khumaini (RA), Mujalladi na 1, shafi na 158
  16. Tabataba'i Yazdi, Al-urwa Al-Wuthgha (Mohashi), 1419 AH, juzu'i na 3, shafi na 397.
  17. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 152.
  18. Naraghi, Mustanad Al-Shia, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 185.
  19. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 373.
  20. Kirki, Jame Al-Maƙased, 1414 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 267.
  21. Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 99.
  22. Mirzai ƙommi, Manahij Al-Ahkam, 1420 AH, shafi na 496.
  23. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha(Mohshi), 1419 AH, juzu'i na 4, shafi na 668.
  24. Imam Khumaini,Tauzihul Al-Masa'il (Mohashi), 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 549, 994 Miladiyya.
  25. <a class="eɗternal teɗt" href="https://makarem.ir/main.aspɗ?typeinfo=21&amp;lid=0&amp;catid=45579&amp;mid=276287">«مخیر بودن نسبت به جهر و اخفات در اذکار»</a>پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله مکارم شیرازی.
  26. Fazel Moƙdad, Kenz al-Irfan, 1425 AH, juzu'i na 1, shafi na 130
  27. Mirzai ƙomi, Ghanaim Al-Alayam, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi.538; Araki, Al-Masa'il Alwadhiha, juzu'i na 1, shafi na 257.

Nassoshi

  • Araki, Muhammad Ali, Al-Masal Al-Wadhiha, ƙum, ofishin yada farfagandar Musulunci na Seminary ƙum, bugu na farko, 1414H.* «جهر و اخفات در نماز»، پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله سیستانی، تاریخ بازدید: ۷ مهر ۱۴۰۲ش.
  • Hakim, Seyyed Mohsen, Mustamsak Al-Urwa Al-Wuthghati, ƙom, Dar Al-Tafsir Institute, 1416 AH.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir Al-Wasila, ƙom, Dar al-Alam, bugu na farko, beta.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, tauzihul Almasa'il (Mohashi), bincike: Sayyid Mohammad Hossein Bani Hashemi Khomeini, Ofishin Daba'ar Musulunci, bugu na 8, 1424H.
  • Khoi, Sayyid Abul ƙasem, Maus'atu Imam Al-Khoei, ƙum, Cibiyar Rayar da Ayyukan Imam Al-Khoei, 1418H.
  • Dehkhoda, Ali Akbar, Dehkhoda ƙamus, bincike na Mohammad Moin da Seyyed Jafar Shahidi, Tehran, Dehkhoda Dictionary Institute, 1377.
  • Tabatabai Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-urwa Al-Wuthgha (Mohashi), ƙom, Islamic Publications Office, bugun farko, 1419H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Khalaf, bincike: kungiyar marubuta, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1407H.
  • Alami, Abulfazl, Fajuheshi dar ilmi Tajweed, ƙum, Yaƙut, 1381.
  • Fazil Moƙdad, Moƙdad bin Abdullah, Kanz al-Irfan Fiƙhu al-ƙur'an, ƙum, Mortazaɓi Publications, bugu na farko, 1425H.
  • Karaki, Ali bin Hossein, Jami Al-Maƙasad fi Sharh al-ƙwa'id, ƙum, Cibiyar Al-Baiti, 1414H.
  • Mohammadi Rishahri, Muhammad, Daneshnameh Alƙur'an wa Hadis, ƙum, Dar Al Hadith Cibiyar Kimiyya da Al'adu, 1391.
  • «مخیر بودن نسبت به جهر و اخفات در اذکار»، پایگاه اطلاع‌رسانی دفتر آیت الله مکارم شیرازی، تاریخ بازدید: ۱۰ مهر ۱۴۰۲ش.
  • Mirzai ƙomi, Abu al-ƙasim bin Muhammad Hasan Gilani, Ghanaim al-Ayam, ƙum, ofishin yada farfagandar Musulunci na Seminary na ƙum, bugu na farko, 1417H.
  • Mirzai ƙomi, Abu al-ƙasim bin Muhammad Hasan Gilani, Manahij Al-Ahkam fi halal ɓa haram al'amurran, ƙum, Islamic Publications Office, bugun farko, 1420 AH.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Jawaher Al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas ƙuchani da Ali Akhundi suka yi bincike a Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1404H.
  • Naraghi, Ahmed bin Mohammad Mahdi, Mustanad al-Shi'a fi Ahkam Al-Sharia, ƙom, Al-Al-Bayt Institute, bugu na farko, 1415 AH.
  • Cibiyar Ilimin Fikihu ta Musulunci, al'adun fikihu a cikin addinin Ahlul-Baiti, Cibiyar Ilimin Fikihu ta Musulunci, 1426H.