Sallar Ɗawafi
Sallar ɗawafi (Larabci: صلاة الطواف) tana daga cikin wajibai cikin ayyukan Hajji da Umara, wannan sallah ta kasance raka’a biyu kamar dai misalin sallar Asubahi, ana yin wannan sallah bayan kammala ɗawafi a bayan Muƙam Ibrahim, wannan sallah ba ta da wani bambanci da sallar ɗawaful Nisa’i sai a cikin niyya,.
Taƙaitaccen Tarihi
Sanya Muƙam Ibrahim matsayi Alƙilba ya kasance yana da dogon tarihi tun zamanin Annabi Ibrahim da Isma’il har zuwa zamanin Annabi (S.A.W) [1] Muslunci ma ya kira yi Musulmai da yin sallah a wannan wuri. [2]
Yanda Ake yin Sallar
Bayan kammala ɗawafin wajibi sai ayi sallah raka’a biyu kamar dai misalin sallar Asubahi ba wajibi ba ne Mazaje su ɗaga sautinsu cikin karatun Fatiha da Sura. ƙudurce niyyar wannan sallah tana da alaƙa ta kai tsaye da ɗawafi: bayan ɗawafin ziyara sai a ƙudurce niyyar yin sallar ɗawafin ziyara, sannan bayan kammala ɗawaful Nisa’i sai a ƙudurce yin sallar ɗawaful Nisa’i ayi sallah raka’a biyu kamar dai misalin sallar Asubahi, kada a samu jinkiri tsakanin ɗawafin da sallarsa. [3]
Wurin Da Ake Sallah
Wajibi a yi sallar ɗawafin wajibi a bayan Muƙam Ibrahim kusa da shi don kada a takurawa Masu ɗawafi. [4] Dangane da waɗanda suke gudanar da ɗawafinsu a bene hawa na biyu sakamakon wani uzuri da suke da shi, amma kuma za su iya saukowa su yi sallah cikin Harami bayan Muƙam Ibrahim haƙiƙa Malamai suna da saɓanin fatawa kan wannan batu. [5] Sallar ɗawafin mustahabbi za a iya yinta a kowanne wuri cikin Masallacin Harami. [6]
Bayanin kula
Nassoshi
- Alƙur'an Alkareem.
- Mahmoudi, Mohammad Reza,Manasik Hajji Mutabik fatawa Imam Khumaini wa Maraji taklidi Izam, Tehran, Cibiyar Binciken Hajji na Jagoran Mashaar, bugu na 4, 2007.
- طبرسی، الفضل بن حسن، مجمع البیان، بیروت، دار احیاء التراث العربی، ۱۳۷۹ق.
- Jawaheri, Muhammad, Alwaidihu fi Sharh Al-Uruwa Al-Wuthƙa, ƙom, al-Arif don wallafe-wallafe, 1436 AH.