Muwalat

Daga wikishia
Wannan wani rubutu ne siffatau game da ra'ayi na fikihu, ba za a iya dogara da shi ba kan ayyukan addini. Domin ayyukan addini a koma zuwa ga wasu madogaran.
Risalar Fikihu

Muwalat, (Larabci: الموالاة ) rashin jinkirtawa tsakannin sasannin wani aiki. Kiyaye muwalat a cikin alwala da sallah yana daga cikin sharuɗɗan ingancinsu, amma a wanka ba wajibi bane kiyaye muwalat, ba'arin malaman fiƙihu na shi'a suna ganin larurar kiyaye muwalat cikin sasannin sigar shari'a cikin uƙud (Ijab da ƙabul). Ma'aunin tantance muwalat yana hannun mutane.

Sanin Ma'anar Kalma Muwalat tana nufin kawo abubuwa guda biyu ɗaya bayan ɗaya.[1] cikin isɗilahin fiƙihu, ana kiran muwalat da kawo sasannin ibada ɗaya bayan ɗaya ba tare da jinkirtawa ba a tsakaninsu.[2] malamai sun sallama tantance muwalat zuwa hannun mutane.[3]

Wuraren Da Muwalat Ya Wajaba

Kiyaye muwalat yana cikin sharuɗɗan ingancin ba'arin ibada, daga jumlarsu akwai:

  • Sallah: sasannin sallah misalin karatu, ruku'u da sujjada wajibi ne a kawo ɗaya bayan ɗaya ba tare da jinkirtawa a tsakaninsu ba. Rashin kiyaye muwalat ta yadda a fahimtar mutane za a iya kiransa yana halin yin sallah ba, hakan yana ɓata sallah.[4] na'am tsawaita ruku'u da sujjada ko kuma karanta surori masu tsayi baya cutar da muwalat.[5]
  • Alwala: yayin alwala bai kamata a samu jinkiri tsakanin wanke gaɓɓai da shafa ba, da yanayin yayin shafar wata gaɓa ya zama danshin ruwan da aka wanke gaɓar da ta gabata har an bari ya bushe.[6]
  • Kiran sallah da iƙama: a bisa fatawar malaman fiƙihu na shi'a daga cikin sharuɗɗan ingancin kiran sallah da iƙama wajibi ne a kiyaye muwalat cikin sassan kiran sallah da iƙama.[7]
  • uƙud shar'i: bisa fatawar ba'arin malaman fiƙihu wajibi ne kiyaye muwalat tsakanin sassan uƙud shar'i. Misalin saye da sayarwa da aure waɗanda suka kasance tare da jefa igiya da karɓa da ake ƙulla su bisa yarda dukkanin ɓangarori biyu.[8]

Mustahabbancin Muwalat A Cikin Wanka

A cewar Faizul Kashani bisa fatawar malaman fiƙihu na imamiyya babu wajabcin kiyaye muwalat a cikin wanka;[9] duk da cewa kiyayewa ɗin mustahabbi ne.[10]

Bayanin kula

  1. Ibn Manzur, Lisan al-Arab, 1414 BC, juzu'i na 15, shafi na 412 (Dhahil Wajah Wali).
  2. Basmaji, Mujam Mustalahat Alfaz Al-Fiqh al-Islami, 2009, shafi na 556.
  3. Meshkini, Mustalahat Al-Fiqhi, 1428H, shafi na 518.
  4. Kashif Al-Ghita, su'al wa jawab, Kashif Al-Ghita Foundation, shafi na 76; Beni Hashemi Khomeini, Tauzihul Al-masa'il, 1383 AH, juzu'i na 1, shafi na 1114.
  5. Beni Hashemi Khomeini,ُ, tauzihul Al-masa'il (Masa'il), 1383 AH, juzu'i na 1, shafi na 603, 1116 AD.
  6. Beni Hashemi Khomeini,ُ, tauzihul Al-masa'il (Masa'il), 1383 AH, juzu'i na 1, shafi na 173, 283 da 284.
  7. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, Islamic Publishing Foundation, juzu'i na 2, shafi na 425.
  8. شیخ انصاری، کتاب المکاسب، ۱۴۱۵ق، ج۳، ص۱۵۷-۱۶۱.
  9. Fayd Kashani, Mu’tasim al-Shi’a, 1429 AH, juzu’i na 1, shafi 423.
  10. Fayd Kashani, Mu’tasim al-Shi’a, 1429 AH, juzu’i na 1, shafi 423.

Nassoshi

  • Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hasan, Tauzihul Al-Masa'il maraji, Tehran, ofishin wallafe-wallafen Musulunci mai alaka da kungiyar malamai ta Kum Seminary Society, 1383.
  • Basmaji, Sayer, Mujam Mustalahat Fiqh, Damascus, 2009.
  • Faiz Kashani, Mohammad Mohsen bin Shah Mortaza, Moatasim al-Shia fi Akhmat al-Sharia, Tehran, Shahid Motahari High School, 1429 AH.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Bin Makram, Harshen Larabawa, Ahmad Fars, Beirut, Darul Fikr Lal-Taba'ah, 1414H.
  • Kashif al-Ghita, Mohammad Hossein bin Ali, tSu'al wa Jawab , Kashif al-Ghita Institute, Beta.
  • Meshkini, Mirza Ali, Tafsirin Al-Fiqh, Kum, Al-Hadi, 1428H.
  • Sheikh Ansari, Morteza bin Mohammad Amin, Kitab al-Makasab wa al-Bai wa al-Khiyarat, Qum, Majalisar Dinkin Duniya mai karrama Sheikh Azam Ansari, 1415H.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-urwa Al-Wuthagha (Mohshi), Qom, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1419 AH.
  • Tabatabai Hakim, Seyyed Mohsen, Mastamsk al-Arwa, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi.